Showing 21001 words to 24000 words out of 52544 words
Chapter 8 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE BY Jidda s Mapi.txt
laifin, yana fad'an haka yawuce d'akin Sabir, Sabir yana kwance yaga Bilal, Aa yaya Bilal Kaine?, eh wallahi Sabir nine ya kake? Lafiya lau Yaya, Amm Sabir dama aika nakeson in baka, Pls idan kaje kasuwa ka siyo min bulala irin dogon nan, Dariya Sabir yayi, yace " yaya Dan Allah me zakayi da bulala?"
"Ina ruwanka, kaide kawai kasiyomin".
Yana fad'a yafita a d'akin.
_washe gari_
Madina ce tazo gaida Minal, tambayarta take ya Umma?
" Umma lafiyarta kalau wallahi, tace in gaisheki sosai, kuma in fad'a miki tana kewarki"
Hmm Umma kenan batasan tafita keya bako? Ai yanzu Madina da ace Umma zatazo ta d'aukeni a cikin gidan nan da nafi kowa farin ciki, Madina wannan gidan k'azamin gidane, babu tsafta a cikin ta, kowa yana cutar da d'an uwanshi, ban tab'a ga Family da basa son junarsu ba irin wannan, kiduba kigani Madina, Daddy yana cutar da Bilal, Bilal yana cutar da ni, Hafeez yana cutar da Daddy, domin Akwai wata rana danaji Hafeez yana waya da abokananshi akan su tari Daddy a hanya zai fita da kud'i yanzu, Hajiya babba tana cutar da jikarta, ta hanyar d'aurata akan turban rashin kunya, Dan Allah Madina wannan Familyn zasu samu Albarka?"
"Gaskiya Minal wannan ba Family bane, to Amma ai ke kinsan gaskiya me ze hana kifad'awa kowa gaskiyar magana ko zasu kintsa Kansu"
Aa Madina babu Wanda ze yadda dani a cikinsu, hasalima duk sun tsane ni, Sabir ne kad'ai nake samun sauk'i a wajenshi, shima yanzu Bilal yace kar in b'ata mishi k'ani, ya zanyi da rayuwata Madina? yaya zanyi? Ni wawiya ce Madina, a lokacin da sukazo tambayar Aurena da nayi bincike da duk haka bata faru ba, Amma babu komai Akwai Allah"
"Gaskiya ne Minal Akwai Allah ki rika yin Addu'o'i safe da yamma, fad'in Alhamdllh da Allahu Akhbar kada yafita a bakinki, sannan Uwa Uba kibi mijinki sahu da k'afa, koba komai Bilal ya Aureki, bai kamata yana fad'a kina fad'a ba, idan kinga ranshi ya b'aci ki bashi hakuri, karki dinga nuna ke ana cutar dake kinji k'awata?"
"Naji Madina kuma na gode, in Allah ya yadda zanyi duk yanda kikace"
"Bilal yafara tausayawa Afrah, koba komai mahaifinta ya rikeni tsakaninshi da Allah, yarinyar tana sona, sannan idan na Aureta zata canja halinta, kuma zan samu lada, na tabba ta da Abbana yana Raye yaga yanda Afrah take sona, to da babu abinda zai hana Auren nan, me ze hana in yadda da buk'atarsu ko sau d'aya ne? Da kuwa Abba na zaiji dad'i"
"Da yamma Daddy yana wajen shakatawa, Bilal yazo ya sameshi, Aa Bilal ya kake? Lafiya lau Daddy, dama wata magana nakeson muyi dakai,
Zuciyat Daddy ne tabada sauti dumm, to Allah yasa ba wata maganar yaji ba"
"Ina...ina jinka Bilal Daddy yafad'a da alamar rashin gaskiya,
" amm Daddy dama ina son in fad'a maka na yadda zan Auri Afrah".
"Da sauri Daddy yad'ago kanshi, Dan gaskata ko Bilal ne yake magana,
Zaka Auri Afrah? Bilal ka yadda har zuciyarka?"
Eh Daddy na yadda zan Aureta koba komai Afrah 'yar uwata ce, kuma da Abba na yana Raye inada tabbacin shi zai had'a Auren nan,
Kuma Daddy dama ina son fad'a maka, ni ban yadda da hatsarin motane kad'ai ya kashe iyayene da k'anwata ba, tabbas Akwai wata kullalliyaa, koma dai menene saina bincika, kuma saina d'au fansa"
"Jikin daddy ne yafara rawa, cikin in ina yafara fad'an hab...hab...haba Bilal meyasa kafiye bincike da zargine?
Bincike fa ba kyau bakaji Allah yace (wala ta jassasuu) ba, kazomin da maganar farin ciki kuma kana kokarin tuno Min da k'anina wanda yafi kowa sona!, Wanda nayi mishi laifi Amma shi yazo wajena yabani hakuri, karka kara wannan maganar Bilal kana jina? To Daddy insha Allahu bazan kara ba,
Yawwa d'an Albarka, yanzu yaushe kakeson ayi bikin naku kaida Afrah?
Daddy ni koda yaushe ma kawai ayi, to to nan da Sati biyu yayi maka?
Eh daddy yayi".
" da dare Minal tana kwance a kasa taji gud'a cikin d'aki, tashi tayi ta shiga Falo, Hajiya babba ce tace "abawa masu gani waje suyi gud'a jikata ta kusa zama Uwar gida agidan Bilal"
"Minal bata gane zancen ba, tadai sake kunne tanajin maganar, kamar Almara"
_To readers Afrah zata Auri Bilal, can you emerging yanda wannan Familyn zata k'aya?_
✔ote & comment
_Jiddah S Mapi_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 17...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
"Aure kuma, Bilal zai Auri Afrah? Bayan cin Amana ta da suke awaje baiyi musu ba harsai ya Aureta?, ya Allah wani irin rayuwa na jefa kaina? Minal kin cuci kanki, Allah yasaka miki da alkhairi, tanajin Hajiya babba tana ta habaici bata tanka mata ba tashige bedroom, idonta cike taff da hawaye"
"Bilal ne yadawo gida yaga Minal kwance akan gado tana bacci, tsaki yaja cikin ranshi yace " yarinya karama da ita sai fitina kamar babba, karasawa yayi zuwa kan gadon, yafara bubbugata ke? Tashi, a firgice Minal ta tashi jin muryanshi, tana kokarin sauka akan gadon, jikin Bilal ne yayi sanyi ganin yanda ta tsorata Dan taji muryarshi, "yaya Bilal kayi hakuri zan sauka maka, ban sani bane bacci ya d'auke ni"
Tausayi tabashi sosai, zuciyarshi ta karye, a hankali ya riko hannunta, yace "babu komai kiyi kwanciyarki zan kwanta a gefe"
Lalle yau da idonta yana gani babu abinda zai hana ta waro su da kyau ta kalli Bilal domin ta tabbatar ko shi yayi maganar, a hankali ta koma kan gadon tayi kwanciyarta tare da Jan bargon daidai wuyarta, lumshe ido Bilal yayi ganin yanda take bacci, kamar wata baby,
"Auzu billahi shine abinda yafito daga bakinshi, me kakeyi haka Bilal? Kar ka bada kanka mana, ya zaka fara tausaya mata da wuri haka? Duk laifin datayi maka? Juyawa yayi yatafi toilet, Alwala yayi yazo ya shimfid'a sallaya yayi sallah raka'a biyu tareda Addu'ar Allah ya bayyana mishi duk wani wanda yake munafurtan shi, yana idarwa yaje ya kwanta akan gadon gefen Minal, yajuya yana kallon fuskarta, Idanunta manya me d'auke da Zara zaran eye lashes, hancinta yanada tsayi sosai, sai d'an karamin bakinta, Wanda tad'an tab'ewa sabida shagwab'a, tanayi mishi yanayi da kanwarshi Nabeela, hannu yasa akan fuskarta yana shafawa, haka har bacci ya d'aukeshi"
_Asuba tagari_
"Minal ce ta bud'e idonta a hankali, ganin Bilal tayi ya rungumeta a jikinshi yana bacci, da alama kuma baccin yana mishi dad'i, a hankali ta zame jikinta daga nashi tana Jan tsaki, haka kawai zai sani a gaba ya rungume, sai ya jira Afrah idan ya Aureta ya rungume, amma dai bani ba, " ke? Me kike cewa?" Cewar Bilal da tun tashin ta shima ya farka,
"Turo baki tayi tace Nidai bance komai ba".
"kifad'a ma kiga dukan da zanyi miki, dama nasa Sabir ya siyomin bulala a kasuwa, na lura ke saida bulala"
"Ai ni ba jaka bace da za'a siya bulala don ni"
"Kiyi magana yanda zanji mana kiga dukan dazanyi miki, Amma kina magana a hankali"
"Sai ka bud'e bakinan Tinda kanada karfi, tafad'a daidai lokacin data rufe kofar toilet d'in"
Bilal shi har mamaki abun yake bashi, ace yarinya karama ta tsaya tana rainashi Amma ya kyaleta? Tsaki yaja kad'an kafin yasauka a kan gadon"
"Hajiya babba da Afrah anata rawan kai Bilal ya yadda zai Auri Afrah, waya ta d'auko takira frnds nata tana fad'a musu ta kusa Aure, Hajiya babba ce ta katse wayar tareda cewa " bafa waya yakamata kiyiba yanzu, tashi zakiyi ki dafawa masoyinki abinci da lemon Apple me sanyin dad'i, tin yanzu ki koyi yanda zaki kula dashi, ki kwace shi gaba d'aya daga wajen wancan Aljanar kina jina?"
"To Hajiya babba yanzu ma kuwa" tafad'a tana mekewa"
"Kitchen Afrah tashiga tareda d'aura tukunyar Abinci, jallof na shinkafa ta dafa, tareda yin lemon Apple, jallof d'in yaji manja da gishiri, tareda had'in gwiwar Barkono, da Uban tumatur, juyewa tayi a plate kafin ta nufi d'akin Bilal, tasan bazata sameshi ba saida Azahar, hakan yasa ta jera a dinning table, tanayi tana wak'arta na habaici, Dan taga Minal awajen, cewa take (matarshi makaho, shalugude, shima makaho, shalugude, yaransu makafi, shalugude)
Minal tana jinta Amma bata ce uffan ba, haka harta gama tayi tafiyarta, Minal bata kulata ba"
"Da Azahar Bilal ne yadawo gida, lokacin Afrah tad'au wanka dawata duguwar Riga, Wanda aka bud'e Kasan, babu laifi tayi kyau, tana ganin Bilal ta mike tareda cewa " sannu da dawowa yaya Bilal"
"Bilal kallonta yayi ta cikin glass nashi, sannan ya murtuk'e fuska yace " yawwa"
"Am yaya Bilal dama na gama maka Abinci, muje nazuba maka ko?
Bilal bayason yawan magana, sai kawai yayi gaba ya kyaleta, shiru Afrah tayi Hajiya babba ce ta lek'o tace mata " bishi mana k'atuwar banza, mara wayo"
"Zumb'ura baki Afrah tayi kafin tabi bayan Bilal, tana zuwa ta Ganshi akan dinning, dad'i taji sosai, ta karaso Inda yake tareda d'aukan plate tazuba mishi, "to yaya Bilal nawa aci Abinci lafiya"
"Bai kulata ba yafara laluben plate d'in, Afrah ganin yana Neman inda plate yake yasa Tamika mishi,
Minal tana jin duk abinda suke Amma bata damu ba sabida tasan ko ta damu babu Wanda zai kulata, Babu ruwanta da familynsu yanzu"
"Ta b'angaren Bilal kuma yayi haka ne Dan ya baiwa Minal haushi, Amma sai yaga bata ma damu ba, Abincin ya d'ebo cike da cokali yakai bakinshi, Unty gishiri ne tafara gaida bakinshi, sai kuma wani irin yaji, da kuma tsamin tumatur, shi yama rasa yanda zai fara tufar da abincin tsabar gishiri, rikewa yayi a bakinshi, yakasa ci yakasa tufarwa, Afrah ce tace " yaya ci Abincinka mana Kasan ban tab'a shiga kitchen ba sai yau, kuma Dan kai nayi gajiyar girki please kaci sosai"
"Saurin tufarwa yayi yace, kin d'ana Abin cin kuwa? Girgiza kai Afrah tayi Alamar Aa, yace okay "gashi ki cinye ko kuma in fasa Auren ki"
Haba yaya me yayi zafi dazaka fasa Aurena? Kaga indai Akan Abinci ne miko min in ciye,
'Daukan plate na Abincin tayi ta kara a flask, kafin tad'au cokali tasa abakinta, taji wani irin gishiri, da sauri ta tufar tareda d'auko kofin ruwa ta kuskure bakinta, Bilal ne yace saita cinye abincin tas kafin tafita, hakan kuwa akayi da kyar da kuma da gumi har ta cinye Abincin,. Tana gamawa tafara shek'a Amai, tsakaninta da Allah"
"Minal sai dariya kawai takeyi"
"Bilal ko kulata baiyi ba yatashi ya tafi, Hajiya babba ce tashigo, tarike Afrah suka tafi cikin gida, meya faru Afrah? Keda kika kaiwa yayanki Abinci saiki fara shek'a Amai?"
Hajiya babba wallahi yaya Bilal mugune baya sona, Dan kawai gishiri yayi yawa a abinci saiya ce saina cinye"
"Kiyi hakuri Afrah, duk abinda yayi miki saikin rama indai ina gidan nan, haka ta lallab'a Afrah har tayi shiru"
"Da yammacin ranar Bilal ne zaune a falo yana duba wasu takaddun company, Minal ce tazo cikin falon, tana kiran yaya Bilal? Yaya Bilal?
Bilal yayi mamakin yanda take kiranshi, "ke lafiya?"
"Yawwa tafad'a tareda zama a gefenshi, tace " yaya dama wata magana nakeson muyi da kai"
Ummm hmm ina jinki, shine Abinda yafad'a"
"Yaya dama inason in rokeka ne, Dan Allah Dan Annabi, Dan darajar iyayenka, ka taimaka ka kaini India a gyara min idona, wallahi ko baiwarka kace in zama, wallahi zanyi"
"Tabashi tausayi sosai yanda take rokanshi, saiya tuna da kanwarshi Nabeelah idan tana rokanshi Abu saita had'ashi da Allah da Annabi, to Amma yasan idan wannan yarinyar tafara ganin duniya to ya Shiga uku da raini, koda shike zeyi matane sabida Allah badan halinta ba"
"Sai nayi shawara, shine abinda yafad'a"
"Yaya Dan Allah kayi shawara me kyau, ina son ganin mahaifiyata, ita kad'ai nake da Aduniya, banida kowa Sai ita"
"Ke nace miki Sai nayi shawara koh?"
"To yaya nagode"
"Shi mamaki ma take bashi yanda ta sunkuyar da kanta tana mishi magana.ba raini ba tsiwa"
"Minal kuma a zuciyarta tace Allah yasa ya yadda, sarkin girman kai da d'agawa"
✔ote & comment
_Jiddah S Mapi_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 18...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
"Bilal ne ya yanke shawarar sai bayan Aurensu da Afrah kafin yakaita India"
"Minal datayi sallah Addu'a kawai take Allah yasa ya yadda, da dare ta kara rok'anshi tace " yaya Bilal Dan Allah ka taimakamin"
Bilal yace "naji Amma sai bayan Aurena da Afrah, idan zaki iya jira idan kuma bazaki iya ba sai ki zauna a haka"
Minal tace "Aa yaya Bilal wallahi zan iya hakura"
Yece "dayafi miki"
_washe gari_
Madina ce tazo gidan, ta fad'awa Minal Umma batada lafiya.
"Minal dajin haka yasa ta shirya wai su tafi "
Madina tace "Aa Minal kibari idan Mijinki ya dawo ki tambayeshi idan ya baki izini sai gobe kije ki duba ta"
Minal tace "Haba Madina sai kace bakisan matsayin Umma awajena ba? Umma fa mahaifiyata ce idan banje na dubata ba waye zai dubata? Sabida Bilal bazanki zuwa duba mahaifiyata ba, kinga idan bazaki kaini ba, to bari na tafi da kaina"
Madina tace "Aa Minal kiyi hakuri, muje dama ni ina guje miki fushin mijinki ne, domin yana kawo fushin ubangiji"
Minal tace "okay nasan bakida niyan tafiya, kinga sai Anjima"
"Da sauri Madina ta riko ta tace Aa wane ni? kinga muje"
"Tafiya sukayi zuwa gidan Umma"
Minal tana Shiga tafara kiran Umma!!!
Umma ce taji muryanta sai ta tashi cikin murna ta rungume Minal.
Tace "yata sannu da zuwa"
Minal hawaye ta share jin muryan Umma tana magana a hankali,
Tace "yawwa Umma ya jikin naki?"
"Da sauki Minal"
'Daki suka shiga Umma ta d'ebo mata ruwa tasha kafin ta tambayeta
"Minal ya naga kin rame? Me yake daminki?"
Minal tarasa me zata fad'awa Umma sai kawai tace "Am Umma nayi rashin lafiya ne acikin kwanakin nan ciwon ciki ne ya dameni, har saida aka kaini Asibiti"
"Asibiti kuma Minal? To meyasa shi mijin naki bai fad'a min ba?"
"Mijina kuma Umma?"
Umma tace "Eh kullum ai yana zuwa nan muyita hira har dare kafin ya tafi"
"Zuciyar Minal ne yabada sauti Dummm, "ta yaya Bilal zaizo gidan nan? Anya ba wani bane yake yiwa Umma karya da sunan Mijina?"
Umma tace "tunanin me kike yi Minal? Ko akwai Matsala ne? "
Minal tace "Aa Umma bawani tunani kawai de bai tab'a fad'amin yana zuwa nan ba"
"To ai ba dole bane ya fad'a miki sabida shi mutumin kirki ne yanada mutunci"
Minal tace "to Umma saidai mu godewa Allah"
Haka suka karasa firansu, Minal ta koma gida da yamma.
"Ta b'angaren Bilal kuma yana zaune a falo yana tunanin ta yaya za'ace Hafeez ya yiwa matarshi jagora? Yakaita gidansu? Da karfi ya furta "dawata akasa".
"Minal ce tafi sallama"
Bilal yace "ke? Ban hanaki Alak'a da Hafeez ba?"
A hankali tace "Hafeez kuma? Me yayi?"
"Okay tambayata ma kike?
Wato ke iskanci a jininki yake, Hafeez ne yayi miki jagora, Kun fita tunda safe shine don bakida kunya sai yanzu zaki shigo min d'aki?"
Minal tace "nifa ban gane me kake cewa ba yaya Bilal, ka fahimtar dani"
"Okay to bari in fahimtar dake, Belt ya ciro yafara zabga mata, kota ina, saida yaga tayi lilis kafin ya tsallakata tareda cewa " kuma nafasa Fitar dake kasar india, saidai kije shi Hafeez d'in ya kaiki"
"Hajiya babba da Afrah Wanda suka lab'e a bakin kofa ne sukayi saurin Baron wajen, Dad'i Afrah takeji, don Bilal ya daki Minal"
Hajiya babba tace "Dama na fad'a miki saikin cire tsoro kafin kiyi nasara, yanzu badan munyi wannan plan d'in ba ai bazai dake ta ba"
Afrah tace "wallahi Hajiya babba baki tab'a birgeni irin na yau ba, nagode miki sosai kakata kuma takwarata"
Hajiya babba tace "ba godiya yakamata kiyimin ba, yanzu zamu fara kirkiro wata munafinci, Wanda zai daina yadda da ita kwatakwata, yaji ya tsaneta".
" to hajiya ke zaki fara kawo shawara"
"Nikuma?" cewar Hajiya babba.
"Ke wai Afrah yaushe zakiyi wayo, bazaki koyi yin Abu da kanki ba? Saidai ni in yi?". To bari kiji daga yau idan baki kirkiro Wani munafincin da za'ayi ba wallahi bazan kara sa bakina a lamarinki ba".
" haba Hajiya gobe ma zan nemo"
"Dayafi miki kam".
"Minal taci kuka harta gode Allah, ita ba dukan ne ya dameta ba zarginta dayake ne yake bata haushe, wannan ai zargine"
Wanka tayi, ko mai takasa shafawa a jikinta tsabar zafi, haka ta daure ta kwanta a kasa, cikin sanyin tiles, ta rufe jikinta da Hijabinta tana tunani, har bacci b'arawo ya saceta"
"Bilal ne yashigo d'akin ya ganta kwance a k'asa, ta takure waje d'aya,
Kawar da kanshi yayi gefe yanajin kamar yayi ball da ita ko zaije sauki a ranshi"
"A zahiri mutuniyar kirki, Amma a bad'ini tafi kowa iskanci, maimakon taji da wannan nakasar Amma tana kara sab'awa Allah chewwww"
Tsallakata yayi yaje ya kwanta yaja bargo.
"Minal ce tafarka cikin dare da zazzab'i me zafi, jikinta har rawan sanyi yake, sanyin tiles d'in ne ya dameta har yakawo mata zazzab'i, tashi tayi cikin rawar sanyi tahau gadon tareda janye bargon Bilal ta lullub'a jikinta dashi"
_Asuba tagari_
Bilal ne yafara bud'e idonshi jin sanyi yayi mishi yawa, sai ganin Minal yayi ta kwanta a kan gadon tana bacci jikinta lullub'e da bargonshi, "ke? Ke? Tashi Dan Ubanki, Ubanki ne yasiya gadon? Shiru yaji babu amsa, ke ba tambayarki nake ba? Shiru har yanzu ba Amsa, bubbugata yayi, yaji batayi magana ba, zuwa yanzu yad'an fara tsorata, hannunta ya d'aga yaga yafad'i, a tsorace yafara bubbugata yana kiran sunanta, Minal!!! Minal!!! Ke? Ke?, har yanzu shiru"
Fita yayi da sauri yaje d'akin Daddy,
Sallama yayi a rud'e.
Yashiga yace "Daddy Minal ta mutu,"
what? Minal kuma ta mutu? Wani irin magana kake
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
By
Jiddah S Mapi
Page 19...
*___________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
"Kayi hauka ne? Meya kasheta?"
Bilal yace "Daddy ni na kasheta, dukanta nayi, da hannuna"
Daddy yace "muje d'akin naku"
"Dasauri suka nufi d'akin Bilal, wurin shiga d'akin ne Bilal tsabar rikicewa, yayi tuntub'e da k'ofa, saura kad'an ya fad'i,
Daddy ne yayi saurin rikeshi, Bilal kabi a hankali mana, kasan ba gani kake ba, meyasa zakayi sauri? Bilal yace " ba komai muje kawai Daddy"
"Suna shiga d'akin, Daddy ya karasa inda Minal take kwance, kallo d'aya yayi mata yagane cewa doguwar suma tayi, yad'an d'aga hannunta yakuma. Sakewa, a hankali ya furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un Bilal meyasa kayi kisan kai?"
"Bilal ne ya zauna a kasa jin wani irin jiri dayake Neman kada shi, yace " Daddy tamutu ko?"
Daddy ne ya girgiza kanshi tareda cewa "Kwarai kuwa, karo na farko da aka