Showing 18001 words to 21000 words out of 52544 words

Chapter 7 - MAKAUNIYA CE BOOK COMPLETE BY Jidda s Mapi.txt

13 Oct 2025

2007

idan kaganta kamar bazata aikata ba, Lalle saita fad'amin meye a tsakaninsu? Kuma yaushe tafara karuwanci? (Niko nace ina ruwanka malam Bilal tinda ba sonta kake ba)"

Minal zuciyarta har bugawa yake tsabar yanda maganar Hafeez ya tsaya mata arai, sandarta tad'auko tafara neman inda flower yake, cikin ikon Allah tasamu tabawa flower ruwa da taimakon mai gadi, godiya tayi mishi takoma cikin gidan d'akin Bilal tanufa danufin ta canja kaya domin na jikinta ya jik'e"

"Bilal ne tsaye cikin d'aki sai kai kawo yake yarasa meya hanashi nutsuwa, Sallama Minal tayi
Cikin tsawa yace "ke daga ina kike?"
Ta tsorata da yanayin maganar A hankali tace
"Yaya Bilal kaifa kasani aiki awaje kuma kake tambayana daga ina nake"
Okay wato zaki fake da aikin Dana saki ko? Kinje kina karuwancinki kicemin Aiki kike.
Niba wannan bama tin yaushe kuka fara harka da Hafeez? Idan kikayimin karya zan cire idonki d'aya yau"

Wallahi yaya Bilal yauma tsautsayi ne yahad'ani dashi, babu abinda yake tsakanina dashi..
Karasowa wajenta yayi "zaki fad'amin gaskiya ko kuma"

Jada baya tafara don tayi matuk'ar tsorata, "Okay guduma zakiyi ko?
Kinsan baki da gaskiya ai dole ki gudu, zaki fad'amin yaushe kika fara karuwanci ko sai nayi abinda nace"

"Wallahi yaya Bilal niba karuwa bace d'an uwanka shine yake nemana da iskanci, kuma ban yadda ba"

"Zaki fad'i gaskiya ne idan jikinki yagaya miki, cire wannan rigan me kamada tolotolon" yaya Bilal me zakamin wallahi niba 'yar iska bace ka yadda dani.

"Zan yadda dakene idan kika fad'amin gaskiya, d'iba da gudu tayi tanason tabar wajen, cikin rashin sa'a taci karo da k'ofar toilet, kanta ne yabugu sosai, baya baya tayi zata fad'i Bilal yana kallonta harta kai kasa, ko motsi bata karayi ba,
Tsallakata yayi yaje wajen frij yabud'e, Goran faro me sanyi ya d'auko, yana daga tsaye yafara kwarara mata ruwa, afirgice ta farfad'o daga suman datayi, wallahi yaya Bilal niba karuwa bace.....hannunshi yasa a bakinshi yace shiiii karki kara bud'e bakinki anan,
Tashi yayi ya cire belt na wandonshi sannan yace " zaki fad'i gaskiya ko kuma?"

"Wallahi yaya Bilal gaskiya nake fad'a maka"
Belt d'in yad'auko yafara watsa mata kota ina ajikinta, ihu takeyi tsakaninta da Allah.

"Afrah wacce suke zaune a falo itada Hajiya babba tafara jin ihu a d'akin Bilal, da sauri ta mike tana cewa " hajiya ihu fa nakeji a d'akin yaya Bilal "
Shine me zakiyi? Cewar hajiya babba,
"Zanje naduba meyake faruwa kar wani Abu yasameshi". Amma wallahi Afrah bakida wayo, waya fad'a miki idan anji ihu a d'akin ma'aurata ana zuwa lek'awa? To kul kada ki kuskura koda watarana ki lek'a su, don dazaran kin lek'a to hawan jini ne zai kamaki,"
Wannan yaron bashida kunya ko kad'an, da ace idonshi abud'e da anyi jarababbe wallahi, cewar hajiya babba"

"Afrah jin haka yasa ta koma ta zauna tana kuka, Hajiya babba wallahi yaya Bilal yana cin Amana na agidannan wannan ai cin fuska ne, gaskiya na gaji, kawai asa Daddy yad'aura mana Aure koda bayaso, bazan jira sai wannan Makauniyar ta haihu ba"
Kiyi hakuri Afrah ta insha Allahu ke kad'ai zaki zauna da Bilal kinji?
To hajiya har yaushe?
Kawo kunnenki kiji cewar hajiya babba,
Da sauri Afrah ta matso da kunnenta, rad'a hajiya tayi mata, nan suna tafa Afrah tana jin dad'i, tace "hakan za'ay Hajiya babba ta"

"Bilal bayan ya gama lakad'awa Minal duka, yashiga toilet yayi Alwala, eye glass nashi yasa, kafin yad'au sandarshi yafita da niyan zuwa masallaci, A falo yatarar dasu Hajiya babba suna hira,
Hajiya tana ganinshi tafara habaici, oo ni Salamatu yara yanzu ba kunya ne dasu ba, ace yaro yanzu kagama tunkushe 'yar mutane har tana ihu, kuma babu kunya ka kara yawo acikin gida, wannan jarabar dame tayi kama?
Bilal bai gane maganarta ba, shidai ya fahimci taji ihun Minal, to ina ruwanta Dan na duki matata? Allah dai yashirya Matar nan" fita yayi ko kara kallonta baiyi ba, Afrah ce tace "Hajiya babba kidaina surutun nan kinga fa ko kallo baki isheshi ba" idan bai kalleni ba ai yajini ko?".

"Daddy da Hafeez ne zaune a cikin d'aki, Hafeez ne yace " Daddy nayi duk abinda kace inyi, kuma naji d'azu har duka yayi mata, yanzu hakama tana kwance a d'aki bata da lafiya"
Daddy ne yayi gyaran murya yace "yawwa my son kasan meyasa nake sonka? Sabida basirarka da iya munafinci, na tabbata yanzu zargi ze shiga tsakaninsu, shi zaiyi zargin tana karuwanci ita kuma zatayi zargin yana iskanci, to yanzu abinda za'ayi ni zanje in kaita asibiti, idan ta warke saimu cusa mata k'in Bilal azuciyarta, daganan saimu Nuna mata buk'atarmu, tayi kokari ta sato mana takaddun shi gaba d'aya, daga nan sai kuma me?
Sai akashesu gaba d'aya Daddy" dariya Daddy yayi yace "Allah yamaka Albarka my son" Ameen daddy".

"Minal tinda uwarta ta haifeta bata tab'a shan wahala irin ta yau ba, jikinta duk yayi tsami, tsanar Bilal ne yashiga zuciyarta bana wasa ba, da kyar tanemo inda sandarta take, da rarrafe ta iso band'aki, ahankali tafara Neman inda bathtub yake, ruwan zafi Dana sanyi ta bud'e, da kyar ta iya shiga cikin bathtub tayi wanka, towel ta lalubo ta d'aura ajikinta tana mejin bak'in cikin Amfani da kayanshi, sallama taji anayi a falo da sauri ta nemi hanyar fita, taje tasa hijabi kafin tanemi hanyar falo, Daddy ne yace " aa sannu Minal, meya faru naga fuskarki a kumbure bakinki kamar ya fashe?"
Shiru Minal tayi Dan dazaran tace zatayi magana to kuka ne zai kubce mata,
Kinyi shiru Nazo in gaidaku kuma saina ga jikinki a farfashe waya dakeki?
Yaya Bilal ne, tafad'a tana kuka,
Me kikayi mishi? Dazaiyi miki irin wannan dukan dako agidan yari ba'ayiwa mutum?
Banyi mishi komai ba, haba wannan ai mugunta ne shi baya duba nakasar dakike d'auke dashi ne? Wannan ai mugunta ne, kinga jeki shirya yanzu mutafi Asibiti kinji?
Minal tace "to nagode Daddy, azuciyarta tace Allah yasa ya shiryu ne ya canja hali"

"Da sauri tanemo kayanta tasa ta lalub'o sandarta tayi hanyar falo, a hankali take tafiyarta jikinta duk ba dad'i" daddy ne yaje yarike sandarta yace "ganinan muje ko?" Gyad'a kanta tayi, suka yi hanyar parking space, Hajiya babba ce tafara tafi tana salati, la'ila ha illallahu muhammadarrasulullahi sallallahu alaihi wasallam, oh ni salamatu me nake gani haka? Umaru Kaine kake yiwa wannan k'azamar yarinyar jagora yau? Allah meyasa kanunamin wannan rana? Allah da raina ka d'auka kafin yamma, tafad'a tana kuka,
Daddy ne yaje yasa Minal a mota, kafin yazo wajen Hajiya babba, yace "mama idan bakisan meyake faruwa ba kidaina saurin magana, ai nine nayi sanadiyyar dukan da Bilal yayi mata, sabida burinmu yakusan cika, ta hanyar yarinyannan zamu samu duk abinda mukeso, idan yaso daga baya sai insa asaceta ya Auri Afrah, koba hakaba?"
Da sauri hajiya babba tace "eh hakane Allah yakiyaye muku hanya, Allah yasa tasamu sauk'i oh ni salamatu dama yarinyar gata kamar karkashi a ruwa, Allah dai yasa karta mutu maka a hanya Mushiga uku"
Ameen Mama"

"Driver yakira yace kaimu general hospital, Nan sukaje general hospital akayi mata duk abinda yakamata, aka had'a mata magunguna da Allurai, kafin sukaje gida,
Bilal daya dawo tin d'azu bega Minal ba kuma hakan be dameshi ba, kwanciya yayi yakira wani a companynshi yake tambaya yaya company, ta d'ayan b'angaren akace "gaskiya yallab'ai company yana Neman b'aci, komai sai rugujewa yake, wannan managern bashida hankali, gashi Latif baya nan, bugu da kari kaima baka nan"
Bilal ne yace "karka damu komai yakusa dawowa daidai nan yakashe wayar yana tinani"

"Minal ce tayi sallama cikin d'akin, ta gaji sosai Dan haka tacire gyallen da d'an kwalinta tayi wurgi dasu, tareda sandarta, laluben inda gado yake tafara harta samu, tsalle tayi ta d'ale gadon tana cewa " wayyo Allah na nagaji" jitayi tafad'i akan Abu Amma batasan ko menene ba, tayi zaton ko garin sauri ne d'azu tabar wani Abu akan gadon, sharewa tayi kawai tayi kwanciyarta akan Abun, ahaka har baccin gajiya ya d'auketa"

"Numfashi Bilal yaja da karfi, jin tayi bacci ajikinshi, ya tattaro sauran nutsuwan daya rage mishi, ya d'agata a hankali ya kwantar da ita agefe, ji yayi jikinta da zafi sosai, hakan yasa ya kara gudun Ac, yaja mata bargo iya kanta kafin yasauka akan gadon, hannunshi yaji ta riko tana cewa "Hafeez karka tafi kafad'a mishi gaskiya, kafad'a mishi abinda yake tsakaninmu, kaji Hafeez? Karufamin Asiri karya kasheni"
Da Alama mafarki takeyi,
Da karfi Bilal ya kwace hannunshi tunawa dayayi yagansu da Hafeez ga kuma irin maganan dayake Fitowa abakinta, yarufa mata Asiri? Zargina ya tabbata kenan, Afusace ya juya ya d'auketa akan gadon yayi wurgi da ita zuwa kasa, karuwar gida,
Shine abinda yafito daga bakinshi"

"Tashi tayi afirgice tace Wayyo Allah Aljanu, ke? nine Aljani? Aa kayi hakuri yaya Bilal bada kai nakeba,
"Dawa kike idan bani ba? My nawane ad'akin?"
Wallahi ba dakai nake ba,
"Ke dalla kimin shiru kafin inci Ubanki karuwar banza kawai ballagaza"

"Yaya Bilal kadaina fad'amin karuwa niba karuwa bace"

"Nafad'a Ke Karuwace, Karuwar ma tagida, wacce take bin kanin mijinta suna lalata, mazan waje basu isheki ba saikin had'a Dana gida, kinyi Asara, dama nasan idonki yariga ya bud'e da kud'i tinda kullum kina wajen talla, barinki ba kud'i riks ne babba, nizan taimaka ina baki sabida karkizo kifara Neman Sabir yaro me hakuri"

"Ya isa!!! Yaya Bilal ya isheka haka, niba karuwa bace kaninka shine babban d'an iska, kuma dakake cewa idona ya bushe ai ban kaika bushewan ido ba, Hafeez yafad'a min kana harka da manyan 'yan mata masu kud'i, an fad'a maka ban San sirrinka bane? Dakake cemin karuwar gida, Kaine d'an iskan gida, tinda har mai aiki kayiwa FYA'DE, Hafeez yafad'amin duk wani abinda kakeyi Wanda babu kyau, sabida kaga ni Makauniya Ce, shiyasa zaka musguna min? Yaya Bilal kasani ni Makauniya Ce ba kurma ba, ganine kawai banayi Amma inajin komai, an fad'a maka nima inason makantar ne? Kuma koda inaso ai Allah ne yayini haka, ko bakasan a cikin Alkur'ani mai girma Allah ya ambaci Makafai ba? Idan kai jahili ne to bari nakoya maka"

"A cikin Alkurni, suratul bak'ara shafi na uku aya ta goma sha takwas Allah ya Ambaci makafai, inda yake cewa (Summun bukmun umyun fahum laa yarji'un)"

✔ote & comment

_Jiddah S Mapi_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 15....

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Fine! tinda kinsan kur'ani, to Aure zanyi kuma mata biyu rana d'aya, don nalura bakida kunya, wata kila idan nakawo wacce zata baki wahala zaki shiga hankalinki"

"Haba Bilal? Bakasan cewa Allah ya halatta maka ka Auri mata hud'u bane? Ko ka manta da inda yake cewa (fankihu ma d'aba lakum minannisa'i masna wa sulasa warba) Ku Auri abinda yayi muku dad'i daga cikin mata biyu ko uku ko kuma hud'u, ni Asuwa dazan ja da maganar Allah, bugu da k'ari niba sonka nake ba, danasan kai za'a Auramin dabanyi kuskuren yadda ba, Amma duk da haka kai mijina ne kanada hakki akaina, Wanda har sai ranar da Muka rabu kafin ya sauka"

"Ummm dama kinsan Al-kur'ani haka, shine kuma kike aikata zina? Ko kin manta inda Allah yake cewa (wala tukribuzzina) kada Ku kusanci zina, wannan kam kin manta ko?"
Cikin zuciyar Minal kuna yake, tarasa meyasa Bilal ya tsaneta, "me nayi maka kake min sharrin mafi munin Abu aduniya?"
Bilal fita yayi tareda bankad'o mata kofar,
"Yanzu aka fara wasan Malam Bilal, cewar Daddy daya tsaya abakin kofa yaji duk abinda sukayi"
Wucewa Bilal yayi, kamar bega kowa ba, Amma zuciyarshi yasan akwai mutum abakin kofa, b'uya yayi a inda yasan baza'a ganshi ba, tsayawa yayi yana jiran Wanda yashiga d'akin yafito, cikin ikon Allah saiga Daddy yafito daga d'akin, rud'ani Bilal yashiga, to meya kawo Daddy wajen Minal? Kuma saida nafita kafin yashigo, anya bawata akasa?
Astaghfurullah, nasan akwai wata dalilin dayasa yazo, don daddy ko a mafarki bazai cuceni ba, saidai wannan yarinya me kama da Aljanun, nasan zata iya yin komai Dan ba sona takeba"

Wayarshi ce tafara ruri, yana dubawa yaga sunan Abba yana yawo, zuciyarshi ne tayi dumm, da sauri yafurta "Abban Latif?" Mezan fad'a mishi yanzu? Nashiga Uku.
Daurewa yayi yad'auka "Hello Abba ina wuni? Bilal ba gaisuwa ne yasa nakiraka ba, kasani cewa ni Abokin mahaifinka ne tun muna yara, nasan komai nashi, nasan halinshi mutumin kirkine, tun lokacin dayake Raye ina kula da companyn shi da dama, ban cutar dashi ba sai yanzu daya mutu zan cutar dashi? Bilal kaida wannan Daddyn naka kun bani mamaki, shine abinda zaku saka mana dashi? Shikenan Ai akwai Allah, ina rokan Yashiga tsakanina daku, anjima kazo ka karb'i komai na dukiyarka dayake hannuna, kitt yakashe wayar"
Jikin Bilal yayi la'asar a fili yafurta "da wanne zanji? Da Minal datake cin Amana na, koda tunanin meya shigar da Daddy d'akina, ko kuma Abban Latif dayake so na karb'i komai nawa na wajenshi?"

"Da Afrah zakaji yaya Bilal, ka zubar da duk wata damuwa ka Aureni, nayi maka Alkawarin Ranan daka Aureni zan bankad'o maka sirrin dakake son kasani, cewar Afrah wacce hajiya babba ta aikota takira Daddy, da zuwanta taga Bilal yana lab'e itama saita lab'e"

"Juyowa Bilal yayi yana kallon Afrah, wacce tasha Riga da wando, hannun rigan an yanka dogo dogo kamar jelar shanu, Tsaki yaja yaci gaba da tafiyarshi"
Dasauri ta tari gabanshi ta tsunkuya har kasa tarike kafarshi "yaya Bilal nasan nayi maka kaifi a rayuwarka, wallahi na tuba bazan kara ba, idan kace kar in kara sa wando da gyalle wallahi bazan kara ba, nidai kawai ka Amince zaka Aureni koda baka sona, ka dubi girman Allah ka yadda da buk'ata ta, wallahi idan naganka da wannan matsiyaciyar matar taka, sai naji zuciyata kamar zata fashe tsabar kishi, bana son ka rab'e ta ko kad'an, hasalima kwana dakukeyi a d'aki d'aya shiyafi komai d'agamin hankali, yaya Bilal ka taimakawa k'anwarka, please"

"Baiyi mata magana ba kawai ya kwace kafarshi yabar wajen, baisan wani yanayi yake ciki ba, shin tsanarta yakeji ko tausayinta? Baisan meyasa yarinyar take sonshi dayawa ba, son datake yimishi yayi Over, shi yanzu ji yake kamar ya tattara kayanshi yagudu yabar garin Gombe ma gaba d'aya, yaje inda babu Wanda ya sanshi, yayi rayuwa cikin farin ciki ba irin rayuwar dayake ciki ba, wata zuciyar kuma tace " idan ka tafi wa zaiyi maka binceken Abinda yake faruwa? Kamata ace nad'au fansar Ran iyaye na Dana k'anwata kafin nabar duniyar ma baki d'ayanta"

"Hajiya babba ce ta karaso inda Afrah take kwance tana kuka, d'agota tayi tana mata matsifa, " Haba Afrah, ya zaki zubar da Ajin ki na 'ya mace ki sunkuya har kasa kina rokan namiji ya Aureki? Duk abinda kukayi ina jinku, Kinaso ki taunawa mahaifinki Asiri akan Namiji? To ki sani idan kika taunawa mahaifinki Asiri, kika Auri wannan d'an iskan yaron, kinga wannan jikin naki kamar an sawa fulawa yist? To wallahi saikin koma kamar matarshi tsabar ramewa, kai gara itama ai halittar tace haka, kuma ita idan ta rame zatayi kyau, sabida Asalinta Farace, Amma ke idan badan man bilicin ba ai da sai gyaran Allah, ko kallo bazaki ishi mutane ba, kinga ga rama ga bak'antaka saiki dawo kamar An soya kwad'o"

"Haba Hajiya babba wannan ai cin fuskata kike"
Waya fad'a miki?
Ni gaskiya nake fad'a gara ki hakura mushawo kan matsalar a hankali, tinda Allah yarufa mana Asiri kina shafa man dazakiyi haske, gaki da jikinki tab'as b'as, sai mubi komai a hankali ko?"
"Gyad'a kai Afrah tayi nan suka nufi d'akin Hajiya babba suna kullace kullace".

"gidansu Latif Bilal ya nufa, d'akin Abban Latif ya nufa danufin bashi hakuri, yana sallama Abba yamike yace "yawwa ga takaddun gidajenka, da companonin ka, Bilal banason komai yakara shiga tsakaninmu, Wata shari'ar kuma sai a lahira"
Bilal hakuri yarink'a bawa Abba, tareda ce mishi bincike yakeson ayi shiyasa Yace a ajiye Latif, kuma babu abinda 'yan sanda zasuyi mishi, da kyar Abba ya hakura, kafin Bilal yatafi"

"Latif ana kulawa dashi sosai a station, Idan kaganshi baza kayi zaton kamashi akayi ba, har wani haske yakeyi"

_washe gari_
"Minal ce zaune kan d'aya daga cikin kujerun d'akin, muryan Afrah taji tana cewa " Haba yaya Bilal meyasa zakayi shiru, ko kana tsoron kada matarka tajimu ne? Ni gaskiya idan zamuyi soyayyarmu kawai mu fito fili mu nunawa duniya, adaina wani b'oye b'oye, kowa tasan Akwai Aure tsakaninmu dakai, Dan Allah kayi magana yaya Bilal nawa kajiii?"

Zuciyar Minal ce tayi wani kara dummm "soyayya suke yi dama? Haba no wonder Ruwa bata tsami banza, yanda take nuna kishi afili nasan Akwai wani Abu a kasa, Ashe sune manyan karuwan gida, yake kora kunya da hauka?
Allah yashirya al'ummar musulmai"

Murmushin nasara Afrah tayi ganin yanayin fuskar Minal ya sauya, azuciyarta tace "zakiga munafinci yarinya, sai kin bar gidannan da kafarki, bankad'o kofar tayi Alamar ta tafi".

"Bilal ne yafito daga toilet, sabida yana d'an jin surutu kad'an kad'an " wannan yarinyar kodai Aljanu gareta, idan ba Aljanu ba wazaiyi magana shi kad'ai"
Bud'e kofar falo yayi, nan yaganta zaune ita kada'ai "ke? Dawa kike surutu?"

Minal kuma gani tayi ya mugun raina mata wayo, yanzu sugama magana da Budurwarshi kuma yazo yana tambayarta dawa take magana?
Murmushin karfin hali tayi kafin tace "da budurwarka wacce tafito daga d'akin nan yanzu muke magana"

Budurwata? Cewar Bilal "lalle kin tabbata me Aljanu,
To Allah yakawo sauk'i"


✔ote & comment

_Jiddah S Mapi_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi


Page 16...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


"Ni banida Aljanu hasalima kora kunya kakeyi da hauka, ina kara tunatar maka niba kurma bace ni MAKAUNIYA CE, naji duk abinda tafad'a, sandarta ta d'auko zata shiga bedroom yayi saurin rikewa, " ke me kike nufi? Dan bakya ganin komai shiyasa zaki min sharri? Ni nahanaki gani? Ko ni na toshe idanunki? Wato kina jin bak'in cikin ina kallon duniya ke bakya gani ko? To indai hassada ne haka zaki kare a Makauniya"

"Na yadda yaya Bilal koda nakare a Makauniya Allah yasani ni Makauniya ce a ido, Amma ba'a zuciya ba irin naka, Kaine ka Makance da duniya, kud'in Ku ya makantar daku, daga kai har kannenka, Amma ni idona ne kad'ai a Makance ba Zuciyata ba, tana gama fad'an haka ta sakar mishi sandar tafara Neman hanya da hannunta har ta iso bedroom"

"Kwankwaso yarike yana kallon ikon Allah, lalle yarinyar nan tana Neman ta rainani dayawa, bata da laifi nida nake kyaleta ne da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login