Showing 21001 words to 21643 words out of 21643 words
Chapter 8 - Alaqaqai Part 1 Complete Hausa Novel By NAZIR ADAM SALIHI.txt
duk duniya babu wanda ya isa ya fitar dani daga zargin sa.
Kaga malam ya isa Jeka kawai abin da kayi da ma ya isa.. Lauriyya ta yunkura acikin motar ta leko da kanta tace.
Watarana zamu sake haduwa Hilal.... Nayi maka alkawari. Nagode Allah ya saka maka.
Mutumin ya tashi motar sannan ya dubi Mahaifiyar lauriyya yace.
GATA DAI YANZU AI MUN GANTA KIN YARDA DAI YANZU BA SAYAR DA ITA NAYI BA KO?
Yana gama fadin haka sai ya sawa motar giya suka harba aguje.
Koda suka tafi sai cincirindon yaran dake kallon diramar suka rufa musu baya aguje suna shewa me yiwuwa da yake sun saba ganin jaruman shirin fim na taruwa agurin sun dauko ko wani sabon fim din aka shirya musu.
.
Kusan mintuna biyar ina nan tsaye sannan sai na juya na nufo cikin ofishina koda na shiga sai Naji shiru kamar makabarta zuciyata tayi kuna bakin ciki da takaici suka lullube Ni hakika rashin lauriyya kusa dani ba karamin rashi bane.
Ba'a dade ba sai Naji kafafuna duk sunyi rauni kamar bazasu iya daukata ba dan haka sai na nufi kujerar da lauriyya take zama a tunani wai ko zata dauke min kewa na zauna a kai ina zama sai Naji duk kasala ta lullube ni dan haka saina dauki kafafuna na dora su akan teburin sannan na lumshe idanuna na fara tunanin matsayina a yanzu.
TA LEKO TA KOMA. Nace da kaina babu Fadila na rasa lauriyya ga shi kuma nayi sallama da zama Miloniya.
Ina Nan zauna sai nafara kiyashin kudaden da ake Bina bashi. Cikin zuciyata a iya sanina ana Bina kudi kusan dubu dari shida da hamsin wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina.
Dole ne nasan duk yanda zanyi na biya su kudin su tun da dai wacce ke tarairayata da kwantar min da hankalin ma an dauke ta.
.
Daga inda nake zaune ina iya hangen sabuwar motar da mahaifin fadila Yabani tana sheki acikin rana nasan banida wani zabi daya wuce na sayar da motar na biya mutane basussukan su zuciyata tayi kuna tuni labari ya ya fara yada duniyar fim cewa na sake shigowa gari domin duk cikin JARUMAI maza babu mai shiga motar da takai tawa a yanzu dan haka sayar da ita ba karamar faduwa bace.
To amma banida zabi. Na lumshe idanuna sannan nace da kaina dan samari Hilal sayar da motar ka biya mutane bashin su ai zama lafiya yafi zama dan sarki ina yanke shawarar sai Naji nafara samun saukin rayuwa cikin zuciyata.
Naji wani dadi ya lullube ni sa'ar dana tuna da cewa motar zatayi tsada idan na sayar da ita dole ne na samu rarar kudin da zanci gaba da juyawa acikin harkar fim.
.
Can kuma sai wani tunani ya Fado min nan da nan na zabura ai kuwa da zan maida duk abubuwan da suka faru akaina tun daga daren shekaran jiya zuwa yau fim. Ba karamar karbuwa zanyi ba murna ta cika ni sai nafara tunanin sunan da ya kamata na sa masa. Sai kuma tunanin wahalar dana sha kafin na jefar da JARIRIN nan tafado min tabbas ALAKAKAI zan Sawa fim din
.
Kwarai kuwa cikin zumudi saina tuma kafata da karfi akan teburin sannan ne to naji wani abu ya Fado daga karkashin teburin. Cikin sauri saina sunkuya na dauka.
JAKA ne ya Fado.
Yawun bakina ya kafe zuciyata tafara harbawa cikin sauri a kwance a tsakar dakin jakar lauriyya ce data kawo min adaren jiya dauke da sarkokin nan masu tsada jikina na rawa na bude jakar.
Suna nan kamar yadda suke suna daukar idanu.
.
Lauriyya!! Nakira sunan ta cikin murna da farin ciki yanzu kam nasan bana bukatar saina sayar da motata dan biyan bashi.
.
Jikina na rawa na Mike tsaye ni kadai kamar mahaukaci nafara juya jakar dake kyalkyali a hannuna kawai sai Naji na fashe da dariya sannan Nace da kaina...
HILAL DAN DUNIYA ALLAH KE SON KA BA MUTANEN DUNIYAR FIM BA..
.
KARSHE.....
.
Nazir Adam Salih (NAS)