Showing 15001 words to 15823 words out of 15823 words
Chapter 6 - Kadangarun Bariki Part 1 Complete Hausa Novel By Mrs Sadauki.docx
Isha'i Baba ya dawo,da Umma ta sanar da shi maimakon ya ji haushi sai cikin Ameera da yayi ya shiga dukan ta "ƙarya kike munafukar banza yawon iskanci kika tafi ke ga karuwa shine da Alhaji ya baki kuɗi ki kawo min sai kika zaɓi zuwa Bariki to Allah ya isa ban yafe maki ba"ya na zaginta ya na dukanta da halbi.
Sai da Umma ta ga zai hallaka mata ƴa sannan ta jaye ta,tace "haba Malam ta yaya za ka rinƙa jifar ƴar cikin ka da mugayen lafuza?"cike da bala'i Baba yace "ƙarya ce nayi ba karuwa ce ba?"cikin jin haushi Umma ta maida martani tace "in karuwa ce mi zai sa ta dawo gida ?"
Baba ya nufi ƙofar fita yace "so ta ke ta zama KARUWAR GIDA ta yadda babu wanda zai tuhumeta a kan karuwancin sai dai ba'a gida na ba ta je can ta ƙarata a duniyar *ƘADANGARUN BARIKI*"
Washegari
Wanka ta kuma yi sannan tayi tsarki da ruwan bagaruwa wanda Umma tace in ta na yin haka kullum tsaf za ta liƙe ta tsuke,ta na cikin banɗaki ta ke jiyo zage-zagen da Baba ke yi ya na aibanta ta.
"Za ki fito ko sai na shigo banɗakin na ci burar ubanki?"ta ji Baba na faɗa ya na jijiga ƙyauren banɗakin kamar zai cire sa,jiki na kyarma ta jawo zane tayi ɗaurin ƙirji sannan ta buɗe ƙyauren.
Naushi ya kai mata a kumci ya na zaginta,Ameera ta fashe da kuka ta nufi ɗaki.
★★★ NIAMEY
Waleed ya karɓi haihuwar Waleedat inda ta haifo kyawawan ƴaƴanta maza masu kama da uban su,tun da aka yi haihuwar Waleed ya kasa tsaye ya kasa zaune kullum cikin zarya ya ke wannan yasa ya mance shaf da batun zuwa dubo Mai Gadi sai yau da ya tuna.
Cikin baƙin rai ya nufi Pays-Bas sai wani gangame fuska ya ke,ya zo daidai inda ya ke parking su Lamira suka fito daga cikin gidan su.
Murmurshi tayi ta na ce ma su Fa'iza "irin waccan motar zan saya in nayi kuɗi"ta faɗa ta na nuni da yatsanta daidai ne Waleed ya fito.
Wani irin ƙuri Lamira ta yi masa ta na jin wani irin sonsa ya shigeta lokaci ɗaya,ba tayi ƙasa da gwiwa ba ta taka gun sa.
"Mai kyawu mi ya kawo quartier ɗin mu?"ta tambaya lokacin da ta zo gat da Waleed wanda ke ƙoƙarin rufe mota,juyowa yayi ya na ƙare ma kyakkyawar fuskarta kallo ganin haka ya sa Lamira sakin murmushi cike da duniyancin da Bibalo ke koya mata tace "gaskiya ba ka kyauta ma kan ka ba da har ka shigo wannan unguwa mai datti haka,am nace amman kai baƙo ne ko?"samun kansa yayi da gyaɗa mata kai ya na mai cigaba da sake kallonta.
Lamira tayi murmurshi tace "ayya shine ka rasa inda za ka sauka sai Pays-Bas unguwar da babu komi sai ƙazanta da sabro?"tayi maganar ta na taɓe baki kafin daga bisani ta ɗauko ƙullin gyaɗa biyu ta miƙa masa.
Karɓa yayi ɗago kansa da zai yi suka haɗa ido da Nabeela wacce ta dawo daga makaranta,juyawa Lamira tayi ganin ya kafe waje guda da ido.Wata muguwar harara ta watsa ma Nabeela kafin tace "ka bar kallonta kar ta ɓata ka duk ƴan ɗakinsu mugun hali ne da su kamar uwar su,am nace mai kyau miye sunan ka?"murmurshin gefen baki yayi yace "ki canka da kan ki"ya na gama faɗa yayi gaba ya na mai zuba gyadar cikin aljihu.
Da sauri Nabeela ta shige gida ta na sharar hawaye kafin kuma ta fito waje inda tun tuni su Lamira sun yi wucewar su.
Marfin motar Waleed ta kama cikin mamakin ta sai kuwa ta ji ta a buɗe,gidan baya ta buda ta shige sai magana ta ke ita ɗaya.
Ta na tsinkayan Waleed tayi sauri ta kwanta ruf ta yadda ba zai ganin ta ba,Waleed kuwa da ya zo sai da ya dubi gidan su Nabeela kafin ya shiga motar shi.
Ƙyaci yayi bayan ya yi ma motar key a fili ya furta "sai na sa ƴar fillo(cewa da Lamira) ta ɗauko min ke ta kawo min ke cikin dubara ba dai kin ce sona kike ba to za ko ki gani yadda zan mayar da ke abar kwatance in rinƙa gana maki azabar da ba ki taɓa sanin akwai kalar ta a duniya ba" gaban Nabeela ne ya faɗi jin abinda Waleed ɗin ke cewa,ta kawo kanta da kanta ga ajalin ta ba ta san lokacin da wani tari ya zo mata ba.Da sauri Waleed ya taka burki ya na mai waiwayo suka haɗa ido biyu da Nabeela wacce tsantsar tsoro ya bayyana ƙarara kan fuskar ta......
*Nan zan tsaya da book one masu son cigaba za ku biya 200₦ ta account ɗin da na bada a waccan page ɗin,ƴan Niger kuma carte airtel ta 300f sai ku turo shaidar biya ta WhatsApp* +22795045822
In an yi payement zan cigaba in shaa Allah
