Showing 18001 words to 21000 words out of 66367 words

Chapter 7 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

riko hannun ta yayi yace "Me zakiyi?" Bata ce Masa komai ba, kallon Kan gadon yayi yaga b'arnan da yayi jini ta ko Ina, dafe kansa yayi ya maida kallon sa gunta sai yaji tausayin ta ya kamashi shi duk baiyi tunanin ita virgin bace, karba'an zanin yayi ya d'aga ta yayi ya kaita ban d'aki ya had'a ruwan zafi sannan ya soma ta aciki, ihu ta kurma tana kokarin Tashi, yayi saurin danne ta, yace "I'm sorry is for your own good, Zaki ji dad'in hakan" rose sai kuka take wiwi, tana bubbuga baff d'in da hannun ta, tana ciza leb'e sai hawaye kukan ma har kasa yi tayi sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa ta ya Ciro ta ya kaita bed room ya kwantar da ita, Tashi tayi ta hau sa kayan ta, yace "Ina Kuma Zaki je?"


Cikin kuka Tace "Gida" riko hannun ta yayi yace " meyasa baki fad'a min ba?"
Tace "Me zan fad'a maka?"
"Ashe dama ke budurwa ce?"
Murmushin takaici tayi tace "da me ka d'auke Ni?"
Shima murmushin yayi yace "Babu, Amma da kin fad'a min da na yi Miki a hankali Amma ki duba kiga b'arnan da nayi" Yana nuna Mata Kan gado da Yar yatsa, kau da Kai tayi tace "Ai ya Riga ya wuce Ni Zan tafi gida"
Yace "ki kwana a Nan Mana kawai sai ki koma da safe"
"A'a Mamata bata gida Rahila zata damu idan bata ganni ba yanzu nasan tana chan ta damu"
"Okay Bari na sa a maida ke gida"
"A'a bana bukata" sai ya d'aga kafad'ar sa alamun ko in kula, bayan ta gama Sanya kayan ta,ta nufi hanyar fita, ji ta yi ta kasa tafi, wani Kara ta sa tana ciza leb'e da gudu ya karaso inda take yace "What happened? Me ya same ki?"




Rose kasa magana tayi sai hawaye ya Kuma cewa "Sai da nace ki kwana sabida nasan na ji Miki ciwo sosai please ki bari a Kai ki gida" Kai kawai ta d'aga Masa, shi da kansa ya fitar da ita har waje sannan ya Kira driver yazo ya maida ita tana ganin sun iso layin su tace Masa ya tsaya, sauka tayi tana tafiya a hankali har ta Isa gida a fili Tace "Yau me Zan fad'awa Rahila idan taga irin tafiyar da nake dole ta gane" shiru tayi sannan tace "kawai zance Mata na gurd'e ne" sai ta kusa Kanta cikin gidan, Rahila na zaune ta zuba uban tagumi, tana ganin Rose ta taso da gudu, ta riko hannun ta Tace "Sister Ina Kika Shiga ne Ina ta Neman ki tun safe?"
Kirkiran Murmushi Rose tayi tace "Na d'an fita ne" da Karfi Rahila ta jaa hannun Rose, ihu Rose tayi Mai uban kara har sai da Rahila ta tsorata Tace "Me ya faru? Kinji ciwo ne?"
Kai kawai ta d'aga Mata, Tace "sannu sannu ya akayi haka? A Ina ciwon yake?"
"A kafa na" kawai tace Mata a takaice, Rahila Tace "Na gani?" Cikin nuna kula da tausayawa,Rose Tace "A'a please ki taimaka ki had'a min ruwan wanka Mai zafi sosai sai na Kama gun zanji sauki"
"Toh shikenan" sai ta shige kitchen, Rahila Kuma ta Shiga d'aki ta kwanta jikin ta duk ciwo.


B'angaren su Daniyah kuma, sai gyara kayayyakin su suke, sai da suka tabbatar Basu manta komai ba sannan suka kwanta don bacci.


Yarima tunda Rose ta fita, ya rasa me zaiyi duk duniyar ba dad'i, a ransa yace "Rose Virgin ce, Kash I could have known da na dad'e da auren ta, Amma yanzu bazan iya auren ta ba sabida yanzu ita ba virgin bace, shaidan da akeyi wa mahifitar su gaskiya ce na tabbata kanwarta ma Virgin ce" murmushin gefen baki yayi yace "Rahila zan aura she'll be my wife" cikin tunanin Nan ya yi bacci.


*Washe Gari*
Granny da su Daniyah sun Gama shiri, dukkanin Yan gidan basu ji dad'i ba, Amma ance bako rab'a ne, Daddy ne ya turo musu driver tun asuba ya taso hakan yasa karfe takwas ya karaso basu tsaya b'ata lokaci ba suka Shiga mota sai gida.


Rose ta kwana jikin ta duk ciwo har Saida zazzabi ya kamata, Rahila ce take ta aikin kula da ita duk da Bata San mene ne silar rashin lafiyan nata ba, chemist taje a ka had'a wa yar Uwarta maganun Nan zazzabi taci Sa'a ya Mata aiki, don ta samu sauki sosai kamar ba ita ba.


*Bayan Sati*
Fada na gani a cike, sai suratai ake shigowar, Sarki da matar sa da Kuma Yarima yasa gun yayi shiru, bayan sun gaida su cikin girmamawa kowa ya samu guri ya zauna, Sarki ya ce "Dukkanin ku Kun San dalilin zaman Nan a yau, magana ne Akan Yarima yayi kokarin yiwa wata yarinyar fyad'e, Ina so yarinyar Nan ta fito tazo tayi magana a gaban kowa"
Kowa na gun sai kalle kalle suke, sarki yace "Ko Bata kusa ne?" Kaka ne ya Mike bayan ya gaida su yace "Jikita ce sunyi almost a week da tafiya dama hutu suka zo Kuma ya Kare sun koma makaranta"


Wani mutumi yace "Your Majesty ai na fad'a maka ka tsaya a yi bincike tukunna, kaga tasan bata da gaskiya shiyasa ta gudu"
Kaka yace "No ba haka bane na fad'a muku dalilin tafiyar ta"
Sarki yace "Hakan na nufin kunyi wa Yarima sharri ko? Ka fad'a min gaskiya ko na sa a kashe ka yanzun Nan"
Murmushin takaici Kaka yayi yace "Eh dama zaka sa kashe Ni, sabida Kai ba Sarki bane mai adalci duk sanda aka kawo maka karar an ga masoya biyu ba ka yin bincike babu ruwanka da gaskiyar su ko babu Nan take kake bada umarni a kashe su, Amma dake Yarima d'an Kane yau sati d'aya yake abinda ya ga dama a garin nan, so what idana ka kashe Ni, garin da ka kasa kula da mutanen cikin ta, garin da an Maida mu tamkar kiyashi a kashe mu lokacin da aka so a Wurin da aka so, gara a kashe Ni ko zan huta da bakin cikin garin Nan" ya karasa maganar ya na share hawayen da ya gangaro Masa, dukkanin jama'ar gun jikin su yayi sanyi matar Sarki kuka take sosai mikewa tayi tace "Tabbas maganar Mutumin Nan gaskiya ne ba karya cikin ta, hakika ka Zama mugu azzalami Mai son zuciyar sa, ko kad'an Raina bai b'aci ba Jin ance yayi yunkurin yiwa Daliyah fyad'e Yarinyar Nan kana ganin ta kaga nitsassiya ta fito daga gidan tarbiya daga maganganun ta na gane hakan Kai ko da ace ta Masa sharrin ne ai tayi dai dai, sabida d'a guda d'aya ka kashe matasa maza da Mata sama da ashirin a iya sani na Banda Wanda kake sawa a yi b'oye" Maida kallon ta tayi ga Yarima tace "If not because I'm your mother da na dad'e da tsine maka sannan na maka fatan Shiga duniya, Wai virgin, hmm can you swear in front of everyone that you are a virgin?" ta karasa maganar cikin kuka, Yarima takaicin Duniya ce ta ishe shi, tasowa yayi ya suguna a gaban ta yace "Mummy it was never my intention someone should be killed because of me, it's all father's fault"
A tsawace tace "Would you shut up your dirty mouth, kana ganin yanda ake kashe Mata Kuma kasan gari zai cika gari ne in da matasa sabida aure zasuyi sun hayayyafa Amma Sabi da Kai..... Sabida Kai sun rasa Rayukan su, I swear to the almighty dama niya na, na maka sharrin kayi wa wata fyad'e Amma sai suka rigani" kallon ta yayi a razane yace "Mom?" Ta amsa da "Yes Kai man kashe ka kowa ya huta."
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Mu had'u a page na gaba
Please comment and share
Milhat Ce🥰
Yar Terawa


🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE```9️⃣0️⃣↪️1️⃣0️⃣0️⃣0️⃣


```PREVIOUSLY```
A tsawace tace "would you shut up your dirty mouth, kana ganin yanda ake kashe matasa Kuma kasan gari ba zai cika gari ne in da matasa sabida aure zasuyi su hayayyafa Amma sabida Kai..... Sabida Kai sun rasa Rayukan su, I swear to the almighty dama niya na, maka Shirin kayi wa wata fyad'e Amma sai suka rigani" kallon ta yayi a razane yace "Mom?" Ta amsa da "Yes Kai ma a kashe ka kowa ya huta."
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
.............Cikin kuka yace "God have mercy on me, please mom forgive me"
Ture shi tayi ta nuna jama'ar dake zaune a gun tace "ask for their forgiveness not mine, su kayi wa laifi sabida haka ka roki gafarar su ba nawa ba"


Tashi yayi ya durkusa a gaban su Yana kuka Mai cin Rai ya had'a hannayen sa guri guda yace "Please forgive me I know I have wronged you all, ban chanchani yafiyar ku ba Amma ku daure ki yafe min please" ya karasa maganar cikin kuka, kowa na gun Saida suka ji tausayin sa, sai wani daga cikin mutanen yace "zamu hakura Amma da Sharad'i" cikin sauri yace "Na mene ne I'm willing to do what so ever don ku yafe min" gyaran murya Mutumin yayi yace "Yanzun Nan anan gun zaka zab'i Mata a cikin Yan matan dake Nan gurin" yace "Zanyi zanyi" Tashi yayi ya Fara Dubawa ko zai ga Rose Amma Bai ganta ba charaaf idon sa ya fad'a akan Rahila zuwa yayi har inda take ya riko hannun ta, mutanen gun duk sun cika da mamaki, har gaban mahaifiyar sa ya kawo suka tsuguna yace "Mom I choose Rahila as my wife" guri ya kaure da ihu, juyowar da Yarima yayi sai idon sa ya sauka akan rose da alokacin ta shigo, hawaye ne masu zafi suka sauka Mata tayi saurin fita daga fadar ba tare da kowa ya ganta ba sai shi yariman.......


Wani irin Murmushi yayi sannan yace "Ai alkwari nayi bazan Auri Wacce ba virgin ba" a zuciyar sa yake magarnan Nan,Mommy tasa musu Albarka da dukkanin mutanen gun, Sarki ya Mike Yace "Duk Naji abubuwan da kuka Ce, hakika na zalunce ku Ni ba adalin Sarki bane ba, Kuyi hakuri ki yafe min Ni Zan sauka da ga Kan kujerar tawa in yaso sai ku zab'i Wanda ya dace" jikin su duk yayi sanyi, Kaka ya tashi yace "A'a baza a yi haka ba kujerar gadon ta kayi bazaiyu ka sauka ba har sai ranar da ka mutu magajin ka ya gaje ka, Kuma dalilin abubuwan da kayi duk a Kan Yarima ne tunda ya dawo daga American if not muna Jin dad'in Zama da Kai, ko ya kukace Yan Uwa?" daga masu cewa haka ne sai masu ihu da tafi.


Sarki yace "Nagode Nagode, may the almighty God give me the strength to do what is right for all of us" suka amsa da Amen.
Rose na barin gun gida ta nufa ta Fara tattar kayanta, Mahaifiyar ta Ce ta shigo Tace "Rose Ina Zaki je?"
Tace "Mama kin San naje fada don Jin hukuncin da Za'a yanke wa Yarima Ina Shiga sai Naga..........Nan ta Sanar Mata da dukkanin abinda ta ji ta gani ta Karasa maganar cikin kuka, Mama ta jawo ta jikin ta ta rungumeta tace "Rose Naji duk abubuwan da Kika ce yanzu da kike had'a Kaya ina Zaki je?"
"Gurin dangin Mahaifina"
Iska Mai zafi Mama ta sauke Tace "Toh shikenan Chan ma gida ne Amma yaushe Zaki dawo?"
"Zan dawo Mama idan aka Gama bikin nasu, nayi mamakin abinda Rahila tamin Amma Bakomai duniya ce,please Mama Kar ki hanani tafiya" Murmushi Mama tayi ta shafo fuskanta Tace "Bazan hanaki ba Zan tayaki ma shirya kayan da kaina, Kuma Zaki ga Zaki samu Miji Wanda ya dace dake kinji? Kuma Kar ki rike kanwar ki a rai" Murmushin ita ma tayi tace "Nagode Mama" suka rungumi juna sannan suka Shiga shirya Mata Kaya suna gamawa har tasha Mama ta raka ta tayi Mata fatan Allah ya tsare.


Mama na Isa gida taga gidan a cike fil har sai da ta tsorata, Rahila ce ta riko hannun ta,tana Murmushi tace "Mama ki shigo" Yarima ya taso Shima ya riko d'ayan hannun Mama yace "Welcome" kirkiran Murmushi Mama tayi, suka kaita mazaunin da aka tanadar Mata, Kun San Yan gargajiya koman su daban ne da al'adun mutane, Nan da Nan aka Fara d'aura aure, Giya a ka sa Kofi Rahila ta nemi inda mijinta yake tasa Masa a Baki yasha sannan ya sa Mata na bakin sa, sai Wurin ya kaure da ihu da tafi.
Mama duk Bata so auren Nan ba sabida da Rose ya kamata ayi bikin Nan ba da Rahila ba.


*KANO*
Tunda su daniya suka Isa gida, sai tarairayar su ake musamman Daniyah sai hidama ake ta musu, Hira suke sosai suna bawa Daddy da Mummy Labarin abubuwan da ya faru a chan, Granny kuma sai aikin kallon su take Amma basu yi Kuskuren fad'a Masa risk d'in da Daliyah ta d'auka ba.


Daddy yace "Kun dawo yanzu sai Kuyi Shirin Komawa makaranta da Islamiyya"


Daniyah Tace "Daddy ai sai results d'in mu ya fito ko?"
Dafe kansa yayi ya kalli Momy yace "Kinga na manta da maganar results d'in su, please jeki d'auko, ai kin San inda yake ko?"
"Eh" a takaice ta shi cikin mintuna biyu ta dawo ta Mika Masa wata brown envelope, bud'ewa yayi ya zaro paper guda biyu ya Miki wa ko Wacce ta ta, Daniyah Naga ta doka tsalle tace "wow Daddy Naji dad'i sosai science class fa na samu"
Murmushi yayi yace "Eh science class dama kince Nurse Kika so ki Zama ko?"
"Eh Daddy Amma yanzu na canza Shawara"
"Tooooh!! zuwa me?"
"Doctor Daddy, Naga zai fi dacewa Dani kaga sai a Rika kirana da Dr Daniyah"
Duk suka Fara dariya, Daddy ya maida kallon ga Daliyah yace "My princess ya dai Naga bakiyi murna da ganin result d'inki ba ko Kema science d'in kike so Ne?"
Murmushin gefen baki tayi tace "A'a Daddy Ina son art d'in Amma ban gama yanke shawarar abinda zanyi ba shiyasa nayi shiru."


Dariya Daddy yayi yace "Wannan ai ba wata matsala bace ba yanzu fa SS1 zakuje Kinga da sauran time sai fa kunyi WAEC Kan Kuyi JAMB sannan Ku nemi admission Kinga kina da tsawon lokacin da zakiyi tunani a Kai"
Ajiyar zuciya tayi tace "Kuma hakane fa Ni wallahi duk na manta ma"
Murmushi kawaii yayi, wurin ya d'anyi shiru sannan yace "Mama Ina fatan dai Basu Baki ciwon Kai a chan kauye ba"
Mama Tace "ko kad'an ai yaran sun fara girma an rage rashin jii."
Yace "Alhamdulillah"
Mommy Tace "Lokacin sallah fa yayi ya kamata Muje mu yi sallah ko?"
Daddy yace "hakane" had'e da mikewa yace "Ku tashi Muje masallaci" Huzaifa da Yusuf suka tashi suka bi bayan Daddy, Daniyah da Daliyah Kuma suka Shiga d'akin su Haka ma Momy da Mama.


Bayan sun idar da sallah, duk suka fito suka zauna a Parlor, suna kallo su Daddy Basu shigo ba har Saida suka idar da sallar ishah, mommy Tace "Muje muyi sallar Isha Kan su Daddyn ku su shigo,ba musu sukayi yanda tace "suna idar da sallan suka Shiga kitchen, Nan suka shirya abinci yayi dai dai da shigowar su Daddy,Nan suka zauna suka ci abinci bayan sun gama Daddy yace "Ya kamata ku kwanta da wuri gobe Muje mu sayo muku uniform ko?"


Uwani Tace "Oh!! Su Daliyah an girma za'a shigo senior set"
Dariya Daliyah Tayi Tace "kuji min Aunty Khadee da wata magana, da so kike na dauwama a junior set?"
"A'a bance ba abin nufi ada ma a Yaya kuka Gama da uncle Ameer da Aunty Maryam ko da yake Kun rabu ai yanzu tunda yanzu side d'in mu zaku dawo"
Daniyah Tace "ai kuwa sun huta don nifa gani nake ma kamar Uncle Ameer tsoron ta yake ji"
Dariya Daliyah Tayi Amma a zuciyar ta Tace "Ba Dole yaji tsorona ba Ni na manta chakwakiyar da na had'a ma"


Daddy yace "Surutun Nan ya Isa haka kuje Kuyi bacci" ba musu duk suka watse, Uwani,Liyah da Daniyah suka tattare Kan dinning, mommy da Daddy suka koma parlor Granny Kuma Tace "Ni kwanciyar zanyi na gaji sosai" suka amsa da Allah ya fidda gajiya, Bata Ce komai ba ta haura sama.


Washe Gari
Bayan sun karya sun Taya mommy aiki a kitchen, sukayi wanka suka shirya tsaf cikin shigar su ta bakar abaya Mai hula, Daniyah Baki da pink Daliyah Kuma Red and black.


Suna Isa Daddy yasa aka yanka musu kala uku uku, aka saya wa Uwani Biyu, suna tsaye aka d'inka musu suka dawo gida.
Uwani na ganin sabbin Uniform tayi ta murna dake yau asabar shiyasa bata je makaranta ba, Tace "Wow kinga ranar Monday Zan Shiga school da sabon uniform"
Daniyah tace "Su Aunty Khadee sai kace yau za'a Fara zuwa makarantar" cikin zolaya, Aunty Khadee Tace "Sai Kuma kiyi ai, Baki san sabon Abu da Shiga Rai bane shiyasa"
Daliyah Tace "Toh muka muce me? tunda kinga ranar Monday za mu Shiga SS1?"
"Oho muku ku kuka sani Ni dai kaina na sani"


Huzaifa yace "Aunty Liyah nifa tunda kuka dawo Naga kin nitsu sosai hatta yanayin maganar ki ya canza inda a yanda muka sanki ne zuwa yanzu da kunyi fad'a da Aunty Khadee yafi a 'kirga"


Yusuf yace "Kamar ka Shiga Raina, Nima Wallahi abin na bani mamaki, sai Kuma Aunty Daniya ta koya surutu da tsokana, ko dai canza suna kukayi ne?"
Aunty Khadee tace "Ashe ba Ni kad'ai na lura da hakan ba, gaskiya Daniyah kin koyi surutu sosai kamar bake ba?"
Murmushi Daniyah tayi tace "Yau Naga ikon Allah!!! Toh dan Allah so kuke na Zama kurma ko me?"
Daliyah Tace "Ke dallah rabu dasu ke Kika kula su ma"
Yusuf yace "Nikam na Shiga d'aki bacci nake ji sai la'asar Zan fito"
Huzaifa yace "Nima baccin nake ji Wallahi mu Shiga kawai"


Daniyah Tace "Nima baccin zanyi" Uwani Tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login