Showing 21001 words to 24000 words out of 66367 words
Chapter 8 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
"Me haka Kun wani had'a baki kowa Wai bacci bacci?"
Daliyah Tace "Kinga Aunty Khadee manta dasu, Zo Muje d'akin Mommy mu Taya ta Hira tunda Daddy ya fita"
"Hahahaha yau Kuma d'akin Mommy? Granny d'in Kuma fa?"
"Granny fa kusan wata mukayi tare Amma nayi kewar Mommy sosai wallahi."
Murmushi tayi tace "Toh Tashi Muje" suna shiga suka samu Mommy na zaune tana kallon Zeeworld, Daliyah na kallon TV taga ansa *TWIST OF FATE* cikin sauri ta Shiga ta zauna, Mommy tace "Liyah ke Wai yaushe zakiyi hankali ne? Ki shigo d'aki ba sallama?"
Aunty Khadee tace "Aunty kin fa santa da maitar kallon Zeeworld musamman ma Wannan Shirin sai a hankali"
Kad'a Kai Mama tayi tace "Tooh!! Allah ya shirya, Ina Daniyar take?"
"Wai bacci zatayi" aunty Khadee ta bawa mommy amsa, don ita Daliyah kwata kwata hankalin ta yayi nisa da kallo.
Yau take Monday kowacce ta shirya tsaf cikin sabbin Uniform d'in su, sunyi matukar kyau musamman Ma Twins, driver d'in su ya d'auke su, saida aka Fara dropping d'in Su Huzaifa kan aka wuce da dasu Daliyah.
Daliyah na Shiga class ta jiyo muryar Fareedah tace "Oyoyo Oyoyo Qawata" da gudu Daliyah ta Karasa inda take, suka rungumi juna duk yan ajin sai kallon su suke, sun San 'kawancen su saidai sabbin xuwa ne basu San su ba"
Zama sukayi a back bench suna hirar yaushe gamo, suna cikin hakan malama ta shigo, ajin yayi shiru, ta Fara darasi, Daliyah ta nitsu sosai Kuma tana fahimtar abinda akeyi, Fareedah kokarin jaan Liyah da Hira Amma Taki kulata, har sai da Malamar ta fita, Tace "Haba Faree Kina ganin malama na kiyarwa Kuma kike surutu?"
Zaro Ido Fareedah tayi tace "Iko Sai Mai sama! Yau Liyah Kece Kika fad'an Hakan?"
"Aaaah sa wasa da me kike d'auke Ni?"
"marasa jin magana da rashin son karatu na d'auke ki"
Murmushin takaici Daliyah tayi Tace "A baya Kenan Amma a yanzu na canza zanyi karatu sabida shine dalilin zuwata makarantar Nan sannan na cikawa Mahaifina burin sa naso yaga mun Zama manyan Mata a cikin kasar Nan, Kema Ina Mai Baki Shawara da ki canza in ko baza kiyi hakan ba kawance na dake yanzun Nan Zan datse ta"
Fareedah ganin Daliyah fa dagaske take hakan yasa Tace "Toh shikenan insha Allah Nima zanyi kokari Naga nayi karatun Amma nasan akwai dalili Mai Karfi Wanda yasa Kika canza tunanin ki, mene ne yasa?"
Murmushin gefen baki tayi tace "Gidan mu suna kokarin nuna bambamcin tsakani na da Yar Uwata, hakan Sam bai min dad'i ba, tun daga ranar na d'auki alwashin zanyi karatu fiye da ita"
Murmushi Fareedah tayi Tace "Haba no wonder Allah ya taimake mu Ni fa dama Daniyah ba burgeni take ba Wallahi ko kad'an"
Wani irin kallo Liyah tayi Mata Wanda yasa tasha jinin jikinta tace "Ke!!! Kar kiji nace Miki na daina harkar Nan kice Zaki Raina min wayo, Daniyah fa Kanwata Ce My Twins for that matter, Kar ki sake Kuskuren Nan in ba Haka ba wallahi jikin ki ya d'au na yakuwa"
"Haba Qawata yi hakuri Baki San Wasa bane Haba dan Allah"
Harararta Liyah tayi Tace "ya dai fi Miki"
Fareedah Tace "Kinga Uncle Ameer fa ya shigo last week sau biyu Neman ki"
Zaro Ido Liyah tayi Tace "Nema na kuma? Nikam na Shiga uku"
"Kamar ya kin Shiga uku me ya faru?"
Kirkiran Murmushi tayi Tace "Bakomai Zan San yanda zanyi dashi ne"
"Wai me Kika Masa ne?"
Murmushin gefen baki tayi tace "Ke dai Bari is a long story"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Milhaat Ce
Yar Terawa
PLEASE COMMENT AND SHARE
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣0️⃣0️⃣↪️1️⃣1️⃣0️⃣
Fareedah Tace "Kinga Uncle Ameer ya shigo last week sau biyu Neman ki"
Zaro Ido Liyah tayi Tace" Nema na kuma? Nikam na Shiga uku, Zan San yanda zanyi dashi ne"
"Wai me kika Masa ne?"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Ke dai Bari is a long story"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
......... "Make it brief Mana Liyah Wallahi Kar kiso kiga yanda fuskar sa yake Rai a 'bace yake tambayar ki, shi ya d'auka ma kin bar makarantar ne"
"Ke dai Bari, yanzu saura period uku muna fita break zanje naji dalilin da yasa yake Nema na"
Haka kuwa akayi suna fita break ta nufi side d'in su Uncle Ameer, Yana ganin ta ya Fara washe baki, yace "Haba Liyah Ina Kika Shiga ne? Nake ta Neman ki I thought kin bar makarantar tamu ne ai"
Murmushi ita ma tayi Tace "Uncle nayi tafiya ne Shiyasa Amma meyasa kake ta Nema Haka?"
Dariya yayi yace "Maganar Khadija Mana nifa so nake tana gama makarantar Nan a Mana aure"
Tace "Da wa!!
Wani irin kallo ya Mata yace "Aaaah! da Khadija Mana Kar ki Raina min hankali Mana"
"Haba uncle me abun rainin hankali anan? Tambaya ce fa amsa kawaii zaka bani, Amma tunda Naga abun naka da fad'a kake so muyi Bismillah" ta juya da niyar tafiya yace "Dawo dawo Zo Mana Liyah, princess Liyah kin San fa Ke Sarauniya ce bai kamata kike b'ata ranki a Kan 'yar karamar magana"
"Uncle Kenan shikenan tunda kace Haka Bari na fad'a maka gaskiya aunty Khadee ba aure zatayi yanzu ba, Policy na (dokan) gidan mu sai mun Gama jami'a Kan muyi aure kaga yanzu tana ss² , kusan shekaru Bakwai kenan ta rage Mata"
"Haba bazai Kai Hakaba jami'a ai four years ne"
"Eh Ina sane" ta gyara sayuwar ta ta fidddo hannun ta daga cikin hannun rigar sanyin da tasa Tace "Kaga ss² take yanzu Dole mu irga dashi tunda first term ne zuwa ss³ Kuma kaga 2 years, sai tayi jamb a shekarar idan taci Sa'a taci sai ta wuce makarantar idan Kuma Bata ci ba kaga Dole ta zauna zaman shekara d'aya"
Shiru yayi Yana kallon ta sai Tace "Kaga 2+4=6 in Kuma bata ci jamb ba sai tayi 7years ka fahimta yanzu?"
"Eh na fahimta Amma a ganin ki me mafita?"
"Ai mafita d'aya ne ka hakura har sai ta gama"
"Haba ma haba!! Na jira ta har sai ta gama?" Ki Kare min kallo nifa ba yaro bane ba na bawa talatin baya yanzu na Kara shekaru d'aya d'aya har bakwai ai na kad'e ga mutuwa yanzu ba babba ba yaro" dariya Ce taso ta kufce Mata, tace "Yauwa Nima dai hakan na gani kawai ka manta da maganar ta"
Yace "Liyah Kenan ashe dama a gidan ku take Amma Kika ce min makwaftan Kune?"
Sosa keya tayi a zuciyar ta tace "Tirkashiii Ni wallahi na manta ma na masa wannan karyan" a fili Kuma Tace "Uncle yaushe mukayi Haka da Kai? Kila dai ka manta ne Amma Ni dai nasan na fad'a maka gidan mu d'aya da ita kanwar Mommyn mu Ce, gaskiya uncle tsufa yazo"
Dariya yayi yace "Toh shikenan na hakura da ita, to ya maganar gifts da kud'aden da nake baki ki Kai Mata?"
"Yana gunta Mana"
"Toh a karb'o min kayana" fuska a tamke yayi maganar Kakar bashi ya gama dariya yanzu ba
"Uncle Kar ka bada Ni Mana Kar ka Zama irin mazan Nan masu gajeren tunani Wai kawai don sun bada kyauta matsala ta d'an gifta sai suce a maida musu kayan su yawane Wallahi ba girman ka bane ba"
"Eh na yadda gajeren tunani ne da ni kawai ki karb'o min ko Rai ya b'aci" Liyah ganin dagaske so yake ta dawo Masa da kud'in tace "Anyi an gama Zan karb'o maka Amma ka sani daga Nan ofishin principal nayi Zan fad'a Masa kasa ni na had'a ka da student Kuyi Soyayya Kuma kasan babban laifi ne Malami ya nemi student d'insa, na biyu Kuma kana leken malamai Mata in ka manta Ni ban manta ba" tana maganar tana tafiya,da sauri ya Sha gaban ta yace "Liyah Wasa nake Miki Wallahi na bar Mata kud'in har abada ke baki San Wasa ba eh?"
Fuska a tamke tace "Bamu son kud'in ka Zan dawo maka dashi gobe kila zai taimake ka a gaba don nasan ka Gama aiki a makarantar Nan da zaran principal yaji maganar Nan"
Magiya ya Shiga yi Mata Yana bata hakuri har ji yake kamar ya durkusa a gaban ta, Liyah sai da ta jaa masa Rai Kan tace "To shikenan Amma daga yau Kar ka sake zuwa nema na Kar ka Kuma min magana sai dai in maganar ta shafi makaranta"
Murya na rawa yace "Na yarda Wallahi na yarda"
Tace "Good Nikam na tafi" ta barshi a gun Yana tsaye Baki a bude, yace "Yarinyar da bata shekaru Sha Bakwai bace take waina Ni, Kaaai Ameer tirr da irin halinka Dole ma ja canza tsarin Rayuwa ta" ya koma ya zauna, Liyah na fita ta tsaya ta dafe kirjin ta tace "Alhamdulillah na gama da wannan matsalar Allah ya tsare na gaba" ta koma class, tana Shiga aka kad'a kararrawa Nan suka cigaba darusa.
Uwani, Daliyah da Daniyah sun Maida hankali su sosai Akan karatun su, a yaune Uwani suka gama WAEC da NECO d'in su saura jiran saka mako, su Liyah Kuma zuwa yanzu suna ss², Alhamdulillah results ya fito Uwani taci nine credits both WAEC and NECO, sannan registration na JAMB ta ci 198, Daddy da ya ga haka ba karamin murna yayi ba, shi ya shige Mata gaba gurin ganin ta samu admission, bai d'au tsawon lokaci ba Admission ya fito Kuma ta samu a B.U.K tayi applying Mass Communication Amma sai suka ba Public administration, ta ki karb'a Daddy yace Mata "Khadija yanzu fa kasar Nan sai kayi karatun ka kashe kan ka da karatu Kuma ka rasa aikin yi,ko Kuma kiga Wanda ya karanta health Yana aiiki a banki, so kawai kiyi addu'a Allah yasa hakan shine Alhairi a gare ki Sam kar kiyi fushi da zab'in da Allah ya Miki"
Iska ta hura a bakin ta Tace "Shikenan Daddy insha Allah Zan karb'i admission d'in Kuma na kaunaci course d'in" ta kalli Mama da Mummy Tace "Ku taya mu da addu'a don addu'ar kuce kad'ai zata taimaka Mana"
Mummy Tace "Uwani Addu'a Kam ai kullum Cikin ta muke sai ki dage da karatu, sannan kisa tsoron Allah a zuciyar ki"
Granny Tace "Kwarai kuwa idan kike rike Allah shi kad'ai baza ki tab'e ba, sannan sallah, sallah wannan Kar ki yi wasa da ita, kin San fa sallah shine kad'ai abinda ya banbanta musulmi da kafiri, sabida haka Kar kiyi Wasa da sallah"
Mama Tace "Maganar Mama gaskiya ce sannan Kinga kawaye ki guji sharri kawaye da samari ba kowa zakiyi kawance da ita ba,akwai kawaye na Kwarai sannan akwai b'ata gari Kar kiyi saurin sake jiki da kawa har sai kin ga halayanta sun yi dai dai ta tarbiyar da muka Miki kinji ko"
Kai ta d'aga alamun "Eh" Daddy yace "Duk abubuwan da yakamata na fad'a Momyn Ku da Mama sun Riga sun fad'e ta, sai dai d'an abun da baza a rasa ba, kamar yanda suka kace kawaye da samari Basu kad'ai ba, harda lecturers d'in Kar ki Bari ko gaisuwa ta had'a ki da lecturer bare ma ya shaida fuskan ki daga Nan fa idan kin Masa zai Fara bibiyan ki ne, ya nemi ki biya Masa bukata idan Kuma Kika ki sai ya b'ata Miki results so ki kiyaye, tsakanin ki dashi lectures Yana gamawa zai fita kin game ko?"
Kai a kasa tana kokarin b'oye hawayen da suka zubo mata Tace "Nagode sosai Daddy insha Allah Zan yi yanda kuka ce"
"bakomai Khadija Allah ya Miki Albarka"
Duk suka amsa da "Ameen."
Uwani (Khadija) ta Fara attending lectures d'inta hankali kwance, musamman Daddy ya Nemo Mata driver da yake kaita cikin makaranta duk sanda take da lectures Kuma ya koma ya d'auko ta.
*Wannan Kenan*
Ina labarin Sabir??🤔
Sabir tare suke da Khadija tunda dama set d'in su d'aya ne, Khadija na Art class shi Kuma Yana science class.
Bayan sakamakon gama secondary School d'in ya fito Shima ya ci sosai, hakan yasa Mahaifin sa yace bazaiyi makaranta a kasar Nan ba sai ya turashi Oxford University,tunda ya tafi baida wani tunani da ya wuce na Liyah.
Kwance yake a d'akin sa ya kwanta da baya idon sa na kallon sling iska Mai zafi ya hura yace "Ya Allah ka yaye min Soyayyar Liyah, duk sanda nayi kokarin cire ta a Raina sai naji Soyayyar ta da kaunar ta na ninkuwa a zuciya ta, abinda takaicin ma Bata San Ina yi ba"
Tashi yayi ya zauna ya dafe kansa duk sanda ya Fara tunanin ta sai yaji zazzabi Mai zafi ya Kama shi, a fili yace "Ya Allah Kaine Allah idan Soyayyar da nakeyi wa Liyah ba Alhairi bane a gareni kayi gaggawan cire ta a Raina in Kuma ba Alhairi bace ka musanya min shi da mafifciyar Alhairi" Yana Kai Nan ya Mike ya Shiga toilet yayi wanka bai d'au lokaci ba ya fito ya shirya don Yana da lectures karfe goma gashi yanzu Tara da rabi a gaggauce ya gama ya fita.
Rayuwa tana tafiya Normal yanda ake so, Fareedah da Liyah kawancen su yayi Karfi fiye da yadda yake da, karatu suke sosai Wanda yasa duk Yan gidan su Liyah abun ke basu mamaki tare da farin ciki, a b'angaren islamiya kuma abun ba a cewa komai ko Wacce daga cikin su tana iya bakin kokarin ta kwaf cikin makarantar sune kan gaba hakan yasa inda za'a yi inter state competition Daniyah da Liyah na ciki, hakan yasa Daddy alfahari dasu, ya musu alkawarin suna gama secondary School zai saya ko Wacce system da Waya Mai tsada, sukayi ta murna hakan ya Kara musu karfin gwiwa suka Kara karatu Akan Wanda suke yi.
Alhamdulillah a yaune suka gama jarabawar su ta karshe, a yayin da Khadija take aji biyu haka ma Sabir.
Zaune suke a parlor suna Hira sai Daniyah tace "Aunty Khadee ya Labarin Sabir ne Kam, Kuna tare ne? Haka kawai naji yau ya fad'o min a Rai"
Khadija rufe littafin dake hannun ta tayi tace "Tsohon zance ai Sabir ya kai kusan two years baya kasar Nan"
Zaro Ido Daniyah tayi tace "Haba dai! To Ina yaje"
"Yana Oxford University"
Daniyah Tace "Wow! Yana cikin manyan makarantu na duniya, Amma nayi Masa murna me yake karanta?"
"Ina ga kamar Medicine ne don tun muna makaranta ake kiransa da Dr Sabir Yana matukar so ya Zama likita"
Liyah Tace "Kaai kunbi Kun dami mutane da wani Wai sabir, Ni wallahi ko kad'an guy d'in baya burgeni"
Daniyah tace "Kin ma Isa kice baya burge ki, kina ganin had'edden guy gashi kyakkyawa Mai structure irin wanda mata suke so"
Khadija tace "Nima dai haka na gani, Wallahi Ni kaina Yana burgeni gashi da ilimi both boko da addini Wallahi Sabir ko makiyinsa ne yasan yayi Saida yaki fad'a sabida kiyayya irin ta Makiya"
Liyah baki ta tab'e Tace "well kunsan fa shi ra'ayi rigace ko wa da irin tasa Ni dai bai min ba"
Daniyah Tace "Kanki akeji"
Ta amsa da "Ko Kuma naku ba, tunda bai ma San kunayi ba, Kinga tashi Muje mu shirya Muje muyi registration d'in Nan"
Khadija Tace "Yauwa dama so nake na tambaye ku me zaku cika ne?"
Daniyah Tace "Kin sani da son aikin asibiti Zan sa Medicine first choice sannan pharmacy second choice"
Liyah Tace "Ni Kuma Law Zan saka sannan na biyun na sake sa musu Law"
Khadija Tace "Yauwa hakan ya kamata kiyi, Daniyah Kema fa hakan ya kamata ki Sa musu hakan zai nuna musu kina son abin in yaso sai ki Sa pharmacy a third choice"
"Toh shikenan aunty Khadee Zan gyara Bari Muje mu shirya kin San ana layi sosai"
Khadija tace "Chaap! Ai Ni Zan fad'a muku"
Dariya suka Yi had'e da mikewa suka nufi saman su, bayan sun shirya suka Shiga d'akin mummy suka mata Sallama sannan sukayi wa Granny Sallama ta musu fatan "Allah ya tsare ya Kuma bada Sa'a" dake Daddy baya Gari, sukayiwa khadija Sallama ta musu fatan Alhairi,Kai tsaye suka nufi parking space driver ya Kai su CBT center suka samu layi sosai har sai daf da maghrib suka gama.
Suna shigowa parlor suka tarar ba kowa da alama sun Shiga yin sallah ne don suna shigowa unguwar suka ji an Shiga sallah Kai tsaye d'akin su suka nufu a gajiye Daniyah ta Shiga ban d'aki ta Watsa ruwa sannan ta d'aura da alwala, Liyah ma hakan tayi duk su biyun kayan bacci suka sa Riga da wando Liyah nata jaa Daniyah Kuma pink" (da alama favorite colors d'in su Kenan).🤔
Kasa suka sauko suka tarar da Momy, Granny da Khadija na zaune suna kallo, Mommy na ganin suna tace "Aah! my twins yaushe kuka shigo?"
Murmushi Liyah tayi tace "Mommy tun d'azu mun shigo gidan shiru shiyasa muka haura sama muka watsa ruwa"
Granny tace "Daniyah me Haka kin wani yankwane kamar karkashin da baida gata?"
"Granny Wallahi tsantsar gajiya ne ga yunwar da nake ji"
Dariya Liyah tayi tace "wato akwai karkashin da baida gata Kenan?"
Granny Tace "Eh Mana"
Mummy Tace "Ayya sannu da gajiya kam Tashi Muje dining nayi serving d'in ku"
Khadija Tace "A'a Aunty zauna Bari Ni nayi serving d'in su" sai ta mike Mummy Kuma ta koma ta zauna, suna zuwa dining table Shiga zuba musu abincin patan doya ne Taki kayan had'i gashi an sa masa alayyahu, Liyah na gani ta lashe baki Tace "Wow! Girkin yau don ni akayi"
Khadija Tace "Aci dai a hankali" babu Wanda ya amsa tunda suka faraci babu wanda yace kala har sai da suka koshi sannan suka Sha lemon kwalba, sai suka dawo parlor Suma ayi kallon dasu, sai Yusuf da Huzaifa suka shigo da Sallama a bakin su, bayan sun gaida su, Huzaifa yace "Sisters ya registration din dai? Kun Samu Kun Gama ko?"
Liyah Tace "eh wallahi Amma fa dakyar"
Yusuf yace "tunda Kun gama ai da sauki, saura jarabawar Allah ya bada Sa'a Kuna point fiye da yanda ake bukata"
Duk suka amsa da "Ameen"
A yaune