Showing 261001 words to 264000 words out of 287659 words
Chapter 88 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) Complete BY By Boss Bature .txt
magana, to me zata ce masu? Itama fa A tsoroce take da abunda ya faru na mutuwarsu Unaiza.
Muryar Rubina a hargitse tace"Babban abunda nake jimawa, Ƴan uwan mu da aka kwashe Shin suna araye ko sun mutu, bamusan a wani hali su ke aciki ba, Tun da yanzu mun fahimci cewa kashe mu ake yi, Lalata rayuwarmu ake yi a kwashe wani sashe na jikin mu! Kamar yarda aka yi ma Unaiza, Da Majnoon......." Bugun zuciyar Angel ne ya ƙaru tunawa da Mazan su da aka kwashe, ba ita ba Hatta su Deeja damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Tabbas Suna fuskantar barazana a cikin rayuwarsu.
"baƙin Cikin da mu ke ƙunsa da barazanar da muke fuskanta sun isa su sa zuciyoyin mu su buga mu mutu" Eve ce tayi maganar tana faman huci, idanuwanta a zazzare, ruwan hawaye ne kwance a cikinsu. Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, mutun biyar ne basu tanka ba, sai da su ka yi mai isar su tukunna Deeja ta miƙe cikin kakkausar murya ta soma magana tana duban kowan nan su.
"Na yi mamakin jin maganganun da harsunan ku su ke furtawa, saboda abun da ya faru ne yasa ku ke kokwanto Akan Addinin da Angel tazo mana dashi, Kun bani kunya duk da na fahimci cewa ba'a cikin hayyacin ku kuke ba, banaso mu yi abunda zamuyi danasani acikin rayuwar mu, Angel ba ita bace silar halin da muka shiga ba, Akan me za ku dinga ɗaura mata nauyin komai akanta! Yarinyar nan fa ƙanwar mu ce, babu wanda bai girmeta ba a cikin mu...."
Numfasawa Deeja ta yi a yayin da take bin fuskokin su da kallo.
"Ya ku ke so tayi da ranta ne? Kalaman ku zasu iya sanyawa ta zauce, itama fa tana jin raɗaɗin da mu ke ji, saboda ta ɗaurawa kanta nauyin kula da rayuwar mu, so ku ke ku ƙara sanya mata damuwa har zuciyarta ta buga mu rasa ta? Meyasa za ku yi kokwanto akan addinin da tazo mana dashi? Saboda kun ji shiru har yau Allah bai kawo mana ɗauki ba? Ƙaddarar mu ce tazo a haka, ba lallai bane mu moriya rayuwar duniyar nan ba, amma ku tuna abunda Angel ta faɗa mana, ko kun manta ne, zai iya yiwuwa namu jin daɗin ba anan yake ba, sai ranar da muka koma ga mahaliccin mu! Itafa wannan rayuwar duniyar ƙanƙanuwa ce jin daɗinta na wucin gadi ne, kowa zai mutu ne, damu da wanda ke rayuwa awajen kurkukun nan da waɗanda suka azabtar da rayuwar mu, kaf zamu koma agare shi ne, mutuwa dole ce, zamu mutu zamu koma ga Allah, za'ayi mana hisabi tsakanin mu dasu! Allah zai bi mana haƙƙin mu, zasu ɗanɗani kuɗarsu, Ai mu abun farin ciki ne agare mu, Haƙƙinmu ya rataya akan wuyan waɗanda suke sarrafa rayuwar mu, don haka daga yau bana son wani ya ƙara yin kukan mutuwa acikin mu, Mu sanya wa ranmu cewa dole mu rasa wani acikin mu, ko muna so ko ba mu so, dole mu mutu, Mu zama masu tawakkali kada mu butulce wa Ubangijinmu, Abun da na fahimta wanda ba lallai bane ku fahince shiba, Allah shine ya ƙaddara zuwan Angel a gidan kurkukun nan donta sanar damu komai agame dashi, yanzu mu musulmai ne, kuma munyi imani da Allah, don haka babu gudu babu ja da baya, Duk runtsi duk wuya kada mu kuskura Mu rasa ƙwarin giwar da mu ke da shi, tsakanin mu da Angel sai godiya, Allah ya saka mata alkhairi, Allah ya bata ikon cigaba da taimakon mu...."
Kalaman Deeja sun sanyaya zuciyar Angel, Jikin kowan nan su Ya yi sanyi, sun yi danasanin maganganun da suka soma gaya mata, kusan atare suka haɗa baki suna bata haƙuri haɗi da lallashinta, hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalinta yayi ba, har lokacin bata ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul ba'
Deeja tace masu su share hawayensu, Su yi rayuwar su tamkar babu abunda ya faru dasu, suka masa mata da toh, Duk da sun san abune mai wuya su dawo kamar yarda suke ada, A ranar sun ɗan samu sunci abincin Da Jamimah ta ajiye masu a cikin kwando, Bayan sun kammala ci, Kowan nan su ya yi wanka, A saman gadajen su suka kwakkwanta, zuciyoyin su a ƙuntace.
Rayuwar prisoners ta zama abun tausayi Cikin kwanakin nan, jimamin rashin ƴan uwansu ya hanasu sakat, Babu wasa babu dariya, kullum fuskokin su a bushe su ke, abu ɗaya ne su ke yi su ji daɗin shi, su kuma samu natsuwa da kwanciyar Hankali, Karatun qur'ani da Angel ta ke yi masu tsakar dare, a lokacin da take samun damar yin shi murya abuɗe ba tare da ta samu targarɗa ba, tasha ware kanta ita kaɗai, Ta ke6e a sashen toilet ɗinsu, ta ɗaga hannayenta sama hawaye nabin fuskarta, ta dinga roƙon Allah akan ya taimaka mata, kada yasa taji kunya a idanuwansu, ya agaza masu yajiƙan su, Ya kawo masu mafita ko dan taci ka masu alƙawarin data ɗaukar masu na ku6utar dasu daga Cikin kurkukun ƙaddara!
Ta zama abun tausayi, ga duk mai imani idan yaga yadda ta ke roƙon Allah sai ya matse mata ƙwalla. dukkan wasu ladubban yin addu'a ta iyasu, Saboda an koyar da ita, mutun biyun nan sun bata gudummuwa a cikin rayuwarta, shiyasa bazata ta6a mantawa dasu ba, mutun na farko Mahaifinta Tajuddeen, nagartaccen uba wanda ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, lokacin da Unaiza ta bata labarin nata uban daya tarwatsa rayuwarta, sai taji ta ƙara ƙaunar daddynta, kuma har aranta taji cewa Mahaifinta bazai ta6a iya sadaukar da ita ba, ɗan adam ba abun yarda bane, amma ita ta yarda dashi har cikin ranta, saboda tasan halin daddynta ita shaida ce akan shi, ko dabba bazai Iya sadaukar ba balle ita da ya ɗauke ta tamkar ranshi! Mutum na biyu da bazata ta6a mantawa ba, ANEELERH CE, matsayin da ta bata a cikin zuciyarta na mahaifiyarta ne data gudu tabarta, Aneelerh uwace ta gari agare ta, dayawa wasu abubuwan da Angel ta iya da suka shafi addini da rayuwar duniya, Aneelerh ce ta koyar da ita su, hatta karatun makaranta idan aka yi mata, Aneelerh ce ke ƙara koya mata shi idan daddynta bai nan, Tana matuƙar son aunty aneelerh, kuma bata zarginta cikin waɗanda su ka sadaukar da ita! bayan aunty aneelerh da daddynta babu wani shege da take tunanin zata ɗaga ma ƙafa, muddin ta fita daga cikin kurkukun nan sun shiga uku, Hatta hajiya Adama da uncle Abdallah, da Alhaji ubaid kakanta, da maigadin gidansu, da abokan dadynta na wurin aiki, da makwabtan dake a kusa da gidansu kaf ɗinsu abun zargine awurinta, Ba wanda ta cire a cikinsu, dama kawai take jira ta samu, duk wani mai hannu acikin sadaukar da su, sai ta binciko su, alwashine ta ɗaukarwa kanta, shiyasa bata son ta dawwama agidan kurkukun saboda idan har tana aciki bazata ta6a Iya gano su wanene shuwagabannin kurkukun ba, Dole sai tana awaje zata samu damar gano munafukan, ta ci buri akan su, musamman mahaifin Unaiza JAN WUYA, wannan ɗan tahalikin duk ranar daya bari Angel ta dira ƙafarta daga cikin kurkuku, sunanshi matacce, muddin ta gano shi.
Tuntuni Angel ta ɗauko Jotter ɗin unaiza da ta ajiye mata a cikin toilet ɗinsu, tare da pant ɗin data bata kyauta, tana matuƙar son pant ɗin musamman da ya fito daga hannun Unaiza, yanzu haka pant ɗin yana sanye a jikinta ko wanke shi ba ta yi ba, saboda ta shaida tsaftar da ke a jikin shi, daga gani ranar da za'a kawota kurkukun ta sanya shi a jikinta, saboda sabuntakar shi. a cikin backpact ɗin Unaiza ta sanya jotter ɗin tare da biro din duka ta tura su ciki ta zage zip ɗinta, tana fatan Allah ya bata damar isar da wasiyyarta.
Bayin Allah sun zubama sarautar Allah ido, almost two month Yau, babu labarin su Haris, Danish kuwa yafi kowa daɗewa don Yana acikin wata na uku da aka tafi dashi, tsakaninsu dasu addu'ace wadda ba fashi, kullum ne sai sunyi masu ita tare da waɗan da su ka rasu.
💔PRISONERS💔
Wuraren marece, Angel tana kwance saman gadonta, ta rungume pillow a ƙirjinta, ba zaka ta6a gane awani hali ta ke a ciki ba, ta lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci, Azeeza ce kwance a gefenta saman gadonta, Jamimah tana asaman bayanta ta haye ta ɗaura kanta, sun zamar mata alaƙaƙai, Kullum suna atare da ita, tana matuƙar son jinsu a tare da ita, babu mai yin magana a cikinsu, Parveen tana a kuɗundune cikin bargo saman gadon majnoon, kullum nan take kwana, da hannunta ta wanke jinin da ke abargon shi, ta gyara gadon taci gaba da kwana saman shi, saboda ƙaunar da ta ke yiwa majnoon ɗinta, wani lokacin har pillown shi ta ke yi ma wasa a matsayin majnoon kamar mai ta6in hankali.
Sarah na a zaune saman shimfiɗarta tare da Hibba da eve sai yasmin da rubina, babu mai magana acikin su duk sun yi zugudum, Deeja tana a kwance saman gadon Haris idonta na fuskantar ceilling, kowa dai da abunda ke damun shi, itama Hanna tana a naɗe saman gadonta.
Saukowa batul ta yi daga saman gadonta, Ta nufi sashen toilet ɗinsu, ba tare da kowa Ya ankara da ita ba, shigarta ke da wuya Angel ta buɗe idanuwanta muryarta asanyaye tace da jimamah ta sauka zata miƙe, zame jikinta ta yi daga na jamimah ta sauko daga saman gadon, Jikin ta duk ba ƙwari ga ramar da ta yi.
Sashen toilet ɗinsu ta nufa, tana shiga ta soma jin shessheƙar kukan batul, Hankalinta yai mugun tashi, bata zo da niyar tabi bayanta ba, tunawa da furennin dake a cikin tukunyar fulawar nan ne yasa ta zo sashen makewayin nasu, tun bayan rasuwar Unaiza babu wanda ke ba furennin ruwa saboda halin da su ka shiga, Cikin sanɗa ta nufi ƙopar toilet ɗin da batul ta shiga, A hankali ta tura ƙopar tare da Leƙa kanta ciki, karaf idanuwanta su ka sauka akan Batul da ke ta faman leƙa cikin wandonta da ta zame kamar wani abu ta ke dubawa,
Jin motsin shigowar mutun yasa ta firgice ta ɗago da idanuwanta fuskarta sharkaf da hawaye suna haɗa ido da Angel tasha jinin jikinta, da sauri ta gyara zaman wandon jikin ta.
"Batul me ya ke damun ki? Na jiyo shessheƙar kukan ki ne," wahalallan yawu ta haɗi, ba tare data furta mata komai ba.
Hakan ba ƙaramin ɗaga ma Angel hankali yai ba, fargabarta kar ace wani abu ne ya sami gabanta shiyasa ta ke kuka
"Ƴar uwata rabin raina, dan Allah ki faɗamin meke damun ki, Na yi maki alƙawarin bazan faɗama kowa ba, Hankalina ya tashi dana ga kina duba wandon Jikin ki, ina tsoron ace wani abu ne ke damun ki"
Ta ƙarasa maganar yayin da take nufar batul, girgiza mata kai ta dinga yi muryarta Ƙasa ƙasa take faɗin"Kada ki matso kusa dani Angel, babu abunda ke damuna, lafiyata qalau....." adabarbarce ta yi maganar.
"ƙarya ki ke yi min batul! Wai har ni zaki 6oye ma abunda ke damun ki? Me ki ka ɗauke ni ne? Nifa ƴar uwarkice, idan baki faɗamin ba wa zaki faɗa mawa, ni dama tun da aka dawo mana dake ban yarda dake ba, meyasa zaki 6oye min abunda su ka yi maki"? Fuskarta a ɗaure ta yi maganar, kafin taci gaba da cewa"Allah yajiƙan unaiza ba ta mutu ba sai da ta sanar dani komai daya faru da ita, don haka ki daina 6oye min, idan har kina son zaman lafiya to ki faɗamin me aka yi maki!! Cikin shessheƙar kuka batul tace"nifa ba abunda ya faru dani, ki daina tambayata bana so ki tafi kawai," Jinjina kai Angel tayi tare da sassauta muryarta"Its ok xan tafi batul tun da baki so in sani," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi ƙopar fita, ajiyar zuciya batul ta sauke duk a tunaninta Angel tafiya zata yi tabar toilet ɗin ashe ƙopa ta je ta rufe don kada sauti Ya fita, jamlock Ta sanya ta datse ƙopar da kyau, fuskarta a ɗauke ta juyo ta kalli batul dake manne jikin bango, jikinta sai kerma yake yi
"Zaki Faɗamin meke damun ki ko kuwa kin fi so in bi ta ƙarfi"! Shiru batul bata tanka mata ba, sai faman zazzare mata idanuwanta take Yi, Cizon le6e Angel tayi tare da naɗe hannun rigarta, gadan gadan ta nufi batul, ganin tana tunkarota yasa batul ta bar jikin bangon ta watsa da gudu da niyar ta fuce, Cikin rashin sa'a Angel ta cafko Sumar kanta, ta janyota da ƙarfi ta maka ta jikin bango ta yadda bazata ji zafi ba, Faɗane ya kaure a tsakanin su, Sai nishi su ke yi sun cakumi juna, ga jikin nasu duk ba ƙwari, tuni sun haɗa uban gumi, ƙarfi Angel ta sanya wurin kada batul ƙasa, tare da sanya hannu ta damƙi wandon jikinta ta soma kiciniyar zame mata shi daga jikinta, duk don ta gane ma idonta abunda batul ke 6oye mata........."
💋PRISONERS💋
Ba ta kai ga ƙarasa cire wandon ba, sautin dariyar Batul ta janyo hankalin ta ga kallon fuskarta, tsabar mamaki ne yasa Angel ta sakar mata trouser ɗinta, ta tsaya tana kallon ikon Allah sai tiƙar dariya ta ke yi kamar ba ita bace ta ke ku ka.
"Batul bana son iya shege, menene haka? Dariyar me ki ke yi mini? Kin fara sanya mi kokwanto akan ki" ta yi maganar tana binta da kallon tuhuma yunƙurawa batul ta yi tare da miƙe wa ta zaune, Sumar kanta duk ta tarwaste har ta saman fuskarta, tana dariya ta sanya hannu tare da yaye sumar ta mayar da ita bayanta, A hankali ta ke bin fuskar Angel da kallo, ta haɗe rai har wani huci ta ke yi.
"Meyasa ki ke yi mini haka? Ko dan saboda kin ga na damu da ke ne? rai a6ace ta yi maganar, shiru batul taƙi magana sai kallonta ta ke yi,
Gyaɗa kai Angel ta yi"shikenan tunda na zama abun tsokana a wurin ki zan tashi in koma ɗaki, don't ever expect me to worry about you anymore."
Ƙoƙarin miƙewa ta yi da niyar ta fuce daga cikin toilet ɗin, muryar batul ce ta dakatar da ita.
"Ba za ki iya daina damuwa dani ba, that's why ki ka sanya mini ido, ko bacci nake yi idon ki a kaina, duk wani motsi idan na yi sai kin ji ba'asin shi, irin wannan ƙauna haka........" ta yi maganar da zolaya, hakan ba ƙaramin 6ata ran Angel yai ba.
"Nifa ba abunda ke damuna, lafiyata qalau, don kin ga ina bincikar trouser ɗina shiyasa ki ka ɗaga hankalin ki nasan me ki ke tunani nima abunda na ke tunani kenan, sai dai abun da mu ke hasashe bashi ba ne, It's just a rash
ya fito min a wurin, ya addabe ni da ƙaiƙayi, ɗazu dana kwanta bacci, nayi mafarkin Unaizah, hankalina na ya tashi, a lokacin bansan ƙurji bane nadai ji zafi a wurin, gani nake kamar zai yi irin na unaiza, kin ji dalilin dayasa na shigo toilet ina shessheƙar ku ka tare da bincika wandona don inga menene awurin daya haddasa min jin ƙaiƙayi, ban yi tsammanin za ki biyo ni ba, amma tunkafin ki shigo naji motsin mutun nan take raina ya bani cewar Ke ce, shiyasa na ƙara sautin kukan nawa don in firgitar da ke......." bata ƙarasa maganar ba, ta tuntsire da dariya ganin irin kallon rainin wayon da Angel ta ke Yi mata, tana a tsaye ta ruƙe qugu.
"Idan ba ki yarda da magana ta ba, zan nuna ma ki" ta yi maganar tare da sanya hannu tana ƙoƙarin zame wandon jikinta.
"Bana so ba sai na gani ba" ta faɗa tana harararta
"Idan ban nuna maki ba hankalin ki bazai kwanta dani ba, " bata jira jin me zata ƙara ce mata ba, ta yi saurin zame wandon kaɗan ta yadda tsiraicinta bazai baiyana ba, ƙaramin ƙurjine yayi jawur dashi daga gani ba ƙaramin zafi ya ke yi mata ba, Ajiyar zuciya Angel ta sauke hankalinta har ya kwanta, gyara wandon batul ta yi ba tare da ta ɗauke idon ta daga kan fuskar Angel.
Zuƙunnawa Angel ta yi agabanta"Idan har ba ki so raina ya 6aci to ki faɗamin me aka yi maki tsawon time da Giants su ka ɗauke ki," ganin irin kallon da batul ke yi mata ne yasa ta kuma cewa"Kada ki ce zaki 6oye mini komai batul, idan har baki so nima wata rana in 6oye maki wani abu dangane dani, "
A tsanake ta soma magana tana kallon cikin idonta
"Angel bayan an ɗauke ni daga cikin ku, kamar yarda na faɗa maku, ɗaki ne su ka kaini ni kaɗai, a saman gadon su ka kwantar dani, bakomai zan iya tunawa ba, na dai san sun cire min kayan jiki na, sannan Naji ana shafa jikina ta ko'ina, ba tare dana iya motsawa ba, kafin daga bisani naji ana tsotse......." bata ƙarasa ba ganin yadda Angel ta runtse idanuwanta, muryarta ƙasa ƙasa tace mata ina sauraronki ki ci gaba da magana
"Jinin da ke fitowa ta gabana shi naji ana tsotse shi"
Zuciyar Angel tuni ta soma tashi.
"Naji zafi sosai kamar zan zauce, tsawon lokaci Ana tsotse shi har zuwa time da naji bacci ya ɗauke ni, daga nan bansan me ya faru ba, lokacin da na farka banga komai ba, sai kayan abincin da aka ajiye mini Saman table, a bunda ban yarda dashi ba a cikin kayan abincin akwai wani luluyayyan abu fari fat guda ɗaya aka ajiye shi a tsakiyar tsokokin Nama......."
Ba ta kai ƙarshen zancen nata ba, Angel ta yi saurin katse ta da cewa" Allah yasa ba ki ci ba" jin haka yasa ta haɗiyi yawu fuskarta da alamun damuwa tace"Naci Angel, yunwa nake ji sosai a lokacin, komai sai da na ci"
Angel tace"amma bayan kinci sai me ya biyo baya"?
Numfasawa Batul ta yi kafin taci gaba da cewa"bugun zuciyata ne ya ƙaru, na dinga jin faɗuwar gaba,