Showing 6001 words to 6886 words out of 6886 words
Chapter 3 - KUNDIN ALAJABI Book 2 Complete by Mansur Usman Sufi .txt
Aljani Sulsaini ya yi ƙara luhhh! Domin ya zillewa ifritan, amma sai hakan ya faskara domin kadoni ya kai ga hakan wani daga cikin ifritan me nacin tsiya ya kafta masa sara a kafaɗarshi, saboda matuƙar ƙarfin sara sai da Jauharul-layal ya kurma wawan ihu, saboda raɗaɗi da zugin da ya ji.
Sa’adda jaruma Sulairat taga halin da muke ciki, kuma ta fahimci cewa a koda yaushe ɗayanmu na iya raya rayuwar shi, sai kawai ta shiga amfani da ƙarfin shirin tsafi amma ya zamo a banza, domin da idan ta yi TSATSUBA ta turawa ifritan Kibbau na huta da zarar sun doshi inda suke sai suka zama farin haske su ɓace ɓat!
Ana cikin wannan wannan fafatawa ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya tayi duhu dunɗum! Tamkar DARE BIYU ne ya haɗu waje guda, kuma aka dinga kwantsama tsawa da walƙiya kai ka ce za’a kece da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya.
Daga can sai aka ga wata shirgegiyar halitta ta bayyana a sararin samaniya, halittar tana da matuƙar girma fiye da aljani Jauharul-layal, tana ɗauke da fuka-fukai goma a tsakiyar kanta tana ɗauke da wani zabgegen ƙaho mai kama da na rago, batun munin fuskarta kuwa sai abin da idanu suka gani kawai, a gadon bayanta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi. Kaico! Haƙiƙa wannan halitta ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Darmanu manzon uwar mayu Ummul-Sharri, wanda ta tura domin ya ɗauko mata taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar.
Sa’adda kowa ya yi arba da aljani Darmanu sai aka tsayar da yaƙi kallo ya koma kanshi.
Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo sai daga bisani aljani Darmanu ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da saukar aradu wacce ta ɗimauta duk wata halitta dake wajen hatta ifritu Sulsaini da yaranshi, a lokaci guda ya tsuke bakinshi ya fara magana cikin wata irin kakkausar murya mai kama haniniyar doki yana mai cewa
“Ya ku waɗannan ƙananan halittu ma’abota ƘARAR KWANA ku yi sani cewa ban zo nan domin kallon fafatawar da kuke yi ba, face sai domin ya karɓi taswirar fadar sarkin bokaye domin na kaiwa uwar matsafan duniya Ummul-Sharri, kira na a gare ku shine ku gaggauta miƙo min taswirar cikin ruwan sanyi domin na yi maku kisa mafi sauƙi ba tare da kun sha wahala ba, ta hanyar da daddatsa sassan jikkunanku.
Kafin Darmanu ya gama rufe bakinshi ifritu Sulsaini ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka masa tsawa ya ce “ ya kai wannan maƙetaci kuma wanda rarraunar zuciyarshi ke yaudarar sa ka ji sani cewa ka tafka babban kuskure, da kake tunanin za ka ƙwaci taswira daga hannun Jaruma Raudatul-abyad, bayan muna gab da mallakarta, wato kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi”.
Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Sulsaini sai aljani Darmanu ya fusata ainun, idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe, kawai sai ya miƙa hannunshi izuwa sama sai ga wata zabgegiyar takobi ta bayyana ta haske, take ya yi ɗauki izuwa kan Sulsaini da tawagarshi, ana haɗuwa aka yi KARON BATTA, nan fa aka garƙame da sabon gumurzu mai matuƙar muni ban tsoro gami da tashin hankali, a wannan karon sai artabun ya canja salo, domin a wannan karon duk inda aljani Darmanu ya sanya a gaba sai dai kaga yaran ifritu Sulsaini na sheƙawa barzahu, takobinshi na raba sassan jikkunansu.
Nan fa muka shiga raba idanu domin ba su san wane ɓangare zamu shigarwa yaƙin ba, tun da dukkanin su abokan gabarmu ne.
Muna cikin wannan hali ne wata dabara ta faɗo min, koda samun mafitar sai kawai na yiwa aljani Jauharul-layal inkiya ta wutsiyaar idanu, koda ya fahimci abin da nake nufi sai ya faki idanun TAWAGAR ABOKAN GABA ya kaɗa fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! ya keta cikin gajimare ya fara tsala azababban gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya muka ɓace ɓat! Har muka daina hango so.
Lokacin da muka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna gudun tsira da rayuka, sai ƙarfin gudun Jauharul-layal ya fara raguwa ainun saboda gumurzun da aka sha, domin hakan sai aka yanke shawarar mu yada zango domin mu huce gajiyar dake tattare da mu, cikin hanzari Jauharu ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! Ya sauka a turba, inda muka saukar ya kasance daji mai tattare da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu gami da sarƙaƙiya, muna sauka ne dukkaninmu kowa ya sha jinin jikinshi, domin da ganin dajin ba a rasa miyagun halittu masu cutarwa ba.
Da yake akwai inuwar bishiyu sai ya zamana cewa bamu kafa tanti ba, aka fito da abin kalaci kowa ya shiga kimtsa cikinshi.
A wannan lokaci ne jaruma Sulairat ta duba mu tayi gyaran murya sannan ta ce “tun da a halin yanzu dukkaninmun mun samu natsuwa zan cigaba da baku labarin abin da ya wakana da abbana tare da manyan sarakunan duniya uku, inda ta ɗora da hikayar kamar haka:-
Mu haɗu a littafi na 3 domin jin cigaban wannan kayataccen littafi
Mansur Usman Sufi
08137237071