Showing 3001 words to 4479 words out of 4479 words
Chapter 2 - MAKASHIN MAZA Book 1 Littafin Yaki Complete by Abdul'aziz Sani Madakin Gini .txt
sabon tunani. Take ya ji duniyar gaba daya tai masa zafi, sai da ya sami kusan rabin sa'a sannan ya dago kai ya dubi boka Zafaratu yace "Ya sarkin bokaye, hakika na ji duk bayaninka kuma na yi tunani na tabbatar da cewa bani. da wata mafita face na bi shawararka, saboda hak na amince zan koma gida na sake neman taimakon Doña Arjalu, kuma zan amince da dukkanin sharuddan da ya shimfida mini."
Da jin haka murna ta kama boka Zafaratu yace "Hakika ka yi tunani mai kyau, kuma idan har ka yi
hakan ka tsare mutuncinka da namu daga sharrin abokan gabarmu mabiya addinin Musulunci"
A cikin wannan dare sarki Larmisu da matarsa Lamsiya tare da 'yan rakiyarsu suka kimtsa suka koma garin Ban nur. Da zuwa kai tsaye suka wuce izuwa gidan boka Arjalu, sarkı Larmisu ya gabatar da bukatarsa.
Yayın da Arjalu ya ji bukatar sarki, sai yai shiru ya sunkuyar da kansa kasa, jim kadan ya dago yace "Ya sarkin sarakai, ka sani cewa kamar shekaru hudu da suka gabata na taba zuwa gareka na nemi wata alfarma amma ka ki amincewa, wannan alfarma ba komai ba ce face ka bani auren kuyangarka Samali, idan har kana so na baka aljani Daskin sai ka bani abu uku, abu na farko shi ne ina so ka daura aurena da kuyanga Samali, abu na biyu ina so ka raba dukiyarka gaba daya kasu biyu ka bani kaso guda, abu na uku ka raba kasarka biyu ka bani rabi na mulka, in dai kai haka zan baka aron aljani Daskin ya je yai maka wannan aiki." -
Sa'adda sarki Larmisu ya ji wadannan sharadai sai bakin ciki ya mamaye zuciyarsa, bai san sa'adda kwalla ta zo masa ba, duk tashin hankalin da ya shiga a baya _sai ya ji kamar ruwan sanyi ne akan wanda zai shiga nan gaba idan ya rabu da wadannan abubuwa guda uku, wadanda boka Arjalu ya bukata daga gareshi. Abu na farko dai ita kuyanga Samali tun tana shekara shida
sarki Larmisu ya kwato ta daga hannun wani sarki da Karfin tsiya, ma'ana sai da ya yake shi. Samali kyakkyawar yarinya ce wadda bokayen duniya na wannan lokaci suka tabbatar da cewa duk sarkin daya aureta ba shi ba talauci har bada, kuma ba za'a taßа cinsa da yaki ba. Bokayen sunce ba za'a auri Samali ba sai ta kai shekara ashirin a duniya, a halin yanzu shekararta goma sha takwas kenan yana kowonta, a yanzu kyawun Samali ya bayyana sosai karara a fili yadda duk namijin daya dubeta sai ya kamu da sha'awarta. Bakin cikin sarki Larmisu shi ne yanzu saura shekara biyu lokacin daurin aurensu da Samali yayi gashi boka Arjalu zai raba shi da ita. Abu na biyu wanda ya sosa ran sarki Larmisu shi ne ya tabbatar da cewa idan ya raba dukiyarsa da kasarsa biyu ya baiwa Arjalu rabi, ai tamkar sun zama daya ne. Idan suka zama daidai kuwa babu mamaki wata ran Arjalu ya neme korarsa daga Bar nur ya mamaye garin gaba daya. wannan shi ne abin da yai ta kai komo a cikin zuciyar sarki Larmisu.
"Ya sarkin sarakai lafiya na ji ka yi shiru?" Boka Arjalu ya tambaye shi
Larmisu ya dago kai ya dube shi sannan ya dubi Lamsiya yai shiru, jam kadan kuma ya sake dago kai yace "Ya kai wannan boka kasan ance aikin mai shawara baya baci sai dai ba sirri, na ji duk sharaddan
da ka shimfida mini, kuma zan je na yi shawara, zaka ji daga gare ni gobe da yamma."
Take su ka yi sallama, sarki Larmisu da Lamsiya suka tafi gida, dakarun rakiya na biye da su.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Larmisu da boka Arjalu, bayan ya dawo daga ziyarar boka Zafaratu na birnin Hazaras.
***
A can birnin Kashmir kuwa rayuwar Bilal ta kasance cikin yawan bautar Allah dare da rana, yana zaune ne tare da iyayensa wadanda suka kasance ma abota ilimin addinin Musulunci, da yawan jama'a sukan zo garesu daukar karatu fanni-fanni, sunan mahaifin Bilal Ababakari, kuma sunan mahaifiyarsa Hasiya.
Ababakari ya kasance mai farauta, yayi tafiye- tafiye zuwa kasashe da dama a duniya, saboda haka ba shi da tsayayyen wurin zama guda. Wannan sana'a tasa ita ce ta kawo shi birnin Kashmir, amma usulinsa ya fito ne daga yankin kasashen larabawa, kuma yana da cikakken tarihin kakannin kakanninsa a rubuce cikin wani kundi. Wannan kudi na tarihinsa ya na ajiye ne a cikin wata farar akwatu wadda aka yi ta da tagulla.
Tun Bilal yana yaro karami ya taso ya ke gının wannan akwatu a tare da mahaifiniša, kuma bai tafa ganiu ranar da ya bude ta ba. A duk abubuwan da Ababakarı ya mallaka a duniya babu abinda ya fi taka tsantsan da shi sama da wannan farar akwari, haria matarsa Hasiya bata taba bude wannan akwati ba, bare taga abin da ke ciki, duk sa'adda Ababakari ya so bude akwatin, ya kan bari dare ya raba sannan ya budeta. wannan al'amari ba karamin barwa iyalansa mamaki ya ke ba. shi dai Bilal ya kudurce a ransa komai daren dadewa in dai wannan akwatun na nan sai ya ga abin da ke cikinta, duk da ya san mahaifin nasa ba zai amince da hakan ba. Ita dai akwatun an rufe ta da wata katuwar kuba ta musamman, wadda Bilal bai taba ganin katuwar kuba irin ta ba. bare ya nemo mukulli da zai iya budeta.
A halin yanzu Bilal ya cika shekara ashirin da biyu cif-cif a duniya, kuma ya sami ilimin addinin Musulunci mai yawa, a bangaren sana'a kuwa ya kware akan farauta, domin sau tari tare suke tafiye-tafiye da mahaifin nasa. Duk sa'adda Ababakari zai vi tafiya yakan tafi tareda farar akwatunsa, bai taba barinta a gida ba.
Wata rana tafiya ta kama Ababakari wadda ya so yayita tare da Bilal, amma Bilal ya kamu da zazzabi mai zafi. A bisa dole Ababakari ya hakura da ya tafiya da Bilal, ya bar shi a gida. Bayan Ababakari ya gama
shirya kayansa bisa rakumi a kofar gida, sar ya koma cikin gida domin ya dauko farar akwatun nan tasa, shigarsa ke da wuya aka aiko cewa ana sallama da shi. A wannan lokaci tuni ya dauko akwatun har ya iso zaure. ko da ya ji cewar wani abokin kasuwancinsa ne ya zo za su gana, sai ya ajiye akwatun a zaure ya fita da niyyar idan sun gama ganawa zai dawo ya dauka. Daman tuni a wannan lokaci yayi sallama da Hasiya da Bilal har ma yai masa addu'ar Allah ya ba shi lafiya. Bayan sun dan zanta tsawon dan lokaci sai suka rabu, Ababakar ya hau kan rakuminsa yai gaba.
Lokacin da Hasiya ta fara kokarin hada abinci a tsakar gida sai ta ji motsin akuya a zaure tana kusur- kusur. da yake wannan ba sabon al'amari ba ne sai ta ci gaba a aikinta. Jim kadan ta ji kursur-kusur din yayi yawa, don haka sai ta mike ta nufi zauren don tsoron kada akuyar ta kawo shara ta bata wurin, ai kuwa da zuwanta ta iske akuyar na ta kokawa da farar akwatun nan ta mijinta, a iya tunanin akuyar akwai sharar abinci a cikin akwatun domin an saba zubawa a cikin akwatun shara a daidai inda aka ajiye wannan akwatin.
Ko da Hasiya tai ido biyu da wannan akwati sai ta ji zuciyarta ta buga da karfi, cikin hanzari ta kori akuyar ta dau akwatin ta koma cikin gida tana mamakin dalilin da yasa Ababakari bai tafi da ita ba, shin mance akwatin yayi, ko kuwa yana sane ya barta? Kai sam-
in Ababakari ba zat taba barin wannan akwatin ba a azure yana sane, don haka babu shakka mantata yayi, amsar da Hasiya ta baiwa kanta kenan.
Yana daga kwance bisa shimfida a cikin daki ya ruke casbaha yana istigfari, ta shigo rike da farar akwatin a hunnunta, ko da idanunsa su kai arba da ita ya ga abın da ke hannunta sai ya mike zumbur kamar bai tuba ko da ciwon kai ba. cikin tsananin mamaki ya dubets yače "Unami ya akai Abba ya baki wannan akwatın!"
Hasiya ta yi murmushin jin dadin ganin ya mike zaune, tare da mamaki, sannan ta zauna daf da shi tace "Kai kuma ya akai ka samu lafiya yanzu-yanzu?"
Lokaci guda suka yi dariya "Wallahi ni kaina ban san yadda akai ba, ni dai ina ganin wannan akwatun a hannunki sai na ji kamar an yaye mini rashin lafiyar"
Hasiya tace "Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki shi ne mai bayarwa kuma shi ne mai hanawa"
"Haka ya ke Ummi" Bilal ya fasdl, sannan shi ma ya sake godiya ga Allah.
"Kamar yadda ka ga akwatun nan yanzu a hannuna haka nima na ganta ajiye a zaure, bana raba daya biyu mahaifinka ne ya manta ta, hakika na san zai yi matukar bakin ciki idan har ya tuno da cewa ya barta a
Mu haɗu a Makashin Maza littafi Na biyu Domin jin cigaban wannan kayataccen littafi.
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
08137237071