Showing 189001 words to 192000 words out of 201974 words

Chapter 64 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

02 Jun 2024

41584

ta ƙeƙashe ƙasa babu inda zata je sai taga dadin ta, dan dole suka dunguma zuwa ɗakin da aka kwantar dashi,da taimakin wani dr abokin Aslma don ɗakin ba'a bari a shiga Aslam baiyi niyar zuwa ba kawai dan yana jin nauyin Alhaji Abdur-rahman ne amma ba dan Allah yaje ba dan ko kaɗan baiji tausayin Dad ba kwata kwata mutumin ya sire mai, gani yake ma alhakin su ne ya kama shi na zuwa da yayi bagatatan ya musu asarar ciki. Alhaji Abdur-rahman ne gaba yana rike da hannun zee sai Aslam dasu Mami biye dashi, dukkannin su saida zuciyar su ta girgiza da ganin yadda Dad ya koma cikin abin da baifi awa ashirin da huɗu ba, wani gigitaccen ƙara zee ta saki tare da durkushe wa a gaban bed ɗin da Dad ke kwance, Asmah ma tuni ta fashe da kuka hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba, wai mutumin daya zo jiya ya nemi wulakansu haka, lallai Allah ba abin wasa bane, Mami ma sai dauke kwalla takeyi, na tausayin zee da mahaifin ta, Aslam kam take idanunshi suka kala sukayi jajur, duk yadda yake jin haushin Dad a zuciyar shi sai da ya tausaya mai, lallai ɗan Adam ba'a bakin komai yake ba, ganin yadda zee ke kururwa tana kuka, yasa Dr saurin basu umarnin su fita su bar mara lafiya shi kaiɗai kar su bata musu aiki, daƙer Aslam ya janyeta daga ɗakin, koda suka fito yace tazo ya kaita gida tayi wanka ƙin yarda tayi ta tafi, Asmah ma sarkin tausayi cewa tayi zata zauna tare da zee, ya kada dambu taliya amma suka ƙi bin shi, karshe shi da Mami ne kawai suka bar asibitin mami ta wuce da little can family hause dan zaman asibiti bai kamace shi ba. A nan suka wuni tare a asibiti sallah kawai ke tada su, daga inda suke zaune, sai bayan la'asa Alhaji Abdur-rahman ya musu abinci daga gida sa, , daga ita har Asmah babu wanda ya kalli inda abincin yake, saidai nan kuma Dad ya farka daga alluran barcin da aka mishi, sun so shiga su ganshi amma Dr ya hana ganin sun matsa yasa da'ker ya bar Alhaji Abdur-rahman ya shiga, ya samu Dad idanunshi a bude harass sai dai hawaye kawai yake zirararwa, ya tausaya mai amma hakan bai hana shi rufeshi da fada ba ya kuma sanar dashi abin da zuwan shi gidan Aslam a jiya ya janyo, karshe kuma ya daura da nasiha,daga yadda Dad ke kuka yana Neman gafarar shi,shi kamshi ya tabbatar yayi nadama sosai harda cewa a kira zee da Aslam ya nemi gafarar su, Alhaji Abdur-rahman ya hana tare da cewa taya bari ya kara samun sauki tukun, daga karshe ya koma barci saboda karfin magungunan da aka bashi yanzu bayan farkawanshi. Bayan isha'e Aslam da Abba da Alhaji baba suka zo asibe ko za a basuyi ba Alhaji Abdur-rahman shima ya dawo da ta masallaci . Mami ne data koma gida ta labarta wa Abba abun da ke faruwa shine fa ya sanar wa su daddy da Alhaji baba sun tausaya matuka duk da sunji tsiyar daya tafka Allah ya kama shi. Bayan sun gaggaisa Alhaji Abdur-rahman yace bari yaje yaji daga bakin Dr ko zasu iya shiga su ganshi dan ɗazu jikin da sauƙi, kafin ma ya kai ga tafiya wata nurse ta nufosu da sauri tana haki, dukkan su ido suka zuba mata zuciyoyin su na tsistsin kewa, tace "wacece zee da Alhaji Abdur-rahman da Aslam da karima a cikin ku." Zabura zee dake rungume jikin Asmah tayi ta mike, Aslam ne ya bata amsa da "gamu nan duka." Tace "Dr yace kuzo maza patient ɗin ku yana son ganin ku da gaggawa." Da sauri kuwa suka rufa mata baya dukkansu zuwa ɗakin, Dr ɗaya suka samu da nurse ɗaya akan Dad suna faman bashi taimakon da zasu iya, kimanin mintuna ashirin kenan da farkawanshi, tunda ya farka jikin shi ya ƙara rikice gaba ɗaya sai dai bakin shi bai mutu ba sunan zee da Aslam, Alhaji Abdur-rahman da karima, kawai yake kira a wahalce, ganin yanayin da yake ciki ne kawai yasa Dr ya zare mai karin ruwan da jini da duk wani na'ura dake jikin sa dan jikin shi ha bashi wannan mutumin kam da'ker zai kai labari, hakan daya gani yasa ya aikin nurse dinnan ta kira mutanen da yake nema watakila wasiyya zai bayar, da gudu zee ta karasa gaban shi tana wani irin kuka, mai ban tausayi, da'ker yace "Zainab mutuwa zanyi, ki yafe min." Ciki kuka tace "dadi na baza ka mutu ba in sha Allah zaka warke zafin ciwo ne yasa kake ganin kamar ajalin ka yazo." Murmushi yayi wanda ba kowa bane zai fahimci hakan saboda yadda fuskar shi tayi dameji, yace "mutuwa zanyi Zainab ni nasan abin da na hango, ina mijin ki yake." Aslam dake tsaye daga can baya idanunshi jajur ya karaso gaban Dad, kallon shi Dad yayi ya mika hannunshi guda mai lafiya ya kama hannun Aslam ya manna dana zee dake tsaye kusa da shi cikin maganar shi irin ta marasa lafiya sosai wanda sai mutum ya kasa kunne yake iya gane mai yake fada yace "Aslam kayafe min, nasan na cutar da kai na yi sanadin da ka rasa gudan jikin ka, amma dan Allah karka kulla ceni komai nakeyi akan soyayyar Zainab ce, itace jarabtata duniya tunda na haifeta nake bata wa mutane da yawa rai akan ta indai ita zatai dariya, Allah ya rarabceni da makahon so akan Zainab, kuma har yanzu dana ke kan gabar barin duniya daidai da kwayar zarra banji ɗigo na sonta ya ragu a zuciya ta, ga amanar Zainab nan na bar maka Aslam, duk duniya babu wanda take so sama da kai dan Allah ka kula min da ita ko bayan rai na, dan Allah badan halina ba." kafin ya samu daman kara cewa wani abu tuni harshen shi ya karye sai magana yake yi amma babu mai fahimtar shi, tuni zee ta ƙara ruɗewa tare da fashe da wani irin kuka ta faɗa jikin shi ganin haka yasa Aslam janyeta da karfi tana fisgewa ya fice da ita daga ɗakin, Asmah ma dake kuka Abba ya rike hannun ta ya fice da ita waje,Alhaji Abdur-rahman ne ya masto gare shi yana sharar kwallah ya kama hannun shi ya rike gam yana cewa "dan uwana insha Allah baza ka mutu ba, zaka tashin akan kafafun ka zafin ciwo ne." Alhaji baba dake tsaye gefe yana kallon yanayin Dad ya tabbatar wannan kam yana kan gaba, matsowa yayi gare shi ya shiga laƙaba mishi Kalmar shahada, Allah sarki Dad kasa.kamawa yayi sai ya bude baki zai kama kuma maganar ya sarƙe, karshe idanun shi ya shiga kafewa kumfa na fitowa daga bakin shi, take kuma jikin shi ya fara sakewa a hankali kuma kanshi ya karye gefe.............






Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,Allah kajiqan iyayen}






Page 131




Mutuwar Dad ya girgiza zukatan mutane da dama, duk wanda ya tuna abin da ya faru kafin awa ashirin da hudu da suka shude, sai ya kara tsarkake lamarin ubangiji ya kuma kara tabbatar wa lallai rai ba'a bakin komai yake ba, lokacin da labarin rasuwar Dad ya riski zee kusan zaucewa tayi, take ta fisge daga rikon da Aslam ya mata ta nufi ɗakin da gawar Dad kwance da mahaukacin gudu, tana yin arba da gawar Dad take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. kwanan keso Dad yayi saboda da daddare ya cika. Washe gari Karfe tara Mom ta iso a birkice , bata yarda cewa Dad ya rasu ba saida tayi arba da shi kwance baya motsi lulluɓe da farin alawayyo, take ta ƙara birkicewa ta shiga zunduma ihu tana kururuwa da birgima kamar wata arniya maimakon ta mishi addu'a, rarrashin duniya an mata taƙi ta haƙura har aka gaji aka yi kyale ta, masu zagi da alawadai nayi masu tausayi nayi. Karfe goma daidai aka kai Dad makwancin shi na gaskiya, Aslam da duk wani makusancin shi sun halarci jana'izan Dad, tare dashi aka cigaba da karɓan gaisuwa a gidan alhaji Abdur-rahman. Har aka kai Dad aka watse zee bata cikin hayyacin ta, dan tunda ta sume aka kwashe ta aka sake bata gado a asibitin, likitoci suka duƙufa a kanta har aka samu ta farfaɗo, koda ta farfaɗo zabure zabure ta shiga yi tana ihu ce ihu ce lamarin kamar da bugun aljanu ganin haka yasa likita ya zunduma mata alluran barci mai karfin gaske, sai da Dad ya kwana ya wuni a kushewa sannan ta farko,cikin hukuncin ubangiji ta farka cikin hayyacinta sai dai kuma ruwan hawaye ya kasa ƙafewa a idanun ta, a ranar Dr ya bata sallama direct Aslam ya wuce da ita gidan Alhaji Abdur-rahman aka cigaba da zaman makoki tare da ita, duk yan gidan su Aslam sunje sunyi gaisuwa tun daga kan su mummy har su batool da mazajen su, Aslam da Asmah kam kullum nan suke wuni shi yana falon Alhaji Abdur-rahman ana karbar gaisuwa dashi ita kuma tana tare da zee tana kwantar mata da hankali, har zuwa ranar da akayi addu'an fidda'u na kwana uku. Sai da zee tayi kwana bakwai sannan Aslam ya dauko ta, har zuwa lokacin mutuwar Dad nanan daram a ranta, sai dai tayi amfani da shawarar da Asmah ke bata a kulkum ta daina yi mai kuka sai dai in abin ya ciyo ta tayi ta hawaye tana mai addu'a domin tasan shine abin da yafi buƙata a halin yanzu, part guda aka ware wa Mom a gidan Alhaji Abdur-rahman a nan take zaman takaban ta, Allah sarki Dad tasa ta ƙare wasu har sun manta dashi sai wa'inda ya zame wa dole kamar dai zee da Mom da Alhaji Abdur-rahman.


Bayan wata daya da rasuwan Dad, zaman lafiya tsakanin Asmah da zee sai abin da ya ƙaru, zuwa lokacin zee ta koma asalin zee ɗin ta, tayi laushi ta kara miƙa wuya ga lamarin ubangiji, ta dau hakuri da dangana akan rashin mahaifin ta, idan ta tuna shi sai dai kawai ta mishi addu'a, Aslam ma ya dena yi mata wasu abubuwan da yake mata zuwa yanzu dan ba karamin tausayi take bashi ba , musamman idan ya tuna da wasiyyan da mahaifin ta ya bashi da kuma amanar ta daya damƙa a hannnun shi a lakacin yana kan gargarar barin duniya. A bangaren Asmah yau ta wayi gari cikin wani irin yanayi mara daɗi tun cikin dare ta ke jin cikin ta na wani motsi kamar akwai abu mai rai a ciki,dama takanji haka lokaci lokaci cikin kwanakin nan tana sharewa amma na yau sai yayi yawa gashi Aslam ba'a dakin ta yake ba, tun cikin daren tayi ta kiran wayar shi amma yaki shiga, haka ta zauna ta dafe cikin ta tana ta kuka, idan taji motsin yayi yawa sai ta shiga karanta ayatulkursiyu ta tofa, ta firgita ainun da lamarin kafin safiya duk ta fice daga hayyacin ta, kwanaki da cikin ta keta kumbura taje asibiti taga likita, Dr Aysha ta mata duk wani tambayoyi akan alamomin ciki tace bata jin ko daya, kuma duk watan duniya al'ada takeyi, duk wani test daya kamata tayi, tayi harda su scanning babu komai, kwantar mata da hankali Dr tayi tace ba komai kawai tumbi bi ne, ta kiyaye cin abubuwa masu maiko da kitse kuma ta ringa motsa jiki zai baje insha Allah, koda taji haka sai ta tattara lamarin ta watsar kawai tunda dai ita ba ciwo yake mata ba, kuma ma ba wani shegen girma yayi ba itace kawai take ganin abinta sai ko Aslam shi da yake mijin ta , amma idan ba mutum kallon kurulla ya mata ba bazai ga komai ba, shine kuma cikin wannan week ɗin ta farajin motsi motsi a cikin nata, tana dai daurewa tana basarwa don ko Aslam bata fadawa ba, sai dai tayi ta addu'a tana rokon Allah koma menene ya yaye mata, har aka kira sallan assalatu idanun ta biyu bata rintsa ba, da'ker ta lallaɓa tayi sallah, tana idarwa ta farajin kamar ana yaki a cikin har in ta taba tanajin motsin a hannun ta, wayar ta ta dauka ta sake gwada kiran Aslam still bai shiga ganin haka yasa ta juya akalar kiran ta zuwa numbar mummy dama abin da ya hana kiran ta tun jiya dare ne dan karta ɗaga mata hankali, mummy nakan dardumu da asuba tana lazumi taji wayar ta na ringing kamar ta share haka kawai taji zuciyar ta na azalzalan ta akan ko baza ta dauka ba ta duba, ganin sunan Asmah na yawo a saman screen din wayar yasa taji gaban ta ya fadi, a fili ta furta "Asma'u da wannan farar safiyar Allah dai yasa lafiya." Ɗaga kiran tayi ta kara a kunne tare da yin sallama, cikin shehsheka taji muryar Asmah na amsa mata sallama, cikin dan tashin hankali jin Asmah kamar kuka taje tace "subhanallahi! Asma'u mekefaruwa, meya sameki waya taɓa ki?" Dan ita duk a tunanin ta cikin Aslam da zee ne wani ya saka ta kuka a Cikin kuka take ba Mummy labarin abin da ta kwana ji a cikin ta yau, mummy karan kanta abin yadan tsorata ta, wani tunanin ya faɗo mata a rai da sauri ta kauda shi tare da yin istigfari a zuciya, cikin sanyin jiki tace "Ina Aslam ɗin yake to?" Tace "yana ɗakin anty zee yau a can yake kuma tun cikin dare nake ta ta kiran shi wayar shi yaki shiga." Katse kiran mummy tayi tare da cewa "Ina zuwa." Lambar Aslam ta shiga kira itama cikin rashin sa'a yaki shiga, ganin zai bata mata lokaci yasa ta shiga shirya wa dan tafiya gidan Aslam taje taga halin da marainiyar Allah take ciki. A waya ta sanar ma daddy abin dake faruwa shi kanshi lamarin ya daure mishi kai, baiyi kasa a gwuiwa ba yace ta shirya ya kaita, minti 30 ya dauke su zuwa gidan Aslam, har zuwa lokacin Aslam na part ɗin zee dan koda ya dawo masallaci can ya koma da nufin yayi shiri ya sallame ta gaba ɗaya sai ya koma part ɗin Asmah, horn din motar su mummy da kuma ƙaran bude get da mai gadi yayi shiya janyo hankalin shi, yana tsaye gaban mirror yana shirwaya zee na gefen shi tana taimaka mai, kallon juna suka yi da mamaki fal fuskokin su, waye da wannan sanyin safiyar a gidan su, kasa hakuri yayi ya karasa bakin windo ya daga labule ya leka zaro idanu yayi lakacin da yayi arba da motar Daddy kafin ya gama mamaki yaga Mummy ta fito ta nufi part din Asmah, da sauri ya saki labuleb ya juyo ya kalli zee data ke nan tsaye tana jiran taji su waye, yace cikin dan tashin hankali "Daddy da Mummy ne fa." Cikin kaɗuwa tace " A gidan nan da sassafe? To duk yadda akayi ba lafiya." Bai tsaya jin me zata ce ba ya zira jallabiya ya fice da sauri ganin haka yasa ta rufa mishi baya. A can kuryan ɗaki Mummy ta same ta durkushe tana hawaye da sauri ta karasa ta dago ta, ganin mummy yasa ta fashe da kuka, rarrashinta Mummy ta shiga yi "yi shiru Asma'u ya isa haka, yanzu zamuje asibiti insha Allah koma mai ke ciki zasuyi scanning mu gani, asibitin Dr nasidi zamuje babban likitan mata me kuma yana da wankin ido imma jinnu ne ko sihiri zai gane." Kasancewar sanye take da hijabin da tayi sallah yasa mummy kamo hannun ta kawai suka nufi kofar fita, daidai nan Aslam ya iso da sauri zee na biye da shi, ɗaga ido mummy tayi ta musu kallo daya sai taji wani haushin su ya tirnike ta suna can suna soyayya sun bar mata yarinya ita kadai zata mutu a banza ita fa shi yasa auren mai mata bai taba birgeta ba, sama sama ta amsa gaisuwar su, ta wuce su rike da hannun Asmah dole suka matsa mata a hanya, ganin yadda ran ta ke a bace, daddy na hango su ya fito ya bude musu gidan baya, zaunar da ita tayi tare da rufe mata kofar ta zagaya ta shiga mazaunin ta nada suka dauki hanyar asibitin Dr nasidi dake kwangila, suna fita Aslam na fitowa, hankalin shi gaba daya ya tashi dafe kai yayi ya shiga karanto innalillahi wainnailaihi rajiun, ganin haka yasa zee nufar dakin ta da gudu ta dauko makullin mota bata tsaya mai bayani ba ta shiga ta tayar ganin haka yasa shima yayi sauri ya fada ta bi bayan su mummy cikin sa'a ta cim musu saboda traffic light daya tsayar da su, koda suka iso asibitin sun taradda da layi duk da likita bai karaso ba sai Karfe takwas, duk wani zirga zirgan da za'ayi na bude file da sauran su Aslam ne yayi, so yake ya tambayi meke damun Asmah amma yana Shakkar mummy ganin yadda fuskar ta ke daure, kasa jurewa yayi ya nufi ta inda yasan zai iya sanin sauki, wurin daddy, a nan yake jin mekefaruwa, aiko dai hankalin shi ba karamin ta shiga yi ba haryaso yafi Asma'un shiga rudu, takwas daidai Dr nasidi ya iso, mutane da yawa ke gabansu amma kasancewar akwai sanayya a tsananin su, ɗan wani tsohon abokin daddy ne yasa aka musu wuru wuru wanda ba'a rabuwa dashi a Nigeria suka shiga, yana gama jin bayanin ta daga bakin Mummy kallo daya ya mata yasan lamarin ta akwai saka hannun mutanen ta a ciki, amma bai gaya musu haka ba, scanning ya fara mata take ciki ya bayyana yaya uku rerass da ransu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login