Showing 1 words to 3000 words out of 29040 words
Chapter 1 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Part 1 ⏩ 5
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Ina farawa da sunan Allah, ina rokon Allah yasa yanda zanfara littafin nan lafiya Allah yasa ingamashi lafiya.
GARGADI.....
Banyarda wani ko wata su canza mani littafi ba, ko su juya manishi ba, duk wanda yayi haka nabarshi da Allah.
Kuma banyi wannan littafin domin incima wani fuska ko kuma dan inbata mashi rai ba, nayishi ne domin fadakarwa ga mutane.
SADAUKARWA!!!!
Na sadaukar da wannan littafin nawa ga dukkanin mata da maza, domin wannan littafi nakune, Samari da yan matan zamani.
GODIYA!!!!
Ina mika godiyata ga dukkanin masoyana, Allah yabar zumunci, nagode da addu,arku agareni. Wannan littafi nawa kowace irin fassara aka mashi ze bada amsa dede,domin kalmar tana da amsoshi dayawa. KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH????? Nabar maku sauran, ku amsa da kanku😘
Wata motace medauke da samari da yanmata su shida ta kwaso da gudu sun kure kara suna jin sauti acikin motar, babu abinda yake fitowa aciki se shewa da dariya.
Tafiya suke cikin dare da misalin karfe 1:00 na dare, sun taso daga partyn da daya daga cikinsu ya shiryama budurwarshi na murnar zagayowar shekarar haihuwarta.
Gaba daya ba acikin gari sukayi partyn ba, saboda basa son asa masu ido, kasancewarsu yan garin Bauchi hakan yasa suka tafi can kauyen Bununu dake wajen gari.
Awata gona sukayi partyn, mutane dayawa sun halarci gurin, anyi shagali sosai, ansha kayan maye anyi rawa, ganin dare yayi yasa suka tashi, kowa yakama gabanshi.
Wannan motar itace ta karshe, kuma itace ta masu partyn, ko kula da dare basu yiba haka suka kure kara suka kulle glass suna shara gudu, acikin motar ma rawa suke suna shewa.
Dede sun fito daga kauyen, sunzo wani karamin daji, motar tafara hayaki, ganin abinda yake faruwa yasa driver yayi saurin taka burki, gaba dayansu suka fito daga motar.
Daga gaban motar sukayi ashe ruwa ne, yakare nacikin lagireton motar, dubawa sukayi sede kuma babu ruwa ko kadan amotar.
Kafa daya daga cikinsu yasa yadaki tayar motar, dafa kafadarshi wani yayi yace lafiyade Nabeel? Tsaki yaja yace wlh babu ruwa amotar nan Najib,
Daya daga cikin matan mesuna Sumy tace munshiga 3 yanzu honey yazamuyi gashi kowa yatafi, gashi adaji muke, wlh tsoro nakeji.
Jawota Nabeel yayi ya rungumeta yana shafa bayanta yace kiyi hakuri Dear babu abinda ze samemu, kawai kushiga mota ku kwanta muzamu tsareku, tunda yanzu 2 takusa babu inda zamu samu ruwa, idan asuba tayi semu nemi ruwa.
Sumy tace nashiga 3, Khairat, wlh Babanmu besan zanzo nan ba, Mamanmu ce kawai tasani, kuma seda taja mani kunne kada indade, nasan halin Babamu wlh ze iya dukana.
Wadda aka kira da Khairat tace haba Sumy meyasa kincika tsoro, kinsan fa Mamanki tana goyon bayanki bazata bari Babanki yasan kinzo nan ba, nasan zata kareki, kuma wannan party saboda ke mukazo nan.
Amma idan kina ganin akwai matsala ki kirata kice mata motarmu ta lalace, zaki kwana agidanmu. Sumy ta kalli dayar kawarsu tace Zuby bani wayata acikin jaka.
Nabeel yace Sumy kiyi hakuri gurin nan babu network waya bazata shiga ba, kawai kiyi hakuri mubarma Allah gobe. Kallon dayan abokinshi yayi yace Saif miko mana dadduma acikin mota muzauna.
Saif yajuya ze dauko dadduma sukaga mutane sun zagayesu kamar daga sama aka turosu, wasu bakaken mutane ne, masu kama da arnan daji, gaba daya fuskarsu babu alamar imani aciki.
Babu riga ajikinsu, gajeran wando ne, kawai se wani tsumma dasuka daure kugunsu dashi, kowa se zaro idanuwa yakeyi, suna lashe harshe.
Kuka matan suka sa, kowa takama saurayinta suka rike juna jikinsu yana bari. Gaba daya har mazan tsoro yakamasu, wata irin dariya daya daga cikin mutanan yayi,
Kallon sauran yayi beyi magana ba, suka nufosu suna zare ido, haka suka tasa keyarsu suka nufi wata hanya. Tun suna kukan tsoro har suka koma na gajiya, domin bakaramar tafiya sukeyi ba.
Ga duhu dan hasken dasuke haskawa beda wani haske, kuma duk sun anshe wayarsu sun wurgar da ita acan gurin motarsu.
Cikin wani daji suke shiga babu alamun gida agurin, zuwa yanzu matan gaba daya sun fita ahankalinsu, domin tafiyace takusan awa daya da rabi.
Se gurin karfe 3:30 suka isa tsakiyar dajin da bazasu iya gane gaba ba, bare baya, wasu mutane yan uwan wadan da suka taho tare suka gani, sun hura huta suna ta shagali.
Da murna suka tarbi yan uwansu, ganin sun samo masu mutane, domin sun dade basu kama kowa ba, domin mutanan dasuke kauyen Bununu sun gane tarkon dasuke samasu.
Hakan yasa suka dauki matakin dena bin hanyar idan akace karfe 10 tayi, domin da 12 tayi suke fara shawagi atsakanin gurin, dominsu aikinsu kama mutane, su kashe, ko kuma su maidasu bayinsu, matan kuma suyi amfani dasu.
Mutanene masu kama da arnan daji, sam basusan meye imani da tausayi ba, acikin wannan dajin suke zaune, idan sungaji kuma su kara gaba, a wannan dare sukayi sa,ar cafke su Nabeel.
Babu bata lokaci aka turasu cikin wani akurki dan,karami, dan atakure suke, Sumy dasu Zuby se kuka sukeyi, suna dana sanin zuwansu wannan party, mazan kuwa se hakuri suke basu.
Wani katon mutum ne, yafito daga wata bukka, daga ganinshi babu alamun imani atare dashi, dukawa kasa sukayi suna kwasar gaisuwa, hannu yadaga masu, wani yashiga gaba ogan yana binshi abaya sauran suka take mashi baya.
Hanyar inda aka rufe su Nabeel suka nufa saurin bude kofar sukayi fito dasu akayi, Sumy kamar zata saki fitsari dan tsoro, haka sukayi layi se rawar sanyi sukeyi saboda tsoro.
Kallon Zuby yayi yana lashe baki, kallon daya daga cikin yaranshi yayi, nan take suka fahimci abinda yake nufi, hannun Zuby suka kamo, aikuwa saurin kai hannu Saif yayi yariketa,
Fuskarshi a daure dan Saif akwai zuciya, tsawa wani yadaga mashi yana wani irin yare wanda basu san abinda yake fada ba, amma Saif yaki sakinta.
Wani katon karfe dayake hannun wani yasa yabuge hannun Saif da karfi wanda seda Saif yafadi kasa saboda tsananin zafin dayaji hade da sakin wata kara, seda yan uwanshi suka tausaya mashi.
Haka yarika burgima agurin yana rike hannunshi, sunaji suna gani wani yadauki Zuby yanufi bukkar Ogansu da ita tana kuka gwanin ban tausayi, wani ya tura sauran cikin akurkinsu, da kyar su Nabeel suka kama Saif suka shiga ciki.
Zuwa lokacin hannunshi ya kumbura sosai daga gani yasamu buguwa agurin, kwanciya yayi agurin idanuwanshi se zubar da kwalla sukeyi.
Nabeel yace sannu Saif, hakika Allah ya jarabcemu da dede laifinmu, mun saba mashi gashinan tun aduniya mun fara karbar sakamkonmu, dama kuma duk WANDA YATAKA DOKAR ALLAH BAZEGA DEDE BA.
Yanzu gashinan munshigo inda babu wanda yasan ranar fitarmu, bamu sani ba ko zamu fita da rai, daga ganin mutanan nan wlh basuda imani, yanzu kalla sun dauki Zuby Allah kadai yasan mezasuyi mata.
Sumy tace baiwar Allah, wlh nasan baze kyaleta ba, domin yanda yake lashe baki kamar tsohon maye, ni tsoro ma nakeji kada ya goga mata cuta.
Khairat tace mu de munshiga 3, mun cuci kanmu, mun cuci iyayenmu mun dauki muguwar rayuwa mun sama kanmu, muna aikata sabon Allah babu tsoro azuciyarmu, acikinmu babu wanda yataba tunanin wata rana zamu mutu.
Najib ya goge hawayen fuskarshi yace ina ganin addu,a itace abinda yakamata muyi ba wannan surutunba, babbar damuwata yanda ko sallar azahar zuwa isha,i babu wanda yayi acikinmu,
Gaba daya saboda wannan dan iskan partyn daya jaza mana bala,i mun dauki lokacinmu gabadaya na yau mun bama wannan partyn, gashi daga karshe abinda yajawo mana.
Wlh kudi Abbana yabani dubu dari biyar inkaima abokinshi a kaduna, kuma zuwa azahar zeyi amfani dasu, Abba hada bani mota dan kawai in isa da wuri,kunsan yau babu banki, gashi Abba beda kudi a account shiyasa bemashi transfer ba. kuma gashi tunda asuba nayi sallama da gida akan natafi Kaduna,
Amma na ha,inceshi nakashe wayata nataho party, yanzu kudin suna cikin motar, gashi motar tana daji, ga kudi aciki shikenan nasan dole asamu wadan da zasu dauke motar.
Nabeel yace inaganin naku me sauki ne, ni tunda nataso agidanmu nake aikata sabo, Ummi na bata taba hanani ba, gani dan gata agidanmu, ni daya ne, babu abinda nake nema inrasa.
Allah kadai yasan iyakacin matan dana batama rayuwa, nasa Abbana kuka yafi akirga, yayi addu,a haryagaji amma bancanza halina ba, kuma har gobe yana sona,ayau ina matukar dana sani da irin wannan rayuwa dana saka kaina.
Ummi na itace mutum ta farko data bada gudummuwa wajen lalacewar rayuwata, gashi yanzu zan mutu batare dana nemi yafiyar Abbana ba, wlh bazan iya cemaku ga ranar danayi sallah 5 arana ba.
Sannan babban tashin hankalin duk gatan da Ummina tamun wlh yau kusan wata 2 kenan banganta ba, banje na duba jikinta ba, tana cikin tsananin rashin lafiya, wanda Abba ya kaita asibitoci da dama amma bata warke ba.
Daga karshe ma gajiya yayi ya wareta yasa mata masu kula da ita, ko gurinta baya zuwa, gashi yayi aurenshi sede haryanzu beda wani da seni. Ina tsoron kada alhakin Ummina ya kamani, duk da itace silar lalacewata amma nasan UWA UWA CE. Kaichona
Ihun Zuby dasukaji ne yasa gaba dayansu hankalinsu yakara tashi, Saif dayake kwance shima seda yatashi, dan kara yasaki daya fama hannunshi.
Khairat tace shikenan Zuby Allah kadai yasan abinda suke mata, kilama fyade zasuyi mata. Cike da bacin rai Saif yace dan Allah kada kucika mana kunne da kuka,
Ai gara ita taga abunda zasuyi mata, mufa? Babu wanda yasan abinda zefaru dashi, saukinta ma daya dama yar hannuce da senafi tausaya mata idan virgin ce.
Tsaki yaja, ya kalli Nabeel yace dan Allah ni kama mun hannun nan kila zan rage jin zafin danakeji, murmushi Nabeel yayi yace kai mutumina, kana cikin bala,i amma baka dena wanna halin naka na bakar zuciya ba.
Wlh kabi ahankali da mutanan nan idan kace zakayi masu zuciya zasu iya kasheka, Saif yace naji, kawai kama mani,
Wani irin kara Saif yasaki da aka kama mashi hannun, dariya Sumy takusayi ganin wanda yake fada ancika mashi kunne gashi yanzu yana ihu.
Ganin shiru ba,a maido Zuby ba, yasa suka kwanta cike da firgici, Zuby kuwa tana can seda Ogan yagama amfani da ita son ranshi ya mika ma sauran yaranshi, yace abar sauran seda safe yanzu bacci zeyi.
Seda Zuby ta sume masu sannan suka kyaleta, sunso ace Oga yasa andauko sauran matan, amma sanin halin Ogansu yasa suka hakura, agefe guda suka jefar da ita ko motsi batayi suma suka kwanta.
CIKIN GARIN BAUCHI
Kuka kawai Maman sumy takeyi, yanda Baban Sumy yadage yana mata fada, domin tun tana mashi karyar anjima kadan Summay zata dawo har karyarta ta kare,
Malam Haruna yace shikenan Zainab, tunda de bazaki fada mani, inda Sumayya ta tafi ba, shikenan, amma iname tabbatar maki zancire hannuna kome zefaru da ita babu ruwana,
Dama na dade da sanin kece kike goyan bayanta akan duk wani iskanci datakeyi, amma idan nayi maki magana seki kareta, yanzu kince kin aiketa gidan yayarki,
Kuma agabanki nakirata tace rabonta da Sumayya anfi wata guda, amma bakomai, idan kinfison incigaba dasamaku ido tarika kawo maki abun duniya kinaci shikenan.
Dukawa kasa tayi tana kuka tace dan Allah mal. Kayi hakuri, nasan na cutar da diyarmu, na ha,inceka na dade ina boye abubuwan da Sumayya take aikatawa,
Wanda duk nice silar shigarta halin datake ciki saboda tsabar son abun duniya irin nawa, amma wlh yanzu nayi danasani, tunkafin kashigo gidan nan hankalina yake tashe,
Domin tamun alkawarin bazata kai magriba ba, amma nakira wayarta bata shiga, daga karshe ma senaji wayar akashe, ni nasan duk inda Sumayya take tana cikin wani hali,
Dan Allah mal. Kada kayi fushi da ita, ayanzu Sumayya addu,ar mu take bukata, dan duk yawonta bata taba zuwa wani guri ta kwana ba, kayafe mana.
Zama mal. Yayi yana jinjina kai, gaba daya tausayin matarshi yakamashi, hannu yasa yakamo hannunta yace ya isa haka, yanzu abinda nakeso insani wane guri ta tafi?
Maman tace wlh bansan inda suka tafi ba, abinda nasani de partyn zagayowar haihuwarta wani saurayinta yahada mata, amma bansan inda zasuyi ba. Shiru yayi yana goge zufa.
Babban yayan Sumayya dayake tsaye shima kukan yakeyi ya duka kasa yace Baba yanzu kuyi hakuri, yanzu dare yayi, mubarma gobe, se inje innemi wadan da sukaje partyn nasan zamu samu labari daga garesu.
Wata matace kwance adakinta, banda kuka babu abinda takeyi, idanuwanta harsun kumbura, asalinta fara ce amma ayanzu tayi duhu sosai. Fuskarta wasu kuraje ne suka fito mata, jikinta duk ya yamutse saboda tsanin cutar da likitoci da dama sun kasa gane kanta.
Hatta da mijinta ya kebe mata daki ya zuba mata masu aikin dazasu rika kula da ita, sam bayason ganinta idan bame dauriya ba babu wanda ze iya kusantarta domin dakin kanshi wari yake, duk yanda yake samun gyara amma hakan be hanashi wari ba.
Kawarta ce Lawisa tace ya isa haka Ummin Nabeel, kidena kukan haka nan, asirinki baze taba tonuwa ba, domin mun toshe duk wata kofar dazata sa Alhaji yasan abinda kika aikata shekara da shekaru.
Dago kai Ummin Nabeel tayi tace haba Lawisa, nikam nagaji da wanana zunubin danake daukarma kaina, na aikata sabo, nataka DOKAR ALLAH, kinsan kuwa Allah baze barni ba.
Idan ma mutuwa nayi dole akwai wanda zan bari aduniya kinga dole asirina ya tonu, gara tun inada damar tuba, nayi amfani da ita, bazan damu da jin kunyar duniya ba,
Inde Allah ze yafe mani, banida damuwa, ko yanda Allah ya maida Nabeel kadai ya isheni ishara, yaro kamar wanda shedan yayima fitsari akai, duk da hadani cikin wadan da suka bada gudummuwar lalacewar rayuwar Nabeel,
Amma wlh hada zunubin dana aikatama Allah,kina ganin Babanshi ya guje ni, shima kanshi se inyi wata banganshi ba. Idan ma nasamu yazo dubani ko kofar dakin be karasowa daga waje ze gaisheni. shiyasa na kiraki domin infada maki zanje intona asirin da nadade ina boyema Alhaji, idan ma rabuwa zeyi dani banida damuwa matukar ze yafe mani tunda yanzu meyayi saura, tamkar yacireni daga matanshi ne, kina ganin kwanan nan yayi aure, amma ni ya ajeni abanza, wama yasani ko asirin danayi na aureshi yakare.
Lawisa tace naji, kuma nima maganarki tasa jikina yayi sanyi, insha Allah nima daga yau nadena aikata abinda nakeyi, amma babban abin damuwar kince rabonki Nabeel kusan wata daya da rabi bedawo gida ba,
Kuma kinsa akira abokinshi Auwal yace sunje party dashi kuma sun barosu ahanya suntaho, amma gashi haryanzu bedawo ba. Umman Nabeel tace wama yasani koyadawo tunda bazuwa wjena yake ba, kullum yana tare da Babanshi daya dauki so duniya ya dora mashi, sede besan asalin gaskiyar ba. Da zanga Babanshi ma dana sa anfada mashi yasa aduba shi koyadawo. Lawisa tace inaso kibar wannan maganar zuwa gobe, kisa aduba maki koyana shigowa wajen Babanshi, idan ance beshigo ba seki sa afadama Alhajin.
Ummin Nabeel tace shikenan, Allah yadawo dashi lafiya, amma wlh tun dazu gabana yake faduwa. Lawisa tace insha Allah babu komai, Allah de ya kaimu safiyar.
ASALIN LABARIN KOWA YATAKA DOKAR ALLAH.............
Kubiyini domin jin labarin.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Part 5⏩ 10
Lawisa!Lawisa! Na'am ina, jinki fa kike kwala mani kira kamar tsohuwar data shekara 100. Dariya wadda takira Lawisar tayi tana fadin, amma kin cuceni, kina kallona yarinya meji da kuruciyarta kihadani da me shakara 100.
Zama Lawisa tayi tana gyara daurin dan kwalinta tace haba Maimuna, masuji da kuruciyarsu de sunaji, ke kam ai kinzama saura,duka takai mata sukasa dariya tana fadin haryanzu banyi auren farko ba amma kike mani maganar tsufa.
Lawisa tace to a auren meye baki sani ba? Maimuna tace zaki fara ko? Aide dadin abun nida ke duk sana'armu daya. Lawisa tace toyi hakuri kema kinsan wasa nake maki. Yanzu de kitashi mutafi tunda angama komai, wanda ze dauki abincin ma ya dauka harya kai mana shago mutafi kada mutane sufara zuwa ba muje.
Maimuna tace muje, dama ai kece kike bata mana lokacin kin tsaya kina kwalliya kamar wadda ta aje wani. Lawisa tace ke kuwa wannan sana'a tamu ai seda kwalliya, kinsan fa mu na mutane ne musamman maza. Kema ai kina kwalliyar dande kina riga ni shiryawa ne. Haka suka kulle gidansu suka tafi shago.
Maimuna kenan da kawarta Lawisa. Yan cikin garin Darazo ne dake jihar Bauchi, kuma kawaye ne, sede Lawisa ta girmi Maimuna da kadan, kuma Lawisa yar tsintuwa ce, wata rana wani mutum yadawo daga cikin gari da dare ya sameta zaune aksan wata bishiya tana kuka.
A lokacin bazata wuce shekara 9 ba, tsayawa yayi yana tambayarta me yafaru take zaune ita kadai da dare haka? Dago kai tayi tana kuka tace mashi mamarta. Dukawa yayi yana cewa ina mamar taki take? Cikin kuka tace ta tafi.
Ganin dare yana karayi yasa ya jata suka nufi gidanshi. Koda yaje yayima medakinshi bayanin abinda yake faruwa ce tace malan nifa ina tsoron temako a zamanin nan, kasani ko mamar ta ta zuwa tayi tadawo kai kuma zaka shigo da ita, idan kuma tadawo bata gantaba fa?
Zama yayi yana fadin dan Allah kiyi hakuri, ke daga ganin yarinyar nan kinsan bawai unguwa suka fito da mamarta ba. Kibata abinci taci duk da bata da wayau sosai nasan zamu samu wani abu daga gareta.
Bayan taci abinci suka sata gaba suna tambayarta, ya sunanki? Tace Lawisa, to ina mamarki? Ba itace kullum seta dukeni ba, kuma kullum seta zageni tana cewa wai banida Baba. Cike da mamaki suka kalleta.
Mutumin yace to me mamarki takeyi? Yarinyar tace abinci take saidawa, shine naga wani yazo wajenta senaji yace mata ze aureta. Shine da safe tayita dukana tace sena tafi nabarta tunda ita kadai take wahala dani.
To waya kawoki nan? Tace mamana ce tace inzo mutafi unguwa, shine muka hau mota mukazo nan, shine tace inzauna injirata, ni kuma naga bata