Showing 24001 words to 27000 words out of 29040 words
Chapter 9 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt
a'a nagode sekace wata karamar yarinya, yace emana agurina kin wuce haka ai, idan mukayi aure babu abinda bazan maki ba. Murmushi tayi ta bude bakinta yabata.
Kallonta yayi yace hajiyar hijabi, waike ko zafi bakiji kiyita zama da wannna katuwar hijab din? Murmushi tayi tana fadin to yazanyi tunda Baba yace dole sena sa. Nabeel yace kice ba ra'ayinki bane? Ya mutsa fuska tayi tace kasan iyayenmu da tsoro.
Hannu yasa yakamo hijab din yana fadin kuma gashi yadin akwai nauyi, tace wallahi kuwa waishi yafison irinshi, Nabeel yace ai yanada gaskiya, kinga kin boye mani jikina babu wanda ze gani seni. Amma idan muna tare seki rika cirewa sauran mutane kuma ki boye masu.
Murmushi tayi tace kaima kana goyon bayanshi kenan? Yace sosai ma, ai haka akeso, gara inrika gani nikadai, hannu yasa yana fadin bara incire maki, haka ya cire mata dama daga ita se doguwar riga ko dan kwali bata saba.
Gashin kanta ne yazubo harya rufe mata fuska, domin hada ribom din yafitar besani ba. Cak ya tsaya yana kallonta, itako ta dukar da kanta tana murmushi, kara matsowa yayi yana fadin Sweet, wannan gashin naki ne ko sawa kikayi?
Murmushi tayi tace nawa ne mana, hannu yasa yana gyara mata yana fadin aikuwa, gaskiya babu abinda zan ma Allah se godiya daya bani ke, nasan zamu haifi yara masu kyau da gashi, ina matukar son mace me gashi.
Kara kallonta yayi ganin tana murmushi yasa ya duko yana kallon fuskarta har jikinsu yana haduwa, murmushi sukasa gaba daya, hannunta yakamo yana murzawa, kara dukewa tayi tana murmushi, ganin bata hanashi ba yasa yakara matsawa jikinta yana fadin.
Sweet dan Allah kina sona? Kai tadaga mashi, yace sweet wallahi idan narasaki nasan zan iya mutuwa, saurin dagowa tayi tasa hannu ta rufe mashi baki, dariya sukasa yafara yinata cakulkuli suna dariya da haka har suka kwanta cikin dabara Nabeel yafara yimata salonshi, sam Sumy takasa hanashi.
Ganin har ankira magriba basu fitoba yasa Saif yatafi dan yakirasu, yana daga labule yaga halin dasuke ciki yayi saurin sakin,labulen yana murmushi, juyawa falo yayi. Najib yace ya kuma kafito kai daya?
Dariya Saif yasa yana fadin shege abokina, yana can yana harka. Najib yace wai da gaske? Saif yace wallahi kuwa, ammade bansan wane irin game yake bugawa ba. Najib yace muje zuwa de wata rana dole yamanta da maganar aure sucigaba da morewa.
Saif yace inaso Sumy tazo ta tafi gida saboda banaso Babanta yafara hanata fita, ni kuma nafiso kullum su kasance atare hakan zesa soyayyarsu takara zama makusanciya. Wayarshi yadauka yakira Nabeel, seda takusa katsewa ya daga.
Murmushi Saif yayi yace idan kanaso gobe Sumy tadawo to yakamata kufito domin ankira sallah. Cikin lokaci kankani suka fito, Sumy se dukar da kai take, haka tayi masu Zuby sallama, suna fita su Zuby sukasa dariya suna fadin zaki dena kunya ma.
Can daga farkon layinsu Nabeel yayi parking, atare suka kalli juna, kwantar da kai Nabeel yayi saman kujerarshi yana fadin bansan ya zan kasance yau ba, hakika sweet kin iya soyayya me tsayawa arai, ni nasan yau bade inyi bacci ba sede shi baccin ya daukeni.
Lumshe ido tayi tana karajin kaunarshi tana ratsata, kallonshi tayi tace ni kaina nasan yau bazan iya bacci ba,tabbas ayau nasan ina matukar kaunarka, dan Allah my king kada kabari wata ta kwacemun kai. Hannunta yakamo yana fadin sweet daga ke bana tunanin kara kallon wata mace matukar zaki bani duk wata kulawa da nakeso.
Kinsan nidin dangata ne, idan har bansamu kulawa daga gareki ba dole zan kalli wasu matan, Sumy tace ni kuma namaka alkawarin zan baka kulawa wadda babu wata mace data taba baka, sena sa kamanta da kowace mace bayan ni.
Naso ace a hostel nake zaune da nabaka kulawa ta musamman, amma anan nasan Baba baze rika barina ba. Nabeel yace zaki iya sweet, kede kibari mu koma makaranta zamu bama kanmu lokaci sosai, saboda iyayenmu basu san yanda zuciyo yinmu zasu rika wahala ba idan basa tare.
Murmushi tayi tace nakosa akoma wallahi, dariya sukasa, Nabeel yace bara na barki kitafi kada Baba yayi maki fada, turo baki Sumy tayi tana fadin wallahi kamar kada murabu. Murmushi yayi tare dasa hannu aljihu yaciro dubu ashirin ya dora a saman hannunta yana fadin gashi kibama mamata kice ina gaisheta. Godiya tayi mashi tafita tana daga mashi hannu.
Da sallama tashiga gidansu, gabanta ne yafadi ganin Babansu a tsakar gida, Mamanta ce tayi saurin fadin yar halak amma kinyi sauri na dauka ma se anjima zaki dawo ya kika samu su Inna Bintar? Ajiyar zuciya Sumy tasaki tana fadin duk suna lafiya tana gaisheki, ai ina zuwa ko zama banyi ba nabata sakon na juyo ganin yamma tayi.
Dukawa tayi tana fadin Baba sannu da kasuwa, murmushi yayi yana fadin yauwa Sumayya, ai da zan fara fada na dauka tun dazu kika fita? Sumy tace a'a ai bazan karya maka doka ba, nasan bakason infita unguwa da wuri kuma inki dawowa da wuri.
Murmushi yayi yana fadin haka ne, Allah yayi maki albarka, tashi yayi yana fadin nizan fita fira bara na turo maku gidan, sukace seka dawo. Yana fita suka shiga daki, Sumy tace nagode Mama da yau bansan irin fadan daze mani ba. Mamar tace ai banfada mashi gidan kawarki kikaje ba cewa nayi kina gama sallar magriba Inna Binta takirani inabaki wani sako ki kaimata.
Zama tayi tana fadin ai agidansu Mansura Nabeel yasameni muka sha firarmu, yace ingaisheki, kuma ga wannan yace akawoma mamarshi, hannu tasa cikin jakarta taciro kudin daya bata tamika mata.
Sakin baki Mama tayi tana kallon uban kudin da Sumy ta bata, karba tayi hannunta har rawa yake tana fadin ke Sumayya, anya ba mantuwa yayi wajen girgawa ba? Murmushi Sumy tayi tana fadin habade Mama, ai kinsan kowaye Babanshi, kumafa shi kadai suka haifa.
Hannu Mamar ta daga sama tana fadin Allah nagode maka, lallai ayau nasan haihuwa tayi mani rana, shiyasa akace daka haifi gwamna gara ka haifa mashi mata, domin mata Allah yayi mu dajin kai, da ace ke namiji ce komin kyanki sede ki amfanama wasu, ga yayanki nan Allah kadai yasan abinda yake kaima budurwarshi.
Dafata tayi tana fadin kinajiko? Daga yau kada ki kara hanashi ganinki, tunda de akwai gidan kawarki da kuke haduwa kirika zuwa can, ni,nasan mezan rika fadama malan, kuma ai da kun koma makaranta zakufi haduwa ma.
Amma tabbas bazan bari malan yayi mani bakin cikin samun abun duniya ba, tunda de Allah yasa na haifi mace aiko dole abarta muci arziki, domin haihuwar mace arziki ne. Allah yayi maki albarka kinji.
Wannan kudin asusu zan sakasu, nasan kina bukatar kayan kwalliya da sauran na amfani, ke macece kisan yanda zaki fada mashi kinason kayan kwalliya, nasan ze kaiki kisiya amma wadan nan kudin gara mufara tarasu, tashi kije kidauko abincinki.
Nabeel ne kwance saman cinyar Ummanshi tana shafa mashi kai yana bata labarin Sumy, kallonshi tayi tana murmushi tace kasan wani abu? Girgiza mata kai yayi, tace yanzu daka fara soyayya da ita bakaji dadi ba? Murmushi yayi yace naji mana sosai.
Murmushi tayi tace to haka akeso, mutum yagama cin moriyar rayuwarshi sannan yayi iyali, kaganni nan banyi aure da wuri ba, kuma babu irin dadin daban jiba, kuma da lokacin auren yayi gashi nayi, da ace nayi aure da wuri nasan da yanzu na tara yara dayawa, shikenan kuma bazan karajin dadin rayuwata ba.
Shima Abbanka abinda yasa yakiyin aure da wuri saboda bayaso yatarama kanshi damuwa tun yana yaro, amma kai gashi kana shekara 22 kake tunani aure, idan kuma ka kai shekarun Abbanka yazaka koma lokacin?
Abinda yafi maka kabari kugama karatunku sannan kuyi aurenku, kaga yanzu lokacinku ne. Sekuyi soyayya son ranku, kuma aurenku seyafi dadewa saboda kowa yasan halin kowa. Murmushi Nabeel yayi yace haka ne Umma, nima ada nayi tunanin bazata amince muyi soyayya ba ganin ita ustaziya ce shiyasa nace zanyi aure.
Amma ayau ta nunamun itama tana sona, sam hijabin datake sawa be hanata nunamun soyayya ba, murmushi Umma tayi tana fadin ai yawancin masu saka wannan hijabin kawai dansu kauda hankalin mutane ne daga zarginsu, amma bakowace mace bace take amfani da abinda take sawa.
Wani lokacin abinda me hijabi zata aikata wallahi me yawo da kananan kaya bazata aikatashi ba, kuma naji dadi tunda kace ka hakura da auren se kagama, abinda nakeso da kai idan Abbanka yayi maka maganar auren kace mashi iyayen yarinyar da yarinyar sunce se tagama karatu zasuyi mata aure, dan haka kaima kafasa auren seka gama.
Nabeel yace angama Ummata ta kaina, tace yauwa dan autana, tashi ka kaima Auntynka Lawisa farfesu gashi can angama tun dazu naso nabama Babaye ya kaimata na manta kuma banaso ya kwana bataci ba, tashi kafin Abbanka yadawo yana iyacewa Babaye yaje.
A wannan rana Nabeel da Sumy basuyi bacci ba, haka suka rika waya kamar basune suka rabu dazu ba, se wajen asuba ya kyaleta, sam takasa bacci, son Nabeel kawai yake yawo a zuciyarta, bata taba tunanin wannan ranar ba. Takosa a koma makaranta kodan ta nunama mutane matsayinta.
Tun daga wannan rana haduwar Nabeel da Sumy tazama farilla, domin yanzu bada yamma take fita ba, Babanta yana tafiya kasuwa shida yayanta Nabeel yake zuwa inda yake daukarta tafito sutafi.
Haka zasu shiga gari wajen shakatawa suyi yawo su sha fira, wani lokacin kuma suje Yankari acan suke hutawa, a hankali Nabeel yafara canzama Sumy rayuwa, duk yanda tayi shiga haka zasuje gidanshi ta canza wasu kayan su shiga gari.
Idan kaganta bazaka taba cewa Sumayyar daka sani bace, Naseer tun yana kiranta tana dauka tana amsa mashi sama sama har tadena dauka, daga karshe ma tayi diverting call dinshi. Duk wasu kayan bukata Nabeel yana sai mata.
Haka ya bude mata account ya samata kudi masu yawa, duk kayan dayake sai mata babu abinda Babanta ko yayanta suka taba gani, daga ita se Mamanta, idan ma kayan dadi taje dasu haka zasu cinye kafin su dawo.
Kasancewar basa dawowa se sunyi isha'i yasa basu taba kamata bata gida ba, domin duk inda akayi magriba ta dawo gida,duk wannan abun da suke Nabeel betaba neman Sumy da aikata zina ba, domin yana tsoron kada sanadiyar haka su bata.
Bayan sati biyu suka koma makaranta, amma Sumy ko tafito daga gida bata zuwa makarantar suna tare dasu Zuby a gidan Nabeel, sosai suka saba dasu, seda akayi sati biyu da komawa makaranta sannan sukayi shirin shiga. Hatta da kawarta Mansura seda ta kirata taji ko lafiya bata dawo ba, dan Naseer duk yadamu shiyasa yace takirata tunda taki daukar wayarshi.
Tana dauka tace mata lafiya lau kawai tana hutawa ne amma yau zata shigo, Mansura tace dama an lika result kuma kincinye duka dan kinada 3 point. Sumy tace amma naji dadi, sena shigo, Mansura tace Yayanki yana gaisheki, saurin kashe wayar Sumy tayi tana tsaki. Sosai Naseer yaji dadin dawowar dazatayi, aranshi yana fadin tana zuwa kawai ze fada mata yana sonta tun kafin wani yayi mashi shigar sauri.
Saif ne da Nabeel tsaye ajikin mota suna jiransu Zuby domin Najib yaje gida Babanshi yana kiranshi. Kallon Nabeel Saif yayi yana fadin wai abokina har yanzu baka saka kwallo araga ba? Murmushi Nabeel yayi yana fadin rufamun asiri, kanaso nakawo karshen soyayyata da Sweet.
Sumy ba kamar sauran matana take ba, shiyasa nake tsoron tun kararta da wannan bukatar. Murmushi Saif yayi yace lallai abokina da sauranka, kuma kwanan nan zaka tafka baban kuskure domin kayi shuka me kyau amma barruwa yanaso yabaka wahala.
To bara kaji, matukar Sumy tasamu wadda yafika iya bada ruwa yanzu labari zesha banban, kana ganin nida Zuby, ayanzu bata iya kula kowa seni, domin nine mutum na farko dana fara bama flower ta ruwa.
Matukar kanaso soyayyarka da Sumy ta dade dole seka fara bata ruwa idan ba haka ba wallahi shukarka zata mutu. Cike da damuwa Nabeel yace yanzu ya kakeso in bulla ma lamarin? Murmushi Saif yayi yace yanzu kuwa zan fada maka, kuma ayau nakeso agama komai, kawo kunnanka kaji.
Dariya suka sa jin abinda Saif yafada, Nabeel yace haka nakesonka abokina. Su Zuby suna gama shiri suka fito, gaba dayansu kallon Sumy sukayi ganin yanda tayi shiga me kyau,domin kayan datazo dasu daga gida ciresu tayi Zuby tabata wasu tasa.
Sosai tayi kyau, gashin kanta yasha gyara an mata daurin dan kwali kamar tasa gwaggwaro, doguwar rigace ta wani material me shegen tsada tasa, tarike wata jaka da takalminta masu tsada, gyalen ma a kafada ta ajeshi, tayi matukar kyau, kosu Zuby seda suka sara mata.
Har suka karaso basu dena kallonta ba, tana zuwa kusa da Nabeel yayi saurin jawota ya rungumeta yana fadin ina matukar sonki sweety na, gaskiya badan inaso in nunama kowa tauraruwata ayau ba da bazaki fita haka ba.
Amma daga yau kindena fita haka, gara kirikasa after dress, Saif yace haba Nabeel so kake abokanmu suyima budurwarka dariya, kasanfa kafi kowa iya wanka ya za'ayi ace budurwarka takasa yin wanka me kyau.
Nabeel yace ina tsoron malaman mu, Zuby tace haba Nabeel, kama dena wannan maganar babu wani namijin daze iya kusantar Sumy matukar yasan kuna tare, shiyasa mukeso yau ka nunama kowa Sumy takace, ke kuma Sumy kada kiji kunya wannan itace damarku.
Hannuta yakama suka shiga mota. Lokacin da suka isa harabar depertment dinsu mutane suka samu cike suna jiran malamin, bayan sun tsaya su Zuby da Saif da Khairat suka fara fita, can Nabeel yafito haka kowa ya zuba mashi ido domin aranar yayi kyau, kusan colour daya sukasa shida Sumy.
Zaga yawa yayi ya budema Sumy kofa, kafarta daya tafara saukowa sannan ta fiddo dayar,hannu ya mika mata takama nashi tafito, tana fitowa yajawota tafada jikinshi yarike mata kugunta da hannunshi.
Saboda tsananin mamaki babu wanda ya iya magana, wasu sun ganeta, wasu kuma kallon sani suke mata, Naseer da Mansura kuwa sun riga kowa ganeta, Naseer jiyayi kanshi yana juyawa, kara murtsike idonshi yayi domin ya tabbatar da Sumayyar daya sani ce?
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Part 50 ⏩ 55
Samun waje Naseer yayi yazauna domin jiyake kamar zuciyarshi zata buga, da gaske wannan Sumayyarshi ce? Yarinyar da ko magana bata iya yi sosai, kullum cikin hijabi take amma itace yau tare da mutanan da sukafi kowa rashin ji. Dafe kai yayi yana addu'a.
Nabeel ne cikin daga murya yace Assalamu Alaikum, inaso kudan bani aron hankalinku domin inaso nagabatar maku da matar dazan aura da zarar mungama school insha Allah. Bakowa bace se Sumayya Labaran, Sumy.
Ina fatan zaku tayani da addu'a domin samun nasarar aurenta. Tafi aka samasu wasu daga cikin abokanshi suka rika ihu suna tayashi murna, wani ne yace agaskiya abokina ka iya zabe, domin kazabo tauraruwar cikin matan course dinmu.
Allah ya nuna mana wannan rana musha biki na yan course daya, dariya akasa Nabeel ya ciro bandir din 200 yamika mashi, ai nan waje yakara rikicewa da tafi, kara kamo Sumy yayi batayi aune ba taji bakinshi cikin nata yana mata kiss.
Gaba daya wajen yakara daukar ihu da tafi, yana cire bakinshi ta maida kanta saman kafadarshi, domin gaba daya kunya ta kamata, Saif yace mun duba munga gobe da misalin karfe 1 muke gama lectures, dan haka muna gayyatarku taron taya Nabeel da Sumy murnar fara soyayyarsu. Za'ayi taron ne a gidan Nabeel dayake Nasarawa idan mungama lectures duk wanda ze halarci wajen yazo ya karbi address din gidan da pass.
Haka suka shiga class dan hango malaminsu yataho, a waje daya suka zauna Sumy ta hade fuska domin taga wasu se wani kallo suke mata shiyasa tacire kunya tadago kanta tana kallon kowa. Malamin yana zuwa yafara tambayarsu abinda yayi masu.
Sumy ce ta tashi tabashi amsa, har tagama bayani malamin besan tagama ba, domin ya shagala wajen kallonta🤣. Wani irin bakin ciki ne yakama Nabeel, gaba daya ajin kuma aka sa dariya, can malamin ya ankara yayi saurin gyara glass dinshi yana kame kame.
Tashi Nabeel yayi yana harararshi yakama hannun Sumy suka fito gaban aji, kallon malamin yayi yana fadin malan wannan itace matar dazan aura nan da wani lokaci. Kasa malamin yayi da kanshi, gaba daya kunyar abinda yayi takamashi. Jan hannunta Nabeel yayi sukabar class din.
Haka ajin yakara daukar dariya, da kyar yasamu ya dedeta ajin yacigaba da darasinshi, ko lokaci be bari yacika ba ya sallamesu. Haka kowa yafito yana gulmarshi. Naseer kuwa zaune kawai yake yakasa tashi, idanuwanshi sunyi ja.
Wani abokinshi ne yazo yadafashi yana fadin haba Naseer, meyasa zaka sama ranka damuwa akan wadda batama san kanayi ba? Ai yanzu ko Sumayya tace tana sonka wallahi kawuce da ajinta, domin babu wanda besan duk macen dataje wajen Nabeel tazama saura ba.
Inaso kacire ma kanka damuwa akan Sumayya, rayuwarta ce, kowa yadebo da zafi bakinshi, dan haka taji zata iya ne shiyasa takarbi tayin soyayyarshi, dama can hijabin datake sawa saboda bata waye bane, kuma babu wanda besan irin wadan nan matan ba, dazaran sun waye zasu nuna ma kowa be iya ba.
Naseer yace wallahi ina tausayinta, sam gidansu ba haka yake ba, sharrin Nabeel ne yamaidata haka, amma burin mahaifinta tazamo ta kwarai, duk lokacin da muka gaisa dashi yana fadamun inrika kula mashi da ita, nikadai ya yarda dani kada inbari samarin Jami'a su bata mashi diya.
Nasha fada mashi halin kirki irin na Sumayya, da hazakarta a makaranta, duk lokacin dana fada mashi haka farin ciki ne yake bayyana a fuskarshi, ina matukar tausayin mahaifinta duk ranar dazesan halin da diyarshi tafada, ni na tabbata bawai yaune tadawo makaranta agidansu ba, nasan tana fitowa dasunan zuwa makaranta su tsaya ita dasu Nabeel.
Amma zanje insamu Babanta infada mashi halin datake ciki, kasan icce tun yana danye ake lankwasashi, gara infada mashi yayi saurin daukar mataki tun kafin abun yayi nisa. Abokin yace Naseer kai asuwa? Meye dangantakarka da Sumayya? Kanaso kasa rayuwarka cikin hadari ko? Kana tunanin idan Nabeel yasan kanaso ka kawo mashi wargi akan Sumayya baze iya yin komai akanta ba? Dan Allah kabar wannan maganar.
Naseer yace shikenan nabarta, insha Allah daga yau nabar Sumayya, zanyi kokarin cire sonta azuciyata, dama kyawun halayenta ne suke dibata,