Showing 9001 words to 12000 words out of 29040 words

Chapter 4 - KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH BY Nabila Lawan Zango.txt

zanyi rubutu a babban alkalamina in batashi.


Murmushi Gaje tayi domin ita ta fahimci abinda yake nufi. Rada tayima Maimuna da sauri ta kalleshi. Gaba daya kyamarshi ce takamata, yanzu wannan kazamin zata bama kanta? Dariya yayi yace ba'a mani musu a cikin aikina, idan bakishirya ba, zaku iya tafiya.


Lawisa tace habade, wallahi tashirya, tashi sukayi ita da Gaje tana fadin afito lafiya muna jira daga waje. Maimuna kuwa idanuwanta ne suka cika da kwalla, amma data tuno aikin daza'ayi mata kuma setayi saurin goge idonta.


Haka boka ya shure awa daya shida Maimuna suna aikata masha'a, seda ya moreta san ranshi sannan ya kyaleta. Bayan ta maida kayanta tafito tana sinnar da kai, Gaje se dariya take mata kasa kasa.


Dariya boka yayi yace aikinki zetafi yanda kike sonshi, nagama nawa saura naki, kada kimanta kada yawuce yau, kuma ki tabbatar kinbashi abakinshi. Godiya sukayi mashi tare da aje mashi kudi dubu 50 suka tafi.


Bayan sun koma gida Saraki yakira Maimuna yana fadin haba Gimbiyata ina kikaje yau haka? Nakira wayarki yafi a kirga amma bata shiga, hankalina duk yatashi, haka nazo gidanku nasameshi a kulle.


Murmushi tayi tace ran Saraki ya dade, Allah ya huci zuciyar abin sona, wallahi munje gaishe da wani kawun mu a Bununu shiyasa baka jini ba, kuma nakiraka infada maka bansameka ba.


Ajiyar zuciya yayi yace har naji dadi, amma kada asake mani haka. Maimuna tace angama Sarakina. Yanzu de inaso kazo kaci abinci da rana, na shirya maka abinda kake so. Murmushi yayi yace kai amma nagode, amma meze hana kibari seda dare?


Maimuna tace gaskiya banyarda ba, haka nan idan dare yayi kacemun kagaji, nide da rana nakeso idan kuma bazaka zo ba inji? Dariya yayi yana mamakin yanda Maimuna ta sake dashi yau, Maimuna tace bakace komai ba?


Saraki yace, to Gimbiya duk abinda kikace ai shiza'ayi. Allah ya kaimu anjiman zanzo, murmushi tayi tana fadin yauwa abin sona, Allah yakawo ka lafiya. Tana kashe wayar Lawisa tace iye, ashede yayar tawa ta iya soyayya? Maimuna tace yanda nakeson Saraki ai dole na nuna mashi soyayya. Lawisa tace ammafa wannan sunan yayi.


Maimuna tace shiyasa zanrika kiranshi dashi, amma arika kiranshi da wani Alhaji sekace tsoho. Dariya suka sa Lawisa tace gaskiya kam, tashi muje mudora mashi abincin kada yazo bamu gama ba. Ammafa duk yanda zece kici kice bakicin abun, kindafa wani abu kinci.


Zaune suke afalo an shirya mashi kayan abinci, Maimuna taci kwalliya tayi kyau sosai, Saraki se kallonta yakeyi yana murmushi, shide Allah yasa mashi sonta, tunda yake betaba jin son wata mace kamar nata ba.


Bayan sun gaisa tazuba mashi abinci da zobo a kofi, hannu tasa tadauki kofin tana fadin yau banaso Sarakina yasha wahalar komai, ni na girka kuma nice zan baka. Dariya yayi yana fadin kice yau nidin dan gata ne? Kofin tasa mashi abaki tana fadin kullum ma zaka kasance dangata.


Murmushi yayi yana fadin nagode, haka tafara bashi abinci abaki yanaci yana lumshe ido, kallonta yayi yace to kema kawo in baki. Murmushi tayi tace aini tun ina yarinya banason dambun shinkafa, ko mama ta dafa sede ta dafa mani wani abun.


Jinjina kai yayi yace ina matukar sonshi, kuma ina fata idan kinzo gidana inkoya maki cinshi? Maimuna tace idan har zaka iya koya mani to ni kuma zanyi kokari inkoya badan komai ba sedan yana cikin kalar abincin da kakeso, ni kuma ina matukar son inso abinda kakeso.


Haka sukayita fira har yagama cin abincin, bayan yayi sallar la'asar yace zetafi. Lawisa ce tashigo tana fadin yauwa Yaya, ina ganin maganar tafiyarmu Darazo kawai muje jibi. Kallonta yayi yace wace Darazo kuma?


Murmushi Lawisa tayi tana fadin wajen kawunan mu mana, ai kace kafiso a daura maku aure acan, ni kuma naga ko limami ze iya daura maku aure base anje can ba. Kallonta yayi yace kawai kibar wannan maganar.


Tunda kunce bakuda wasu yan uwa sosai. Kawai zan samu liman din unguwarmu yazama waliyinta se a daura mana aurenmu. Lawisa tace amma yazakayi da yan uwanka? Tsaki yaja yana fadin, Kawuna ne kawai zan fadamawa tunda shine waliyi na, kuma nasan beda wata matsala shide kawai yaji kudi.


Murmushi sukayi, Lawisa tace to ai shikenan duk abinda kakeso shizamubi Yaya. Kallon Maimuna yayi yace Gimbiyata nifa inaso ayi aurenmu da wuri banaso ku wahalar da kanku, duk abun bukata akwai agidana ke kadai yake jira.


Murmushi tayi batace komai ba, kallon Lawisa yayi yace zan baku kudi kushiga kasuwa kuhado kayan lefe, kema kisiyo duk abinda kike so, zanje nasamu Kawu muyi magana nan da sati 2 za'a daura mana aure.


Lawisa tace sati 2 yaya basuyi kadan ba? Murmushi yayi yace habade, kinsan yanzu nakosa inga Gimbiyata akusa dani, ada sam aure be dameni ba, amma haduwata da ita yasa nakeji ko sati daya wahala yakemun batare da ita ba.


Lawisa tace toshikenan Allah yakaimu yasa alkhairi, yace amin, Kema seki hada kayanki dan bazamu barki anan ba. Zaro ido tayi tace gaskiya Yaya kayi hakuri bazan iya bin ku ba, nafiso nazauna nikadai zefi mani. Kallonta yayi yace haba Lawisa nifa bawai zama nacika yiba, kinsan dan kasuwa.


Idan kina tare da ita ai zaki debe mata kewa ko? Lawisa tace tonaji, duk ranar dazaka bar garin nizanje intayata zama harka dawo, amma gaskiya bazanje inzauna daku ba. Jinjina kai yayi yace shikenan tunda kince haka, amma zaki tashi daga gidan nan, akwai wani gidana dayake Yalwan tudu zaki koma can dazama.


Godiya sukayi mashi yace ai bakomai,gobe zan aiko maku kudi zansa Babaye yazo ya kaiku duk inda zakuje. Sukace to sungode. Bayan yatafi Lawisa tace Maimuna kinje de abinda yace, yanzu ya zamuyi gashi dazu boka ya lalata mana aiki.


Tagumi Maimuna tayi tana fadin wallahi nima shinake tunani, ko yaya de ace kaje ma mutum da kwari yafi. Lawisa tace bara ayi magrib muje wajen Gaje, nasan zata temakemu. Maimuna tace yauwa hakan zefi, ko nawa ne zamu bata inde zata hada mana kayan mata.




Haka suka je wajen Gaje, dubu 50 suka aje mata haka ta hada masu kayayyaki masu kyau, tabasu. Haka suka tafi Maimuna tafara amfani dasu. Washe gari Saraki yabama Babaye mota da kudi masu yawan gaske yace yakawo masu kuma ya kaisu kasuwa.


Haka sukarika shirin biki, duk wani abu da suke bukata wajen Gaje suke zuwa, sun maidata uwar dakinsu, kasancewar suna sakar mata kudi yasa ta rikesu hannu biyu, Maimuna takara kyau, gyara ya ansheta.


Medinki yagama mata dinkinta, haka suka shirya komai, ana saura kwana biyu biki Saraki yazo ya daukesu da kayansu yakaisu gidan da Lawisa zata zauna, duk abubuwan bukata yasaka mata, haka suka koma sukaci gaba da shirin bikinsu acan.


Babu wasu kawaye abikin, Gaje ce kawai se mutanan ta data gayyatar masu sukaje, sunyi abinci merai da lafiya Saraki ya kawo masu lemuna kala kala. A masallaci aka daura aurenshi inda Limamin yazama waliyin Maimuna shi kuma Kawunshi.


Manyan mutanan da sukazo daurin auren suna da yawa, kowa yana tayashi murnar auren da yayi, duk wanda yaga Lamido Saraki yasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa. Haka aka gama daurin aurensu akan sadaki dubu 50. Bayan kowa yaci yasha mutane suka fara tafiya.


Aranar da dare Saraki da kanshi yaje dauko amaryarshi, motar matan Kawunshi kuma daban, haka suka shiga gidan, wajen Gaje Lawisa ta kaisu, bayan sun gaisa tayi masu fatan alkhairi, dan sun dauka itace mamar Maimuna. Haka aka fito da Maimuna aka sata motar Saraki, sauran Jama'ar Gaje kuma suka shiga sauran motocin.


Bayan an kaita Saraki yabasu tukuicin dubu 100 haka sukayita godiya sukayi mata sallama, Daki suka shige ita da Lawisa, se kuka sukeyi, Lawisa tace tabbas ayau nasan zanyi kewarki, amma bakomai nasan arzikinki ne yakirawoki, kada kimanta da abinda nafada maki, banaso Yaya yagano wani halinki marar kyau.


Wannan sabon layi ne nasiyo maki, kicire wancan ki karya kisa wannan, banaso kowa yasan kina da wannan layin, kome kenan zamuyi waya, kuma kada kisake ki kirani wayar sirri idan mijinki yana gida, kome zakiyi kirika bari se baya nan. Haka tayi mata sallama suna ta kuka haka suka rabu.


Ango da amarya semuce asha amarci lafiya👫.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA
DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻

Nah
Marubuciyar Zamani


NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)


www.NabilaLady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey


Part 20 ⏩ 25


Haka Saraki da Maimuna suka sha amarcinsu, gaba daya Saraki ya susuce akan Maimuna, be taba cintar kanshi cikin farin ciki ba seda ya auri Maimuna. Domin Maimuna ta iya kula da miji, tasan duk wata hanya da zata sa miji farin ciki.


Gashi ta iya girki kala kala, tunda sukayi aure bata taba bata mashi rai ba, yau satinsu 2 da aure komai na gidan ya canza, hatta da Babaye ta hanashi yin girki itace take bashi, cooler guda ta ware mashi, duk abinda ta dafa seta zuba mashi.


Sam girki baya damunta, kuma baka taba ganin tayi abinci so daya arana, haka kuma ta hana Saraki cin abinci awaje, ko baze dawo gida da rana ba, seta bama Babaye abincinshi ya kai mashi office dinshi.


Yanzu kam hankalinshi ya kwanta, kowa yaganshi yasan yana cikin farin ciki, ga harkar kasuwancinshi se kara habaka takeyi. Babaye yasa ya koyama Maimuna mota, haka ya dauki wata babbar mota me tsadar gaske yabata amatsayin kyautarshi.


Duk halin da Maimuna take ciki kamar a gaban Lawisa akeyinshi, domin babu abinda take boye mata, duk wata kulawa Maimuna tana bama Lawisa, kuma kome ta girka inde na dadi ne seta aiki Babaye ya kaima Lawisa.


Tunda Babaye yake zuwa gidan Lawisa idan taganshi gabanta yake faduwa, shikam sosai take burgeshi, ko Maimuna bata aikeshi gidan ba haka nan yake zuwa mata fira, ita ko sam jikinta yaki yarda dashi, shiyasa ma tace ma Maimuna zata rika kulle gidanta idan ta aikoshi setayi mata waya.


Babu yanda ya iya haka ya kyaleta, domin so 2 yana zuwa yayita buga gidan amma seyaji shiru, ko ya kaimata sako data amsa take kulle gidan yatafi. Cikin siyasa Lawisa tasa saraki ya siya mata mota, domin duk abinda ta tambayeshi yana mata.


Yanajin dadin yanda take kiranshi da Yaya, haka kuma bata taba zuwa gidan idan yana nan, har magana yake mata na rashin zuwanta wajen Maimuna, haka kuma tahana Maimuna tasashi yayi mata wani abu. Wannan abun da sukeyi bakaramin kara masu kima yake a idonshi ba.


Kuma sosai yake ma Lawisa aike, a yanzu Lawisa tazama babbar mace, duk inda zata shiga a garin bauchi to acikin mota take zuwa, yanzu harkarta ta cigaba, harda kana nan samari takeyi, sede kuma itace take biyansu, idan kuma manyan Alhazai ne sune suke biya.


Ko wane namiji sede yazo gidanta, dan ita bata zuwa gidan kowa, haka zalika bata kwanciya ita kadai, kasan cewar gidanta ba cikin mutane yake ba, hakan yasa takeyin abinda taga dama, duk wannan hidimar da sukeyi basu manta da Gaje ba, domin yanzu tazama yar uwarsu.


Watan Maimuna 5 ta aure amma haryanzu shiru babu komai, sosai Saraki yafara damuwa, domin ya kwallafa ranshi akan samun haihuwa, gashi yanaso yaje asibiti sede yana tsoron abinda zeje yajiyo, hakan yasa ya kara hakuri.


Ana cikin haka tafiya ta kamashi zuwa China, kuma tafiyar sati 2 ce, bayan ya fadama Maimuna zasu tafi unguwa seta tuno da zuwansu wajen boka, kallonshi tayi tace gaskiya banajin dadin jikina kawai katafi tunda sati 2 ne, wani lokacin idan zakaje semu tafi tare. Murmushi yayi yace kode zan samu da ne?


Murmushi tayi tace kawaide inajin gajiya ne a jikina shiyasa, kaga kada mutafi naje na kwanta na hanaka aikin daya kaika. Jinjina kai yayi yace sannu, aikece ba kya gajiya,ko aikin gidan nan ya isa yasaki gajiya.


Nace maki kirika abinci so daya idan yaso na dare semu fita muci awaje amma kince baki yarda ba. Murmushi tayi tace nifa bana son abincin waje, kama dena wannan maganar. Dariya yayi yana fadin kina tsoron kada wata ta kwace maki ni ko? Hararshi tayi tace ai babu wadda zata kwacemun kai.


Bara na hada maka kayan dazaka tafi dasu, kallonta yayi yace amma gaskiya naso ace tare zamu tafi, amma idan naji nakasa hakura kawai zan dawo, murmushi tayi tace aikuwa fushi zanyi da kai matukar kadawo baka gama abinda ya kaika ba, kasande inason duk wani abu daze kawo maka cigaba.


Dan haka kadena kawo wasa acikin harkar kasuwancinka. Jinjina kai yayi yace hakane, shiyasa kullum nakema Allah godiya daya bani ke, domin kinsan muhimmancin komai nawa, Allah yayi maki albarka.


Zansa Babaye yarika kula da komai, har nadawo, kuma Lawisa zata dawo nan domin ta tayaki kwana. Haka tagama hada mashi kaya, kitchen ta nufa domin ta dauko ma Babaye abincinshi, hanyar waje ta nufa domin takirashi yazo ya dauka taga yau ya dade bezo ya karba ba.


Cak ta tsaya tana kallon abinda yake faruwa, wata budurwace taga tafito daga bangaren Babaye shi kuma yana bayanta se dariya sukeyi, seda ya leko sannan yayi mata alamar ta taho, haka ya rakata har gate, ya bude mata tafita sannan yanufo gidan domin ya karbi abincinshi.


Saurin komawa tayi tana mamaki dama Babaye yana kawo mata? Jinjina kai tayi se kuma ta tuna abinda Lawisa tace mata idan yaje seyayi ta kallonta. Bayan yashigo suka gaisa tace Babaye ai naleka inkiraka naga bakazo ka karbi abincinka ba se naga baka nan.


Kanshi yafara sosawa yana fadin wallahi nashiga dakine nadan kwanta se bacci ya daukeni. Murmushi tayi tace Allah sarki, gashinan kadauka.


Washe gari haka Saraki yakira Lawisa yace tadawo nan gidan dazama kafin yadawo, bayan sun gama yayimasu sallama ya ajema maimuna kudi masu yawan gaske, Babaye yatafi kaishi airpot.


Zaune suke agaban boka suna sauraron abinda ze fada masu. Dariya yayi yana fadin amarya kinsha kamshi, shine ko akawo mana cincin din biki. Murmushi sukayi, Lawisa tace ai kasan bawani babban biki akayi ba, bamuyi tuya ba.


Kallon Maimuna yayi yana fadin, kamar yanda nace maki idan anyi bikinki zan fada maki abinda zakiyi, abu na farko dazen fada maki, mijinki baya haihuwa. Kuma bazaki taba haihuwa dashi ba, kuma nasan mijinki yana matukar son haihuwa.


Sede haryanzu betaba sanin laifin daga gareshi yake ba, ajiya kafin kuzo nayi bincike akanshi sosai, kuma matukar baki haihuba dole seya kara aure, dan haka zanyi maki aiki 3, na farko zansa mashi tsanar kowace mace da sunan aure.


Na biyu kuma zan kauda mashi hankalinshi akan zuwa wajen likita domin yaduba lafiyarshi. Abu na 3, kuma wannan aikinki ne. Inaso kifada mani mutumin da mijinki yafi kusanci dashi? Shiru Maimuna tayi tana tunani.


Lawisa ce tace gaskiya boka babu wanda muka sani wanda yafi kusanci dashi sama da wani mutumi dayake gidanshi, domin bamu san abokan aikinshi ba, amma shi wannan mutumin sunfi shekara 2 suna zaune agida daya.


Wata irin dariya yayi yana fadin, hakika babu wanda yafi kusanci dashi kamarshi, dan haka dashine zamuyi wannan aikin. Saurin dago kai sukayi suna akallonshi. Daure fuska yayi yana fadin Babaye ko? Kai suka daga mashi.


Wata kwarya ya dauko yana fadin, mijinki yayi tafiya ayau,kuma ze dawo nan da sati 2, amma bazan barshi yadawo ba se nan da wata 1,domin aikin dazan saki yana bukatar sati 4. Idanuwa kawai suka zuba mashi suna jiran abinda ze fada masu.


Dago jajayen idanuwanshi yayi yace daga yau inaso Babaye ya maye gurbin mijinki harya dawo. A zabure suka mike tsaye kamar zasu fadi. Wata irin tsawa ya daka masu wadda seda
tasasu gigicewa. Haka suka zauna kamar zasu saki fitsari.


Kara kallonta yayi yana fadin, idan har kinaso mucigaba da tafiya dake, daga yau kada ki kara nuna tsorata akan duk wani aiki dazan saki, idan ba haka ba zansa aljanu suyi maki aiki. Cikin rawar murya Lawisa tace tuba muke.


Wani garin magani ya dauko yabama Maimuna yace wannan shikadai zan baki, amma bazan te makeki akan yanda zaki shawo kan Babaye ba, sede idan kukayi kwanciya ta farko shine zaki dafa mashi abinci da wannan garin maganin, dayaci shikenan ze manta duk wani abu da kukayi dama wanda zakuyi daga yau har sati 4.


Kuma daga wannan sati hudun da zakuyi atare shikenan bazaku kara aikata komai ba, domin bukata zata biya, kuma baze kara kallonki da kun aikata wani abu ba, komai ze wuce agurinshi, sede duk ranar da asirinki ya tonu dole ze tuna komai. Sannan adakin mijinki da kuke kwanciyar aure dashi anan nakeso kurika kwana kedashi har nan da tsawon sati 4.


Idan har kika kasa shawo kanshi ayau to ina me tabbatar maki zaki rasa mijinki, domin ze karo aure wanda zesa soyayyarki ta rauna na azuciyarshi. ke macece kisan yanda zaki shawo kan Babaye. Idanuwan Maimuna cike da kwalla tace atemaka mani boka, idan narasa Saraki bansan yazanyi ba.


Idan Babaye yaki amincewa da bukatata nasan zetona mani asiri kuma Saraki korata zeyi. Dariya yasa yana fadin shikenan za temakeki da abu daya, wata laya yamiko mata yana fadin, bazakiyi amfani da ita ba harse kinga yaki amincewa da bukatarki sannan zakiyi amfani da ita, amma kada kice daga kin gwada sodaya zaki danna.


Domin ko kinyi bazatayi aiki ba, se kinga tura takai bango sannan. Hannu biyu tasa ta amsa tana godiya, dubu dari 2 suka aje mashi yace sena kara ganinki. Dariya yasa yana wasu surutai.


Zaune suke a falo Maimuna ta buga tagumi, dafata Lawisa tayi tana fadin haba Maimuna, meye baki gani ba? Meye ze baki tsoro arayuwa yanzu? Kada kimanta tun kina secondary kika rasa budurcinki, duk wannan be baki tsoro ba se wannan karamin abun?


Kuma fa Boka yace da kunyi na yau ze manta duk abinda yafaru da wanda ze faru wanda zaku aikata matukar yaci magani acikin abincinki. Maimuna tace Lawisa nasan mutuncina ze zube a idon Babaye.


Murmushi Lawisa tayi tace lallai Maimuna bansan bakiyi kwari ba , domin idan har wannan karamin abun ze gagareki to wallahi gudo warki daga gida batada amfani. To bara kiji, idan dare yayi kiyi wanka, kiyi kwalliya da matsiyatan kaya masu jan hankali, sannan kileka ki kira Babaye.


Yana zuwa cikin tashin hankali kice mashi kinajin motsi adakin mijinki, tunda kince mun Babaye manemin mata ne, nasan bazakisha wahala wajen kamashi ba. Yana shiga dakin kawai ki kulle kofar ki fada mashi.


Babu wani lafiyayyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login