Showing 27001 words to 27756 words out of 27756 words

Chapter 10 - KULU BOOK COMPLETE DOCUMENT BY RIAMCOOL.txt

RIAMCOOL   

20 Dec 2024

2367

ya ɗauki zafi




zoben nan aka fara sakawa Bayi wan da kowa aka saka mawa bai kawo jaa, duk layin wani idan yazo sai zuciyata ta sake bugawa, ga ko ina da tsaro babu damar guduwa, layi ne yazo kan Bintu wacce daga ita sai ni, hawayen dake maƙale a idanuwanta na shanye lokacin da layi yazo kaina hannayena na miƙa ina mai rintse idanuwana, da fatan Allah ya sa ba nice Jinin JOHAAN ba, shirun da naji na ƴan daƙiƙu ya bani damar buɗe idanuwana, wani kalar zaro idanuwa nai ina girgiza kai ganin Zoben ya nuna ja a dutsen, bakina ya fara rawa hawaye suka fara fitowa a ciki




kowa na wajen sosai yake kallona musamman Sarkin dake man da wani kalar tsinannan kallo mai nuna zallar tsana, ban ida dawowa daga ruɗun dana tafi fa naji an wani harɗeni da sarƙa mai masifar zafi wacce tai sanadiyyar faɗuwata ƙasa kaina na buguwa da girkakken dutsen dake ajiye, nan take na ƙwalla ƙarar azaba jini na tsartuwa




Tun lokacin da jan ya kawo a zoben ABIODUN ya rintse idanuwansa bai ida dawowa hayyacinsa ba sai da yaji ƙararta buɗe idanuwansa yai yaci karo da jinin dake tsartuwa a goshinta da bai kasance mai dauriya da wayancewa ba tsab za ka iya karantar yanayinsa na shiga tashin hankali




Bintu kuwa wacce bata da dauriya tuni ta fashe da kuka tana furta "na higa ukku ni Bintu za su kashe Kulu" da mugun gudu ta nufi wajen mai martaba tana faɗuwa " mai martaba kai man rai karka kahe mun ƴar uwa"


ƙafarsa Mai martaba ya saka yana shure Bintu tare da bada umarni a haɗata da Kulu a ɗaure wacce turjejen da take da burburwa ya harduƙa wani Dogari ya bugaa mata babban ƙarfen dake hannunsa a kai wanda ta tafi Luuu ta faɗa a hannun *MATEO* wan da shigowarsa kenan a masarautar da wani kalar kallo yabi ta yana ida yada ita ƙasa tare da yatsina fuska


Ihuuu mai ƙarfi na fasa ganin numfashinta ya tsaya cakk, ga jinin dake zuba tamkar an buɗe famfo,cikin rashin imani wani bafaden ya fara jana da sarƙar a ƙasa wanda duk inda ya ja sai wurin ya kwalje yana tsirtuwar jini


Har akan ƙafar mai martaba aka jawoni wan da a lokacin na fara ganin dishi_dishi bakina ya gaza buɗe wa,cikin rashin imani da tsana Adewale Femi ya saka ƙafafuwansa yana take man wuya tare bubbuga mun sandar hannunsa, hannu ya miƙa aka bashi babban karfen daya tanada a cikin wuta hannayena ya kama yana aza mun ƙarfen yayin daya sake buga mun kai da wani dutsen nan take jinin ya biyo hancina da baki, yayin da naji dukkan wani numfashi da motsi ya tsaya mun




Wata gigitacciyar ƙara ABIODUN ya saki yayin da hankalin mutane ya dawo kanshi a ciki harda mai martaba, dake kallonsa a mamaki ganin yanda jikinsa ke rawa haka zalika hawaye na biyo kuncinsa


"Abinda kake gudu tabbas ya faru me yasa za ka min haka ba ita ya kamata ka hukunta ba ni yadace ka fara hukuntawa kafin ita domin ita ba tada laifi nine da laifi da har na aureta,a halin yanzun ta zama mallakin ita ɗin matata ce ita ce wacce na zaɓa akan rayuwar masarautar .........."








Alhm anan na kawo qarshen littafin kulu Book 1 mu haɗe a Book Two


*To fa yanzun wasan ya fara,yanzun ne lvr kulu da buɗe shafin ƙaddararta zai soma,shin me ke faruwa da masarauta JOHAAN , su waye ke ƙulla tuggu da makircin kashe ARUSH da Yaronta,wace ƙaddara ce ta bibiyi Arush a tsawon shekaru ,wace mai sace Mata yara wacce ita ce sanadin sace Kulu a halin yanzu kuma take neman kawar da ita, shin za tayi galaba wajen haukatar da Arush kuma ta kashe Kulu kamar yanda tai iƙirari shin wai wace gaba ce tsakanin masarautu biyu da har HANDAASH ta tsani jinin JOHAAN shin ya Kulu da Bintu za su kasance kashesu za a yi kokuwa, me zai biyo baya baya ga jin furucin ABIODUN, ku biyoni a Book Two wan da zai baku amsoshinku ya warware muku cakwakiya da sarƙaƙkiyar dake ciki, ku sani fa KULU ba a fara komai a cikinsa ba yanzune lvrn zai fara cike da tarin abubuwa, idan kina son mallakar na biyu za ki biya ɗari Ukku kacal ta wannan Account ɗin 9074759493 Maryam zubairu sani opay bnk idan kuma kati ne za ki turo na ₦400 za ku turu shaidar biyanku ta wannan number 09074759493*








*Mai son tuntubata ga number 09074759493 or 08109554986 *

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login