Showing 18001 words to 21000 words out of 27756 words

Chapter 7 - KULU BOOK COMPLETE DOCUMENT BY RIAMCOOL.txt

RIAMCOOL   

20 Dec 2024

2368

can go"










Ok na furta ina russunawa ƙasa na fice, wani wahalallen ajiyar zuciya ya saki yana taune lips nashi na ƙasa, sam ya gaza fahimtar al'amarin da akwai tarin ƙaddarori da dama dake tunkarosa shi ya san da haka, bai san lkcn da wasu tarin hawaye Masu raɗadi suka zubo masa ba wan da shi kaɗai ne yasan dalilin zubarsu


Tun lkcn dana fita nake sauri sauri ina sauka daga Stairs ɗin,kaina na Sara min tamkar zai tsage gida biyu, ga wani zazzaɓi da nake jin yana son rufeni, na tabbatar bai rasa nasaba da yunwar dake ƙwaƙular hanjin cikina,




Kai tsaye inda muke karɓan Abincimmu na nufa ina bin layi har yazo kaina, Flat na miƙa aka zuba min Teba da miyar kuɓewa wacce sam ba sonta nake ba amma tsabar yunwar dake addabana zai sakani naci




Wuri ɗaya na samu ina zama tare da zubawa Flat ɗin Abincin ido ruwan hawaye na ambaliya a kwarmin idanuwa wllhy ko a mafarki ban taɓa tunanin zanyi rayuwa kalar wannan ba, na tabbatar da qaddara zanen zabo ce, haka zalika ina ji a jikina yanzu ne Alƙalamin ƙaddarata ya soma rubuta ƙaddararriyar rayuwana, yau she ne zan cinye jarabtar da Ubangiji ya ɗora min? wannan ne ban sani ba, Allah da ya jarabceni da hakan shi zai yaye man damuwata, na tabbatar da Ubangiji ba wai baya sona bane da har yayi ni haka ya mayar dani ƙasƙantacciya, wacce na zamto baiwa mai bautawa wasu tun ban san wace ni ba ban mallaki hankalina ba, "yanzu haka zan ƙare wane zai auri baiwa?? na samu nima rayuwar ƴanci na tabbatar a haka rayuwata zata qare cikin azaba da bautatawa ba tare dana raya sunnar ma'aiki ba," na ƙarshe mgn a hankali tare da sake zubar wasu siraran hawaye waɗanda ban san ranar daina zubarsu ba






ba don raina yaso ba haka naɗan tsatstsakura naci ba tare da ina jin daɗin Abincin ba,






Kwanaki na tafiya makwanni na shuɗewa sam babu wani canji haka koda yaushe nake azabtuwa da ayyuka waɗanda suka lillinku,sosai na fara ƴar rama tsabar damuwa dana fara sakawa kaina, wani lkcn nakan sha kuka ba adadi, ban da mai rarrashina sai Bintu wani lkcn kuma sai dai na rarrashi kaina,




A hankali nake bin bishiyoyin cikin masarautar da kallo ina mai lumshe idanuwana wannan shi ne karo na farko da nai tafiya mai tsayi a masarautar nan harya kawoni ya zuwa wajen daya wadatu da korayen bishiyu, ga wani sassanyan ni'ima da iska dake ratsa jikina ban san lokacin dana saki murmushi ba ina nufar babbar ceɗiyar da ta wadatu da ganyayyaki harta saki wadatacciyar inuwa mai sanyi,zamewa wajen nayi ina mai sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da duban gefena wan da nake jin sautin tafiya, saurin janye idanuwana nayi ganin wan da ke tunkaroni fuskarsa ɗauke da wadataccen murmushi wan da yake fallasa man abubuwa da dama, "Prince ABIODUN " na ambata a hankali zuciyana na sake man dukan ukku ukku duk tako ɗaya da zai yi




A hankali ya fara yawo da idanuwansa ya zuwa fuskarta yana mai sake sakin murmushin daya ƙara fallasa sirrin kyawunsa, "JOSINA" ya ambata a hankali wan da wannan sunan da shine yake kirana,sakamakon ce masa da nai sunana ne a haka






ba tare da na ɗago da fuskana ba na amsa da "Yes Sir" ina mai sake makure jikina waje ɗaya, ɗan ɓata fuska yai yana furta "Stop calling me Sir" ya faɗa a shagwaɓe




shiru nai ba tare da na bashi amsa ba ina mai wasa da yatsun hannayena




"you can be a friend from today" naji saukar muryarsa wacce tai man ámsa kuwa sanna na daina jin wani gamsasshen iska na ratsa jikina, lkc guda na tsinci kaina da zuba masa idanuwa waɗanda lkc guda suka tara ruwan hawaye, "wllhy sam ban dace da kamar ka Mutum mai daraja da ƙima a idon duniya za kayi Abota da ƙasƙantacciyar baiwa kamarni ba, na tabbatar na amince ban yiwa maka adalci ba,kayi haƙuri na zauna a iya matsayin da nake" na ƙarshe zance da sauke idanuwana a ƙasa




Shi kanshi ya san da cewar tabbas gsky ta faɗa amma sai dai sam zuciyarsa taƙi bashi damar gazgata hakan,sannan bai taɓa jin cewar zai iya cika Alqawarin Mahaifinsa KULU ita ce sanadin dukkan juyawar rayuwarsa da buɗe masa shafin kundin ƙaddararsa


A hankali ya sauke idanuwansa a kanta yana mai furta "ke sam ba baiwa bace kar kiyi tunanin ko ban san asalin ki ba, ki sani tun kafin shigowarki a masarautar nan na san da cewar ƙaddarata zata gibta a tsakanina dake,tun ganin farko da nai maki Alƙalamin ƙaddarata ya sauya, nasan asalinki nasan jininki, a wannan karin KINGDOM OF JOHAAN sunyi nasara, sai yanxu na idar da gazgata zancen mahaifina cewar ba hasashena bane" wan da duk wannan zancen da yake yana yi ne da harshen turanci wanda idanuwansa sun kaɗa sunyi, ja lkc ɗaya jijiyoyin kansa sukai ruɗu ruɗu, yana miƙewa ya bar wajen




Kallo na bisa dashi wan da sam na kasa gane zancen da yake man "ko dai ya zare" na furta a hankali "na san jininki a wannan karon KINGDOM OF JOHAAN" na maimaita mgnr ƙarshensa a hankali wacce ita ce tafi tsaya man,sosai na shiga tunanuka da dama da kuma ruɗu, da damuwa






*ABIODUN*


Tun lkcn da ya bar wajen KULU ya samu wata bishiya yana zamewa a hankali wasu siraran hawaye Masu zafi suka fara wanke masa fuska ya gaza sarrafa kansa a ta wannan ɓangaren wace ƙaddara ce ke gabatoshi da son haɗa jini da maƙiyansa, tun tasowarsa babu wani abin da yafi tsana sama da KINGDOM OF JOHAAN, sai dai jarabta da ƙaddarar ce zata kasance a haka KINGDOM OF JOHAAN sunyi nasara a wannan karon ba zai iya tsallake tarkonsu


Ya faɗa komar son KULU son da ba zai iya ciresa ba son da yake ji koda yankan naman jikinsa take ba zai iya rabuwa da idata ba, a da bai gazgata cewar ita ɗin jinin JOHAAN bace sai da bincikensa ya tabbatar masa haka zalika idanuwanta sun tabbatar masa da ita ɗin wacece ................






*RIAMCOOL ce*


*Writer of*




RUSHEWAR RAYUWA


BAYAN WUYA


ANYA UBA NE


AND NOW




*KULU*
[10/23, 9:04 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u




*Masu so daga farko kuyi fllwng wannan channel ɗin*


*KULU*


*BY RIAMCOOL*


*MIKIYA WRITER'S ASSO......*




*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM*


P.25&26


A hankali siririn hawaye suka soma zarya a kumatunsa, wan da bai san da zubarsu ba sai dai yaji ɗuminsa, kenan hasashen tsayin shekaru da bincike zai tabbata, sosai ya daɗe a bakin bishiyar yana mai jin zuciyarsa da tamkar ba a ƙirjinsa take ba




Ganin kansa ya fara sara masa ya saka shi miƙewa yana fitowa in da ya bar fadawansa nan ya samesu ba tare da yai magana ba ya fara tafiya tamkar wan da aka zarewa lakka, kai tsaye sashensa ya nufa domin bai san wata hayaniya, yana so ne ya keɓe shi kaɗai ya samu nutsuwa da damar yanke mafita






Ruwa ya samu ya ɗan ƙara watsawa yana kwanciya zaɓi ɗaya gareshi ko dai yabi mafitar da Mahaifinsa ya yanke na barin masarautar ko kuma ya faɗa wa Mahaifinsa wacece KULU 'sai dai a ɓangare ɗaya na zuciyarsa bai jin shawara ta biyun za ta yiyu muddin Mahaifinsa ya gano wace ita a Masarautar nan to tabbas kuwa mummunan hukunci ne zai yanke a kanta wan da bai fatan tabbatuwar hakan, sosai yai nisa a dogon tunani wan da sai dai yaji hannu na yawo a fuskarshi, buɗe idanuwan nasa yai yana saukesa akan Awujonsa wacce itama ta kafesa da idanuwa tana mai karantar yanayinsa




"Think about what you are" ta tambayesa cikin kulawa da ƴar damuwa, yatsina fuska yai yana furta "nothing I have a headache" da damuwa fal a ranta ta furta
" let me call you Family Doctor"




"No I will drink medicine, tea I need to drink" ya furta a ɗan shagwaɓe murmushi tai tana shafa kanshi tare da miƙewa sawa tai aka haɗa masa wanda da kanta ta bashi yasha sannan ta bashi maganin sai da taga yai bacci sannan ta bar ɗakin






*KULU*


ni kuwa sosai na daɗe a wajen ba tare dana gano kalma ɗaya da yake nufi ba, ganin ba zan gano ba ya sakani miƙewa ina nufar sashen Bayi ban sami kowa ba sai Bintu wacce ke kwance itama a lokacin zazzaɓi ne ya rufeta,




zama nai ina mai taɓa jikin nata naji da sauƙi domin babu zafi, "kin sha magani?" na tambaye ta a hankali




girgiza kai tayi hawaye na fita a idanuwanta "a a ban sha ba, ban san inda ake karɓowa bane"


shiru nayi ina share mata hawayen daga bisani nima na haɗe kaina da guiwa ina mai sake jin matsatsin rayuwa,




Washe gari tun da na tashi na gabatar da aikina tsaf komai na haɗa masa sai sannan na tafi dan sam ba nison haɗuwata dashi, nufina idan ya gama nazo na kwashe wuraren da yaci abinci


Bayan an ɗan jima na koma sai dai yanda na kawo Abincin haka na iske shi da alamar ma ko taɓawa ba ayi ba, Bedroom ɗin na shiga sai dai ƙarar ruwan da naji ya tabbatar min da cewar yana Toilet , Wani wahalallen numfashi na sauke "kenan haƙata bata cimma ruwa ba?" na tambayi kaina




Ina tsaye a wajen ya fito ba tare da na kalles ba na furta "Morning Sir"




hannayensa zube a Aljihun wando fuskarsa da wadataccen murmushi ya furta "Morning too"




kujeran Dining ɗin na ja masa ya zauna tare da serving ɗin shi ,


"sit down and eat" ya furta ba tare da ya kalleni ba, zaro idanuwa nai ina girgiza masa kai alamar ba zanci ba, ɓata fuska yai yana furta "I will stop eating too if you don't eat."


Kallonsa nai ina sakin murmushi da mamakin yadda yake tamkar wani ƙaramin yaro, ba tare da naso ba haka na zauna naci Abincin duk yanda naso tafiya hanani yai yana zuba min fira wan da nima samun wuri ya sa na manta matsayin da nake na biye masa,




Bayan watanni kaɗan wanda a lokacin mun cika shekara ɗaya a masarautar sosai abubuwan suka juye man yanda banyi zato da tsammani ba, ta tsakanina da Prince ABIODUN,sosai muka shaƙu shaƙuwar da na gaza tantancewa, wacce a hankali ta fara rikiɗa ya zuwa soyayya me zafi wacce ni kaina a lkcn nasan da cewar tabbas ba'a kamu da son ABIODUN duk da nasan yaudarar kaina nake ko kaɗan ba zan taɓa zamowa mallakinsa ba duba da matsayin da nake








hawaye ne suka fara wanke mun fuska lkcn da na tuna ba fa zan taɓa mallakarsa ba, hannayen da naji a kuncina shi ne ya bani damar ɗago da idanuwana na saukesu a kansa wan da shima kallon nawa yake


"why are you crying" ya tambaya a hankali da ƴar damuwa "Remembering that there was a time when we parted and all the pain we did with you,na faɗa a hankali da ƙara shigar da manyan idanuwana a nashi waɗanda suka tara ƙwalla girgiza kai yayi yana furta "Don't even think about that, I'm not ready for a life of separation, we'll have each other for a long time even though I know who you are." ya faɗa yana mai furzar da iska hannayensa na a fuskana wan da a hankali ya fara yawo dashi ya zuwa wani sashe na jikina wan da yake san cimma wani ɓangare saurin riƙe hannayensa nai ina girgiza masa kai


Ina mai furta "Ka daina taɓa jikin da bai zama mallakinka ba, duk da nasan kai a Addininka bai zama laifi ba amma a nawa Addini ina saɓawa Ubangiji ko kaɗan ni ɗin nasan ba zan taɓa mallakarka ba ko da ace kowa naka ya yarda za mu zama mallakin juna Addinina bai bani damar mallakarka ba sbd Addinina da naka ba ɗaya ba" na furta ina mai sauke idanuwana a ƙasa




hannun nashi ya fizge yana mai mani kallon me nake nufi, "Josmie ban gane abin da kike nufi ba" ya furta




"Eh ba za ka gane ba sbd ko kaɗan baka fahimceni sannan tun da nake da kai ba ka taɓa sanin wacece ni ba ya nai rayuwa miye Asalina wannan duk baka sani ba" na furta ina mai sake nisantar jikina da nashi


A ɗan zafafe ya fara magana "Josina Don't think that I don't know what I'm doing, don't play with my mind, you know that I know who you are, you are the bloodline of the kingdom of Johaan and the daughter of the king Valentino"




Sosai brain ɗina ya cunkushe da maganganunsa na gaza gane me yake nufi me yasa yake kirana da jinin wata masarauta baya ga ni ɗin ba wata bace face baiwa wacce bata san mulki ko sarauta ba baya ga bauta, sannan ƙasƙantacciya har yake wani kirana da ni ɗin jinin wani mulki ce sannan ƴar wani sarki wai Valentino




"ka yarda da abinda na ce maka wallahi ni sam ban san wata masarauta wai ita JOHAAN ba za kayi mamaki idan nace maka ni ɗin tsintacciyar marar ƴanci ce ban san wani mulki ko sarauta ba, a zamana da kai na wani san daɗin zama da mutum kafin wanzuwar ka Ni kaɗai ce a duniyata hasali ma ba nida iyaye tun asali ban sansu ba, ni ɗin tsintacciya ce marar ƴanci rashin ƴancina ne har ya saka ni zamowa baiwa a masarautarku zatona ko tunani bai taɓa kawo man da cewar zan yi wata rayuwa a masarauta ba, ni ɗin sam ba ƴar asalin yanki bace, za ka ƙara mamakin jin cewar ni ɗin daga AREWA nazo masarautarku ka yarda dani ban san wata Masarauta ita JOHAAN ba" na faɗa da son ya gazgata zancena




Mamadin naga yarda a idanuwansa sai naga yana bina da wani tsinannan kallo wan da tun zamana da shi bai taɓa man wato kallon kin raina man hankali da kuma ƙarya nai masa................








*Posting zai dawo a iya kwanaki biyar ma'ana zan cire Asabar da Lahadi *






RIAMCOOL ce


*Writer of*




RUSHEWAR RAYUWA


BAYAN WUYA


ANYA UBA NE


AND NOW


*KULU*
[10/23, 9:05 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u




*Duk wacce ke so daga farko za ki iya fllwin Channel ɗina*


*KULU*


*BY RIAMCOOL*


*MIKIYA WRITER'S ASSO.....*


*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM*




*P.27&28*




"Josina don't think I don't know what I'm doing You think that I will believe all the words you say to me" ya faɗa da zummar miƙewa, hannayenshi na riƙo ina mai sake narkar da idanuwana hawaye cike tab ciki, girgiza masa kai na fara yi ina furta "Abin da na faɗa maka gsky ne wllhy ni sam ban san wata Masarauta JOHAAN ba ka yarda dani, ina mai maka rantsuwa da Ubangijin daya halicceni ni sam ba ma ƴar Asalin yankin nan bace ka yarda dani"




Jikinsa a matuƙar sanyaye ya ranƙwafo yana saka hannayensa ya share man hawayen dake ambaliya tare da sake tsurawa ƙwayar idona kallo tamkar mai son gano wani abun, a hankali ya furzar da iskan bakinsa yana furta "kince ba kisan JOHAAN ba amma ni tabbas naga jinin JOHAAN a ƙwayar idanuwanki"




"Prince ABIODUN kar kayi saurin yanke hukunci furucin da kake na cewar kasan wace ni, ka janye shi, ni kaina ban san wace ni ba, ban san Asalina ba, waye ya haifeni duk ban sani, ba"




Wani zazzafan iska ya sake furzarwa yana mai lumshe idanuwansa wan da ya kusan kai 5 minute ba tare da yai magana ba sbd yanda yake ji, "kenan ita ɗin ba tasan wace ita ba, ba tare da manufa aka turo ta masarautarsu ba, duk da ta kasance jinin masarautar JOHAAN ce wato ƙaddara ita ce sanadin turota, taya zai fuskanci wannan al'amari???" Yaiwa kansa wannan tarin tambayoyin wan da ba shi da mai bashi amsa






A hankali ya buɗe idanuwan nasa yana zuba su a fuskarta cikin gazgatar da zancenta ya furta "na yarda dake da abin da kika faɗa man, ina son daga yanzu ki cire ran cewar ba za ki mallakeni ba, ki sa a ranki na zama naki,duk da ni kaina nasan ko zan haɗiyi zuciya na mutu ba lallai iyayena da masu mara musu baya su amince ba"




"Ni kaina na san da hakan sannan ko da ace sun Amince bai zama lallai ni na mallakeka ba, Addinina bai yarje min ba" na furta




Murmushin takaici ya saki yana furta "har iyanzu na rasa gane wane Addinin ne kike magana da har bai yarje miki da aurena ba, Josmie na gaza gane kanki ko dai ba sona kike ba iƙirari ne kawai a baki, ko dai kin shigo masarautar nan dan ki uzzurawa rayuwata da soyayyarki, Why kike son cutar da rayuwata ta hanyar sanyaya man jiki da kalamanki, kin san kalmar da nafi tsana naji ta fito a bakinki na cewar ba za mu mallaki juna ba tsakanina dake" ya faɗa da idanuwansa waɗan da suka fara canza launi


hannayensa na saki ina mai miƙewa ba tare da nai masa magana ba har sai da na ɗaga ƙafafuwana da zummar tafiya "kayi haƙuri da abinda nake faɗa maka na san da cewar kai ma ka san da gsky nake faɗa sai dai hangen ka na son cimma ƙudirinka ya hanaka gane abinda kake son cimmawa," Ina gama faɗin hakan na wuce zuciyata na mai sake buga mun na tabbatar da nayi gangancin faɗawa soyayyar ABIODUN wan da ban lura da illar hakan ba sai a yanzun








Manyan idanuwansa ya rufe yana mai gazgata zancenta but why he will do it is not their fault, it is his heart's fault da har ya gaza yarda da gaskiyar da yake gani, "Soluwole ka taimakeni" ya furta a hankali






*Adewale Femi*




Duk yan da yaso hankalinsa ya kwanta akan ABIODUN sam ya gaza hakan har a ƙarƙashin zuciyarsa ya gaza yarda da in har ABIODUN bai bar Masarautar sa ba ba zai tsallake tarkon JOHAAN ba,




Zazzzafan iskan dake bakinsa ya furzar yana mai lumshe idanuwansa zuciyarsa na sake buga masa a duk tsawon daƙiƙa ya tabbatar da ba zata daina buga masa ba har sai Jinin JOHAAN ya bar masarautar nan, da kanshi yake son gano wace ce ita da har ta sake a masarautar sa ba tare da wani yaga alama ba zai yi shiri sosai,dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login