Showing 3001 words to 4355 words out of 4355 words
Chapter 2 - KUNDIN TSATSUBA book 1 Complete littafin Yaki by Abdul'aziz Sani Madakin Gini .txt
     Daga can sarkin bokayen ya ce "Ya sarkin duniya, hakika ka zo mana da babban al' amari, amma abin da nake so da kai shi ne ka ba mu kwana uku mu je mu yi naziri, lallai ba zamu dawo nan ba sai da hanyar biyan bukata."
Ko da jin haka, sai fuskar sarki Lu'umanu ta fadada da murmushi ya ce "To shike nan, ku tafi na sallame ku, zan kasance mai sauraronku nan da kwana ukun."
Nan take suka watse suka bar sarki zaune shi kadai a turakarsa, yana nazarin al'amarin a ransa.
             Da kwanaki uku suka cika, sai sarkin bokaye da tawagarsa suka dawo ga sarki. Bayan sun kwashi gaisuwa, sai sarkin bokaye ya ce "Ya mai duniya, gaba dayanmu mun dukufa wajen bincike bisa samun biyan bukatarka, amma ba mu kai ga samun malita ba, face abu guda."
Sarki Lu'umanu va gyara zama ya ce "Ina sauraro, maza ka fadi malitar na ju
          "Idan har kana so ka samu biyan bukata, sai any kogon Zuhurum an samo tsumin dodo Kirayanu, ka sha sannan matarka zata sami juna biyu. Ya kai wannan sarki, ka yi sani cewa daga nan zuwa kogon Zuhurum tafiya ce ta shekara darı da goma sha biyu ga basamudan gwarzon saurayın aljani mai takama da karfi da samartaka. Haka kuma ka sani cewa, shi dodo Kirayanu shiryayye ne, babu wani sthiri ko karli da zai va tasiri akan sa face hikima da dabaru. A iya bincikenmu, duk duniyar nan aljani daya ne zai iya gajarce wannan tafiya a maimakon shekara dari da goma sha biyu, yayi kwana dari da goma sha biyu. Ba wani ba ne face aljani Markahul Sabus. Ka sai cewa, shi wannan aljani, shi ne mafi kyau daga cikin samarin aljanun duniya. A halin yanzu vana kan tsakiyar balagarsa, domin shekarunsa na haihuwa ba su wuce dari shida da arba in ba. saboda karfinsa da hikimarsa ake masa lakabi da Abul Hikima, wato baban hikima. A tarihin ravuwarsa bai taba sa bukata a gabansa ta gagare shi ba. Ya kai wannan sarki, ka yi sani cewa na tuntußi wannan aljani, kuma ya amince zai je kogon Zuhurum ya debo maka tsimin dodo Kirayanu, amma bisa sharadi guda. Sharadin shi ne ba zai fadi ladansa ba har sai ya zo da wannan tsumi."
           Ko da sarkin bokaye ya zo nan a zaneensa, sai sarki Lu'umanu yai shiru bai će komai ba, ya shiga tunani. Daga can sai ya dubi sarkin bokaye ya ee "Ni ma na amince, amma sai idan Markahul Sabus ba zai nemi raina ko mulkina ba, amma ko me ya ke so zan ba shi. Kuma ina so ku gargade shi da cewa idan ya kuskura ya saba daga umarnina.
zansa shi a cikin kurkukun da ba zai taba fitowa ba har iyakar tsawon rayuwarsa."
             Sarkin bokaye da jama'arsa na jin haka, suka yi zugum cikin jinjina al'amarin. Daga can sarkin bokaye ya ce "Ya mai duniya, ai masu iya magana sun ce, ciniki baya yiwuwa sai ga wuri ga kaya, bari na kira Markahul Sabus don ka jajance a tsakaninku."
"Ka yi daidai sarkin bokaye." Sarki Lu'umanu ya fadi yana mai yin murmushin samun nutsuwa.
               Nan take sarkin bokaye ya fiddo wani dan karamin kaskon tsafi, ya sa itatuwan turare a ciki ya kunna musu wata, wani irin jan hayaki ya fara tashi. Kawai sai ya shiga kiran suna aljani Markahul Sabus, yana yi masa kirari da cewar "Ya sadaukin aljanun duniya! Kai ne jarumi uban jarumai. Kai ne Abul Hikima, mai biyan dukkan bukata. Ya kai ruwan teku mai girgiza duniya. Ya balbalin wuta mai kone jeji. Kai ne girgije mai sanya inuwa ga mabukaci. Fito da izzarka da kwarjininka gaban sarkin duniya."
            Sarkin bokaye na gama fadın haka, sai garin gaba daya ya sauya launi, hadari ya gangamo aka fara walkiya da tsawa, kai ka ce ruwan sama ne zai kece. Daga can sai aka ga Kasa ta tsage a tsakiyar fadar sarki Lu'umanu, wani gabjejen aljani mai cikar sura da kwarjini ya bayyana Bambancinsa da bil'adama abu biyu ne kawai, yana da fukafukai a kuibin cikinsa hagu da dama, sannan yana da doguwar jela wadda saboda tsawonta har shatar kasa take idan yana tafiya bisa turba.
              Aljanin ya dubi sarki Lu'umanu ya risina ya kwashi gaisuwa, sannan ya juya ga sarkin bokaye ya ce "Cia ni na amsa kira, a kan me ake nema na a yanzu?"
Sarkin bokaye ya mike tsaye ya ce "Ya kai Markahul Sabus, ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba, sau domin bukatar nan ta sarkinmu da na shaida maka. Sarki ya amince da sharadın da ka gindaya bisa abu biyu, ya ce idan har ba zaka nemi ransa da mulkinsa ba, kome kake so zai baka, amma idan ka bijirewa umarninsa zai saka cikin kurkukun da har abada ba mai iya fito da kai."
          Ko da jin wannan batu, sai Markahul Sabus ya tuntsire da mahaukaciyar dariya, wadda tasa fadar gaba daya ta hau girgiza, har sai da yayi shiru sannan wuri ya tsaya cak.
          "Ashe har akwai wani bil'adama da yake tunanin zai iya kama ni ya Isare, ya kai wannan sarki, hakika ka vi babban kuskure, domin ni ne gagarau uban kangararru. Gaba dayan sarakunan aljanu ma sun rasa yadda za su yi da ni, bare sarakunan bil'adama. Abinda nake so da käi ya wanman sarki, kawai mu tsava bisa alkawari banda tunanin nuna isa da iko.
          Ko da jin haka, sai sarki Lu'umanu yayi murmushi mai nuna yarda da kai, ya nuna aljani Makahul Sabus da dan yatsa ya ce "Kai wannan aljani, ina mai ja maka kunne da ka kıyayi bil'adama, domin hatsabibancinmu ya fi na ku. Ka sani cewa, duk yadda kake tsammaninamo mun wuce haka. Na rantse da darajar karagata, idan har ka kuskura ka yi ba
daidai ba, zaka ga ikona."
            Sa'adda sarki Lu'umanu da aljani Markahul Sabus ke wannan cacar bakin, tuni cikim bokayen ya duri ruwa, in banda sarkin bokayen babu wanda jikinga bai kamit kyarina ha, den isoron kada Markahul Sabes ya fusata ya hallakar dar parin paha daya.
          Ba zato sai Markahul Sabus ya tuntsire da dariya ya "Ai shike nan lokaci zai bambance komai, yanzu me kaka bukata da ni Sarki Lu'umano ya sake yin murmushi a karo na hiyu ya ce "Bukata ta da kai kawai ka tafi izuwa kogun Zuhurum ka debo mini tsumin dodo Kirayanu, ka kawo mini. Da zuwanka zan biya kowace irin bukata ka furta Aljani Markahul Sabus yayi uurmishi ya ce "Na amince, kuma yanzun nan zan tali zuwa biyan bukatarka, ba zan dawo ba sai bayan kwana dan da sha biyu.
          Markahul Sabus na gama fadin haka, sai ga matar sarki Jatisa ta shigo cikin fadar tare da kuyangi suna take mata haya. Da shigowarta tayi atha da aljani Markahul Sabus, nan ta suka Kurawa juna ido. Har sai da ta je ta zauna daf da sarki Lu'umanu tana waigensa. Shi kuwa Markahul Sabus idanunsa na tsave a kanta ko fiftawa ba sa yi, tuni ya safi duniy ar begcnta, saboda tsananin ɗimaucewa ya matsa inda Fatisa ke  zaune sar ta dubi sarki cikin murmushi ta ce "Wannan kuma waye daga cikin bokaven Duniya 
     
Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na biyu domin jin cigaban wannan kayataccen littafi
Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071









