Showing 9001 words to 10405 words out of 10405 words

Chapter 4 - BAKAR GABA 1 LITTAFIN YAKI COMPLETE BY ZIDANE .txt

Zidane   

28 Dec 2024

3381

domin bazatayi kyauba.
yana gama fadin haka sai ya kada linzamin
dokinsa ya shige cikin dajin yabar markazulu
atsaye.
nan take ya bace bat tamkar bai taba
wanzuwab.
shikuma yarima saiman kutsa kai cikin dajin
cikin gaggawa.
a wannan lokaci zuciyarsa cike take da
zumudin isa tsakiyar wannan daji don biyan
bukatarsa.
sai daya shafe sa'a shida yana tafiya acikin
dajin sannan ya iso karshensa tun daga nesa
ya dinga ganin dake cikinsa wasu irin many
manya
kirar mutanen farko
jikinsu amurde yake tamkar sassaka su akayi
da itace.
fuskokinsu cike suke da gashi kai kace
gwaggwan birine
suna da jajjayen idanuwa tamkar angasa dan
buda awuta.
koda suka lura da tahowar yarima saiman
sai daya daga cikinsu ya zaro wani kahon
giwa ya busa
nan take wata kara ta cika dajin gaba daya
tare da amsa kuwwa.
nan dan ragowar dakarun dake dajin suka
lura da abin da yake faruwa
nantake suka ruga da gudu suka soma debo
makaman yakinsu domin tunkarar yarima
saiman.
sudai wadannan arnan dajin sunada matukar
yawa domin zasu kai su dubu goma.
sannan suna karkashin mulkin wani
hatsabibin matsafi wanda yake
shugabantarsu.
kuma yasan dalilin zuwan yarima saiman
don haka yasananr da ragowar dakarunsu
don su san da zuwansa
yarima saiman yana isa kusa da inda
dakarun suke sai yaja linzamin dokinsa ya
tsaya cak
sannan ya budi baki yace
ku ma'abota rayuwar daji kananun jarumai
wadanda suke tsoron rayuwa da mutane yan
uwansu tamkar dabbobi
to yau ni saiman na zo wannan birni domin
na yakeku na zubar da jininku na hana
zuluncin da kukeyi adoron kasa da kwacen
da kukeyiwa matafiya akan hanyarsu.
nayi alkawarin saina hallakar daku muddin
bazaku yarda da sharadin danazo muku
dashiba.
sharadin kuwa shine
inaso ku mikomini takibin sihirin da kuke
bautawa cikin ruwansanyi domin mu rabu
lafiya daku batare da an zubar da jini ba…
kafin ygama fadar maganar dake bakinsa sai
su shugaban wadannan arnan daji yafito
asukwane bisa wani ingarman doki ya tsaya
agaban dakarunsa.
sannan ya bushe da dariya
ya dubi yarima saiman yace lallai kayi
kuskure da kake tunanin zaka kwaci
maigirma takobin sihiri a hannunmu.
inaso kasani cewa koda mutanen duniyane
zasu taru basu isaba balle kai mutum daya
tak
yana zuwa nan a zancensa sai ya umarci
arnan dajin dasu harbowa yarima saiman
kibiyoyinsu
nantake kuwa suka dana baka sukaharbo
masa .
saiga sararin samaniya tacika da kibiyoyi
sannan suka durfafo kan yariman saiman
nantake yarima saimanya zare takobinsa.
sannan yasawani silken sihiri ya lullube
dokinsa da ita gaba daya
sanna ya shiga kade kibiyoyin da suke harbo
masa cikin zafin nama,juriya da bajinta.
wohoho hakika jarumtaka baiwace duk
wabda allah yabaiwa ya huta.
wani abin mamaki shine gani yadda yarima
saiman yake kare hare haren da kibiyoyin
suke kawo masa cikin kankanin lokaci.
sai gashi anrasa kibiya ko guda daya wacce
zatq iya lakutar jikinsa.
sai bayan yan dakiku sannan kibiyoyin suka
kare.
nan fa dakarun suka rufo kansa aka kachame
da azababben yaki nagaban kwatance.
idan kaji ance ga ki gudu to sa gudu ne bai
zoba.
domin duk da karfin damtse irin na
wadannan dakru sai yarima saiman shi kadai
ya gagaresu suka rasa yadda zasuyi dashi.
domin yana wata jarumtaka ne taban al'ajabi
wacce na tsaya fasaltamaka itama bata
lokaci ne domin duk kwatancen mai kwatace
bai isa ya fasalta maka irin yaki da yakeyi
ba.
awannan lokaci kasa ta soma girgiza,kura ta
turnuke sararin samaniya saboda
kwarmatsuwar da suke yi akan kasa.
karar karafa ta cika dodon kunne,tare daihun
mazaje,jini ya dinga fallatsi akan kasa
tamkar an bude magudanar ruwa
awannan lokaci sabodane saboda tsananin
bala'i tsuntsaye suka dinga tashi suna
chanza sheka.
barewa suka dinga fadawa garken zakuna
basu sani ba don su ceci ransu.
duk inda yarima saiman yasa gaba saidai
kaga mazaje suna zubewa kasa tamkar ana
sassabe agona.
duk da irin wannan mummunar barna da
yake musu batasa sunja da bayaba.saboda
tsananin naci tamkar basu ake kashewaba.
sai wani irin karaji sukeyi suna dada kunno
kai cikin rashin tsoro da yarda dakai.
shi kuwa ya wanzu yana mai zare musu
ruhin numfashinsu tamkar mala'ikan mutuwa Sai da suka shafe sa'a uku suna fafat
wannan kazamin yaki tsakanin arnan dajin da
yarima saiman.
an rasa wanda zai sami galaba akansa
ana cikin wannan haline yarima saiman yaji
an gabza masa naushi da kafa agadon baya
saboda karfin naushin sai da yarima saiman
yayi tsalle kamar an janye shi da majaujawa.
kamar zai fadi kasa amma saboda tsananin
jarumtaka sai yarima saiman ya juya jikinsa
a sararin samaniya
sannan ya dire bisa kafafunsa.
amma kafin ya dawo cikin haiyyacinsa sai ya
sake jin an kara gabza masa wani sabon
naushin a kirji wanda yafi na farko.
saboda karfin naushin sai da yaji kamar
kashushuwan kirjinsa sun kakkarye.
bakowa ne yayi masa wannan duka face
shugaban wadannan arnan daji.
nan take ya takarkare ya bushe da dariyar
farinciki sannan ya dubi yarima saiman yace
lallai ka cika mai tsautsayin wahala tunda
har kake shirin raba mu da takobin sihirin
mu
yanzu kai a haka zakaje ka yaki dodo garjaju
har ka sami tsumin tsafinsa.
sannan kaje fadar sarkin aljanu ka rabasu da
miftahul darul sihir?
hakika yanzu zaka hallaka sannan naje na
kama ragowar mutanen da suke tare da kai
namai dasu bayin mu.
yana zuwa daidai nan a zanncensa saiya
zare takobinsa ya nufo kan yarima saiman da
nufin tsige masa kai.
ba zato ba tsammani sai yaji wata irin iska
mai karfi ta taso ta shureshi ta damfara shi
da kasa
bakowa bane yayi wannan aikiba face aljani
markazulu
nan take ya tashi yarima saiman zaune yace
kai jeka ka tari shugaban yan fashin
ni kuma zanje na tari ragowar dakarun in
yaso idan na gama dasu sai in taimakama.
yana zuwa daidainan azancensa sai ya shige
cikin dakarun ya hausu da sara da suka ta
ko ina babu kakkautawa duka inda ya nufa
saidai kaga arnan dajin na zuba a kasa
tamkar ana sassabe agona.
shi kuwa yarima saiman sai ya gyara rukon
takobinsa
ya nufi inda shugaban arnan dajin yake kai
tsaye.
nan fa aka soma kallon kallo a tsakaninsu
kai da gani kasan kar ce ta san kar.
har na tsawon dakiku daga chan sai suka ja
da baya kamar tazarar taku goma
atsakaninsu.
sannan suka gyara rukon takobinsu
suka rugo kan juna suka kacame da
azababben yaki mai matukar muni fiye da
wanda akeyi tsakanin aljani markazulu da
ragowar dakarun arnan dajin.
sai fadan nasu ya zamo abin tsoro kuma
abin sha'awa sakamakon yadda suke fadanda
dukkan karfin su.
shidai shugaban wadannan arnan daji wani
irin gabjejen mutum ne mai kirar muatanen
farko
sannan yana da manya manyan idanu jajaye
masu matukar kwarjini.
kirjijsa faffada ne cike da gashi.sai kace
zaki.
yana da manya manyan damatsa kamar
jerasu akayi.
kai duk inda mutum mai suffar karfi yakai to
wannan mutum yafishi cika ido
shi kuwa yarima saiman sai ya zama dan
karami akansa.
amma duk da haka sai gashi ya kasa samun
nasara akan yarima saiman saboda matukar
karfin damtsensa.
dajuriyarsa da kuma nacinsa.
hakika yarima saiman ya isa a jinjina masa
ganin yadda yake yaki da mutumin da ya
fisyi kwarjin da cika idanu.
dukkansu suna yi fadanne cikin mugun nufi
da burin salwantar da rayukan juna.
koda suka dau wani lokaci suna wannan
fafatawa .
sai dukkansu suka ja da baya.
suna hararar juna kamar zakaru.
daga chan suka sake falfalowa da gudu suka
sake kachamewa azababben yaki fiye da
farko.
sai gashi suna hadawa da sara da suka
sama da kasa.
har tsalle sukeyi suna kai farmaki ko kuma
wani lokacin kaga suna zamiya akasa.
awannan karon ma sai aka kasa samun
wanda zai nasara daga chan sai shugaban
arnan dajin yayi wurgi da takobinsa.
sannan yace da yarima saiman
tunda dai munga salon fadan namu iri
dayane to mai zai hana mu gwada karfin
damtsen mu banbance tsakanin aya da
tsakuwa.
kodajin haka sai yarima saiman yayi
murmushin yadda dakai sannan yayi wulli da
takobinsa.
nan take suka kachame da kokawa.
awannan lokaci sai fadan nasu ya chanja
salo domin ana fara fadanne kowanne daga
cikinsu jikinsa ya fara gaya masa.
duk sa'adda yarima saiman ya sami nasarar
dukan shugaban yan fashin sai kaga shima
ya rama kamar dama chan sun tsara haka
fadan zai kasance.
ana cikin haka yarima saiman yaga idan
suka ci gaba da fadan ahaka to zasu iya yi
ragas.
kawai sai ya shammaci shugaban arnan dajin
ya yi tsalle ya kama kansa ya murde sannan
ya wullar da gawarsa gefe daya.
koda ragowar arnan dajinsuka ga gawar
shugabansu a kasa sai suka zubar da
makamansu.
suka ruga da gudu nan take yarima saiman
ya tashi ya dinga taimakawa markazulu suka
dinga binsu suna rafkewa.
kafin cikar wasu yan dakiku sun gana
hallakasu.
koda suka karar dasu sai yarima saiman ya
juyo ya dubi markazilu sannan yace .
wai kai meyasa kake bibiyata ne shin ban
hanaka biyoni ba?
kodajin wannan tambaya sai markazulu yace
kayi hakuri yakai wannan jarumin jarumai
bana biyo ka bane don na cuce ka ba.
na biyo kane kawai don nasan ra'ayin mu
daya dani dakai ma'ana na yakar boka
ulumanu.
kodajin haka sai yarima ya sake tambayar sa
yace to menene dalilin da yas a kake da
burin yakarsa?
kodajin wannan tambaya sai aljani markazulu
yayi shiru kamar bazaice komi ba.
daga chan sai yace
mun sami sabani da uban gidanane
sakamakon nima na sami babban matsayi a
fannin sihir.
koda gama jin haka sai yarima saiman
jinjina kansa azuciyarsa yace tabbas akwai
wani boyayyan sirri a zuciyar markazulu.
don haka dolene nasa idanu aknsa.
kawai sai yace da markazulu.
shikenan na amince da tafiya tare da kai.
amma da sharadi.
sharadin kuwa shine bazakaci amanarmu ba.
kodajin haka sai markazulu yace na amince
da wannan sharadi naka.
nan take suka kama hanya suka shiga cikin
garin arnan dajin.
sai da suka wuce sa'a biyu sannan suka iso
kofar wani babbar fada..
Suleiman Zidane kd
Whatsapp. 08161272634


LIKE AND COMMENTS IS OUR ENCOURAGEME
DOMIN SAMUN CIGABAN SAI KU KASANCE DA MU A KODA YAUSHE
DAGA
Suleiman Zidane kd
Whatsapp. 08161272634

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login