Showing 9001 words to 10435 words out of 10435 words

Chapter 4 - Deen House Book Complete By Oum Hairan .txt

04 Jun 2024

9495

abun yana neman fara shiga jikinta yau sai takejin yanayin kasancewar tasu taƙi barin sassan jikinta har wani lumshe idanu takeyi a ranta tana raya dole fah ta shirya yaƙi dashi kafin ya kaita ya baro.


Kusan raba dare tayi tana tunani da safe kamar yanda ya faɗa mata tun ranar jiya tare suka fita dake dama tayi Jamb suka shiga b.u.k ya gama mata duk wasu cuku² na makaranta sannan suka nufi hanyar gida ko a motar so yake ya lalubeta amma babu dama saboda motar farin glass ke gareta suna zuwa gida kuwa tayi wuf ta shige ciki tayi saa ta ishe Nafisa ta dawo tayi ajiyar zuciya ta tsallake wannan tarkon saura wani, shikuwa fuskar nan kamar an aika masa uwarsa ta mutu haka ya shigo Nafisa ta rinƙa tambayarsa menene yana ƙwafa karshe ya tashi ya fice a gidan Zainab tabi bayansa da harara sarai Nafisa taga irin mugun kallon da ƙanwar mijin nata tabi mijin nata dashi tayi murmushi tace.


“Wai meye ya hadaki da Yayan naki ne?" Numfashi ta sauke ta basar da zancen da cewa “Nayi tunanin da wuri zaki dawo sai naga har mun fita baki dawo ba" hira suka fara ƙarshe suka tashi suka shiga kitchen suka ɗora abinci sukaci suka sake shantakewa da hira Nafisa akwai Magana.
Surutun ta har damun Zainab yakeyi data gaji ta shige ɗaki bata jima da shiga ba taji an buɗe ƙofar an shigo ta ɗago sukayi ido huɗu ya miƙa mata kwalin waya ya juya ya fita tabi kwalin da kallo cike da farin ciki Allah yayita da son waya a rayuwarta shiyasa tayi murna da wannan kyauta ta bazata ta zauna ta ɓareta waya ce babba da gaske ta daɗe tana juya wayar kafin ta kunna ta murna ta cikata ganin harda layi a ciki nan ta rinƙa shige² tanajin farin ciki na mamaye ta batasan ya shigo ba Saida taji ya fizge wayar ta ɗago fuskarta a sake tace.


“Wlh naji daɗi sosai na wayar nan Ya Deen inason waya ko don chat" kallon da yake yi mata ne yasata shiga hankalinta ya tako ya zauna kusa da ita yace “Meye tsakaninki da Zaharaddeen?" Da sauri ta ɗago tace “Wai Ya Zain?" Jinjina mata kai yayi tayi murmushi tace “Babu komai sai zumunci da aminci...." “Da kuma soyayya ko?" Ya faɗa yana miƙewa yaci gaba da cewa “Ba damuwata kiyi soyayya dashi ba kawai dai zan faɗa Miki koda bazaki yarda ba Zainab bakida mijin da ya fini jinki nakeyi matsayin matata shiyasa nake mu'amala ta mata da miji dake ba kuma zan fasa ba naje nayiwa Abba magana kamar yanda nayi Miki jiya yaƙi amincewa to dalilin dole zaisa ya amince tunda bazasu yarje min ta maslaha ba"
Ficewa yayi ta taɓe baki tace “tunda kai ka haifeshi ai saikayi masa dolen" tashi tayi ta fara bincika kayanta ta dauko number Zain tasa a wayar ta kirashi bugu biyu ya daga muryarsa a kasalce tace “Allah shi taimaki Yayana...." Ya cafe da cewa “kuma mijinki” dariya tayi tace “ashe zaka ɗauki murya ta" yace “ko cikin dubu ko cikin ciwon ajali Muryar matata bazata taɓa ɓacemin ba" nan take labarta masa tayi waya yayi murna yace “Dama inason Inna dawo na roƙi alfarmar Abba ya barki ki riƙe waya ashe kafin nazo ma Deen zai samamin mafita.


Murmushi tayi na yaƙe tace “Na daɗe inason na sanar dakai amincewata da kuma zaɓarka da nayi Ya Zain amma dai Abba bazaisa aurenmu da nisa ba ko?" Cikin matsanancin farin ciki yace “Wayyoh daɗi ƙanwata insha Allahu jibi zanzo zanyiwa Abba magana na kusa gama komai yanzu ma abinda ya tsaida ma'aikatar da nake ne sukeson riƙeni so zan dai nemi alfarma nazo serious ina buƙatar aure" sunsha hirarsu ta ƙauna Zainab ta manta da wata damuwa ta rasa meye yasa indai tana tare da Ya Zain bata tuna wata damuwar duniya.
Kamar yanda ya alƙawarta mata kuwa hakance ta faru ranar Alhamis ya shigo Kano baije gida ba Saida yazo gidan yayan nasa suka sha hira da abar ƙaunarsa Nafisa na tsokanarsa yanata dariya sai yammaci ya nufi gida, da dare kuwa sunga bala'i da Deen ya dawo ya samu labarin zuwan Zain gidan abin har tsoro ya bawa Nafisa tace “To wai kai ina ruwanka da lamarin Soyayyarsu tana sonsa shima yana sonta saboda haka wannan aure ikon Allah ne kawai zai hana yinsa" bai bata amsa ba ya shige ɗakinsa yana fatali da komai cikin tashin hankali yake cewa “Akanme Abba zaimin haka meyesa zai bawa Zain Zainab bayan yasani Ni nafi cancantar mallakarta?


Da dare ta fito kitchen don ɗaukar abinci ya ritsata acan ta juyo da sauri tsoron shaiɗancinsa takeyi yanda taga idanunsa ya kaɗa ya sake firgitata ta ɗauki abincin ta juya zata fice ya cafko hannunta ya mannata da ƙirjinsa yace “zuwa yanzu ya kamata ace kinyi sabon da bazaki yarda a rabamu ba amma na fahimci ke ba wannan ne a gabanki ba Zainab meye da Zain wanda banidashi uwa ɗaya uba ɗaya fa ta kawomu duniya dashi me kike tunanin samu a gurinsa wanda bazaki samu a gurina ba?"
Shiru tayi masa kanta a ƙasa ya sanya hannu ya ɗagota ya ɗora bakinsa a kuncinta ya lashe hawayen firgicin daya zubo mata yace “Wlh bazan bari na rasaki ba zan iya yima Zain kyautar komai amma banda ke don nafisa buƙatarki...." Da wannan ya fara lalubeta zuciyarta takai maƙura zuwa yanzu dole ta rinƙa ƙoƙarin ƙwatar kanta hakanne yasata tureshi ya sake cafkota ta kuwa wawuri cup na glass idanunta na tsiyayar da hawaye tace “Na rantse da Allah ka kuma taɓani saina illataka...." Damƙar damtsenta yayi batare da yayi tsammani ba yaji danshi a goshinsa ya sake ta da sauri dafawar da zai yi yaji kwalba cake a goshinsa jini yana tsartuwa aikuwa tana ganin hakan ta ɗiba da gudu bai iya tareta ba.


Saboda tsabar tsananin mamaki da takaici ita kuwa tana fita ɗakinta ta faɗa tayi masa key ya fito bugun duniya taƙi buɗewa takaici yasashi komawa ɗakinsa zuciyarsa na bijiro masa da irin matakin da zai ɗauka, shigarta ɗakin babu daɗewa wayarta tayi ƙara ganin Number Umma Tsoro ya kamata ta kara wayar muryarta na rawa tace.
“Don Allah Umma ki yafemin wlh babu yanda zanyi ne inajin tsoron kar na....." Katseta Umma tayi da cewa “karkije me? Meye ya faru Zainab yayi Miki wani abu ne?" Ajiyar zuciya tayi tace “Aa Umma babu komai" numfashi Umma ta daidaita tace “ok to gobe da safe kizo gida tunda shi bashi da hankali bare mutunci zaman gidan nasa ma kin daina" wata ajiyar zuciya me ƙarfi Zainab ta saki cike da farin ciki tace “da wuri ma kuwa Umma" tana aje wayar ta fara haɗa kayanta ranta da zuciyarta wasai tace “Allah zai rabani da ƙaya"
Shi kuwa ya gama yanke hukunci da kansa yayi dressing gurin da taji masa ciwon ya kwanta da sassafe kuwa ya ɗauki hanyar Garko cikin Sa'a ya tarar da Mal Tsalha ƙanin kakansu a zaurensa da Almajirai yana ganinsa yace.


“Ikon Allah mutumin birni kaine a tafe haka babu zato" murmushi yayi ya zauna suka gaisa Mal Tsalha ya dubesa da kyau yace “Mutumin birni ina marainiyar Allah Zainabu Allah sarki rayuwa jiya na gama kukan rashin mahaifiyarta Ubaidah mutuniyar kirki shikuwa Ibrahim saidai fatan Allah ya ƙwatoshi hannun wannan azzalumar mata daya aura sun cutar da Ubaidah matuƙa" shafa sumarsa yayi yace “Wlh Mal abin sai addu'a wannan mata ina ganin tsafi takeyi yanzu fa baba Ibrahim ko gidanmu baya zuwa yama ce ya yafe ƴar tasa bayaso. am dama Mal akan maganar Zainab ɗin ne ta kawoni......" Nan ya zage ya rinƙa shiryashi da ƙarairayi abinka da mutumin ƙauye take ya hau ya zauna yanata salati yace “Yanzu yarinyar nan haka ta zama ashe kaico Ni Ɗalhatu ina ganin rayuwa aikuwa indai da gaske kanasonta bazaka bar garin nan ba Saida igiyar auren Zainabu a hannunka yaron nan kaidai Allah yayi maka albarka ka taimaki maraici kayi zumunci"......


********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels


WhatsApp Number: 08138873799




Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login