Showing 6001 words to 9000 words out of 9862 words
Tayi tana tinanin yazatayi da ita? Amma ganin batasamu wata mafitarba kawai seta gyara mata kwanciyarta tareda komawa gefe tana kallonta, sedai ko minti 20 batayi awurinba wani mugun zafi yataso mata sabida Bata Sababa ba yadda za'ayi Ta'iya zama a tudu ba'acikin ruwaba. Amma ahakan tadaure kusan minti 35 sedai zafin naneman illatata Hakan yasa tafad'a cikin ruwan babu shiri....seda Tayi nitso nakusan minti 3 kana tafito bayan wasu minti 3 tak'ara komawa ruwan akayi wasu minti 3 tak'ara fitowa,, atakyaice dai ahakan suka kwana har inda gari yawaye tashiga ruwa tafito tana gadin Isseta d'in...sedai abunda yabata mamaki shine shigarda Tayi ruwan na k'arshe Koda tafito tasamu Isseta kwance akan wata y'ar katifa me kyau sosai Kuma anyi mata shimfid'a kamar wata y'ar baby. Abun yayi bala'in Bata mamaki sedai kafin tasamu zarafinyin wani abun Sega wata kyakkyawar mace tafito itama rabinta kifine rabinta mutin sedai banbancinsu ita maah taruwace itako wannan ta tudu ce( gawanda Basu fahimta ba ga takyaitaccen bayani. "Dama ita wannan aljanar wato hajo ruwa kala biyu ce Allah yahalitta d'aya acikin ruwa take d'aya Kuma a bakin ruwa take ma'ana akan dutse wadda Sam Bata damuda ruwaba Amma Kuma tanashiga ciki. Itako taruwa Sam batason Tasha iska sedai Kuma ahakan tana fitowa waje. To kunji yadda suke sabida Hakan idan Kun fahimta ita wannan data fito ayanzu takan dutse ceπ§)
Ajiyar zuciya maah tasauke ganin aminiyar tata domin ko acikinsu akwai way'anda Allah ke had'a jininsu sukasance abokanai ko k'awaye.....k'arasawa Tayi wurin maah suka gaisa kama tagayamata itace tayima Isseta Hakan Dama tinjiya tana kuleda ita Bata cikin ruwa Bata waje Hakan yasa taduba abunda takeyi awajen ganinta tareda wannan yarinyarne yasata fito domin Taga ko wacece sekuma Taga Ashe maryama ce...hakane kam wlh anan takwana domin matsala sukasamu da babanta a,nan maah tabawa wannan k'awar tata labarin abunda yafaru agidansu maryama....sosai tajajanta abun inda tad'auki alkawarin Tayata kulada Isseta.
To acan gida kuwa mama bintu Bata rintsaba yadda Taga Rana haka Taga dare tin lokacinda yah Kabir yasanarda ita shikam bega Isseta ba gashi Kuma bataji dagasu sulaiman ba Hakan yak'ara hanata samun nutsuwa inbanda addu'a babu abunda takeyi..misalin k'arfe 8:00am halima tashigo gidan Domin itama da Isseta takwana aranta Sam takasa samun sukuni ayadda Taga Isseta cikin tashin hankali jiya bayan sundawo Hakan yasa tazo tinda safennan Dan Taga Isseta d'in taji mike faruwa sedai tana shiga taji abunda Sam hankalinta baze d'auka ba, wai Isseta Bata kwana agidaba Suma nemanta sukeyi acewar mamansu Yah balah. Inda iyya hassi tak'ara dacewa tinda safe tafita ajiyan Kuma haryanzu batadawoba...tofa wannan zancen shine yasaka kokwanto azuciyar halima domin dai jiya tareda ita suka fita Kuma atare suka dawo to miyasa yanzu sukecewa wai tinsafe ne batanan? Wannan abun yayi bala'in d'aga hankalin halima Hakan yasa Takoma gida tana kuka bilhaqqi tasanarda innarta abunda yafaru........mama bintu kuwa se yanzu su sulaiman suka kirata suna sanarda ita cewar Sam basuga Isseta ba sunnemeta sama da k'asa Amma Basu gantaba. Tofa awannan lokacin tashin hankalin mama bintu yak'aru yadda bakwatinani Tayi kuka harta godewa Allah, cikin tashin hankali da mugun b'acin Rai tanufi d'akin Malam Musa Abba kenan, azaune tasameshi Shima yabuga uban tagimi. Cikin takaici da bak'in cikin wannan abun dayayi tace "wlh Malam Bakaga komaiba tagumi yanzu kafara tinda kakori maryama daga gidannan nasan kanada yak'ini akan cewar lokacin bukatar ta yakusa Kuma idan wannan lokacin yazo sekatanadi amsar badawa akan b'atanta domin wlh bazan tab'a rufamaka asiriba akan wannan al'amarin, kabiyewa son zuciya da makircin matanka kajefamu cikin tashin hankalin da bamusan lokacin fitarshiba. D'an shiru Tayi kamun tanisa tacigabada fad'ar inaga kunshiryawa k'are rayuwarku ne agidan kaso konace kashiryawa k'are rayuwarka agidan kaso shiyasa kayi hakan, domin idansu basusan wacece maryama ba aikai kasani Amma katake sanin, shikenan zamuga yadda abun zek'are, tana gama fad'ar Hakan tafice warta ranta amugun b'ace...Abba kuwa da tinda tafara magana hankalinshi yak'ara tashi matik'a se ayanzu yake K'ara danasani akan abunda ya aikata tabbas yad'ebo ruwan dafa kanshi zekuwa dahu idan ba Allah yaceceshiba. (Humm Malam Musa kenanπseyanzu kasan Hakanπ tukunna ma wacece maryama dahar kuke wannan zantukan akanta?π€)
Lagos
Banana island
Kwance yake akan makeken gadonshi Yana sharar bacci sedai daga ganin yadda yake baccin kasan cewar bayajin dad'in yinshi kawai de yanayine...wayarshi ce dage kan bedside table tafara rurin neman d'auki akarona biyu, cikin baccin yaji Kiran wayar
yadameshi Hakan yasa yad'aga batareda myyaduba me kiranshiba tareda Kara
wayar akunnenshi. Daga D'aya b'angaren general aliyu yace "hello mejo zanfito yanzu muhad'u a
airport please lokaci yakusa karmu rasa jirgi. "Okay kawai yace tareda yanke wayar seyanzu ma yatinada yaune tafiyarsu, Hakan yasa yamik'e jikinshi duk badad'i yanufi bathroom tareda rufo k'ofar. Seda yayi brush kana yayi wanka domin tinda yayi sallar asuba Yakoma bacci betashiba seyanzu da general aliyu yatadashi, seda yagama wankan yatsaya kallon halittarshi dake atsaye kullun kamar abunda yake ciyarwa. D'an k'aramun tsaki yaja kamun yajanyo towel ze D'aura kawai idonshi yasauka akan k'ofar bathroom d'in inda akad'an bud'e k'ofar kad'an ana lek'enshi, wani Irin waro Ido yayi kamun yad'aura towel d'in ahanzarce yanufi k'ofar, Amma kamun yak'arasa tuni akabar jikin k'ofar. Yana fitowa wulgawar mace kawai yagani ta glass din window d'akin, Hakan yasa yajanyo jallabiyyarshi kawai yazura tareda fitowa daga bathroom d'in amugun hasale. Yana fitowa parlor yayi turuss ganin Ummi kawai a perlor Tama goge'goge ga dukkan alamu sharace zatayi....k'ank'ance golden eyes dinshi yayi kamar yadda yakeyi idan zeyi wata tijarar Yanabinta dawani mugun kallo cikin mugun mamakinta datafasar zuciya. Allah sarki baiwar Allah itako se aikinta takeyi batamasanda yanayiba...shikuwa gabaki d'aya k'wak'walwarshi tagama bashi cewar itace ke lek'enshi kawai tanason renamai hankaline shiyasa Tayi kamar shara zatayi mishi, sabida tasan kafin tagudu yakamata bari tayimishi pretending.
Cikin bala'i yadaka mata tsawarda seda tasaki glass cup d'inda ke hannunta tana zare Ido, cikin tafasar da zuciyarshi keyi yabud'e Baki babu alamar rahama a murmushi yace "Ummi ni sa'arkine? Sabida Kinga nabaki damar shiga part na shine zakimaidani abokin wasarki? Mikike nema ajikina? Mikikesan gani ataredani dahar Zaki iya lek'e na abayi? Ina yayanki Ummi har renin dakikayimun yakai Hakan? Yatambaya Yana wani Irin huci kamar kumurci.....Ido Ummi tazaro cikin tashin hankali da mugun fargaba tabud'e Baki cikin inna'inna take fad'ar "wlh..wlh Allah ya najeeb narantse da Allah bani ba...gum Tayi dabakinta tanaja Baya ganin yayo kanta gadan gadan kamar mayunwacin zaki.
"Dakata najeeb karka kuskura katab'amun yarinya wlh kaji nagayamaka. Yatsinkayo muryar dadynsu Hakan yasa yatsaya cak batareda yak'arasa gurintaba Kuma besauke hannunshi dayayi niyyar marintaba....shikuwa dady karasowa yayi cikin parlor yazo gab da najeeb d'in kana yace "wai miyake damunkane najeeb? Kanada hankali kuwa? K'annen Nakane zaka Saka agaba damugun alkaba'i? Jiya kadaki mansura kana fad'ar wai tazo gunku tsirara yanzu kuwa zaka daki Ummi kana fad'ar tana lek'enka abayi shinwai minene matsalar kane? Kodan kaga nasaka maka Ido shine Zakayi abunda kaga dama, sokakeyi kalalatamun yarane ko Yaya? Awannan karon d'agowa najeeb yayi arazane cikin mugun mamakin kalaman mahaifin nashi yake kallonshi. "Yes najeeb kallon me kakemun? Koba hakabane? Inba lalatamun su kakesanyiba zaka zauna kana musu wannan furucinne? idan mace kakeso atareda Kai bazaka nema awajeba se acikin gida? Humm shikenan ai nasan maganinka, Yana gama fad'ar Hakan yacewa Ummi Maza tawuce seda yasakata agaba kana yabi bayanta sukabar part d'in nashi.
Da kallo mejo najeeb yabisu harsuka b'acewa ganinshi gabaki d'aya yadaskare awurin da mamakin mahaifin nashi domin Sam beyi tinanin k'iyayyar da dady kemasa takai Hakanba, shinkodai bashine yahaifeshiba? Yayiwa kanshi wannan tambayar dabame bashi amsarta ayanzu...ganin tsayuwar ba'abunda zata k'ara mishi Sema b'ata lokacinshi dayake k'arayi gaya sekiranshi general aliyu keyi Hakan yasa Yakoma bedroom dinshi kawai cikin kunar Rai yashiga shiryawa komai beshafaba tirare kawai yafesa tareda Saka kayan yafito janyeda jakar kayanshi, Yana fitowa yaga captain Jameel nazaune a perlor cikin sauri yataso tareda d'aukar jakar sukafito a general parlor yagasu Hajiya Umma da mama zaune se Munir da siyana ga mansura gefe da bandage d'inta duk ajiki. Kallo D'aya yayimusu tareda d'auke kanshi yace "Umma zamuyi tafiyane, semun dawo mama daga Hakan yasakai zefice batareda yajira cewarsuba. "Allah yakikeye Kuma yasa ayi akan nasara, cewar mama...yayinda Umma kuwa tamik'e cikin sauri tana fad'ar zonan my son. Haryakai bakin k'ofar fita parlor yatsaya, shikuwa captain Jameel yayi ficewarshi. Tana zuwa kuwa hannunshi takama tareda nufar bedroom d'inta dashi seda tamayarda k'ofar tarufe kana tad'auko fruit salad a wani D'an jug tabashi tareda manna mishi kiss a ride lips dinshi kamar yadda tasaba kana tarungumeshi ajikinta tsam kamar wasu mata da muji, Kuma tak'i sakeshi kusan minti 2 seda yanemi cire jikinshi daga nata Dan kanshi kana tasakeshi, tareda k'ara manna mishi kiss a kumata tace "adawo lpy yaron Umma...shidai k'ala bece mataba kawai juyawa yayi tafiyarshi..da kallo tarakashi tana tasbihi ga uban gijinda yabata wannan yaron Allah yasani tana mugun son najeeb cikin y'ay'anta tana rokon Allah yabata ikon b'oye soyayyar shi kar Y'an uwanshi sugano tafisonshi akansu domin tasan tabbas Hakan zehaifarda matsala atsakaninsu.
Shikuwa Yana fitowa yafice daga gidan kotakan k'anenshi bebiba dayaji suna masa adawo lpy Allah ya kiyaye...a perking space yasamu captain Jameel tareda zugar yaranshi, ruwan roba yakarb'a ahannun captain Jameel d'in yawanke bakinshi kana yashiga motar domin befito da Hankey ba Kuma shidai yatsani wannan kiss d'in da Umma kemishi akan lips sedai ba yadda zeyida ita mahaifiyarshi ce babu abunda zatayi agareshi yace aa Amma Badan Hakanba tayaya zebari wai mace ta tsotsar masa Baki, Allah yasauwak'e mishi wahala da kayan K'azanta. Dawannan tinanin motocin su sukabar gidan inda suka nufi airport kaitsaye acan suka samu general aliyu datashi zugar. Suna Isa kuwa babu wani b'ata lokaci jirginsu yatashi zuwa k'asar nigar......!
MEJO NAJEEB PAID BOOK NE akan nera 500 kacal game bukatar complete dinshi kuwa 1k ne domin complete dinshi yafito idan kishirya biya Zaki iya tura kudinki a wannan account d'in π 2276776261 sha'awanatu kasim UBA Bank kana kitura shedar biyanki a wannan nomber π 09112799371 on WhatsApp ko kikira wannan nomber π 07037092176 π
Autar alheri βοΈ
πͺ½πͺ½πͺ½πͺ½πͺ½πͺ½πͺ½πͺ½πͺ½
π§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ
πͺ½πͺ½ *MEJO NAJEEB*πͺ½πͺ½
(Labari me sark'ak'iya ban al'ajabi rikici zalunci soyayya cin Amana dakuma romantic π)
Daga alkalamin Autar alheri βοΈ
MEJO NAJEEB PAID BOOK NE YANZU MUKE FREE BOOK 1 IDAN MUKA SHIGO BOOK 2 SHINE ZAKI BIYA KARKI KARANTAMUN ABUNA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA MUDDIN KIKA FITARMUN DA BOOK KO KIKAKARANTA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA KEDA ALLAH.
Book 1
Page 19 & 20
Inaga wannan page shine end book 1 free yak'are idan kinada bukatar complete dinshi Zaki biyan 1k domin samun complete inkuma update kikeso Zaki biyan 500 kacal. Idan kinshirya biya Zaki iya tura kudinki a wannan account d'in π 2276776261 sha'awanatu kasim UBA Bank kana kitura shedar biyanki a wannan nomber π 09112799371 on WhatsApp ko kikira wannan nomber π 07037092176.
"Jirginsu nasauka a k'asar nigar sukad'auki dauki mota drop zuwa fadar shugaban k'asar nigar Alhaji Abdulsalam Idris suna zuwa sukasamu damar shiga fad'ar shugan k'asar kasancewarsu sojoji basusha wahalar shigaba dudda cewar ba sojojin k'asar bane Amma daganinsu kansan cewar ko acikin sojojin Nigeria manyane. Abakin k'ofar shiga office din shugaban k'asar suka tsaya inda Fe,A d'inshi yashiga gun alhaji Abdulsalam Idris domin nema musu iso abunshi dudda cewar babusu acikin jadawalin wanda zegana dasu aranar Amma haka akasama musu gurbi dole kasancewarsu manyan mutane dukda k'ananun shekarrunsu ammadole abasu girma sbd manyan muk'amansu....fitowa f,a yayi yagaya musu zasu iya shiga domin ya,isarda sak'onzuwansu. Hahan yasa suka shiga office d'in kaitsaye. Azaune suka sameshi akan kujerar office d'inshi kyakkyawan dajjo farin buzu mecikar haiba da kamala. Gaidashi sukayi cikin girmama dudda cewar sunzone da b'acin Rai Amma kwarjinin dattijon yahanasu bayyanarda b'acin ran nasu.
Shima agunshi hakanne domin Hakan kawai yaran suka birgeshi Hakan yasa ya amsa musu cikin sakin fuska da kulawa, daganan yabasu wurin zama...seda sukazauna cikin girmamawa suka shiga koramai bayanin abunda yakawosu kamar Hakan "ranka yadad'e munzune akan wani al'amari dayake faruwa ak'asarmu sabida bamuji komai daga manyanmuba gameda wannan abun shiyasa mukazo muji Koda Saka hannun k'asar nigar ne ake wannan aikin. Tsayawa general aliyu yayi yad'an Kalli dattijon kamun yacigabada fad'ar "wannan abun kuwa bakomai bane face aikinda sojojin k'asar Nan keyi a Nigeria Kuma munga babu Saka hannun kowacce hukuma ta sojojin Nigeria akan wannan al'amarin shiyasa mukazo domin abun yayi k'amari Kuma way'anda suke wannan yak'in dasu bay'an Nigeria bane Y'an south African ne.
"Murmushi wannan kyakkyawan dattijon yayi kana yace "kunada gaskiya Y'an samari dudda cewar bansan sunayenkuba Amma suturar jikinku tagayamin mukamanku acikin hukumar soja, to zance na gaskiya dasaka hannunmu awannan aikin yafad'a Yana kallon najeeb dayaga tinda aliyu yafara magana kanshi ak'asa yake.
Murmushi yayi kana yacigabada fad'ar "abunda yasa muka Bada umurnin yinshi kuwa shine way'annan mutanen hak'ar ma'adanan kasashen mutane sukeyi nacikin k'asa wanda bakowane ze iya fahimtarsu ba sedai kafin sukaigayin abunda suke buk'ata general faruk ya'ankara da b'arnarda suke Neman yiwa Niger Hakan yasa yafarmakesu alokaci d'aya to dasukaga Hakan sesuka gudu izuwa Nigeria tinda Basu samu abunda sukeda buk'ataba anan shiyasa suka tsallaka can. Ganin Hakan yasa general faruk yasanarda shuwaga bannin hukumarsu inda sukazo Neman Saka hannuna akan suriskesu Nigeria tinda Basu samu nasarar kamasu ananba suka gudu. mutin biyu kawai suka kama Kuma basune manyaba acikin wannan kungiyar tasu dake wannan ta'addancinga k'asashen duniya.. D'an shiru yayi Yana kallon yanayinsu kafin yacigabada fad'ar "wannan abun nasu ba'iya nigar da Nigeria yatsayaba har kasashen k'etarema domin kuwa hukumar sojojin ganah nemansu sukeyi hakama chadi, kyamarun, India, Pakistan, dakuma k'asarsuma wato south Africa...dukkan way'annan kasashen nemansu akeyi ruwa ajallo Kuma ankasa samun nasarar kamasu annanema akasamu kama mutin biyu Hakan yasa dasuka tsallaka Nigeria mukanemi izinin shiga Nigeria yin wannan aikin agun shugaban k'asarku Amma bamuda masaniya akan hukumarku sedai inada tabbacin cewa shugaban k'asar Nigeria ya tattauna da wasu daga cikin manyan sojojinku akan wannan problem d'in. To Amma Kuma ance daga cikin sojojin Nigeria akwai way'anda kejagorantar sojojin nigar acan yobe tareda general faruk. Yak'arasa zancen Yana kallonsu.
Kallon najeeb aliyu yayi yaga haryanzu be d'ago kanshiba Hakan yasa yamayarda kallonshi akan dattijon yace "ikon Allah gaskiya duk bamada wannan masaniyar ranka yadad'e Amma abincinkenda mukayi babu wani sojan Nigeria awurin gaskiya barama kaga yafad'a yana bud'e computer dinshi dakoyoshe suna tareda ita shiga nunamai abubuwanda kefaruwa acan yayi....cikin mamaki alhaji Abdulsalam Idris ke kallon video tabbas babu sojojin Nigeria aciki to Amma ya'akayi Hakan tafaru? Yayiwa kanshi tambayar da bame bashi amsarta ayanzu....cikin mamaki Yakoma kallon general aliyu kana yace Tabbas babu sojojin Nigeria anan Amma abunda shuwaga banninku suka gaya mana kenan domin harda bayanan sojojin dasuka jagoranci aiki sukaturo mana.. Se wannan lokacin mejo najeeb yad'ago kanshi tareda bud'e Baki cikin sweet voice dinshi dayagama sauyawa sabida b'acinrai yace "please ranka yadad'e kozamu iyasamun bayanan sojojin? Kokuma sunansu da hukumarda suke aiki please. "D'an shiru dattijon yayi kamun yace gaskiya bayanansu basa office d'innan Amma sunansu ance D'aya MEJO NAJEEB SAHABI KHAMIS DALA da GENERAL ALIYU HAIDAR AMEEN...Ido suka waro atare kamun sukalli juna cikin mugun mamakin wannan k'ullin da'akamusu. Maganar alhaji Abdulsalam Idris ce tadoki dodon kunnensu inda yake cewa "Amma bayanansu kubari nasaka adauko muku nabarsu a gida, Kuma ance zak'ak'uran sojojine way'anda Nigeria kejidasu ahalin yanzu tabbas zasu iya kama way'annan b'ata k'asar sedai idan basuso yin Hakanba domin yakanyu atare sukeda Y'an zagon kasan k'ila da had'in bakinsu ake wannan abun Amma ba wanda yakeda tabbaci akan Hakan sedai aikinda zasuyi ayanzu shine ze tabbatarda gaskiyar Ina suka dosa, idan akwai Saka hannunsu ko babu...Yana kaiwa k'arshe najeeb yamik'e tsaye domin harnaman jikinshi tafarfasa yakeyi inda wata Irin zufa tashiga ketomishi Tako Ina sabida mugun b'acin Rai da tashin hankali, kenan so akeyi ab'ata musu suna shiyasa aka shirya musu wannan abun akasanarda cewar sune kejagorantar sojojin Nigeria da Niger alhalin ko sanin antura ayi wannan aikin basuyiba wannan wanne Irin sharrine....shikuwa general aliyu yayi namujin k'ok'ari wurin b'oye nashi b'acin Ran inda yacewa alhaji Abdulsalam base an karb'o musu bayananba sungane ko suwaye kejagorantar aikin sabida Hakan zasu samesu acan. "Murmushi kawai dattijon yayi tareda yimusu fatan alhairi sukayi sallama kana general aliyu yabibayan mejo najeeb datuni yafice.
Aharabar gidan gwamnatin yasameshi harya shiga mota, shiga Shima yayi kamun yadibi najeeb d'in yace "miye abunyi mejo? Inazamu dosa yanzu? "Nigeria jihar yobe yafad'a atakyaice...dagajin Hakan aliyu bek'ara cewa komai yayinda captain Jameel kebinsuda Ido domin ko general aliyu dabecika nuna b'acin ranshi afiliba yau kallo d'aya zakamishi kasan ranshi amugun b'ace yake. Amma Hakan yabarsu kawai yanabinsu da Ido tinda Basu shiga dashi cikiba balle yasan abunda aka tattauna gashi Kuma yaji za'akoma Nigeria ko hutawa basuyiba..... kaitsaye airport memotar yakaisu suka biyashi, shikam yayi tafiyarshi. Anan suka Siya ticket d'in y'amma, bayan sunbiya suka zaunanan suna jiran lokacin tashin jirgin yayi. kamun wannan lokacinne suka samu sukayi wanka suka canja kaya acikin airport d'in domin akwai dakunan bak'i. Se bayan sund'an hutane yatinada fruit salad d'inda Hajiya Umma tabashi, D'an tsaki yaja tinawada amotafa yabarshi Hakan yasa captain Jameel tafiya yasiyo musu yoghurt da gasarshiyar kaza, anan suka d'anci sukayi sallah, Basu jima dagamawaba lokacin tashin jirgin yayi Hakan yasa suka fito kawai tareda koma hawa jirgi domin juya Nigeria.
A abuja jirgin yasauka Hakan yasa suka shiga Neman wanda zekaisu Legos ko yobe state Amma firrr ba'asamuba babu yadda Basu bugaba Amma babu jirgin ayau sedai gobe sukuwa bazasu iya Jira har gobeba..suna yatse suna tinanin yazasuyi kowada abunda yadameshi musamman Mero najeeb dayakejin ciwonshi nason tashi gakuma b'acin Rai karfin haline kawai yakeyi....captain Jameel ne yak'araso inda suke tsaye Yana fad'ar "Sr wlh ba'asamu jirgin dazetashiba Koda da yammane wai sedai jirgin ruwa idan Muna buk'ata Shima yanzu zetashi Kuma Anambara state zeje idan ya'ajiyemu a yobe se yawuce Amma ta gombe zebi. "Okay badamuwa bara muhaushi kawai zefi ai, cewar general aliyu Yana kamo hannun mejo najeeb d'in. Domin shidai komi beceba sabida yanayin ciwonshi se k'aruwa yakeyi gaya inbanda fad'uwa babu abunda gabanshi keyi da tsinkewar zuciya, Amma yadakewa ranshi domin komai kwakwarka baka Isa kace yanada wata matsalar ba sedai kallo d'aya zakamishi kasan cewa yanacikin mugun b'acin Rai dubada yadda kyakkyawar fuskarshi ke ahad'e kamar besan minene dariyaba...dahakan suka hau jirgin kuwan inda suka d'auki hanya atake semuce Allah yasaukesu