Showing 60001 words to 63000 words out of 68304 words

Chapter 21 - KWANKWASON JIMINA Book (1) Hausa Novels by Nana Hafsatu MX.txt

17 Jan 2025

4976

Nawraah. Ke din KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA...."


"Ai kuwa dai Hamma gaya mata. Wannan idan ta fara kuka samari da alama kowanne sai ya sakata kuka Allah kuwa. " Ashfeef ya fada Yana Kai mata rankwashi ta goce tana dariya.


Suka saka dariya baki daya ciki harda Amnah dake kyakyatawa. Ashir ya dube su daya bayan daya Yana goge hawayen fuskar sa dake tsiyaya yace,


'haka nake son ku kasance ko da yaushe cikin farin ciki . Da dariya dauke a fuskokin ku. Allah ya dawwamar daku cikin farin ciki ya yaye muku dukkanin damuwa ya nisanta ku da damuwar dake cin ku ya lullube ku da rahamar sa allahumma Aameen"


"Aameen Hamma tare da Kai."


"Eh mana hamma ka dena cire kanka dan Allah"


Murmushi yayi Yana gyara Kai yace,


"Ai idan kuka kasance cikin farin ciki ku kadai ma ya wadatar. Ni kune nawa farin cikin. Farin cikin ku shine nawa, ganin ku cikin farin ciki shi ke faranta rai na da zuciyata da gangar jiki na. Yan uwana, Ashfeef , Nawraah da Amnah kune farin cikina,. Da ke sanyaya ya Kuma lullube zuciya da ran Hamman ku Ashir a Koda yaushe. Allah ya jikan iyayen mu da rahama Allah ya gafarta musu Allah yasa aljanna makoma ce agare su"


"Allahumma Aameen Hamma"


"Inshaa Allah Hamma"


"Aameen"


Yauwa Amnah ta. Ya ce da Amnah Yana lakutar kumatun ta.


"Zaki Sha alawa?"


"Eh" ta fada tana tafa hannuwan ta.


"Nawraah jeku sayo alawa please. Ungo ki taho da omo da sabulu zan mana wanki sun taru. Kowa ya curo nasa"


"Tohm Amma dan Allah Hamma ka bari muyi kowa yayi nasa"


"Aa ban amince ba. Illa dai Ashfeef zakayi dauraya ka shanya. Ke Kuma ku zauna da amnah idan Kun dawo daga sayo alawar ki koya mata karatu"


"Tohm Hamma inshaa Allah. Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa"


"Aameen Yaa Rabbi jam'an..."


Mikewa yayi ya shiga hada kayan su da sukai datti Yana kaiwa wajen rariya zai wanke. Ashfeef ma ya dakko bokitai ya fara ebo ruwa Yana tarawa a babban baho Wanda zasuyi wankin dashii....


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_




_ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_




_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*




_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 21:02] Maman: _K'K'J_
_(M/W/S)_




_✍️:MX_




_48_


_ADVERT👇👇_


_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_




_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_


_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_


_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._


_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
:::::::::


::::




Rufe kofar gidan tayi ahankali, Ta shirya tsaf cikin riga da zani na atamfa ta yafa mayafin ta ta rike yar jaka. Ta sauka daga yar matattakalar da ake haurawa ahau gidan nasu


Da sauri ta wuce har tana tuntube ta rankwafa kasa dataje wajen dakin su Amnah ta durkusa ta wuce da sauri tana saye fuska.


Dan adaidaita ta tare ta shiga ciki . Bata mance da kwatancen gidan data karba ba awajen direban daya kawo wa su Ashir kayan abinci kwanakin bayan tun da ran bappah junaidu.


Har kofar gidan ya kaita ta sauka ta lalubo kudin sa a jaka tana kallon darin biyun ta dan adaidaita, ya wafce da karfi ganin taki bashi, ta tsirawa wa kudin idanu. Alokacin Kuma Nusaiba tunani take dama bata zo ba da ta kafa ta daba don tanason ta saka data ta hau duniyar online.


Baki ta wangame alokacin data Isa kofar gidan tana yaba tsaruwa irin tasa tamkar a gidajen da ake nunawa a talabijin na masu kudi.


Ta nufi gate din tanata sauri masu gadin suka tareta.


"Ya ke Ina Zaki?"


"Wajen hajiya nazo."


"Wacace? Bantaba ganin ki ba anan gidan"


"Tabbas bakuwar fuska ce kam, Bana kasar ne"


Nusaiba ta dashare baki tana sosa kasan keyarta ta sake cewa,


"Kawatace matar gidan"


daya daga cikin masu gadin ya bushe da daria har yana rike ciki ya kalleta tun daga kasan kafarta zuwa fuskar ta . Gaba daya ko alamar daukar kalar ire iren kawayen hajiyar tasu batai ba. Don haka ya grigiza Kai hana tabe baki yace,


"Ba nan gidan bane Ina tunanin kinyi batan Kai"


"Banyi ba fa. Gidan Dr bintu mana. Zan maka karya ne"


"Kirata awaya " ya fada yana rera fito.


Nusaiba ta zaro idanu tana janyo wayarta ta fara latse latsen karya ta danna wajen kira ta kara a kunnenta,


"Eh nazo bintu. Okay bari na shigo. Ai masu gadin nan naki ki canza su basuda kirki. Na gidah na kin manta korarsu nayi alokacin da suka hana hadiza shiga? Okay gani nan"


Ta nufi kofar kantar kantar zata shiga Mai gadin ya tare kofar da hannun sa yana hura hanci yace,


"Aa... Duk munsan ire iren ku. Ba wata hajia da kika kirawo dan Allah malama ki kama kafa ki koma inda kika fito"


Nusaiba ta saka hannu tana mai nuni da shi tace,


"Ka bude mun na shiga... Ya sunan ka ne?"


"Sunana Naziru gidah Kuma nace ba Zaki shiga ba don bansanki ba bakuwar fuska ce, na biyu Kuma ba wata hajia da kikai waya da ita. Yadda kika zo baki a abude tamkar Zaki handame mu ma kina kallon gidan kowa yasan bakuwa ce ke kuma marar karfi iri na. Don haka ki koma inda kika fito kada kisa na saka miki shocking wallahi" ya karasa fada Yana daga shocking din hannunsa. Wata waya Mai karafuna ajiki tanata hartsatsi


"Naziru ko? Ka kyauta ko? Zan nuna maka wacece ni a kasar nan"


"Mtsc" Yaja tsaki yana komawa kan kujerar sa Yana rera baitin wata waka,


Cikin ikon Allah sai ga fitowar motar direban rannan data gani. Ta dashare baki tana daga masa hannu. Ya yi murmushi shima yace,


"Ina wuni? Hajia ta...?"


"Kwarai ta Naduka.... "


"Tasan Zaki zo ne?"


"Munyi waya ai tana ciki"


"Eh tana nan. Ya haka nazman ka barta a tsaye ko wani abun kake?"


Naziru ya dube shi yana kallon nusaiba yace,


"Ka Santa ne?"


"Na kakkai su hajia gidan ...........


Ta katse shi da sauri tana murmushi tace,


"Bai sanni ba ne na masa uzuri. Bari na shiga"


Ta kutsa Kai ta gaban Naziru Mai gadi ta shiga ciki. Ba yadda ya iya ya koma wajen zaman sa ya zauna. Shi Kuma direban ya wuce tsalallaken titi wajen masu kankana...


Ko data shiga bata San kan gidan ba sai da sata Mai aiki ta nuna nata kofar da zata shiga.


Ta shiga ciki bakinta dauke da sallama. Kai tsaye ta shiga parlorn ta hakimce ta zauna ba kowa aciki


Sai daga baya Dr bintu ta sakko tana gyara dankwalin ta. Ta dubeta tana kallonta sama sama,


"Wacece wannan din?"


"Ah hajia ni ce fa. Matar bappan su nawrah "


"Oh" ta fada tana dubanta shekeke. Dake Itama Dr bintu akwai jin Kai


"Baki iya gaisuwa bane? " Ta sake tambayar ta tana mata kallon tara saura kwata ganin yadda ta babbake akan kujera ta harde kafafu..


"Oh Ina kwana?"


"Lafiya. Meke tafe dake?"


"Dama zuwa nayi akan kayan abincin da kuke bayarwa kwana biyu shiru. "


"Ajiya kuka bamu ne? Na dauka niyyace da temakon musulunci mukayi iyayinmu ko dolen ku akan mu take?"


"Hajia kwantar da hankalin ki ni bada wani abun na ce haka ba. Kuma ni a bayan ki nake wallahi"


"Bangane me kike nufi ba malama"


"Ina nufin rannan ba Nawraah na fadin wasu maganganu ba da kukazo? nufina ki kwantar da hankalin ki nasan komai Kuma bazan bar wani abu ya taso ba muddin kika bani bukatin da nake nema"


Dr bintu tayi shiru gabanta na bugawa tasan komai? Kenan tasan Alhaji Sambaso mijinta shi yake kashe malama Hindu


'kjnsan komai fa kikace .?"


"Kwarai na sani harda wani abun da ke bakida masaniya ma akansa" Nusaiba ta kara da qarya tana karya Kai bayan ba abunda ta sani


Dr bintu ta gyada kai tana gyara zamanta tace,


"Me kike bukata?"


"Kudi... Kayan abinci.., sutura irin ta ku ta manya. Kuma ba su Nawraah zaa kaiwa ba gidana zaa kawo. Sannan suma su Nawraah ki kawo kudi a basu. Idan kika dore akan haka to shikenan Ina Mai tabbatar Miki komai ya wuce. "


Dr bintu ta gyada Kai. Ta mike ta dakko jakarta hannunta na rawa. Ta ciro check dinta ta dakko biro ta rubuta kudi masu yawa ta mikawa nusaiba.


"Ki dauki rabi ki basu rabi su nawrahn."


"Bakida damuwa ai awajena ma suke agidana ni nake dawainiya dasu ta komai daga abinci zuwa sutura"


"Allah sarki. "


"Kayan abincin fa?"


"Zan aiko a kawo miki inshaa Allah. Zaki iya tafiya yanzu Ina da abubuwa ne agabana"


Nusaiba ta gyara zaman ta ta dakko wayarta ta rike tana gyara mayafi tace.


"Dan daukeni da wayar ki a haka sai ki tura mun dan Allah"😂


Ba abun Dr bintu tayi, Ba musu ta dauki wayarta ta dau hotunan nusaiba ta tura mata a lokacin


Sannan nusaiba ta mike ta futa sukayi sallama. Ta tsaya a gate ta gaggasawa Mai gadin magana yayi banza da ita yana Jin rediyo harda Mai dakuwa ta Zagi.


Tana tafe tana addu'ar Allah yasa kar Dr bintu ta gane batasan komai ba. Wani bangaren na zuciyar ta Kuma na mamaki hadi da tabbacin lallai akwai wani boyayyen lamari da suke boyewa. Kuma koma menene Nawraah tasan wani kaso daga ciki...


Gidah ta koma ranta fes. Ta boye kudin har nasu Nawraah ta hanasu taki basu. Taki Kuma gayawa kowa kudin data samu da inda taje. Tace wai neman aiki taje a Naduka crescent. Matar ta bata dubu goma tace tayi cefane. Ranar dai abinci har da nama akai kowa yanata mamaki.


Dr bintu na lekan nusaiba ta taafi. Jikinta na rawa ta nufi parlorn Mai gidan nata Yana zaune yana karanta jarida ta zauna akusa da shi tana yarfe hannu tace,


"Nusaiba dinnan tazo komai tac har abunda bansani ba ta sani...


A firgice ya juya ya dubeta bai San sanda ya furta Cewar,


"Tasan ni na tunkuda junaidu Mai gidan Hindu ta baranda ya mutu ma kenan."


Dr bintu ta mike tana zaro idanu tana girgiza kai tace,


"Alhaji.... Kana nufin kace shima kashe shi kayi? Kacemun ya fado bai taka tsani ba ya rasu. Ashe ashe Alhaji Kai ka kashe shi?. Ka kashe matar sa shima din kaje ka kashe shi. Alhaji wace iriyar rayuwa ce. Kisa fa? Kamai da rai tamkar kiyashi Alhaji? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Wallahi tallahi nagaji. Yanzu kenan tunda itama ta sani zaka bita ka kasheta kenan?"


Alhaji Sambaso ya girgiza kai yana harde hannuwa ban roko yace,


"Wallahi bada sani na kashe shi ba. Fada muke na turashi ya Fadi ya mutu. Ki yarda Dani bintu. Zancen gaskia kenan. Ita kuma bansan a inda taji ba Allah"


"To magana ta gaskia Alhaji na tsame hannuwanaa akan ka. Maganar Hindu na rufa maka asiri kace kuskure ne na bar maganar. Amman ka sake kashe musu mahaifiy saboda Allah. Wato kenan itama wannan kasheta zakai ko? Daman tazo tana bukatar kudi da kayan abinci da sutura idan baa bataba ba zaa samu matsala. Saboda tana cewa ita kadai ce tasan yadda zatai da Nawraah komai ya wuce "


"Karki damu duk abunda takeso zaa mata. Allah zaa yi. Kome tameso. Ni ki yafemun kinji?"


"Wace bintu ce zata yafe maka? Ka nemi yafiyar Allah dai ka Kuma roki gafarar iyalin su. Ba ruwana acikin Allah kuwa."


"Trust me baa abunda zanwa matar nan Allah shima shi ya takalo ni Yana gayamun maganganu Yana marina kinga abunda ya faru kenan"


"Alhaji koma meyake maka sai kayi enduring ka kashe masa mata,shi tunda acikin bacin rai yake. Idan ya huce sai ka gyara amma ka kashe shi?"


"Tasu ta kare ne su. Ya za'ai da wannan matar. "


"Yanzu dai inada aiki asibiti idan na gama cikin week dinnan zanyi tunani"


"Yauwa bintu na Allah ya miki albarka."


Mikewa tayi ta fice ta nufi asibutin tah dake bayan unguwar, gabanta nata faduwa . Ko da direba ya sauketa ma ta dade Bata futa daga mota ba saboda tunanin data tafi


:;;;




Kwanaki suka shude. Alokacin Ashir har ya fara hada kudade sosai na Sanya Nawraah a jamia.


Ranar wata laraba da yammaci Dr bintu taje gidan na nusaiba ta Sha mamaki dataga gidan dama aciki suke rayuwa


Ta zauna tana kyamatar ko'ina. Aka kawo mata ruwa ma taki Sha. Suka gaysa da nusaiban ta tambayi nusaiban abinda take so.


Nusaiban tace yaran su sun samu gurbi a jami'ar Al-Haramein. Amman ba kudin da zasu shiga. Kuma an dena daukar daliban tallafi.


Dr bintu tace ba damuwa. Satin sama zaa biga musu admission letter. Makarantar harda share din mai gidan ta Dana hajja qibdiyya. Don haka zaa basu scholarship khauta su nawa ne. Nusaiba tace su hudu ne . Layla, Nawraah, Ashfeef da Kuma Ahmad.


Dr bintu tace ba damuwa zaa basu gurbin karatu. Itama yayanta biyu daya zata fara daga kevel one . Dayan Kuma a babban gurbi yake zai karaa karatu ne . ..


Hakan kuwa akayi ana shiga satin aka bugo admission letters aka Aiko dasu akace nanda sati biyu suzo su fara daukar darasi a jami'ar Al-Haramein dake Naduka crescent.


Hakika su Nawraah sunyi murna. Musamman Ashir daya kasa boye farin cikin sa. Ashfeef da Nawraah ma harda su a gurbin karatun.


Wani bangare na zuciyar Nawraah Kuma na kokonto akan amincin Dr bintu da Nusaiba. Don haka ta zuba musu Ido kawai tana nazartar su....


:;;




Ashir na zaune akan kujera... Ya sayo second fairly used din waya dake hannun sa..


Ya ciccire komai na wayar ya mayar kan second din daya saya. Ya kuma bar su akan ta ainhin. Recordings din wakokin Nawraah data yiyyi ya ajiye mata su ya Kuma tura wasu a wadda ya sayo ..


Daya bayan daya ya shiga danna wakokin larabawa yana saurara duk Wanda batai masa ba ya goge akan wayar daya sayo yayinda dayar Kuma ya ajiye don Nawraah yake son ya barwa duka tunda yanzu ta shiga jamia tana bukatar browsing assignment da sauran su. Tasa Kuma sai Ashfeef ya dinga amfani da ita.


Yaje kan wani recording na wakar Maher Zain. Har zai goge sai Kuma ya cigaba da saurara jin tanada dadi. Maganganu ya fara ju suna fitowa daga wayar yayinda recording din wayar baa jinsa sai can daga kasa.


Kamar zai goge sai Kuma ya cigaba da saurara Yana ji....jikinsa ya dau rawa jin maganar da macen da mijin keyi. Da sanda ummy take basu hakuri tana bataji komai ba.


Mikewa yayi a tsaye . Whatsapp dinsa ne yayi kara. Ya duba wayar dake hannun sa. Ganin fefen bidiyo ne aka tura Masa da wata number ta waje. Yana budewa hankalin sa ya tashi na daga abunda ya gani


Jikinsa na bari ya tura budiyon daya wayar daya barwa Nawraah . Ya sake dubawa zai kira number data turo yaga ta bace bat bata kan WhatsApp gaba daya idan ya kirama sai ace batakan network


Fita yayi ransa na zugi. Har zai fuce baki daya sai Kuma ya kwaso shanyar da Nawraah tayi ya Kai mata dakin ya koma ya gyara ko'ina ya shigar musu da takalman su da kayan wasan Amnah daki ganin garin da hadari.


Ya koma ciki ya dakko Dan balangun daya sayo musu basanan ya dora akan katifar su ya fita


Yana rufo kofar sai ga Nawraah ta dawo rike da hannun Amnah


"Hamma Ina zaka?"


"Ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo inshaa Allah. Ungo rike wayar nan taki ce. Ki dinga browsing na assignment da itaa idan kin fara jamia..duk rintsi duk wuya kada ki bari wayar nan fa subule daga hannun ki. Kar ki bawa kowa, Na roke ki da girman Allah kuma recordings din wayar nan kada ki jisu har sai kin shig aji na biyu zaki shiga na uku, sai na hudun kammala jamia kinji ko? . Allah yabada saa"


"Hamma meye haka kamar Wanda zaiyi tafiya ba dawowa? Nagode Allah ya saka da alkhairi Amin"


"Aameen ya Hayyu waayum. Sai na dawo. "


Ficewa yayi dasauri bayan ya yiwa Amnah wasa Yana lakuce mata kumatu


Kai tsaye ya nufi ofishin Alhaji Sambaso ya ci sa'a kuwa yana nan. Akayi masa iso ya shiga


Yana shiga dama Alhaji Sambaso shi kadai ne. Ashir cikin zafin nama ya cikumi wuyan sa yana kunna masa recording din wayar nan.


'kai ka kashe ummy.... Kuma ka kashe abbiey..." Ya karasa fada Yana daga wayar sa.


"Kaga komai nan evidence ne cikin nan. Inshaa Allah rayuwar ka sai ta tagayyara sai ka zama abun tausayi. Zakasha mamaki"


"Ka tsaya muyi magana yaro"


"Magana? Hahaha zakayi magana aagaban hukuma da gaban Allah ranar gobe kiyama"


Ficewa yayi. Alhaji Sambaso ya saka hannu ya shafo habar sa Yana furzar da iskar bakinsa Mai zafi . Wayar sa ya dauka ya rubuta sako ya koma ya zauna Yana shafe kansa.


Ba jimawa can wayar sa tayi haske ...ya dauka yana dubawa hamdala yayi ya kwantar da kansa akan kujera Yana sauke ajiyar zuciya..


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login