Showing 66001 words to 68304 words out of 68304 words
Chapter 23 - KWANKWASON JIMINA Book (1) Hausa Novels by Nana Hafsatu MX.txt
Nusaiba ta janyo ta ta bayan rigarta ,
"Ina zakije? Ba bu inda Zaki bita. Koma ki zauna ba Zaki koyo wannan halayyar tata ba ta fita gaba gadi kullum a titi ",
Bappah junaidu daya kasa magana saboda tsananin bakin ciki kawai ya durkusa ya gyara zaman takalman sa ya shige cikin gidah
Nusaiba tabi bayan Nawraah da harara tana yatsina fuska tana gatsine gatsine .
Ko da Nawraah suka futa tsayawa tayi ajikin bango tana kife kanta hawaye ne masu dimi suka shiga zirara daga idanun ta na bakin cikin kalaman nusaiba.
"Kenan zargina take? Zargina take Ina aikata wani abun awaje kenan na haramci! Yaushe nake fita nida kullum Ina gidah? Yaa Allah kana gani Allah ka mun sakayya. Allah ka dubemu ka saka mana. "
Ta share hawayen ta ta cigaba da tafiya tana rike da hannun Amnah. Baki daya ta gama tsorota da halayen nusaiba. Ta Kuma gama yanke kundurinta kawai
"Ko guduwa zamuyi mu bar garin? To muje Ina? Ko mu rama abunda take mana mu fasa window ta karfi? Kai Yaa Allah Yaa Allah" ta karasa fada tana dafe kanta dake mata tsananin ciwo
Suna ta tafiya har zuwa Naduka crescent. Suka tsaya awani shago ta dakko nera hamsin din wajenta ta sayawa Amnah biscuit da alawa kamar Koda yaushe. Ta kan Dan fitar da ita haka su sha iska saboda dakin da suke babu window. Gidan su nusaiba Kuma da sunje shan fanka take fara hararae su. Shysa Nawraah take dan zagawa da Amnah su sha iskar Allah ta waje. Ko Amnah taji dadin jikin ta. suka cigaba da tafiya..
Tana daga Kai ta sauke akan dankareriyar jami'ar nan da akace sun samu gurbin karatu ta Al-Haramein Naduka.
Tsayawa tayi sosai tana yaba kyawu da tsaruwar ginin na makarantae. Sai kache a turai.
Manya manyan gidaje ne na masu kudi a layin harda gate dinsa layin . Ya hadu kwarai matuka layin dan Bata taba zuwa nan haka ba ta shagala tanata kallon ko'ina lungu da sako.
Kallon ta ya sauka akan tankamemen wani katon gidah an rubuta masa NADUKA GRAND ORPHANAGE PALACE a kasan Kuma an rubuta (Gidan Marayu) gidan marayun na kallon wani sugnoard da taketa tunanin a inda tasan sunan wato DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING....
Zuciyarta da gangar jikinta nata ingizata ta shiga cikin katafaren gidan marayun janye da hannun Amnah. Ga mata nan Yara da manya harda Wanda ake rikewa a hannu Kuma duk marayun ne.
Ga Kuma wani bangare daga hagu can an saka wasu manyan wayoyi na karfe anyi Katanga an rufe wajen maza ne can kuma bangaren su
Da sauri ta shiga cikin reception/waiting area. Sukaga matar in charge of wajen Nawraah ta karasa ta gayshe da ita hakama Amnah
"Meke tafe daku Yan kanne na?" Matar ta tanbaye su.
Nawraah ta dan sunkuar da kai tana lankwasa Yan yatsunta tace
"Marayu ne iyayen mu sun rasu da babban wan mu. Daga ni da kanwata sai dayan yayan mu muka rage. Bamuda wani sauran gata da yarage mana. Shine Allah yasa na biyo nan yankin haka naga nan gidan marayun. Bansani ba ko kuna daukar marayu ko Yaya a abun yake?"
"Allah sarki Allah ya jikan su da ra rahama. Daga wace ungeua kukazo kenan?"
"Aameen Yaa rabbi. Daga Naduka zone muke"
"Okay to .. bakuda wasu Yan uwa ne haka da sauran su?"
Nawraah tayi shiru tana tunani. Wane yan uwan Zata ce bayan yan uwan nasu sun juya musu baya. Da su da babu su duk daya ne. Bappa Auwalu ne Kuma yayi iya yinsa, matar sa tafi karfin sa. Shi ma Kuma bashida halin da zai iya rike su, da sauri tace,
"Ba muda kowa. Duk sun rasu dama daga birnin bunza mu kazo da iyayen mu Kuma daya bayan daya cikin kankanin lokaci duk suka rasu kowanne ba rata da daya sosai "
"Allah ya rahama musu"
"Aameen yaa rabbi"
"Abunda za ai shine. Kuje kuzo da yayan naku da kayan ku kawai. Din yanzu ma ba paper da form da sauran su.."
"Toh inshaa Allah"
"Nagode sosai. , bari muje"
Nawraah ta mata sallama suka fita. Sunzo zasu wuce ta kofar signboard din gidan dazu taga wata zungureriyar mota da alama kaya ne aciki, sai wasu biyu masu matukar tsada da fara da blue hadaddun motoci, sun bi bayan babbar motar suka nufi gidan dataga signboard din DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING. Motocin suka tunkari gate din da alama mutanen gidan ne sukayi tafiya suka dawo alokacin.
Tayar dayar motar bayan ta sache alokacin direban ya kasa jarasa shiga da motar gidan. Gashi sauran motocin ba dama su shiga. Motar ta tokare...
Wata kyakkyawa mata tafito daga cikin bayan motar owners corner tana gyara mayafin ta..
Bayan tafito ne wani matashin saurayi shima ya futa daga bayan moyar Yana latsa wayar hannun sa.
"Anees...." Matar takira shi da alama mahaifiyar sa ce saboda tsananin kamar da suke.
"Naam Mami"
"Yi sauri mu shiga mana. Ka tsaya. "
"To mami"
Yana biye da ita a baya suma yan sauran dayar motar suka fito daga ciki. Harda babban mutumi. Kana gani kasan mahaifin su ne. Yana tafe da waya a kunnen sa yana amsawa.
Can kuma sai ga mace da namiji suma da Nawraah take kyauta zaton Yan gidah daya ne. Saboda suna kama.
"Anees, junior meye haka kuzo mu shiga gidah mana. Ke Hayfa duba bayan mota na manta USB cord na ki dakkomin "
'Anees, Junior, Hayfa...." Nawraah ta shiga nanata sunayen su tana waywayawa baya har suka shige cikin gidan su.
Itada Nawraah suka dauki hanyar gidah a filin ball taga Ashfef Yana buga karasa ta sanar da shi duk abubuwan da akayi tundaga gidahn Bappah Auwalu da nusaiba ya zuwa gidan marayun data gani. Kan zasu koma da zama nan
Ashfeef bayi musu ba. Yayi addu'ar Allah ya zaba musu abunda yafi alkhairi idan zaman dakin tumakin ne alkhairi Allah ya zaunar da su idan kuma tashin su ne Mafi alkhairi Allah ya hada su da Mutanen kwarai
Suka koma gidah Nawraah ta fara hada musu kayan su ta gama tsaf. Asubar fari suka bar gidan suka nufi gidan marayun...
*ALHAJI SAMBASO AVENUE*
Shirye shiryen dawowar yaran Dr bintu takeyi. Kowanne da irin abincin da yake so..
Karfe hudu na yamma jirgin su ya sauka..direba yaje ya dakko su
Matashin saurayi ne mai jini a jika. Wanda mahaifiyar su Dr bintu ta nufe sy tana musu lale marhaban..
Marwan ya rungume mahaifiyar tasu Yana murmushi. Harda kunan Dadi. Lily kuwa ko ajikinta ta yi murmushi kawai tana yrigzia Kai.
:;;
..... Bappah Auwalu ya nemo su Nawraah Yana rokon su dawo kusa da shi Nawraah tace gaskia zaman su ya kare agidan nan. Yana rokon sa suna rokon sa ya kyale su
Domin dakuna ne da gado hudu a dakin gidan marayun... Kowanne daki
Itada Amnah kowacce da gadonta sai Kuma wasu yammata suma guda biyu suma da gadajen su. . Da tv dinsu harda fridge mashaa Allah ga fanka da ac, ac din kunnawa ake a kashe idan tayi awa biyu. ..
A dole bappah Auwalu ya hakura ya barsu Amman sai da yayi hawayen nadama musanman kasancewar matar sa Nusaiba itace silar komai, komai ya baci da 'yayan dan uwan nasa shakikan sa...
Haka ya hakura ya koma gidah zuciyar sa na kuna...
Ranar lahadi su Nawraah da Layla suka sukaje kasuwa suka dan sassayo kayan gwanjo.saboda zuwa school .
Suka shirya tsaf. Layla ta bugawa Nawraah suka nufi makaranta ranar washegari..
*Al-Haramein university*
Baki daya kusan rabin daliban tsayawa sukai suna kallon su Nawraah suna musu dariya. Ganin Shigar su daa kallo daya zakai musu kasan talakawa ne.
Cikin haka suna shiga ba dadewa sai ga motocin biyu sun shigo ta ciki suna yar tsere. Dalibai aka taru akan su. Motocin ma kadai abun kallo ne.
Saura kadan ya Nawraah data tsaya tana duba jakarta . Ya fito a harzuke Ya daddanna mata horn taki matsawa, ashe bataji ba hankalin ta ya tafi kan Jakarta, Yan kudin ta naira dari da Ashfeef ya bata taci abinci ne bata gani ba.
Futa yayi da niyyar mata magana a tsawace. Marwan ya futo da sauri daga tasa motar Yana rike hannun anees daya yiwa Nawraah nuni da yatsa Yana dubanta. Yasan shi da zuciya.
"Ke daga fuskar ki, How dare you? Ba ki gani ne ko ke bebiya ce. ?"
Nawraah ta daga Kai jin an mata magana kanta a kasa sa, don Sam bata ji ko gansu ba sai alokacin, hankalin ta baya jikin ta. Cikinta nata kugin yunwa..
Tana dagowa suka zuba mata idanu atare. Anees ya nemi abunda zai fada mata a abakin sa ya rasa. Haka Marwaan daya kasa hakuri ya lankwasa kansa Yana dubanta.
Tayi musu matukar kyau fiye yadda alkalami zai rubut. Rakabewa tayi ta gefen su ta wuce, ganin sun mata shiru...
"Senior man na nayi new catch ta. Ina Kai nayi mata ma ni wannan yarinyar kallo daya tatafi Dani, zan auretaa" Marwaan ya fada Yana shafa keyar sa
Anees Yana so yace shima ya fara jin wani ahu akanta sai Kuma yayi shiru jin abunda Marwan ya fada. Don dama ba iya magana zai yi ba haka halin sa yake. Kuma bayason wani ya hadasu da abokin sa, kasancewar iyayen su aminai ne suma Kuma aminan juna ne.
Har ta kule musu gano basu dai na kallon ta ba musanman Anees da idanunsa suke sexy eyes kamar Mai bacci yadda yake kallon ta da idanunsa daya narjse akanta Kai kanka sai Kaji wani irin idan kai ake ma. Zamu iya Kiran kallon da love at first sight. A hausan ce kallo daya yayi mata zuciyar sa sai ta kamu.
Tana yin nisa dai dai wasu kujeru ta zauna tana mayarda numfashi. Layla ta karasa wajen tana dafa kafadar ta,
'kai kiban tsoro wallahi ..."
"Dalla dan abun tsoron baya Miki yaw?. Na tambayi sunan su. Kinga wancen dogon me haske kamar balarabe sunan sa ANEES ABUBAKHR DOLLARS.... wancen dayan abokin nasa shima kyakkyawa wayyo har na fola shi Kuma sunan sa MARWAN SAMBASO, ance iyayen su nada share a makarantar nan. Iyayen su multi billionaires ne. Amma baban ANEES din yafi baban MARWAN kudi. Alhaji Sambaso... Shine sunan mahaifin MARWAN! Shi kuma baban ANEES din sunan sa Dr. Abubakhr dollars"
Nawraah tayi shiru tana tunani aina tasan sunan ma? Tamkar tasan su ko sunayen su take ji? To amma a Ina? Sam ta kasa ganewa ta yamutsa fuska kawai ta riko hannun Layla suka tafi.
Layla nata tsokanar ta tace,
"Wannan ace su biyu su so ki, lalle zaa sha gwagwarmaya.. Kinga kallon da kowannen su yake miki kuwa? Tab akwai kallo agaba Nawruhs........"
Nawraah tayi murmushi kawai tana girgiza kai tache,
"Rufamin asiri Laylus..."
Kai tsaye suka nufi department dinsu na course din da zasu karanta. Wato department of CRIMINOLOGY...
TIRKASHI!!! Akwai sauran ruguntsumi agaba....
:::
#RICH VS POOR
#CRIMINOLOGY/CRIME/CONVICT
#ROMANCE
#LOVE/AL-HUB HAYAT
#LIFE-PARTNERS
#KAUNA MARAR GAURAYE
_Alhamdu Lil Laahi! Duka duka anan ni Nana hafsatu zan dire alqalami na... Wannan shine shafin karshe na kashi daya na wannan littafi mai suna a sama. Wato mun kammala shafukan *BOOK ONE...* sai kuma bayan mun kammala Ibadah ta watan ramadhan inshaa Allahu. Anyi bikin sallah. Da yardar Allah sai mu dora daga inda muka tsaya. Wato zamu dora da sabbin shafukan *BOOK TWO* kenan..._
_Ina fatan masoya wannan littafi zasu cigaba da karantawa idan muka fara posting *BOOK TWO* Bayan bikin sallah Inshaa Allahu .. ayi hakuri da yadda littafin wannan karon yazo. Fata dai Allah yasa mu amfana da darussan ciki, Ya hadamu a ladan duka. kurakuren dake ciki rabbana ya yafe mun da ku baki daya .. Aaameen_
_Kowane dan adam tara yake bai cika goma ba. Ina neman afuwar dukkanin wanda na batawa rai farawar littafin nan zuwa inda na tsaya . Allah yasa muyi Ibadah karbabbiya Allahumma Aameen_
_Aje a saya turaruwa masu matukar kyau da kamsasawa. A kamfanin YERWA INCENSE AND MORE. Idan kunje kuce a hada muku da mukammaria da set din zafafa biyar... Idan anje ache daga zafafa biyar ne akwai ragi....08095215215_
_Ina masu son samun gwaggwabar lada ta ciyarwa da azumi?HGL CHARITY FOUNDATION ta kawo muku komai cikin sauki, Masu nera ashirin , hamsin, dari da sama da haka. Ko kayan abinci ma zaku iya bayarwa don talafawa mubakata. Tarauni Kano... 9044191709 OPAY... zaa yi kunu, kosai, abinci, ruwan sanyi, da duk yadda hali ya kama a dafa abawa mabukata masu azumi, Dan Allah a saka ko nawane a sami lada idan kayan abincin nema sai a Kira number opay din akai musu gidah Allah ya hadamu a ladan duka Aaameen_
_Tohm masoya makaranta zafafa. Yankin KWANKWASON JIMINA.... MAI WUYAR SHAFAWA.. Anan zan dasa aya. Sai cigaban a littafi na biyu (BOOK TWO) idan Allah ya kai mu bayan sallah da yardar Allah_
_Allahumma Ballighna Ramadhan! Allah yasa muyi Ibadah karbabbiya. Allah kuma yasa ayi sallah lafiya Allahumma Aameen..._
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_