Showing 1 words to 3000 words out of 8023 words

Chapter 1 - HAQQI COMPLETE BOOK BY Princess Aysha Muhammad (Humaira) .txt

Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)




[5/17, 15:33] Umar Dalha: ☠HAQQI☠











✍🏾mr. melody💥











🌙april-2017











IT'S PAGE 1⃣-1⃣0⃣ ONLY
AND
⇨BEST ON A TRUE LIFE⇦









Page1⃣&2⃣












*Dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatima-bintu👩‍👧*












~Actually this what was happened to our elder brother and our friend also, finally he has answered Allah's call already since last two years ago. May your gentle soul rest in perfect peace (muhammad abdullahi) ameeen~










βismillahir rahmanir rahim








Ranar saturday quarter to 11 O'clock morning na
tashi daga ghetto nayi shaye-shaye na fitar
hankali wiwi, madaran suku die, coideen, drugs
kai in takaice muku zancen duk wani abu da kuka sani
mai gusar da hankali banda giya sai dana sha shi sannan na
kama hanyan gida. Tafiya nake ina malangarine kamar akwalan keke yara su kayi dan-dazo suna min ihu suna cewa “yayi marisa ya sha capsule sha" idanu na a rufe suke kuf! kamar mai bacci saboda shawuwan da nayi, nan take na lalubi duwatsu a kasa jifa kawai na fara yi kota ina kamar zararre har na fasawa malam yusuf limamin unguwar mu kai, yaran duk suka watse kowa sai gudu yake ga sabon mahaukaci.
Saukan bulalai kawai na fara ji a jiki na any how, manyan unguwar mune suka nad'a min na jaki a bisa abunda na aikata na rashin hankali. A
wurin na fad'i kasa sai bacci ga kwatami da bola
a gefe. Nine ban farka ba sai bayan sallah'n la'asar ba wanda yazo ya tashe ni balle ya jany'e ni daga gefen kwatamin, sai naji duk jiki na yana
min zafi da rad'ad'i ga wani uban yunwan da
nake ji a hankali na lalla6a na tafi gida. Zuciya a dakule na bankad'e kofan gidan na kutsa kai ciki, kasantuwar gidan namu na haya ne duk matan gidan suka shige shashin su da y'ay'an su gudun kada na illata su, kitchen na wuce na shiga
bubbud'e tukwane kamar wanda yayi ajiya amma
ban samu koda k'anzo ba hakan yasa na shiga
kwalawa mahaifiya ta kira a tsawace daso!
Daso!! Tana kyarma ta fito da tsohon cikin ta
haihuwa yau ko gobe, “ina abinci na!?" nan ta fara kame-kame “umh umh yi hakuri muh'du,
wallahi ban zata zaka bukaci abincin bane shi
yasa na baiwa su fatima d'azu" “me! Abincin nawa?,
wallahi karya kike, uban ki ne yake nemowa ko
uba na?" “dan Allah kay...." maganar da ban bari ta karasa ba kenan na wanke ta da mari tas! A
kuncin ta na hagu na sake d'ago ta da wani marin a kuncin ta na dama nan fa na hau yin ball da ita tana kuka “wallahi yau sai kin
yabawa aya zakin ta, sai na kashe ki na kuma
kashe d'an dake cikin ki" wallahi haka nayi ta jibgan mahaifiya ta ko tausayin ta bana ji, nan ta shiga rera kukan neman agaji tana kuka mai cin rai wai ga d'an data haifa nan yana dukan ta instead of ko zagi kada ya jawo mata, wallahi musa ina baku labari duk sanda na tuna abubuwan da na yiwa mamata a rayuwa sai naji kamar na kyastawa kaina wuta ko zan d'an ji sauk'i a cikin zuciya ta, nida aboki na aliyu da ake bamu labarin banda hawaye babu abunda muke yi, gaskiya *HAQQI* ba wasa bane dan wallahi ya zarce tunanin mutum balle aljan, duk wanda ya san muh'd idan ya kalle shi a cikin wannan halin wallahi sai yayi masa kuka, ya kumbura sosai na fitar hankali domin rigan jikin sa sai in an raba shi kashi biyu sannan zan d'au daya a hakan ma zai min yawa, a wannan halin da yake ciki duk da cewa ba wanda yasan gawan fari amma wallahi shi bana tunanin zai wayi gari da rai, duk wanda bai san meke faruwa bama zaiyi tunanin cewa ko yana dauke da wani cuta ne amma wallahi al-hak'i ne kawai ke bin sa. Any where lets back to our normal business, ni kuwa ko a kwalar riga ta balle naji tausayin d'an dake cikin cikin ta sai kace ba ita ta haife ni ba.
Shovel na dauko na shure ta da kafa ta fad'i kasa na d'aga shovel d'in zan kwad'a mata ta saki kara iya karfin ta hakan yasa ali, hamza
da dauda shigowa cikin gidan a guje suka bankad'e ni
gefe nayi tangal-tangal kamar zan fad'i ali ya hauni da masifa “mahaukacin ina ne kai? Wannan ba mahaifiyar ka
bace Dan uban ka? Ko baka san da ciki a jikin ta bane kayi mata duka haka?" kafin na ankara naji saukan mari on my left cheek tas! Wallahi har sai dana ga star-stars, d'agowa nayi naga hamza ne tsaye a kai na kafin nayi yunk'urin tashi ya kai min a wonderful punch a fuska ta wanda yasa baki da hanci na suka
fashe.
Dama hamza ko ransa ba a 6ace yake ba yana cracking sosai during speaking balle a yanzu dana ga ya harzuka sosai zagin ma ya kasa yimin sai bugun da yake ta kai min any how. Dukkanin su
abokai na ne and also my age mate sai dai yadda nake jin tsoron su bana
tsoron wani mahaluki a duniya ban san dalili ba, a cikin su hamza ne kad'ai abokin shaye-shaye na amma ali da dauda basu ta6a shan koda tramol ba balle other drugs masu gusar da hankali.
With hamza's cracky voice yace “kai dan
uwar ka wannan ba uwar ka bace? Wani irin
kwaya ka sha yau?" ali da dauda suna can wurin
mamata data ke rera kuka suna bata hakuri daga karshe suka tattara ta izuwa dak'i. Duk wannan chakwakiyar da muke yi ba wanda ya shigo haka zalika ba matar data fito a cikin gidan. Kamani su kayi suka min d'aurin sweet wato sama d'auri k'asa d'auri da igiyan shany'a sannan su kayi waje dani.
Garden suka kai ni inda babu wanda zaiji sautin kuka na balle ya kawo min agaji. As always kamar yadda nasan dauda da hamza basa rabuwa da bulalan cable mai baki goma a jikin su, with my big surprise gani nayi sun d'aga riga gami ciro bulalan cabels d'in a kunkumin su, kowa yana rik'e da nasa. Hamza da crackcy voice nasa yace “yau zaka ci uban ka, in
shaye-shaye ne zaka nuna min ne? yaushe Ka fara shan kwaya ne harda zaka je ka sha wani drugs wanda ko gajiya bazai iya cire min ba zaka zo ka yiwa mamar ka duka?" ihu
nake yi tsakani da Allah ina basu hak'uri can naga ali ya zame jikin sa ya bar wurin ashe dai shima bulalan yaje tsinkowa, kawai ganin sa nayi ya fito da santalelen bulalan k'aya yana zuge gany'any'akin dake jikin bulalan. Ai kuwa volume na ihun nawa ya dad'u kamar wanda yaga mala'ikan mutuwa saboda yadda naga sun had'e rai suna wani zazzaro min na mujiya nasan dakuwa zanyi na fitar hankali wanda idan aka kaini asibiti sai likitoci sun tambaye ni da damisa nayi fad'a koda zaki.
Without noticing of anything naji sauk'an duka tun ina ihu har murya na ya dashe sai sautin saukan bulalai kawai ke tashi a wurin, sai da nayi laushi sosai
sannan suka kyale ni, nafi 2 hours ban san a ina nake ba farkawa kawai nayi na ganni kwance a kan gadon asibiti da drip a hannu na wai ashe har sun kawoni gida mahaifina na yayi ta masifa daga karshe ya kirawo y'an Qato da gora a kayi gaba dasu a kan cewa sai time d'in dana farka zasu bada bailing. wallahi na daku a wannan ranan jiki na ya farfashe sosai ko ta ina kwarzanin bulalan k'ayan ali ne sai kuma fashewan da jiki na yayi wannan kuma na bulalan cabel nasu hamza ne.
*~*~*~*~*~*
The following day, 8㏂ mamata ce da kanta taje tayi bailing d'in su hamza daga office na y'an qato da gora suka dawo gida. Ni kuwa bayan likita yazo ya dubani yayi prescribing min wasu medicines d'in da ya aika wata nurse ta d'ebo masa a dispensary sannan ya had'a mana da takaddar sallamar mu tare da yiwa baba na gargad'in cewa kada a sake bari na, na sha kwaya saboda kwayoyin da nake sha sunfi karfin jini na baba na yace “toh zamu kiyaye insha Allahu doctor". bayan mun dawo gida kannena aisha da fatima sun dawo daga tallan awara baban mu yace “ke aisha?" “na'am baba" ta amsa mai “dauko mana tabarma da sauri" bayan ta dauk'o ya umarce ta data shimfid'a min tabarman. Bararrajewa nayi a kan tabarman, baban mu ya shiga kwalawa mamar mu kira “daso?! Daso!?, wai baza ki fito bane?" “Gani nan zuwa" ta fito tana mai cizon le6e da turo cikin ta “yanzu ke maryam ashe baki da mutunci? Baki da hankali? D'an nawa tilo kika zuba ido abokan sa su kayi mai dukan tsiya eyyeh?" “Haba malam? Kai kenan baza ka daina d'aurewa karya gindi ba? yaro yana neman halaka ni y'an albarka suka kwace ni a hannun sa da kyar amma kake wannan furucin?" Ta kare maganar cikin sautin kuka, haushin ta kawai na fara ji take na fara kwarara mata ashar baba na yana ji amma haka ya kyale ni na rinka zagin mahaifiya ta wacce a yanzu ita take kula dani day and night duk da cewa abubuwan da nayi mata a rayuwa are unforgettable and unforgivable ne amma a haka take bani kulawa na musamman, ban ta6a sanin tana sona ba sai dana fad'a cikin wannan bala'in mai tsanani, tunda mahaifiya ta ta haife ni ban ta6a sata farin ciki ba kullum sai nayi mata abunda za tayi kuka amma bata ta6a bud'e bakin ta tace min muh'd Allah ya wadai da kai ba. Musa, Aliyu wallahi na zalinci kaina, ku duba kuga yadda na dawo? Duk wanda ya kalle ni sau d'aya baya marmarin ya sake kallo na amma ga uwata nan wacce na raina wacce na tsana ba tare da tamin komai ba ita take caring d'ina. Nayi kashi, fitsari ta wanke, nayi amai ta goge, idan kayana sunyi daud'a ta wanke min su ta kuma yimin wanka, sai kuma ya fashe da kuka mai tsuma zuciya abun tausayi da shi. Yana shesshek'a yace “yanzu dare yayi musa, quarter to 10㏘ ya kamata kuje gida ku huta zuwa gobe insha Allahu sai mu daura daga inda muka tsaya, hawaye ne kawai ke forming on our both left and right cheecks nida aliyu nace “Allah ya kaimu da rai da kuma lafiya, sai da safe" yace ameen Allah ya nuna mana, ko uffan aliyu ya kasa cewa sai hawayen da yake ta zubarwa muka fice daga dak'in. Mahaifiyar sa ce zaune a kofar dak'in bisa tabarma muna wiping off our tears with hanky nace “toh mama mu zamu wuce sai da safe" “toh musa ku huta gajiya ko? mun gode! Mun gode!! Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci" da kyar aliyu ya iya bud'e baki yace “ameen" “aliyu ka gaida min maman ku sosai da gajiya and you also musa" da “toh" muka amsa mata sannan muka fice...




😊мr. мεισdγ🍉




[5/17, 15:33] Umar Dalha: *LITTAFI* HAQQI☠













✍🏾mr. melody💥














🌙april-2017













page3⃣&4⃣












*Dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatima-bintu👩‍👧*








Yau take sunday ban fita wurin aiki na ba kasantuwar ina hutu, bayan nayi wanka around 9㏂ na kira aliyu a waya not long enough sai gashi yazo muka wuce al-arfat
shopping complex muka d'anyi sayayyan drinks daga ciki akwai maltina, bitter lemon, exotic, fresh milk da sauran su, a k'alla dai munyi spending kud'i 1k sannan muka wuce gidan su muh'd. Kamar kullum yau ma mahaifiyar sace zaune a gefen sa da kanta take feeding d'in sa break fast da soyayyan doya mai kwai sai black tea. “yau Kune a gidan namu da safe haka?" “hmm eh wallahi mama, ina kwana?" Muka fad'a tare da aliyu yayin da muka durkushe har k'asa “lafiya qalau y'ay'an nan, ya su maman ku da sauran yaran?" “kowa lafiya qalau wallahi mama, ya mai jiki?" “toh ga mai jiki dai, sai addu'ah" “Allah sarki, Toh Allah ya bashi lafiya ya kuma sa kaffara ne" da “ameen" ta amsa mana sannan ta fice ta bamu wuri muka zauna gami da ajiye shopping d'in da muka yo masa a gefen sa. Kallon sa kawai na tsaya yi saboda naga kumburin nasa ya dad'u ba kamar na jiya ba, “sannu muh'd, Allah ya baka lafiya" abunda aliyu ya iya fad'a kenan “ameen aliyu, ina gajiya musa?" “ba gajiya wallahi, kana cin abinci muka katse
ka ko?" fake smile yayi “no karku damu dama i'm
platefull kawai dai ta matsa min dana ci ne that's all" ajiyar zuciya aliyu yayi sannan yace “Allah ya kyautata
karshen mu" mu duka muka ce “ameeen" daga nan dak'in ya dauk'i shiru na wasu y'an dak'ik'u kamar ba halittu a cikin sa duk munyi zugum, chan! aliyu ya nisa sannan yace “anya muh'd zaka iya cigaba da bamu labarin nan kuwa?" “why not?, insha Allahu zan iya don't bother yourself" "toh shikenan muna sauraron ka" na fad'i hakane yayin da nake gyara zama dan
sauraron labarin da kyau.
bayan na fara samun sauk'i daga dukan da su
hamza suka min na d'an fara fita waje dan shan iska, as you know already mahaifin mu jobless ne bashi da aikin fari balle na bak'i, yau shine wannan
gobe shine wancan da ky'ar yake iya samo mana na abinci balle y'an kud'ad'en da zamu biyawa
kawunan mu bukatu dasu, duk da rashin da muke fama da shi na talauci amma a haka idan maitana ya tashi wato kwad'ayin shaye-shaye na idan ya motsa tisa shi nake a gaba har sai ya bani kud'i, wani lokacin ya bani 500 wani lokaci kuma 200 saboda ni kad'ai ne namiji babba a gidan mu shi yasa bana tambayan abu na rasa kamar yadda nima bana tambayar abunda nasan yafi karfin gidan mu. Ta sanadiyar wannan gatan da yake nuna min ne yasa na 6aci dan har yau ban iya wani aikin hannu ba infact ban ta6a yin wata sana'a ba kullum mahaifina ne ke bani kudi, shi kuwa idan na tambaye shi kud'in bani kawai yake yi baya tambayata me zanyi dasu ni kuwa sai naje can ghetto na kashe mana kud'in tas! a kan kayan maye tare da abokai na, na banza.
Wata rana mahaifin mu ya dawo daga gona, gonar
ma ba tasa bane daukan sa haya aka yi wato
barema, ko gida ban kyale sa ya shiga ba na tare
shi a bakin kofar gidan ba tare dana kar6i icen da ya d'auko ba balle nace masa sannu da zuwa. Kai
tsaye nace “baba bani da kud'i fah kuma ina jin
yunwa" “toh baka ci abinci bane ko basu girka bane?"
fuska na 6ata “ni in za'a bani a bani ba wai a tisa ni a gaba da tambayoyi ba, in kuwa baza a bani bane let me know shine kawai ehe!" sai daya d'an 6ata lokaci yana kallo na finally ya d'an karkace ya zaro 1k yace “toh gashi kaje ka kawo min 800 yanzu" kar6an kud'in kawai nayi ba tare da nayi godiya a gare shi ba sai ma y'an kumbure-kumburen dana keyi, reason nayin hakan kuwa shine 200 ya min kad'an. Ghetto na wuce wallahi sai dana ga bayan 200 d'in nan a kan kayan maye sannan na dawo gida.
Rannan mahaifiya ta tana toya awara wa kanne na a kitchen suna kaiwa godiya private school na diro mata ba sallama shiru tayi min gudan kada tayi magana nayi mata wani abun, matsami na
dauk'a na kwashi awara a cikin man tuyan na zuba a plate sannan na barbad'a yaji a kai. Duk abubuwan dana keyi bina kawai take da ido “wai ya da kallo hakane? Ko sai na bad'e idanun da barkono ne sannan zaki daina kallo na?" nayi maganan ina mai zare mata ido kai kace da y'ata nake maganar bada MAHAIFIYA TA ba. “yi hakuri ka jeka, babu komai ai duniya ce" doguwar tsaki naja sannan nace “lahira ce ba duniya ba iskanci kawai" ina kaiwa nan na shige cikin dakin ta na zube a kan single couch nata na d'aura plate na awaran bisa cinya ta sannan na hau awaran da chi like there's no tomorrow. Bayan na cinye awaran sai kuma naji kwad'ayin shaye-shaye na ya motsa and my pocket was dried nan fa na shiga chaje mata dak'i da kwanuka amma ban samu koda kwandala d'aya ba, zuciya a dak'ule zan fita kenan sai kuma nayi step backward kasantuwar mahaifiyar tawa uwar adashe ce sai na karasa kan gadon ta na d'aga pillow, wani jaka na gani irin wanda ake daurawa a k'ugu mai d'an girma haka, nan fa zuciya ta tayi haske ban tsaya wata-wata ba na bud'e jakan, dubu-dubu, dari biyar-biyar sai y'an dari bib-biyu na gani a ciki wanda ni kaina ban san ko nawa bane, tattara su nayi kaf! Zan fita dasu kenan

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login