Showing 3001 words to 6000 words out of 8023 words
Chapter 2 - HAQQI COMPLETE BOOK BY Princess Aysha Muhammad (Humaira) .txt
sai kuma naji tausayin ta ya kamani “yanzu idan na tafi da kud'ad'en nan ai zata iya rasa rayuwar
ta ko?" Tambayar da na yiwa kaina kenan, take imani ya ziyarci ruhi na, 200 kachal! na dauka a cikin kud'in na mayar mata da sauran cikin jakan na tura shi karkashin pillow'n kamar yadda yake as before wanda baza tayi tunanin wani ya ta6a mata kud'i ba.
Ghetto na wuce nayi ta shaye-shaye wanda har sai da zama ya gagara tsayuwa ta gagara, a ghetton ma na kwana tsabakin yadda na shayu na gama ficewa a hayyaci na gaba d'aya.
Hmm muh'd yayi murmushin takaici sannan yace “wannan fah ina
baku labarin aika-aikan dana keyi a cikin gida ne
dan wallahi hatsabibanci na ya wuce nan." Wannan karon ni ko aliyu ba wanda yayi hawaye a cikin mu sai sauraron sa kawai da muke yi, aliyu yace “toh muna sauraron ka muh'd, ka bamu labarin kato6aran
daka tafka a waje amma kafin nan ga wannan ka d'an sha" yayi maganar ne yayin da ya bud'e ledan drinks d'in da muka taho masa da shi ya d'auko maltinan gwan-gwani ya bud'e sannan ya mik'a masa, kad'an ya sha ya ajiye sauran.
Sanin kanku ne musa, a daa lokacin ina ji da kaina iskanci babu wanda bana yi, fannin mugunta da cin zali kuma kowa ya sallama min dan ba'a barni a baya ba. Wata rana da yamma muna zaune chamber ni, ali, hamza, dauda, abdullahi da kuma yusuf muna hira sai ga hassan mamar sa ta aike sa shagon abbo siyan flower, yazo wucewa kenan na kira sa “kai hassan zo nan" ya waiwayo ya kalle ni ba tare da yana zuwa ba, “wai baza ka zo bane?" na fad'a a tsawace still yak'i zuwa na tashi a fusace nayi kansa “kai dan uwarka ba kiran ka nake yi ba?" kuka ciki-ciki ya fara yi na zabga masa tafi yasa ihu “dan uwarka kayi kukan da tushe, in uban ka ya kira mu bama zuwa ne?" Da wannan na kyale shi yayi kwana abin sa, sai da yayi nisa kad'an yayi min dak'uwa yana cewa “kaci uwar shege tsinanne munafiki mugu azzalimi kawai" “ni ka zaga?" na fad'a da d'an ihu gami da pointing na kaina “eh kai d'in mugu kawai, kuma wallahi Allah ya isa na" “ai kuwa yaro ka zama nama dan wallahi idan na kama ka sai naci uwar ka" a haka fa na hana yaro zuwa aike, da isar sa gida bai jima ba sai ga mamar sa ta fito dama bata da hakuri idan ka ta6a mata y'ay'a, daru mu kayi da ita sosai finally abun ya bani haushi nace da ita “sai dai in bazai na fita waje ba, amma wallahi muddin na rik'e shi sai naci uwar sa" “au! Rashin kunyar taka har ya kai kace zaki ci uwar d'ana? Lallai yaron nan mahaukaci ne kai" Da kyar su hamza suka bata hakuri ta amince, dan cewa tayi sai ta kira min police su tafi dani, duk da cewa ina tsoron zuwa bayan canter amma sam! ban nuna mata a fili ba sai dad'a kurari nake.
Haka dai rayuwa ya cigaba da tafiya kullum cikin rikici nake, na daki d'an wannan na daki d'an wancan har y'an unguwa suka kai report wa babana cewa na fita hanyar y'ay'an su ko kuma su dauk'i matakin daya dace, ni dai bana kwa6uwa dan kuwa sai dai ayi ta min surutu amma duk a banza na riga na zama fitinanne na kin karewa idan naje nayo shaye-shaye na dawo gida duk wanda na samu mahaifiya ta ko kanne na sai na jibge su iya son raina baban mu baya cewa komai sai dai idan su hamza ne suka min duka a bisa dukan mamata ko kanne na da nayi. Ina mai tabbatar muku cewa mahaidiya ta, ta kamu da ciwon hawan jini nine ta sanadiya ta. A nan ya fashe mana da kuka yana zubar da hawaye zafafa, in between crying yace “dan Allah aliyu ka kira min *MAHAIFIYA TA* na sake neman gafarar ta" wallahi da wannan furucin nasa ya karya min zuciya ban san lokacin da hawaye suka fara rolling on my both cheeks ba. Kamar yadda ya bukaci aliyu daya kira mai mamar sa not long enough suka shigo tare gaba d'aya hankalin ta ya gama tashi a zaton ta jikin nasa ne ya tashi, a gaban ta muh'd ya zube on his knee gami da duk'ar da kansa k'asa yace “dan Allah dan annabi mama ki yafe min, ki gafarce ni ba dan hali na ba, ban kyautata wa kaina ba ko kad'an, wallahi kaicho na!!" ya kare maganar da kuka mai tsuma zuciya a hankali ya sulale k'asa ya kama kafafun ta yana neman tuba sai kukan da yake yi mai sauti.
😊мr. мεισdγ🍉
[5/17, 15:33] Umar Dalha: *LITTAFI* HAQQI☠
✍🏾mr. melody💥
🌙april-2017
Page5⃣&6⃣
*dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatimah-bintu👩👧*
Tausayin sa ya dad'a lullu6e mata zuciya bata ma san lokacin data fara zubda hawaye ba.
Duk'ar da kaina nayi k'asa wasu zafafan hawaye nake tsiyayarwa na d'an ta6a aliyu nufi na ya tashi mu tafi amma sai ya gyad'a min kai alamun a'a ba yanzu ba, ni kuwa zuciya ta baza ta iya jure ganin muh'd da mahaifiyar suna kuka ba, hakan yasa na tashi zan fita aliyu ya rik'o min hannu ba yadda na iya dole tasa na zauna.
“Muh'd na yafe maka duniya da lakhira, Allah ya baka lafiya ya kuma yima albarka" tayi maganar cikin kuka gami da d'ago sa daga durkushen da yake ta rungume shi shima yayi hugging nata back yana kuka tana bug-buga bayan sa yana cewa “nagode mama Allah ya saka miki da gidan Aljannah, lallai kin cika uwa ta gari" sun d'au lokaci mai tsawo a rungume da juna finally tayi breaking hug d'in a hankali. “mama?" Yayi exclaiming d'in sunan ta da sark'ak'iyar muryar sa “na'am muh'd?" “mama Ina su aisha, fatima da aunty?" Hawayen dake rolling on her both cheeks ne tasa hannu tayi wiping off sannan tace “sun tafi talla, me kake so suyi ma?" “Ba abunda nake so suyi min face gafara, domin na zalince su a rayuwa" ya kare maganar da kuka. Lallai rayuwar muhammad tana k'unshe da darussa bila adadin, wanda mu matasa ya kamata muyi duba ga yadda rayuwar muhammad take a daa can baya, shan kwaya bashi da wani fa'ida kuma ba abunda baya haifarwa, yanzu wani abu da yake damun mu, mu matasa shine wai idan kai baka shan drugs, cigarrete, wiwi, oris da shi-sha (pot) muddin dai baka shan d'aya daga cikin wad'annan haramtattun ababen wai kai baka cika gaye ba, a'uzubillahi, toh kada Allah yasa na cika gayen in dai sai nayi shaye-shaye ne. Wato wani abu d'aya da har yanzu mutane basu fahimta ba shine, turawa sun k'irk'iro shi-sha ne ba dan komai ba sai dan su lalata mana tarbiya wanda iyayen mu suka 6ata shekara da shekaru suna bamu ita. Da farko abunda za muyi la'akari da shi a nan shine: shi-sha da oris duk kamshi d'aya ne dasu sai dai shi oris kamar taba yake a nannad'e, karfa ku manta shi-sha tsani ne wanda mutum zai bi a sauwak'e ya fara shan taba wiwi da sauran su ba tare daya sani ba, kullum ka saba shan shi-sha kana sayan flavor 350 ranar da baka da kud'in sayan flavor'n kuma kana kwad'ayin shan shi-sha cewa za kayi “ba gara naje na saya oris naira goma ba na sha tunda duk kamshi d'aya ne dasu" toh daga ranar da tunanin haka ya fad'owa mutum a rai wallahi tasa ta kare domin shaye-shaye zai fara gadan-gadan kuma dan Allah dear readers ku duba ku gani 80% cikin 100% na mashayan yanzu matasa ne, 70% cikin 100% kuma daga shi-sha suka fara shaye-shaye har suka fara shan wasu kwayoyin, dama shi-sha foundation ne na koyan shaye-shaye wanda turawa suka kafa dan lalata tarbiyan y'ay'an musulmai, yanzu ma abun harta 6aci akwai turare mai kamshin flavor'n shi-sha wai (straw-berry) har mutane suna saya su shafa a jikin su dan rashin hankali, yo! Baka sha amma idan ka had'u da wanda bai san cewa turare bane shikenan kimar ka ta zube a idanun sa, kai bada girki ba amma da warin hayak'i. Allah ka kare mana imanin mu ameen ka kuma tsare mu da muggan abokai domin masu iya magana suna cewa zama da mad'aukin kanwa shike kawo farin kai. Masu sha Allah ya shirye su mu kuma da bama sha Allah ya dad'a tsare mu ameen thummah ameen.
Da kyar na samu nayi convicing na aliyu ya tashi muka tafi gida da sharad'in cewa zamu dawo by 8pm dan jin karshen labarin kasantuwar yau babu zuwa majalis. Haka kuwa aka yi 8pm bayan munci abinci muka wuce gidan. Kai tsaye muka zarce dak'in nasa wannan karon k'anwar sa fatima ce ke gefen sa a zaune tana taya shi hira. Cikin girmamawa ta gaida mu, muka amsa sannan ta tashi ta fice muka zauna.
Da fara'a kwance a fuskar sa yace “Sannun ku da zuwa" “yauwa, ya kaji da jikin naka kuma?" a cewar aliyu “hmmm" kawai yayi ba tare da amsa ba “amma muh'd baza ku koma asibitin nan ba kuwa?" Na fad'i hakan ne yayin da nake kare mai kallo dan wallahi babu alamun sauki a tattare da shi saima abunda ya karu. “eh toh abunda yake kaimu asibitin dama magungunan cin abinci ne da kuma irin abincin da doctor yace ina ciki" “haa'ah, kamar ya? Dama basa duba jikin naka ne duk zuwan ku asibitin?" aliyu yayi maganar da mamaki “eh dama tun kafin jikin nawa yayi tsanani likitan ya shaidawa baban mu cewa ciwo na bana asibiti bane kamar yadda binciken su ya nuna bana d'auke da wata cuta daya sa nake wannan kumburin" ajiyar zuciya nayi sannan nace “kun gwada na gargajiya ne?" Ruwan dake gefen sa a cup ne ya d'aga ya d'an kur6a kad'an ya ajiye ya nisa sannan yace “har gombe an kaini amma bamu dace ba, nifa ina ji a jiki na bazan tashi ba" da sauri nace “subhanallahi, bai kamata ka furta wannan kalmar ba, sai kace ba musulmi ba? ka tuna fa cewa ba abunda ya gagari Allah, Allah gagarau ne saboda haka ka cigaba da addu'a muma cikin yima addu'ar muke a kullum kuma insha Allahu zaka samu lafiya" “toh Allah yasa, nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci" nida abokina aliyu muka masa da ameen. “Toh aliyu ne dama ya matsa min akan lallai-lallai muzo ka karasa mana labarin, zaiyu ka karasa mana yau ko kuwa mu hakura sai gobe?" Lumshe idanun sa yayi a hankali kamar mai jin baci yace "gaskya da zaku hakura sai goben da yafi, saboda ina jin kaina yana sarawa ga kuma baccin da nake ji tun dana gabatar da sallah'n magharib" “kash! Subhanallahi Allah ya yaye, ka sha magani kuwa?" aliyu ya tambaye shi “a'a, ban sha ba amma da zarar na samu nayi bacci zan tashi babu ciwon kan" “toh Allah ya baka lafiya, mu zamu wuce gida sai goben in Allah ya kaimu" na fad'i hakanne yayin da muke mik'ewa tare da aliyu “Allah ya kaimu da rai da kuma lafiya, nagode! Nagode!! Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci" da ameen thummah ameen muka amsa masa sannan muka fice bayan munyi sallama da mahajfiyar sa.
😊mr. melody🍉
[5/17, 15:33] Umar Dalha: *LITTAFI* ☠HAQQI☠
✍🏾mr. melody💥
🌙April-2017
Page7⃣&8⃣
*dedicated to my beloved sisters ummi-aysha & fatimah-bintu👩👧*
Yau take monday muna da general exam na english paper 1-3 Tun 9:30am sai 4:30pm muka kammala. Bayan mun dawo gida so exhausted tare muka ci abinci da aliyu bayan nan ya wuce gida yin wanka nima na fad'a a family bathroom na gidan mu dan watsa ruwa.
30 minutes after sai ga shi ya taho sanye cikin kananan kaya white t-shirt ne mai style da y'ay'an beads da ¾ amry trouser ni kuwa jallabiyar makkah na zurmud'a sannan muka wuce gidan su muh'd dan jin karashin labarin nan nasa. Kai tsaye muka fad'a cikin gidan da sallamar mu matan gidan suka amsa muka gaisa dasu sama-sama sannan muka shige cikin dak'in a inda muka tarar da mamar sa tana bashi abinci a baki.
“Ina yini mama?" muka fad'a tare da aliyu yayin da muke kokarin zuwa kasa “lafiya qalau, sannun ku da zuwa" “yauwa mama, ya mai jikin?" Ajiyar zuciya tayi gami da cewa “wallahi jikin nasa ba wani alamun sauki, jiya iyau koma ince sai dad'uwa yake" na d'ago idanu na, na zuba su kan muh'd wanda tun shigowar mu ya jingine a jikin bango idanun sa a lumshe suke sunyi kanana mini-mini dasu tsabakin kumburin da yayi har za kayi tunanin cewa idanun nasa basa bud'ewa ne. “Allah ya sauwake" cewar aliyu “ameen ya Allah, throughout yau baku zo wurin d'an uwan naku ba sai yanzu, lafiya dai ko?" Murmushin yak'e kawai nayi nace “munje zana jarabawa ne wallahi shi yasa bamu zo ba" “toh Allah ya baku sa'a yasa ku fito da flying colour" da ameen muka bata amsa sannan ta fice. Duk muka yi shiru ba wanda yace koda uffan aliyu ya duk'ar da kansa k'asa kamar me nazarin wani abu, kwallafa idanu na nayi a kan muh'd ina kallon shi cike da tausayawa shi kuwa har yanzu idanun sa a lumshe suke wasu siraran hawaye na gani sun gangaro masa a hankali ya fara yin kuka mara sauti tausayin sa daya min yawa yasa na kasa appeasing d'in sa kamar yadda aliyu ma ya kasa. Yayi kuka mai isar sa ba wanda ya lallashe sa a cikin mu saboda kukan nadama ya keyi bai kamata mu lallashe sa ba, kukan da yayi zai sa ya d'anji sauqi koda kad'an ne a cikin zuciyar sa. Cikin rawar murya yace “sannun ku da zuwa" aliyu ne ya amsa mai da “yauwa" shi d'in ma cikin shesshek'an kuka ne, ya d'aura da cewa “sannu muh'd, Allah yaye ma wannan musiba" kai yake kad'awa a hankali ga kuma hawayen da suke rolling on his cheek “musa baza kayi min magana bane?" Cike da tausayawa na matsa kusa da shi nasa hannu na share masa hawayen da suke sauka kan kumatun sa nace “yi hakuri, sannu kaji? Allah ya baka lafiya ya kuma sa kaffara ne" kukan da nake matsewa ne ya kwace min, gefe na koma na zauna ina matsar kwalla, sai da duk muka saita kawunan mu sannan muh'd ya sauke sassanyar ajiyar zuciya ya kalle ni ya kalli aliyu yace “mu d'aura daga inda muka tsaya jiya ko?" da sauri aliyu ya gyada masa kai gami da cewa “eh".
Muh'd ya sauke sassanyar ajiyar zuciya a karo na biyu gami da gyara jinginuwan sa a jikin bangon ya fara da cewa “as usually dama bani da wani aiki sai dai naje ghetto nayi shaye-shaye sai nayi d'ub nake shigowa cikin unguwa duk yaron dana had'u da shi dukan sa nake tamkar aiko ni aka yi daga sama jama'ar unguwa su kayi ta min magana amma kota kawunan su bana bi sai ma ashar d'in da nake ta faman kwararo musu, baban su usaini ne yazo ya sameni ina langa6e a jikin bango sai wani lumshe ido nake saboda yadda na shawu over, yazo ya sameni ne akan na lakad'awa inusa duka kanin usaini har sai da na fasa masa baki “kai muh'du yanzu abunda kayi ya dace kenan?" Cikin yanayi na shawuwa na kalle shi da ido d'aya nace “daga yau kada ka sake kira na da muh'du, kana ji ko?" Duk da cewa a shaye nake amma da sane na nake fad'in hakan, “yo! Ai sai kaje ka fad'awa uban ka wanda ya rad'a ma sunan kace baka so, ina mai gargad'an ka daka fita a idona na rufe dan wallahi zan sa a daure min kai a garin nan" kallo tara saura quarter nayi masa sannan na tsartar da yawu nace “sunana john daga yau in kuma ka sake kira na da muh'du zaka gane cewa shayi ruwa ne, dan wallahi sai y'ay'an ka sun kasa shaida ka balle matar ka" ya tafa hannun sa yace “innalillahi wa'innaillaihir raju'un!, yanzu kai haukan naka har ya kai kace kai sunan ka john? sunan kafiri?" Tsaki naja na bar wurin sai wani layi nake sai kace mahaukacin jaki, shi kuwa bina kawai yayi da ido baki a wangale. Haka dai a dolen-dole na koma arne in ka kira ni da muh'd na kwararo ma ashar in kuwa john kace sai mu zauna lafiya. Wallahi har yau wasu da john suke kira na wasu kuma da shi suka sanni abun yana bani haushi matuk'a amma ba yadda na iya saboda *NI NAIWA KAINA*. A nan ya fashe mana da kuka yana cizon le6en sa dan takaici, in between crying yace “wallahi shaye-shaye ba abu bane ma kyau, da ban fara shaye-shaye ba, da duk ban tafka rashin hankali dana tafka a duk tsawon rayuwata ba. Nothing is hurting me more and more! like the way that i treated my only mumy harsly like this" kukan nasa ya fad'ad'a Ya sake cewa “peoples are saying what you sow is what you reap either good or bad, yes of course they are right