Showing 36001 words to 36944 words out of 36944 words

Chapter 13 - Karayar Arziki Complele Book Writing by Billyn Abdull .txt

22 Feb 2025

5338

Dan haka tayi k'ok'arin kwace kanta ta gudu amma saiya ruk'ota da k'yau.
Humm guduwa kikeson yine? To aiia tare Muke da babban bak'o.
Da sauri tad'ago ta kallesa, yaya bak'ofa?.
Kansa yad'aga mata, har yanzu idonsa akanta.
To amma miyasa Baka kirani kafad'aminba? Da saina masa binci na Musamman, tunda kace abban bak'one.
Hakane my Asmy yazeed babban bak'one agaremu. Amma kiyi hak'uri Nima a ahanya na tsintoshi.
Ayya to babu damuwa. Amma yanacin garau-garau?.
Gira yad'aga mata, tareda k'ara rungumeta ajikinsa ya ce, "aibakinkine garau-garau d'in. mizai hana yaci sarauniyata."
Dad'ine yake ratsa zuciyar Asma'u aduk lokacin dataji ya Umar yasauya mata wani suna daban, musamman sarauniyata dayake cemata.
Jin tayi luf ajikinsa yasakashi d'agota. Yadai Husanata? Ko kina buk'atar d'umin mijinkine?.
Da Sauri ta d'an tureshi tafice daga d'akin.
Shima bayanta yabi yana dariya k'asa-k'asa.
Afalo ya isketa suna gaisawa da yazeed. Sosai yazeed yaba da tarbiyyar Asma'u.
Ya Umar na fitowa Asma'u tana mik'ewa tafita. Akusadashi ya Umar ya zauna. Yazeed ya kalleshi daikuma ya bushe da dariya.
Harararsa ya Umar yayi. Mikuma yabaka dariya kaikuma?.
Yazeed bai iya maganaba sai dariya, daya kalli ya Umar saiya sake tuntsurewa da dariya. Ganin haka ya Umar Yakuma harararsa. Kai malam yafa isheka, wai miye matsalarkane?.
Cikin dariya yazeed yakunna waya yayma ya Umar hoto.
Da Sauri ya Umar ya warce wayar danson ganin miya faru?.
Idanu yazaro waje, shima saiya fara dariyar. Bakinsa yagani duk jambaki. Da Alama kiss d'in dayayma Asma'u ne yakwaso jambakin.
Sunacikin dariya Asma'u tashigo. Itama suna had'a ido da ya Umar tayi murmushi ta ajiye tiren hannunta. Tun d'azun tana ganin jambakin amma tak'i Sanar masa.
Saving d'insu tayi. Had'd'd'iyar jallop d'in shinkaface wadda taji kayan lambu, dukda babu nama aciki bare kifi sai zabga k'amshi takeyi. Tunkan sufaraci yawunsu ya tsinke suduka. Ta tsiyaya zo6onta dayaji kayan k'amshi a kofuna guda biyu sannan tamik'e. Bismillanku, tafad'a tana mik'ewa.
Tunda suka faracin abinci babu mai iya yima d'an uwansa magana. Ta kurma kawai akeyi, babu Baka sai kunne. Sosai sukaci abincinnan, Dan abincin yayima yazeed dad'i. Shi matsalar dayake fuskanta kenan agidansa, matarsa bata iya girkiba. Ko indome tadafa masa saidai yaci kawai da hak'uri. Amma badan dad'iba kam.
Bayan sunci sunyi dam, suka kora da sassanyan zo6on. Ayanzu kam yazeed yakasa daurewa saida yayi magana.
Kai abokina kana kwasar gara wlhy. Yoni Ina samun haka mizai dameni.


Kallonsa ya Umar yayi yana murmushi jin dad'in an yabama Asma'unsa. Haba abokina Kanada matafa? Yakake fad'ar irin wannan maganar.
Hummm abokina kenan aii kasan ko'a Matan wata tafi wata.
Hakane. ALLAH yasa mudace.
Ameen yazeed yafad'a yana k'ara tsiyaya zo6on akofi.


Bayan sun kammala Asma'u tafito ta kwashe komai. Jok d'in zo6on kawai tabar musu. Daga nan suka cigaba da hira har zuwa magriba.
Sun tattauna abubuwa da dama, ciki harda kud'i da yazeed yabama ya Umar har na 10millions yayi gyaran shagonsa.
A take anan kuma yay masa transfer a Account d'insa.
Yanda kasan gumaka haka ya Umar da Asma'u suka koma awajen. Ya Umar yarungume yazeed yana masa godiya.
A'a Umar babu godiya a tsakaninmu, kayana nakane. Hakama kayanka nawane. ALLAH ne yahad'amu, to dan haka saimu gode masa.
Hakane abokina amma kaid'in nadabanne acikin al'umma. ALLAH ya saukar da farinciki da alkairi arayuwarka da zuriyarka. Yanda ka k'yautata mana kaima ALLAH ya k'autata maka damafiyin haka.
Ameen Umar ngd sosai da addu'arka.
Yanzu abinda yakamata gobe idan ALLAH yakaimu kashirya zamuje wani waje akan kayanka da custom suka rik'e.
Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke. Yazeed wlhy dama mun hak'ura kawai. Duk hanyar danake tunanin kayannan zasu fita nabi, amma kowa saiyace babu yanda zaiyi.
Murmushi yazeed yayi, yadafa kafad'ar ya Umar, karka damu Umar, awannan karon insha ALLAH zasu fito. Aii komai na k'asarmu hanyace. Kaidai karka fidda rai da rahamar ALLAH.
Shikenan yazeed ALLAH yakaimu goben. Ngd ngd ngd.........
Katseshi yazeed yayi da sauri..... Nifa banason godiyarnan. Idan kanayi sainaga tamkar baka d'aukeni d'an uwaba.
Tom kayi hak'uri na daina.
Daganan yazeed yamik'e, rafar 'yan d'ari biyar yabama Asma'u wai tukuycin ciyar dashi daddad'an girki datayi.
Girgiza kanta tayi, idanunta ak'asa, a'a ya yazeed ngd basai kabani tukuyciba. Banmmasan zakuzo tareba da anmaka na musamman aii.
Kai aii wlhy wanna danacima na musamman ne. Ke dai kawai ALLAH yak'ara dank'on k'auna keda abokina. Ngd sosai..
Asaman kafet d'in ya ajiye suka fita..
Godiya sosai tamasa, da sak'on gaisuwa ga iyalinsa sannan takoma ciki, tana mamakin yazeed. Dama akwai irin wad'annan mutanen har yanzu adoron k'asa?.


A can kuwa ya Umar yarakashi har mota yana k'ara masa godiya da k'yak'yk'yawar addu'a shida zuriyar sa. Saida yaga yabar Layin sannan yashigo cikin gida.














*_(((S))........2017_*
*_Luv you all_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login