Showing 6001 words to 9000 words out of 10700 words

Chapter 3 - UWA KO YA Complete Document Book by FAREEDAH GURKU.txt

22 Feb 2025

1679

call me sir",
"Toh daga yau dashi zanna kiranka",
"No, nafison dear",
"Allah ko",
"Eh saboda in kasance kullum ina zuciyarki",
"Ai kullum kana zuciyata dear, sometimes inna tuno baza kadawo ba sai nan da shekara ďaya kwalla nakeyi",
"Kidaina min kuka *D* ,adu'a zaki min saboda in samu nasara a abinda nake nima",
Feenerh da musa kenan,soyayyar su abin sha'awa , in wasa yazo suna ýinsa sosai,in seriousness ne toh zasu dauke shi da mahimmaci sosai gashi suna kaunar juna kamar zasu cinye junar su ,
"Toh shikenan dear, allah yaba da sa'a ,yasa abinda ake nima asamu",
"Ameen *D*",
"Yawwa",
"Toh *D* inada afternoon classes yanzu ,zan kira zuwa anjima inna fito",
"Ok dear, love you",
"Love you too ,bye".
Feenerh tafito daga ďakinta zuwa ďakin iyayenta don ta gaishe su ,tayi musu sallama sanna tashiga,
"Ina kwana mommy",
"Lafiya kalau",
"Ina kwana daddy",
"Lafiya safiya",
"Kun tashi lafiya",
"Lafiya kalau",suka amsa gaba ďaya,
"Yawwa safiya,inada magana dake",
Zuciyar feenerh ya buga ,kar dai daddy ya changing mind ďinshi akan maganar auranta ne,kodai ya maso dashi kusa ne,toh in yayi hakan yazatayi tunda yanzu musa na america.
"Safiya ,yaushe zaku dawo makaranta",
Nan da nan da saukar da numfashi,
"Nan da two weeks daddy",
"Ok toh nawa ne school fees ďin",
"#45,000 ne",
"Toh zan baki jibi ki biya saboda kinga yau da gobe public holiday ne",
"Ok toh daddy",
"Toh shikenan zaki iya tafiya",
"Nagode,yawwa daddy happy independence sannan kuma happy anniversary for nasarawa at 20",
"Same to you dear",
Feenerh tafita tana murmushi.








*tnx for reading....*
*©Fareedah*.


*💟💟 UWA KO ÝA 💟💟*




*Written by:*
*FAREEDAH💚*




*Edited by :ANEELURV😍*






*Dedicated to my lovely mom😍*








*pg 31▶35*








Akwana atashi ba wuya,su feenerh na shirye shiryen komawa skul.
Feenerh zata shiga skul yau saboda zasu fara registration kuma tayi magana da khadija ta sanar da ita cewa ta sameta a skul.
*bayan awa biyu*
"Gaskiya khadija na gaji ,ga kuma rana",
"Toh ai feenerh waje ďaya ya rage amana signing ,kinga ai mun gama",
"Toh shikenan ,amma inaga muna gamawa mu wuce canteen kawai ,saboda yunwa nakeji",
"Okay".
Bayan sun gama sai suka wuce skul canteen ,
"Wat will u lyk to order",
Waiter ta tambeyesu.
"What is special today",feenerh ta faďi
"Local rice and stew",
"Okay ,two plates please",
"Okay ,ma'am wat would you lyk in your stew,beef or chicken",
"Chicken rather",
"Okay ma'am,coming ryt up",
Feenerh suka samu wajen zama ,an kawo abinci ,sukaci in silent bayan sun gama ,suka tashi don suje su biya bills ďin.
"How much ",feenerh ta tambayesu,
"That will be 1200",
"Okay",tasa hannu a jaka zata cire sai taji ance ,
"No problem,it's on us",
Tana juyowa saita ga samari ne guda biyu kuma da ganinsu students ne.
"Sannu ku fa ladies",
"Yawwa sannu",
"Don allah in baxaku damu ba,muna son magana daku",
"Badamuwa",
"Ko zaku iya fa ďa mana sunanku",
"Meyasa,saboda ni bantaba saninku ba ,so meyasa zan baku sunana",
"A'a ,kawai so muke mu zama friends ďinku",
"Ohh sorry ,amma mu matan aure ne kuma mazajenmu sun hana mu magana da samari",
"Haba,ya kike irin wannan maganar nafa saba ganinku a campus kuma nayi tambaya nasan baku da aure",
"Toh meyasa baka tamabayi messenger ďinka sunanmu ba",
"Saboda nafi son inji daga bakinku,kinsan ance *waka a bakin maishi ya fi da ďi*",
"Toh gaskiya kam,maishi bai da niyyar rerawa yanzu,kinga kawata mu wuce gida",
"Haba ýan mata ,lefin me mukayi ,suna fa kawai muka tambaya",
"Wai ku bakwaji ne ,tace maku aure ne damu ,why not ku facing studies ďinku ku daina neman matan aure",khadija tasa baki acikin zancen.
Samarin biyu suka basu hakuri sannan suka wuce,
"Ohni khadija mun gode ba'a waje suka taremu ba ,kinga yanzu da dad ya gansu",
"Eh fa don yacemin yana jiran mu a waje,unserious types waýenan yaran harda rannar registration",
"Eh mana,kinsan rannar ne aka fi taruwa sannan ranar ne kawai zasu iya magana da mata saboda bayan wannan ranar bara ma su gansu ba",
"Lallai fa kowa na lectures".
Suka fita waje ,suka sami ja'afar acikin mota ya ďan kwantar da sit ďin yana hutawa,
"Assalamu alaikum dad"feenerh tace yayin da ta bude kofar baya ta zauna,
"Wa alaikum salam dota,har kun gama kenan",
"Eh fa ,munyi sauri ko",
"Lallai kam",
Khadija ta zagaya ta bude kofar gaba ta shiga ta zauna,
"Keh hajiya ba gaisuwa ne",
"Ohh dad aina aza baka ma ganni ba",
"Shine da sharri haka",
"A'a nina isa",
"Kin ma fi haka,toh yakike",
"Lafiya kalau",
"I hope dai rana bai dameminki sosai ba dear",
Feenerh ta kallesu nan da nan kwalla ya taru mata a ido,saboda sun tuno mata da musa.
Ja'afar ya sauketa a gida sannan ya kai khadija daga nan suka wuce da hirarsu.
Feenerh ta shiga ,tafara jin hayaniyar mutane ,toh koh dai wani abune yafaru agidan ,bata ankara ba taji an rungumota ta baya ana cewa,
"Aunty feenerh kin dawo",
Ta juyo taga ashe ma cousin ďinta ne zuwaira,
"A'a zuwaira kune a garin yau",
"Eh aunty",
"Shiyasa naga anyi rana sosai yau",
"Haba dai aunty ,har da zolaya kuma",
"Tohh,yakike zuwee",
"Lafiya kalau",
"Tare da mamanki kukazo",
"Eh da aunty fati,da aunty ramat da sauran kannena",
"Wai lallai yau munada babban baki a gidanmu",
Feenerh ta karasa ta ďakin mamanta taga dukkan waýen da aka lissafo mata a zaune a ďakin,ta durkusa ta gaishesu,
"Feenerh har kun dawo" aunty larai ta tambayeta,
"Eh aunty",
"Toh ya makaranya ýan boko",aunty ramat tace,
"Lafiya kalau aunty ramu",feenerh ta kirata da lakabinta,
"Toh sannu ki da zuwa ,amaryan gobe",aunty fati tace,
"Bana son sharri aunty fatee",ta karasa ta zauna suka cigaba da hira suna dariya. Ashe bikin yarinyar yayan mamanta suka zo yi wato hadiza.
"Toh amma aunty larai ai bikin saura kwana goma sha hudu,yanaga kunzo da wuri",
"Mun zo da wuri ne saboda mutaya kanwar mu shirye shiryen bikinki",
"Kai aunty ,bikina kuma",
"Eh mana kobaki isa bane",
Feenerh tayi dariya,
"Aunty kenan to ai in kunji daidai ,bikina sai nan da shekara biyu",
"Eh mana ,mun sani mun zo mu fara tattaunawa ne kafin lokacin ,kinsan in muntafi bazamu dawo ba sai in bikinki yaxo".






*tnx for reading...*
*©Fareedah*.


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*




*written by:*
*FAREEDAH💚*








*Edited by :ANEELURV😍*








*Dedicated to my lovely mom😍*








*pg 36▶40*








Angama biki lafiya,kowa ya koma gida amma feenerh bata ma tambayi mamanta ya sukayi da aunty larai ba saboda bata ma kaunar jin maganar aurenta yanzu.
************************************
Karatu yaci gaba,anshiga tsakiyar semester so karatu sukeyi sosai saboda jarabawa ya kusan gabatowa.
Ja'afar kuma yasamu zuwa NYSC ďinsa a first batch sannan kuma an tura shi gari mai nisa har zuwa lagos.
Ranar da zai tafi kamar khadija zatayi kuka ranar,amma yabata hakuri sannan yace mata da yardar allah yana dawowa za'afara maganar aurensu.
Musa da feenerh kuwa soyayyar su tayi gaba domin yanzu kam suna video chatting ta skype so shiyasa kewarsa da takeyi yanzu ya ragu.
Yau weekend ,feenerh na gida tana hutawa a falo ,
"Feenerh?",
Mommy ta kirata.
"Na'am mommy",mommy ta karaso falon ta zauna,
"Feenerh inada magana dake",
"Toh amma mommy i hope ba abinda kuka tattauna da aunty larai bane"
"A'a",
"Okay inaji mommy",
"Magana ne akan auranki",
"Aurena kuma mommy ,amma kince min ba maganar da kukayi da aunty larai bane",
"Eh bashi bane,amma wannan ďinma is about you",
"Toh mommy",
"Feenerh,ni mamanki ne yakamata ace kina consulting ďina akan wasu abubuwa ,ana cewa a mom is her dota's best friend",
"Hakane mom, amma ai mommy duk abinda zanyi sai da saninki kuma bantaba boye miki wani abu ba",
"Feenerh ai bance kin boyemin wani abu ba,amma baki nimi advice ďina akan wasu abubuwa ba",
"Mommy wasu abubuwa kuma",
"Kamar yanda kika sanar da ni da daddynki cewa nan da shekara daya zaki fito da mijin aure amma gashi har rabin shekara shiru",
"Mommy ai lokacin baiyi ba",
"Nasani amma kamar ni mommynki baki fa ďamin sunanshi ba,ko daga ina yake kuma baki fa ďamin halayarsa ba,kobaki son insani ne ko kuma advice ďina ne bakya so",
"Allah sarki mommy ,wallahi ba haka bane",
"Toh yanene",
Feenerh tayi shiru,
"Gashi ko sunanshi ma bansani ba",
Mommy tachigaba da magana,
"Mommy sunanshi musa",
"Musa?",
"Eh mommy",
"Me sunan iyayenshi",
"Sunan babanshi abdullahi ,sunan mamanshi kuma fatima",
"Musa abdullahi",
"Eh".
Mommy tayi shiru tana nazari,anya shine kuwa amma toh za'a iya samun matsalar suna maybe bashi bane,
"Mommy wani abu ne yafaru",
"A'a bakomai ,toh wani aiki yakeyi ko ďan makarantane",
"Lab technician ne a makarantar mu",
"Toh meyasa har yanzu baixo yayi gaisuwa ba",
"Mommy baya gari ,yasamu scholarship yanzu haka yana New York don karasa masters ďinshi",
"Masters kuma feenerh",
"Eh mommy",
"Kice ya ďan manyanta kenan",
"Eh",
"Toh alhamdulillah ba waýenan kananan samarin kikasamu masu rashin kunya ba"
"Waýensu irin samari kuma mommy",
"Irin waýenda suke gaisuwa a tsaye sannan suke magana kamar masu sarki a aljihu",
Feenerh tayi dariya sannan yace,"mommy kenan",
"Toh feenerh shi musa yaushe zai dawo,i hope dai kin fa ďa mishi abinda daddy yace",
"Eh mommy na fa ďa mishi kuma yace ya yarda",
"Toh ya batun dawowarsa",
"Zai dawo nan bada da ďewa ba saboda yanzu dai kam watanni bakwai ya rage mai ya gama course ďinsa",
"Alhamdulillah ,nai masa murna allah kuma ya bashi sa'a " ,
"Ameen mommy",
Sukaci gaba da hirar su irin na *uwa da ýa*.
Bayan sallar isha,feenerh ta kira musa ta video chat na skype,yana ansawa fuskarsa ta fito a screen ďin,
"Hello *D*",
"Dear yakake",
"Lafiya",
"Ya karatun yau",
"Kalau kalau *D*",
"Koda naga fuskarka sai naji sanyi a zuciyata",
"Nima haka *D*,tun dazu nake tason inkira ki amma kin rigani",
"Toh kaima kasan in bankiraka ba bazan iya bacci ba",
"Same here *D*",
"Yau mukayi zancen ka da mommy",
"Tohhh ,i hope dai ba laifi nayi ba",
"A'a ,kawai hira mukayi kuma ta bukaci in bata labarinka shi kenan",
"Okay allah sarki,nima ai nayi laifi yakamata ace naje na gaishesu kafin na tafi",
"Bakomai dear,ai itama batace komai kawai cewa tayi allah sa albarka a karatunka",
"Ameen",
"Meye labari dear",
"Wallahi *D* munkusa zana jarabawar karshe,kinga ina gama zan dawo saboda a daura aurenmu",
"Allah ko dear",
"Da gaske kinga inata siyeyen kayan aure a nan",
"Da wuri haka dear",
"Wuri kuma *D* ,ai gara ayi komai da wuri banson in bata lokaci da yawa",
"Dear kenan,yawwa dama mommy tace tanason gaisawa da kai ,ko inje in kirata",
"Eh badamuwa",
Feenerh ta tafi ďakin mommy takirata ,suna shigowa taga blank screen,ashe ta manta batasa shi a charge ba har ya mutu.
"Tohhh mommy ,ya mutu",
"Badamuwa,sai wata rana".








*tnx for reading....*
*©Fareedah*.


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*




*written by:*
*FAREEDAH💚*




*Edited by:ANEELURV😍*






*Dedicated to my lovely mom😍*






*pg 41▶45*








Musa sun gama zana jarabawar su da yardar allah amma ance su jira nan da wata biyu saboda result ďinsu yafita kafin su koma gida.so zai jira saboda yanzu in yakoma gida bazai dawo ba sai in har sunyi aure da feenerh.
A 'bangaren feenerh kuma suna kan rubuta final paper ďinsu na aji biyu. Sun gama lafiya kalau kawai jiran dawowar musa takeyi koda dai ya fa ďa mata sai nan da wata biyu ,bataji da ďi ba amma ba yanda ta iya tunda ta iya jira har na shekara ďaya,na wata biyu ne bazata iya ba. Sai dai tayi tamai adu'a allah sa result yafito kuma yayi kyau.
Bayan sun gama jarabawar zasu fita su wuce gida sai khadija tace mata ta rakata kasuwa tanason ta duba wani abu.
"Wani abu kuma zaki siya khadija" feenerh ta tambayeta,
"Kawata dama wani zani ne na gani kuma yamin kyau shine nace ki rakani saboda ki gani ko zaiyi kyau da anko",
"Anko?,anko fa kikace khadija",
"Eh mana feenerh, kinsan ja'afar ya dawo daga bautar kasa kuma yace gobe zai aiko gidanmu gaisuwa",
"Kice allah kawata",
"Dagaske nake feenerh",
"Yanzu shikenan khadija zaki aure",
"Eh kawata",
"I hope dai inkinyi aure baza ki dinga mana rawwar ganinki ba",
"Wannan kuma sai ki tambayi daddynki saboda nikam bazan zama matar kule ba",
"Lallai amaryan zamani",
"Toh yaya son ranki".
Sun isa kasuwa ,suka wuce wajen zanuwa ,feenerh taga zani kuma yayi kyau sosai dan haka suka tambayi mutumin kozai iya kawowa in bulk saboda anko zasuyi dashi, ya ce masu badamuwa.
Feenerh takoma gida tasami mommynta ta zayyana mata yadda sukayi da khadija akan maganar aurenta.
"Toh bagashi ba ,kawarki ma zatayi aure",
"Mommy don kawata zatayi aure shikenan nima sai inyi yanzu",
"Toh in bakiyi ba dawa zakina yawa a makaranta kinsan dai in khadija tayi aure mijinta bazai yadda kuna yawo kamar da ba sannan kuma iya sanina dake ita kadai ce close friend ďinki",
"Hakane mommy,amma kinsan ba laifina bane saboda yanzu yana wuya a samu miji kamar daddy shiyasa nakeson insamu na kaina kafin inyi aure",
"Gaskiya ne feenerh,amma yadda kike magana akan musa koda bansanshi ba yanada kirki kuma zai kula da ke sosai",
"Eh mommy,musa nada kirki sosai kuma zai kula dani sosai amma shi da kansa ma yace inyi karatu sosai saboda yanada muhimmanci",
"Lallai yamiki shawara mai kyau ,kullum zancen da kike akanshi kara yarda dashi nake akan yana sonki sosai",
"Mommy musa na sona sosai kuma na tabbata bazai muzguna min a rayuwa ba",
"Haka mukeson namiji yazama,kuma haka mukeson mijin *ýar* mu yazama",
Feenerh ta ďan sukuyar da kanta kasa wai ita kunya.
"Toh feenerh tashi muje kicin ,kinsan daddynki na gari kuma yace tuwon acha yakeso",
"Toh mommy muje",
Sun shige kicin don girkin abincin daddynta bayan sun gama sai feenerh ta dafa indomie da kwai don ita bata jin cin tuwon acha yau.


*Bayan wata biyu (2)*
Feenerh na zaune a ďaki tana karanta novel ďin *jini ďaya* na *aneesa .a. rimi (aneelurv)* sai kiran musa yashigo,
"Hello",
"*D* nagama ,nagama",
"Masha allah dear ,congratulations ",
"Thanks *D*",
"Am so happy for you dear ,allah ya sanya alkhairi aciki",
"Ameen *D*",
"Toh yaushe zaka dawo ",
"Gobe",
"Banda zolaya fa dear",
"Da gaske nake *D*,gobe zan dawo na riga da na booking flight ďin gobe",
"Dagaske dear,yanzu gobe zaka dawo",
"Eh *D*,am coming home",
"Ashe yau bazan iya bacci ba",
"Meyasa ",
"Saboda kar bacci ya daukeni in kasa tashi gobe da wuri saboda inason inzama first person da zai ganka gobe",
"Badamuwa *D*, zaki iya bacci saboda flight ďin sai karfe hudu zai isa",
"Still dai ,murna bazai bari inyi bacci ba",
"Am happy too *D* saboda nayi missing ďinki sosai",
"I miss you more",
"A'a ban yarda ba ,i miss you more",
"Toh shikenan in ka dawo za'a tambayi khadija zata mana shaida",
"Toh har ankai maganar Court ",
"Eh!",
"Toh amin afuwa na yarda you miss me more but i miss you much",
Feenerh tayi dariya,
"Dear kenan ,kanada different ways ďin sa mutum dariya",
"Dole ai ,in bansaki ba wazai saki",
"Dear inaso in canza maka suna",
"Tohhh dawani suna za'ana kirana",
"Zauji (wato miji na da larabci)",
"Har na kai wannan matsayin ,thanks alot *D*",
"You are welcome, i can't wait for tomorrow".
Ahaka feenerh tayi bacci da waya a manne a kunninta har safe yayi.






*tnx for reading...*
*©Fareedah*.


Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)


WHATSAPP NO:
07039625239


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*




*written by:*
*FAREEDAH💚*




*Edited by:ANEELURV😍*






*in dedication to my lovely mom😍*




*pg 51▶55*




Ayau anata shugulgula don kar'ban bako wato musa ,a gidan su feenerh anyi abinci kalakala sannan an gyara gidan ko'ina yana walkiya.
Su musa sun isa gidan su feenerh sai sukayi sallam a kofar waje,laraba ce ta ansa sannan tashigo dasu falo suka zauna.
Laraba takoma ciki ta sanar da dasu cewa ba'kinsu sun iso.
Daddy da mommy suka fito dan gaisawa dasu amma da isarsu falo sai mommy ta tsaya chak tana kallon musa. Anya kuwa shine kodai kammani ne ,kila mafarki takeyi,musa abdullahi ne saurayin ýarta kuma shine ýarta zata aura,nan da nan ta juya ta koma ciki batareda sunyi gaisuwa da mutanin ba. Daddy natajin mamakin ,yaba mutanin hakuri sannan yakoma don kirawo mommy.
A bangaren musa,shi baima ga fuskar mommyn feenerh ba har ta koma ciki ,ya dai ji labarin cewa she is not that old kuma ance she married young.
"Lafiya kuwa aisha",
Daddy yashigo ďaki ya same ta a zaune akan gado tana nazari ,
"Lafiya kalau daddyn feenerh",
"Toh meyasa kika baro falo",
"Nayi mantuwa ne shiyasa",
"Toh ai da kin sanar kafin ki fita haka ai,kinsan baki mukayi kuma zasu zaci ko jan aji mukeyi",
"Kayi hakuri daddyn feenerh",
"Bakomai ,yanzu tashi mutafi",
"Toh",
Mommy ta tashi suka koma falo tana biye da daddy.
Musa na ganin mommy nan da nan shima fuskarsa ya canza ,anya aisha ce kuwa kodai mafarki yakeyi ko kuma mai kama da ita ne.
"Sannuku da zuwa",
Daddy yace,
"Yawwa sunnu mu fa",kawon musa ,mallam labaran ya amsa.
"Kuyi hakuri ,dazun matata ce tayi mantuwa shiyasa ta koma ciki",
"Bakomai",
"Yawwa",
"Ni sunana malam labaran kanin mahaifin musa ,ataikace dai musa ya samemu a gida kuma ya sanardamu cewa akwai wanda yakeso kuma ita yakeson aura,koda muka tambayeshi ko ýar waye sai ya ambato sunanka kuma gaskiya a garin nan mutani kalilan ne basu sanka ba kuma a gaskiya mun yaba shiyasa muka ce toh bari mu tataka har zuwa nan saboda mu nema ma yaronmu auran ýarka",
"Toh alhamdulillah ,naji ďadin zancenka kuma gaskiya abin alfahari ne aga wani naka ace ana so, ýaýa na kowa ne kuma tunda yace yana sonta kuma itama ta amince ai shikenan ,allah ya tabatar mana da alkhairi",
"Ameen",
Malam labaran yacigaba dacewa,"ga kayan gaisuwa mun kawo kuma da kudin gaisuwa " ya mika ma daddy a hannusa.
"Toh mungode",
"Kuma munaso asa mana sadaki saboda mu koma asamana ranar aure",
"Duk abinda zaku kawo alhamdulillah ,ko kuma shi musa ya tambayi safiya metake bukata a matsayin sadaki saboda ita keda hakkin wannan",
"Agaskiya mun gode ma tarban da kuka mana ,muna matukar godiya",
"Bakomai allah yabamu ikon ganin ranar",
"Ameen",
"Toh aisha sai ki tafi ki kawo masu abinci ko",
"Toh ".
Koda musa yaji an anbaci sunan aisha sai jikinsa ya girgiza ,yanzu dama abinda yake kokwanto yazama gaskiya. Nan take ya dauki izinin fita waje sannan yaje motar sa ya zauna shiru yana tunani ,mai yafaru bayan rabuwa,yanzu dama itace maman feenerh ,a gaskiya tun ranar farko daya hadu da feenerh yaga kammani a fuskarta, lallai jini jini ne musamman *jini daya*, yanzu ya zaiyi.
A bangaren mommy kuwa takoma kicin taba laraba umurnin kaima baki abinci ita kuma takoma ďaki ta zauna shiru tarasa mezatayi,sallamar da akayi ne ya dawo da ita,
"Mommy har sun wuce",
"Ohhh feenerh kece,harkin tsoratani",
"Meya faru mommy ,duk hankalinki ya tashi",
"Bakomai ýata",
"Yaza kice bakomai mommy,duk fa zufa kikeyi kowani abune yafaru ne",
"A'a bakomai",
"Nidai ban yarda ba",
"Feenerh...... " bata karasa ba taji kiran daddyn feenerh ,ta tashi da sauri ta fita.
"Toh bakinmu zasu wuce ,kuma suna son ganin feenerh saboda su gaisa",
"Shikenan,bara a kirawota",
Feenerh!!!,
"Naam mommy",
"Kitaso ki saki abaya saboda baki nason ku gaisa",
"Anya zan iya kuwa ,inajin soro",
"Soron me",
"Gani nake kamar bazasu soni ba",
"Wayacemiki haka,ofcurse zasu soki",
"Allah yasa mommy",
Sun shigo falo,feenerh tayi gaisuwa dasu gaba daya sannan suka bata tukuicin gaisuwa kuma sun yaba da ita sosai. Toh daga karshe dai baki sunyi sallama da kowa sannan suka tafi.
Mommy har yanzu hankalinta baya a kwance kuma feenerh tarasa gano meke damunta ,saboda haka tace yau zata gano komai,
"Mommy sannu da hutawa",
"Yawwa ýata",
"Mommy inada tambaya"
"Kekika haifeni",
"Wani irin tambaya ne wannan ",
"Saboda in kekika haifeni bazaki boyemin abinda ke damunki ba,mommy banason ganin bacin ranki kuma mommy kinki

24, February 2025
Shuraihu Usman

trrrrrrrrrr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login