Showing 33001 words to 36000 words out of 51002 words
Allah ya taimaka". "Ameen Abba na".
"Idan ka tashi a Office yau ka biya ta gida ina son magana da kai ne". "Yauwa Abba, amma
lafiya? Ko dai wani abin ya faru ne?" A'a babu komai ko ma menene idan ka taho zaka ji, Abba
ya fad'a a takaice.
Sallama suka yi, jiki a sanyaye Fudel ya maida wayan inda ya d'auko ta.
" Hope lafiya dai ko na ga jikin ka yayi sanyi da yawa ne"?
" Wallahi friend ban san ko me ke damuna ba kawai naji ba dad'i ne da na ji Abba na nema
na, idan ka ji shi yayi irin wannan k'iran to watak'ila wata muhimmiyar magana ce ya ta taso".
Bai wani dad'e a Office d'in Musty ba yayi Sallama da shi ya koma bakin aikin shi yana
k'ok'arin k'arasawa da wuri domin amsa k'iran Abba.
B'angaren Luby kam ba ita ta iso gida ba sai wajen k'arfe d'aya da rabi na rana ta tarar har
su Khairy sun gyara wuri tsafffff ko ina sai kyalli yake yi kamar gidan tsabuwar amarya, ga
k'amshin room freshner da doke hancin ta, Lumshe ido tayi ta bud'e a hankali tana mamakin
yaush-yaushe amma har yaran nan sun gyara wuri haka? Yara kwailaye da su dubi yanda suka
maida mata da gida haka? lallai tsafta akwai dad'i amma a yanda ta samu miji bata jin zata iya
b'ata ma kan ta lokaci ta tsaya gara gida".
Haurawa sama tayi tana mai santin parlourn, tana shigan nata d'akin ta ji wani uban tsami
da d'oyi ya doke hancin ta. Lallai sai yanzu da ta shak'i kanshi ta iya gane d'oyin da d'akin ke
mata, a fusace ta d'ire jakan ta shiga d'akin su Khairy ta bangaji k'ofan da k'arfi bammm har sai
da suka tsorata suka kalle k'ofan a tsorace a zaton su ko b'arayi ne dan sun san gidan babu
kowa sai su da maigadi.
Ganin Luby ce ta shigo Khairy ta had'e rai tace" haba!! a shigo wa mutane d'aki babu
sallama sai kace kafirai?
Luby wacce tun shigowan ta ta rik'e kugu tana k'arkad'a k'afa a matsifance ta yi kan Khairy
ta kai mata bugu a baki" ke ce kafiran ba dai ni ba, yarinya k'arama da ke sai fitinar tsiya,
yarinya idan baki daina min rashin kunya ba sai na nuna miki na fiki fitsara".
"Rik'o inda aka mara tayi tace" kai ka kaiiiiiiiii ni kika mara?"
An mare ki d'in ki yi abinda zaki yi".
Kwafa Khairy ta ja cike da tarin takaici, sanin kan ta ne idan ta kawo raini zata ci uban ta ne
a hannun Luby babu mai kwatanta, dama can burga take musu amma tsorone da ita sosai
kawai dai bakin ta ne baya mutuwa.
"Ku taso ku gyara min d'aki, kun gyara ko ina tsafffff ban da d'ak'i na dan kun raina ni? ku
taso nace!!!!! ta k'are maganar cikin d'agun tsawa.
Aunty Luby Allah Khairy ce ta dage sai lallai mun gyara parlour kawai, wai me yasa zamu
gyara miki site d'in ki ai kin fi son ganin kan ki cikin kazantar tunda bakya tsayawa ki gyara da
kan ki".
"Eyeee lallai yarinyar nan kin cika y'ar rainin wayo, affff haka ma kike ce ko ni zaki kalla
kice k'azama, hmmmm yawan ki ya kai na yanka to yau sai kin raina kan ki a hannu na, ke ma
da kika biye mata ban bar ki a baya ba, gobe idan ta sake zuga ki ki biye mata".
Haka ta tusa su a gaba suka shige d'akin ta suka soma gyara mata d'aki suna jero mata
ruwan Allah ya isa kwando-kwando a zuciyan su.
Su d'aga nan su zakulo datti su d'aga can haka dai suke ta yi ita ko Luby ta tsare guri ta hana
su toshe baki wai ita d'akin ta baya tashi da tsami, idan ta faki idon su ta toshe baki da sauri dan
ita kan ta warin ya ishe ta.
Haka suka gaji suka yi tilisssss babu ko sannu balle godiya har suka gama kana Luby ta
ciro maganin mata na itacen da Aunty Salame ta ba su ta mik'a musu tace" ga wannan ina so
kusa ruwa a pot ku juye wannan a ciki ku dafa min sosai, idan kun gama ku kawo min".
K'arb'a suka yi suka shige d'aki suka fad'a warwassss a kan gad'o Hafsy na sharar kwalla
tace" kin ga abin da taurin kan ki ya ja mana ko? Muna zaman zaman mu kin jazo mana".
"Au d'azu da kike cewa mu gyara mata site d'in nata ba aiki ba?"
"Da mun yi ta ta dad'i da ba ai maga mugunta ba, Allah har cikina ya soma kullewa, baki ji
wani d'oyi da naji ba da na zak'ulo da datti.
Kyal-kyal-kyallllll Khairy ta kyal-kyale da dariya tana rik'e ciki, tunowa tayi da Luby da take
toshe baki a b'oye bata san Khairy ta gan ta ba," shegen kaya taji wari tana wani bame baki ga
mai wayo aradu bata san na ganta ba".
Sai da tayi mai isar ta kana ta bud'e laidan maganin ta fiddo tana jujjuyawa a hannun ta,
me nene wannan sis?
Hasfy da ta cika tayi fammmm tace" oohoo ban sani ba, ba tare aka bamu ba? Me yasa
baki tambaya a can d'in ba".
Shu'umin murmushi ta sake tana jujjuyawa tare da aiyana abubuwa a k'asan ran ta, wallahi
ba za ki ci bulus ba sai na d'auki fansar abin da kika mana".
Waro dara-daran fararen ido Hafsy tayi tace" whattt!!!, ba dai wani abin kike shirin kullawa
ba? Dan na san halin ki".
Ke dai tsaya kiyi kallo yarinya da ni take magana".
" Wayo ni dai na ga takaina Allah sis na gaji da fitinar ki, ban iyawa Ammi zan k'ira a waya
a maida Ni gida. Ba yanda Hafsy bata yi da ita ba ta janye k'udirin ta k'iya, ba don ran ta ya so
ba tayi shiru, dan ta san ko zata kwana tana ba wa Khairy hak'uri baza ta fasa ba.
Da misalin k'arfe 6:30 Fudel na gani ya fito da car key yana tunkarar parking space, fitowan
shi ke da wuya ya ga mutane na bin shi da kallo, bai damu da hakan ba sabida idan da sabo ya
saba da gulman da mutane ke yi a kan shi, shi yasa ma bayan Musty baya kula kowa sai idan
aiki ya had'a shi da mutane. Bud'e mota yayi ya shiga ya tada ta yayi tafiyan shi, ya bar su suna ta aikin tsegumi.
Ba shi ya iso gidan Abba ba sai quater to eight na dare sabida go slow da ya rik'e shi a
hanya.
Tarar da parlourn yayi babu kowa dan Abba tuni ya tafi masallaci, Ammi na d'aki tana sallah
yayin da small Ammi na daga kitchen taji k'aurin abincin da Ammi ta d'ora ta bari.
Muryar Fudel taji yana cewa" small ammi, my ammi ammi where are you?
Fitowa tayi tana mai nuna farin cikin ganin shi, "oyoyo my Son, she ka shigo ban sani ba
ina fama da kitchen ne na jiyo muryar ka, Ammin ka na d'aki tana sallah, Abban ka kuma ya tafi
masallaci tun d'azu bai dawo ba.
"Zama yayi a kan kujerar tare da sakin y'ar k'ara washhhhh na gaji over", bari na jira su a
nan kawai".
"Owk, zata koma da kitchen da tsigar shagwab'a yace" small Ammi yunwa nake ji", cikin
rawar jiki tayi hanyar kitchen tana cewa bari na sama maka wani abin ka ci".
Fitowan Ammin shi kenan ta had'e hannu a bakin k'ofa tana kallon yanda y'ar uwar ta ke
yawan jiki a kan d'an ta, sister kina shagwab'a yaron nan da yawa".
"Ba d'ole ba d'a d'aya tilo, ta fad'a yayin da ta kai k'ofa kitchen.
Gaida mahaifiyar shi yayi, small Ammi ta kawo mishi abinci, yana cikin ci Abba ya shigo nan
ya zauna shima aka zubo mishi na shi ya ci.
Sai da dukan su suka ci suka yi nakkkk kana Abba ya dube Fudel da fuska wacce take
nuna alamar nutsuwa yace" Fudel!!"
Na'am Abba ya amsa yana mamakin yanda mahaifin shi ya k'ira sunan shi kasancewar bai
saba jin hakan ba.
Ina so a cikin satin nan da muke ciki ka shirya akwatin lefe, umurni nake baka ba shawara
ba". Rasssss gaban shi ya fad'i a amma sai ya dake yace" Lefe kuma Abba ko dai Hafsah ake
shirin yi wa aure, ai ta yi kankanta da yawa ina laifin a bari zuwa gaba? ko ma dai me nene ba
muke da hurumin yin lefe ba. Murmushi irin ta su ta manya yayi yace" hmmmmm yaro-yaro ne bai san wuta ba sai ya
tab'a ya ji zafi........., ba Hafsat bace za'a ma aure, kai za mu had'a ka aure da y'ar uwar ka
Ummulkhairi, aure na mutu ka raba.
Gumi ne ya soma sauk'o mishi ya dafe kai cikin tsananin tashin hankali ya maimaita sunan"
Ummulkhairy", wato d'iyar k'anwar Ammin shi kenan yarinyar da ta gama raina shi, sammmmm
bata daga cikin tsarin matan da yake so, ga ta k'aramar yarinya d'anya mai sai d'auka a jikin ta?
"Inalillahi Abba ku min rai bana son Khairy idan kun matsa sai na yi auren nayi muku
alkawarin da kaina zan nemo mata na aura, amma ba Khairy ba tayi kan-kanta da yawa.
Kallon shi small ammi tayi tana mai jin tausayin shi, duk da ran ta bai mata dad'i ba na furta
k'almar ki a kan d'iyar ta amma bai hana tausayin shi ya kama ta ba". Tarin takaici da ya ishe
Ammin shi tace" rufe mana baki sakarai ko mutuwa na kunyar d'aukan ran d'a a gaban
mahaifiyar shi. Kuma auren ka da Khairy ba fashi muddin ita ta amince da kai dan haka ka tashi
ka bamu guri.
A daddafe ya mik'e jiri na neman d'iban shi ya fice, ya shiga mota hawaye na ambaliya a
fuskan shi.
Lallai muddin Khairy ta shiga gidan shi ta tarwatsa mishi dukkan farin cikin shi, yaya zai yi
da Lubyn shi wacce take nuna tsantsar so a gare shi, inaaaaaaaa dole ya bijire ma su Abba,
dole ya nemo mafita ma kan shi.
*Masoyan Littafin Maganin mata na ji ruwa comment yau*
_Ko so kuke na tafi yajin aikin tilastawa Fudel auren Khairy ne_
_ My Wattpad fans kuna biyana wlh domin voting page da kuke yi, ina yin ku over_
*eedatou*
*♀♀ MAGANIN MATA*
♀♀'''Damuwa'''♀♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍✍GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍✍~*
*~We are bearer's of so golden pen~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen,savour our words, for it will cause you no pain.~*
©
*eedatou✍*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*
*Dedicated to my besty Firdausi Mainasara(Feeby)*
4⃣5⃣-4⃣6⃣
A daddafe ya iya jan mota zuwa gida.
A gida kuwa Luby ce ta baje a kan bed tana ta sharar barci cike da tarin mafaikai masu
dad'i, ba saban ba su Luby an d'ana bed, sai juyi take yi tana fidda sautin minshari a hankali.
Barcin minti talatin cif-cif tayi ta tashi, bata tsaya yin sallah ba dan dama can ba yi take yi.
D'akin su Hafsy ta lek'a tana hammar barci tace" kun gama aikin da na baku ne?" Khairy tayi
saurin k'arb'e zancen tace" ina fa muka gama Aunty Luby? kiris ya rage Auntyn mu", ta fad'a da
muryar shekiyancin.
Abinda ya bala'in ba ma Luby mamaki kenan da jin ta kira ta Aunty, yau wace rana?
Har zuciyan ta bata yardar da irin tsarin yaudarar Khairy ba, tamke fuska ta dad'a yi tace"
idan kun gama ku kawo min main parlour", tayi tafiya ta.
Fitan ta ke da wuya Khairy ta d'auko laidan ta fita tana wai-wayan Hafsy tace" ki huta ni zan
yi aikin sis, a zuciyan ta kuwa cewa take" na san zaki iya rusa min plan d'ina yarinya.
Kitchen ta nufa ta d'au post ta dora a wuta tare da zuba ruwa a ciki, tana yi tana rera wak'ar
jarumi Nura M Inuwa tana cewa" shuka khairi kar kayo sharri in kayo sharri za ya koma ma ka
ga sakayar Allah, tana yi tana jujjuya mazaunai tana tafa hannu cikin wani GOLDEN borne shot
da farar top, ta tufke gashin kan ta da ribon shima fari. Kallo d'aya za ka mata ka san tana enjoying moment d'in, sai da ta gama kana ta juya
ruwan maganin a wani roba, ta bud'e fridge ta d'ebo wani gari kad'an a chokali ta watsa kana
tayi hanyar parlour tana sakin killer smile.
Luby dama jira take yi da sauri ta karb'a maganin a hannun ta, ko sannu da aiki babu ta yi
shigewan ta d'aki ta d'au buta ta juye ruwan a ciki.
Kayan ta ta cire daga ita sai pant da bra, ta k'ira wayan Hussy, sai da ta k'ira wayan sau biyu
kana ta d'aga" k'awa ta k'awa ta ki ci duniyan ki da tsinke".
"Hahahaaaa Luby ta sake shewa, ke dai bari kawai aminiyar, nayi ta k'ira baki d'aga ba zato
na ko kin hau network ne".
" Hmmmm ke dai bari kawai mutuniyar k'irisss ya rage na hau network, na ga yau sabis na
daddyn Saleem babu kyau ne, kar sai na gama tsuma jiki na da *MAGANIN* ya kawo min
cikassss.
" Tabbbb ni kam tuni na sa aka dafa min nawa yanzun haka so nake ma tsumama kaina,
yau ra randa guda nake so Suger ya juye min da ruwan jikin shi".
"Heheheeee kina sha'anin ki k'awa ta, kina cin k'aren ki babu babban".
" Ke kin ga tafiya ta bye bari na gyara ma miji na kaina.
Bayan sun yi sallama Luby ta fad'a ban d'aki tana ayyana irin styles d'in da zata kashe
kwalabo da shi a wurin mijin, a take ta d'ebo ruwan da a hannu ta watsa a abin ta.
B'angaren Fudel da taimakon Allah ya samu ya iso cikin gida, bai tsaya ko ina ba sai
hanyar d'akin Luby yayi yana cewa" baby!! baby!!, Wani irin ihu ya ji Luby ta kwalla, da sauri
yayi kan benen yana had'awa da gutun gudu, tura k'ofan da yake daga band'aki ya ke jiyo
muryar nan ya gane cewa a wurin take. Bammmm ya buga k'ofan da k'arfi, abin da ya matuk'ar d'aga mishi hankali, tarar da Luby
yayi a yashe a k'asa tana fifita gaban ta tare da tsala ihu gefe kuwa buta ne.
A kideme ya d'ago ta yana cewa" lafiya, what's happening", babu amsa sai ma hawayen da
ke bin fuskan ta shar-sharrr.
Lura da hannun ta da ke k'asan ta yayi, a take ya d'auke ta ya fito da ita, nan ya dire ta a
tsakiyan bed tare da jawo ta a jikin shi ya d'aga hand d'in ta tare da k'arasa cire mata pant.
Ihu mai k'arfi ta tsala yayin da yake bank'are leds d'in ta, Khairy da tun shigowan Fudel
gidan take yab'e tana jiyo su, tsalle ta doka tana cewa" shegiya ta fad'a tarkon da na nad'a
mata, eeyyaaa Luby sorry to say, tayi shigewan ta tana taku d'as d'asss hankali kwance har ta
shige d'aki". Baby waitttt, tsaya na duba ko menene a wurin, ya fad'a cike da tausayin ta, ita ko sai
dad'a rusa ihu take yi dan ita kad'ai ta san kalan azabar da take sha.
Bud'e abin ke da wuya ya ga inda wajen yayi ja-jawur da shi, sosai hankalin shi ya bala'in
tashi, dole man hankalin shi ya tashi sabida tamk'ar d'aye wajen aka yi.
Tsananin tausayin ta ne ya bala'in kama shi, saurin sakin ta yayi ya nufi kitchen ya d'au
manja da sauri ya shigo d'akin, ya bud'e tare da zuba mata a hq yana shafa matab lokaci- lokaci
yana jero mata " sorry". Yana gama ya maida ya koma gefen ta yana hura mata iskan bakin shi.
A hankali take rage sautin kukan ta, zuwa yanzu eyes d'in ta sun rine zuwa launin ja,
muryar ta kuwa har dishewa yayi.
Yana jin tayi shiru ya rungume ta tsamm a k'irjin shi, "my Luby", "ummm",ta amsa tana
ajiyar heart. Hannu ya sa yana shafa kan ta yace" tell me bayan na tafi me ya same ki? Who did