Showing 1 words to 3000 words out of 19312 words
Chapter 1 - YARINYAR RUWA BOOK COMPLETE AYSHA ALKALI CE.pdf
Typing
{Water gurl}
Yarinyar ruwa
Page 1
Zaune take bakin dutse tana rera wakokinta da tasaba jefa dutse take cikin ruwa
Juyawa naga tayi tana sauraren sautin zuwan jirgin ruwa tana cikin haka tsalle naga tayi tafada
cikin ruwan tabuya
CIKIN JIRGIN RUWA⛴️
Shagalinsu suke hankali kwance ta ko Ina kida na tashi wani matashin saurayi na hango gefe
yana shan coca cola kallonsu kawai yake yana jinjina shirme irin nasu.
Wani daga cikinsune ya taso yana kokarin janshi amma firrr wannan guy yaki yadda yatashi.
"FAHEEM" mai duba na'urar jirgi yakirashi hankali atashe.
Juya wadda zanyi naga wani kyakkyawan saurayi hadadde kuma murdadden namiji
Fari soll dashi.
Tana ganin jirgin tabi bayan jirji nandanan tashiga gefen jirgin tana lekonsu,
can ta hangoshi ya bada baya sai murmushi take tana kara leko, duk da ba ganin fuskarshi
take Yiba.
Tana cikin haka taga zoben ta na haske alamane da kiran mahaifinta da sauri ta wintsilo sai
cikin ruwan.
Lumshe idanu yayi yana kallon ikon Allah yadda ruwa suka taso sukayo kansu.
Page 2
Nan danan aka fara fidda kana nan jiragen ruwa kan kace mey har ruwan sunyo Kansu.
Cikin gaggawa kowa yake fadawa karamin jirgin ruwan harzai fada jirgin ko mey yatuna
oho♀️ yakoma da gudu da baya yana zuwa tsakinyan jirgin yatsaya yana dube dube.
Can ya hango Dan karamin dan kuikuyo dasauri yadakkoshi yajefa Cikin ruwa.
Daidai wannan yarinya tasake fitowa ta tura karen da hannun ta wurin jirgi kafin takarasa gun
saurayi jirgin har ya nutse tare dashi.
Cikin tashin hankali takoma cikin ruwan tanata duba inda zata ganshi amma inah bata
ganshiba
jirgin yana nutsewa yafara kokarin yin iyo amma ina ya kasa Dan bakaramin ruwa banee
Jikinsane ya sake ya tafi can kasan ruwan saura kadan, tariko hannunshi tayi sama da shi
Duk Abunnan da ake sarauniya fauza na kallonsu amadubin tsafinta
Bakin ruwa takawoshi amma ba numfashi atattare dashi cikin razana tafara danna kirjinshi
Page. 3
Amma inah ko alamar rai babu nandannan tasaka bakinta anashi tana jawo ruwanda yasha
tanayi tana danna kirjinshi amma baitashiba
Cire bakinta tayi anashi tafara danna mishi kirshi da karfin gaske tana rera waka can saiga ruwa
nafitowa ta bakinshi
Ajiyan zuciya tayi ta daga ajikinshi
Ahankali yake jiyo sautin wakar da take rerawa tare da kokarin bude idanun amma bishi bishi
yake ganinta
Baikarasa bude idanuba yaga ta fada ruwa nan sojojin da ke nemansa suka karaso gareshi
suna dagashi suka tafi dashi tasu masarautar
Koda takoma hannunta rike da agogon hannunshi murmushi tayi
"FAHEEMA!!!"
Naji ankira abayanta wata matace matashiya
bazasu wuce sa'a gudaba saidai ita faheema tafita koma daga halittar fuska harta jiki mah
Juyowa faheema tayi tace "ya akayi mey ya kawoki nan ya akayi kikasan nan wurin" ta
tambayeta cikin alamar tuhuma.
"Faheema wannan abun dakike shirin aikatawa kuskurene ya za'ayi kiso wannan mutum wanda
ba rayuwa iri daya kukeba?"
"Taya zai iya rayuwa cikin ruwa faheema kinsan ambawa yarima khalil ke baikonku duka wata
daya ne saura"
"Sanin kankine khalil bashida imani zai iya yin komai akanki zaishiga rayuwar mutuminda
baimasan da muba"
Ahasale faheema tayo kan Abaya, wuyanta takamo amugun hasale,
"Karki sake dangantani da wannan shedanin mutum har kike kokarin danganta wanda nake so
fiye da rayuwata dashi" Takarasa a tsawace
Abaya na kokarin kwatar kanta amma ina takasa cikin mawuyacin hali ta fizge agogon hannun
faheema
Bata ankaraba tajita kasa timmmm aguje ta tashi tareda sake agogon tayi fuuuuu ta wuce Dan
wlh inta tsaya faheema zata kashe ta kan maganar
Sarauniya fauza dariya ta sheke tareda buga wani table dake kusa da ita
"Faheema kinyi kuskure babba arayuwarki tason wani mutum ba dana khalil ba saikin
gwammace baki taba sanintaba" tare da kara shekewa da firgitacciyar dariya
Page. 4
Zama faheema tayi tare da rungume agogon kamar ta rungume mai agogon lol
Tunani take ya zatayi itama kanta tasan tadibo abu mai wahalar gaske sbd koda kowa zai
amince bata tunanin mahaifinta wato sarki zai amince
Yazatayi da matsananciyar soyayyar da ta tsinci kanta aciki
"YAZANYI! YAZANYI!! YAZANYI!!!" Takarasa cikin rauni inama mahaifiyata tana kusa nasan ita
kadai zata fahimci halinda nake ciki
Tare da fashewa da kuka koda zan rasa rayuwata sai na rayu dakai
"Zaki rayu da gawa dai inhar ina numfashi faheema ke tawace" ya karasa tare da jawo gashin
kanta da karfin gaske kokarin kwatar kanta take sbd azaba amma ina ko jijjigi hannunshi bayayi
janta yake Tana turjewa shiko saikara janta yake.
NIKO NACE SAIKACE ABIN DOLE ANCE BA'AYI BAKA KYALETA LOL toko dai wani abu
yarima khalil yakeso wurin sarauniya faheema
Share & comment pls
✍️Writing by aishaalkali
Muhadu a page 5 muji yazata kaya
shin mey yarima yakeso wurin sarauniya faheema? wacecec sarauniya faheena ?waye yarima
faheem? shin faheem yanason faheema ?
Sarauniya fauza menene kudurinda kan fahima ?
Cakwakiya
Soyayya
Bandariya
Kiyayya
Mugunta
Izza
Tausayi
Tare da tsantsan nadama kudai kubiyomu muji yaxata kaya taku har kullum eshaalkali. {
water gurl}.
Idan bakuyi comment da sharing ba Zan cigaba da rubutu ba gaskiya✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
AISHAALKALI PALACE✍️
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/DPpBhXyzIVKLbDQwVsQJX
Typing
Water gurl♀️
Yarinya ruwa
Page5&6
Jan hannunta yake da karfi kamar yasamu gwarzon namiji kamar shi
Bai tsaya ko inaba sai cikin dakinshi da shikadai yasan da zamanshi cikin masarautar tasu
Duk wannan abun dayake faheema ta dade da sumewa sbd matsananciyar azaba agogon ta na
makale da ita.
Hankadata yayi "sai inga wanda ya isa zuwa ya fitar dake balle harki kara ganin wancan
mummunan mutumen"
Sai asannan faheema tadawo cikin hayyacinta zatayi magana taci ta kasa kokarin magana
amma inah abin da bazai yuyuba sbd
Yaciri kashin kanta yayi tsafi yacire murya sbd kada tayi yunkurin kiran mahaifinta
Kuka take iya karfinta amma ba halin magana shiko sai kallon Lip's dinta yake. Allah yasani
komi faheema tayi tana burgeshi
Shidai yana sonta koma mey tayi mishi
Yarima
Yarima khalil dane ga sarauniya fauza matar sarki wato mahaifi ga faheema
Mahaifiyar faheema tarasu faheema nada shekara 10 aduniya
Alokacin ita kuma sarauniya fauza takashe mijinta da hannunta khalil yanada shekara 16
Sarauniya fauxa takasance rikakkiyar masafiyarda ta amshi sunanta wani lokacin ita kanta saita
sauya halitta
Taje ta holewarta da bayin masarauta maza
Ana haka mijinta ya kalu balanceta kan abinda take tabari kodon yaronsu ya samu Inga tacciyar
rayuwa amma ina idanunta sun makance sai take gani kamar yanaso ya karbe dantane
awurinta
Cikin Daren ranar mahaifin khalil ya mutu batare da ya shura ba farin ciki wurin fauza bako
karami ba alokacin khalil yana wurin kakarshi acan yake rayuwa
Mutuwar mahaifinshi sarauniya fauza tasamu damar karbarshi awurin kakanninshi
Shima baisoba amma haka fauza ta tsafe dannnata sbd kada yayi gardama
Ahaka khalil yafara ganin abubuwan da mahaifiyarshi take saiya fara sha'awa tayi farin ciki
sosai koba komai ynx tanada magaji
Wannan kenan bangaren sarauniya fauza da yarima khalil
Page 7&8
Sarkin ashib sarkine mai cikakken iko da karfin mulki izza sarauta cikin jinin jikinshi take sbd ta
gadoce
Sarki ashib mahaifine ga sarauniya faheema mai jiran gado mahaifiyar ta itace kadai mata ga
sarki
Auren soyayya sukayi kuma dama shi sarki bayada sha'awar mata barkatai soda yawa ana
kawo mishi yaran sarakai Dan ya aura amma yace matarshi zainab ta isheshi
ana haka sarauniya zainab tayi shekara uku batareda ko barin wata ta taba yiba awannan
lokacin mutane da dama sun yi zaton sarauniya zainab asiri tayima sarki sbd su basu dau tsafi
wani mummunan abu Ba
Hasalima duk abinda zasuyi sai anhada da tsafi kowa zai iyayin abinda yakeso amma kuma
abu dayane Sarki yafi kowa karfin tsafi shida sarauniya
Ananan hankalin kowa yatashi akan rashin haihuwar sarauniya zainab amma banda sarki ashib
bayaso yanuna rauninsa har mutane su fuskanci haka
Anan cikin wannan yanayi aka bidi sarauniya Zainab amma ba'a gantaba duk inda akesa ran
ganinta amma ina abu ya faskara hankalin sarki yayi matukar tashi nan take masarautar ta
dauka kowa na tofah albarkacin bakinshi kan batan ta
Wata takwas kenan da batar sarauniya Zainab duk yanda akayi da sarki domin yakara aure
amma yace shi bazaiyyi aure ba sbd Zainab nanan kuma takusa dawowa gareshi
Haka aka saka mishi ido sarki ynx gaba daya baya zama fada baya tabuka komai amasarautar
kowa abinda yakeso yakeyi
Ranar wata litinin 1st November 2004
Sarauniya Zainab ta haifi yarta mace kyakkyawa fara tasss alokacin sarauniya zainab tana
tareda mahaifiyarta wato kaka hajjo duk tsawon wannan lokacin tana tunanin halinda mijin nata
yake ciki
Saida tayi arba'in sannan ita da mahaifiyarta suka fara shirin dawowa
Page9&10
Koda suka dawo masarauta sarki murna bibbiyu ga yarinyarshi ga matarshi alokacin hadda
walima akayi a masarauta
Ana haka yarinya tafara girma hankalin yaran masarauta duk yatashi sbd koda tayi shekara
takwas yarinya taxama macen asali
Wata Rana tafito daga cikin ruwa tana shan iska bakin teku ananne shikuma khalil ya fito
mugunta sbd wannan lokacin ne masu jirgin ruwa suke wucewa shikuma
Yana matukar jin dadi yimusu mugunta ananne yafara ganin sarauniya faheema tun lokacin da
idanunshi suka sauka kanta yakamu da matsananciyar soyayyarta
Water gurl by eshaalkali✍️
Ita kuma tana ganin jirgin tabi yasanshi jirgin bai tsaya ko inaba sai bakin masarautar jauro
masarautace mai dinbin tarihi da al'adu ma bam banta
Faheema kidawo ammi nakiranki tajiyo sautin muryar abaya kwabe fuska faheema tayi tace
abaya ganinan
Nan ta fada cikin ruwan bata tsaya ko inaba sai wurin mahaifiyarta
Abaya diyar kawar sarauniya Zainab ce wato indo tarasune wurin haihuwar abaya kuma
mahaifinta ya mutu tun indo nada cikin abaya
Haka yasa sarauniya Zainab ta karbi abaya ta hada da yar ta take kulawa dasu atare kamar yan
biyu
Wani abin mamaki tunda aka haifi faheema sarauniya Zainab bata kara koda barin wata bane
Tunda khlil yaga faheema yakoma yasanar da mahaifiyarshi dama abinda fauza ke jira kenan
Taku har kullum eshaalkali
KUBIYONI DOMIN KUJI YAZATA KAYA
Share &comment idan ba comment zandaina posting gaskiya
Water gurl♀️
Writing by aisha alkali✍️✍️Typing
Water gurl♀️
Yarinya ruwa
Page11&12
Alokacin da khalil ya fadama mahaifiyar shi cewa faheema yakeso ya aura bangaren
mahaifiyar faheema tana yawan mafarkin khalil da mahaifiyar shi tayi alkawarin indai tana raye
faheema bazata taba auran khalil ba koda kuwa tana sonshi
Fauza tayi bincike iya bincike amma abun yaci tura sbd haka ta yanke shawarar kawar da
sarauniya Zainab aduniya sai ta maye gurbinta kunga ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya
Na farko zata zama sarauniya mai karfin iko sannan zata cika burin mafi soyuwan dannata
haka sarauniya fauza tayi ta gwagwarmaya har tasamu nasarar raba sarauniya Zainab da
duniya alokacin faheema nada shekara 10 aduniya tayi kuka iya kuka itada mahaifinta dama
kakanninta
Wannan kenan...
Cigaban labari
Haka yaci gaba da azabtar da gimbiya faheema tun mahaifinta baya nemanta har hankalinshi
yatashi wata kwarya yadauko wacce shi kadai yasan da ita
"FAHEEMA!"
ya kira aiko saiga faheema cikin kwarya daure awani wajen hankali tashe ya mike tsaye yana
mamakin wanene yakeda ikon kama gimbiya har yayi mata irin wannan daurin
Bangaren faheem.
Ya takurama mahaifi da mahaifiyarsa kan sai annemo mishi yarinyar da ta ceci rayuwarshi ba
neman da ba'ayiba amma babu lvr
Shiko ya dau alwashin zai jirata koda tsawon rayuwa ce sbd yanaji ajikinshi cewa zata dawo
nesa ko kusa
Haka duk lokacin da
Ya kwanta bacci saiyayi mafarkin tana kiranshi yataimaketa wani wajee mai hadarin gaske abin
na damunshi amma ba yanda ya iya sbd shima yasan mafarki ba gaskiya bane
page13&14
Sarki ashib ranshi yayi mummuna baci alokacin da yagane da sa hannun Dan matarshi wato
surukinshi awurin azabtar da yar shi daya tilo
Iska kawai mahaifinta ya hura saigashi daurin da akayi mata ya warware jin haka yasata
kunkura zatayi kuwa amma saita kasa
Nan mahaifinta ya gane ancire mata magana haka ya koma hura wani iskan saigashi ta furta
"ABIEE" cikin wahaltacciyar muryar ta data dishe sbd wahala
Nan abaya ta bayyana agaban ta tana kuka itama kamar itace aka daure faheema bakijin
magana na gaya miki kicire wannan mutumin acikin rayuwarki amma taurin kai ya hanaki
Shikenan tunda haka kika zabama rayuwarki faheema abaya tafada tare da juyawa zata bar
wurin
"ABAYA" taji ankirata da sanyayyiyar murya idanu ta runtse tanajin wani zafi na ratsa ko wani
loko na jikinta...
ba yawa kuyi hkr wlh yau banida charge shiyasa amma in sha Allah zanyi Post da dare amma
gaskiya banyi alkawariba.
Water gurl ♀️
Writing by Aisha alkali✍️✍️✍️✍️
More comment more update✍️Typing
{Water gurl♀️}
Yarinya ruwa
"Page15&16"
"Abaya kinsa wanene khalil kinfi kowa sani abaya kina tunanin idan na amince da khalil anya
banyi wauta ba kina ganin yadda yake lalata yaran mutane kazama mai lpy marar lpy duk
kusantarsu yake haka kike tunanin khalil zai iya canjawa bayan aurenmu??"
Numfashi abaya ta fesar "faheema ki gane
Dakata malama ynx dubamin ina khalil yake"
Tafin hannunta tabude takira sunan khalil nan khalil ya bayyanan yanata sheke ayarshi da
yammata ba daya ba ba biyu ba
Kauda fuska sukayi baki daya "ni babban abinda yake batamin rai wai ace sarauniya fauza ita
ke kaimishi bayi kuma wai sai wacce tayi mishi wlh bazan iya zabama yarana wannan fasikin
amatsayin uba garesuba ";
"Hakane amma faheema"
"Amma faheema mey?" takatseta ta hanyar mayar mata tambaya!
"Kinsan abinda khalil yace zai aikata lalle zai aikata sannan duk abinda kikeyi mahaifiyarsa
naganinki"
"Taya take ganina Abaya"?
"Wlh duk abinnan damuke tana gani kuma tana jinmmu"
Wani abu Abaya ta ciro daga jikinta kamar sarka tasaka mata awuya indai wannan abun yana
tare dake bazata sake ganin motsinkiba...
"page17&18"
Faheem ne zaune bakin teku yana jefa dutse aruwa yana rerawaka. aduk lokacinda ya rufe
idanunshi yana ganin bishi bishin fuskar ta !!
Saidai har ynx ya kasa mantawa da ita abu daya yake wanda yake rage masa kewa shine rera
wakarda ya jiya abakinta .
zaune take gefen mahaifinta fada yake mata sosai itadai sai hakuri take bashi "FAHEEMA!!"!
yakirata da kakkausar murya !!
"Nan da wata daya zan daura aurenki da khalil"
Maganar mahaifinta haka tajita akunnenta kamar saukar aradu
"Kwarai kuwa daki shirya da karki shirya duk dayane amma nariga na yanke hukunci"
A wannan lokacin faheema kasa tabuka komai tayi sbd wata matsananciyar faduwar gaba
sunan Allah take maimaitawa duk da batasan mey take cewaba
KO ita abakin faheem taji lokacinda yafara bude idanunshi!
Koba komai tasamu natsuwa ta hanyar ambatan Allah nda takeyi
Shuru tayi tacigaba da sauraren mahaifinta yana bata umarni duk abinda yace bata cewa a'a;
Haka gaban faheem ya keta tsinkewa baisan dalili ba yanaji ajikinsbi wani abu zai faru saidai
baisan komai akan haka ba sbd haka yabarwa Allah komai shidai nashi addu'a da zubama
sarautar Allah ido!!
"SBD koshi wani lokacn yana mamakin irin sonda yakema wacce baisan wace irin halitta bace
dan ynx yadaina yimata kallon mutum;
lol faheem ashe kanada saura har ynx baka shirya tunkarar komaiba kenan...!
"Page19&20 "
Tashi tayi jiki ba kwari tatafi turakarta
Bangaren khalil kuwa sarauniya fauza ce take mishi barka kuma bangare daya tana mamakin
yanda akayi ta daina ganin faheema gaba daya so dayawa takan matsa amma sai taga kamar
tukunyar tsafin zata fashe inta cigaba .......
"MASARAUTAR SARKI ABDURRAHAMAN MASARUTACE TA ADDININ MULUNCI DA
MANYAN MALAMAI MAGADA ANNANBAWA"