Showing 6001 words to 8637 words out of 8637 words
Chapter 3 - SAI NA AURETA BOOK COMPLETE BY by NIMCYLUV SARAUTA .pdf
*15↪️16*
*Still free page,gamai so zai iya yimin magana ta wannan number 08119237616*
_pla show me some luv 200 naira only_
Har yaje bakin kofar bedroom ɗinta sai kuma ya tsaya cak,sakamakon tunawa da
yayi da Dina a ɗakin,tsayawa yayi yana neman mafita domin bazai iya bacci ba idan bai ganta
ba,numfashi ya furzar mai zafin gaske sanan ya saka kansa cikin bedroom ɗin,ita kaɗai ya
hanga a tsakiyar bed ɗin ta lullube jikinta da gargo,ƙara sawa yayi wajen bed ɗin,kuka ya fara ji
ƙasa-ƙasa saurin ƙara sawa yayi wajanta sam bai yadda ya ƙarasa kusa da ita ba,zama yayi
gefen bed ɗin daga inda yake yana ganin fuskarta,tsayawa yayi yana kallonta ya rasa mezai ce
domin bai shigo da niyyar yi mata magana ba,amma bazai iya barin cikin halin da take ciki ba,to
mene ya dameta take wannan kukan hakan,shiyasa yaji ya kasa samun sukuni saiya
ganta,gajiya yayi da kukan nata yace.
"Diya kiyi hakuri dukkan tsanani yana tare da sauƙi,nima hakuri kawai nake domin abinda nakeji
a zuciyata bazai taɓa gogewa ba,inajin shine a jalina,kinga dukkanmu muna cikin damuwa
saidai muyi hakuri"
Ajjiyar zuciya ta shiga saukewa,dai-dai ta numfashi ta tayi sannan tace.
"Yaya kasan cewarka cikin damuwa da kunci shine ya sakani cikin damuwa wacce bazai iya
buyeta ba,dan Allah yaya ka gayamin damuwarka kozan iya magan ce maka ita?"
Shuru yayi baice komai ba,Amma shi kaɗai yasan zafin da zuciyarsa keyi masa,duniya tayi
masa duhu baya iya gani komai,baya iya gane komai,wani irin ɗaci ya keji a cikin ransa,baiyi
aune ba yaji ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,bai san lokacin da yayi saurin jawota jikinsa ya
rungome ta tsam a kirjinsa yana buga bayanta alamar rarrashi,magana taci gaba dayi.
"tabbas idan na cika ƴar uwarka kuma kanwarka uwa ɗaya uba ɗaya,inason naji damuwarka
wacce tayi afecting ɗin kulawar da kake ban,Yaya sai dakai nakejin daɗin Rayuwa,Yaya sai
dakai nake ganin haske a zuciyata,meyasa zaka gojeni lokacin da nake buƙatarka cikin
rayuwata" ta faɗi hakan tana dukan kirjinsa.
Hannayenta ya riƙe gam yana ƙare mata kallo kamar bazai magana ba sai yace.
"Diyanatu jin damuwata babu abinda zai ƙara maki sai tashin hankali,kiyi hakuri wannan ba
lokacin kukan ki bane,wannan time ɗi nane,komai yayi zafi maganinsa Allah,kici gaba da sani
cikin addu'oin that is what i want to you pls".
Wayyo Allah ina Rami yake tashiga ta bunne kanta,bata taɓa bakin ciki da damuwa da
makantar taɓa sai yau, koma komai da zata buɗe ido ta kalli yayanta kuma tasan abinda yake
damunsa,gaba ɗaya rike ce masa tayi,kawai neman inda zata saka kanta taji daɗi take,ƙara
makale jikinsa take.
Saurin janyeta yayi daga jikinsa yayi,wani irin shock ya keji,da kyar ya samu tayi shuru kuma ya
rarrashe ta tare dayi mata Al'kawarin zaina zuwa wajanta yana dobata.
After 1 mounth
Kullum babu fashi zai Papi yasa an saukewa Diya alkur'ani,maganin karya sihiri da kuma
addu'oi kullum sai anyi mata,duk da kasan cewar bawai sauƙi ake samu ba,amma hakan baisa
sun daina ba suna saran wata rana za'a dace.
zuwa yanzo M.t ya gama wahala,sosai zuciyarsa keson bugawa,daga yanzo zuwa ko wanne
lokaci zai iya fallasa asirin dake ɓuye cikin ransa,yayi addu'ar harya gaji,yayi kuka wanda ya
haddasa masa ciwon kai wanda baya taɓa sauka harya saba dashi.
kamar yadda yayi mata al'ƙawari yana zuwa yana dobata wanda hakan ke sata jin daɗi koma
komai hakan zaisa ya rage jin abinda yake ji.
Zuwa yanzo tun Mamu na damuwa akan al'amarin M.t harta gaji ta zubawa ikon Allah ido,bawai
dan tana jin daɗin ganinsa haka ba.
Durkoshe yake gaban Papi yana sauraran abinda zaice.
"Wato Muktar ka rainani ko?nizan baka umarni kaƙi bi ko?"
Sunkuyar da kansa yayi ƙasa sannan yace.
"A'a Papi ba haka bane,wacce zan zaɓa a matsin mata itace ban samu ba"
ɗan kallonsa Papi yayi lokaci guda kuma ya ɗauke idonsa yace.
"That is great,kashirya gobe kaje ka gano ƴar abokina ruma,kafin Papi ya ƙarasa magana tari ya
sarƙe M.t cikin tausayin halin da ɗan nasa yake ciki yace.
"sannu daman baka da lafiya ne,kar manta da goben kafin ya ƙara sa tari ya gama Sarƙe M.t
zuciyarsa ya danne kafin kace me ya fara tarin jini.
*SAI NA AURETA*
_(luv crises)_
*NA'IMA SULAIMAN*
(nimcy luv)
*17↪️18*
*Free page*
*gamai son book ɗin 200 naira only08119237616*
_Nasan cewa kuɗi kuka biya sannan kuka karanta,amma yana da kyau idan kun karanta
nasan kun karanta ta hanyar yin sharshi akan page ɗin da akai,kuyi hakuri da rashin update_
kafin kace me ya fara tarin jini,cikin tashin hankali Papi yayi kansa yana masa
sannu,gaba ɗaya M.t ya gama fita daga haiyacinsa,hannu yasa ya danne saitin zuciyarsa haɗe
da kiran sunan Allah guda 99,Papi ne yaci gaba da buga bayansa harya samu tarin ya lafa
masa,sannu kawai yake jera masa,ya ɗau tsahun lokaci kafin ya samu nutsuwarsa ta dai-dai
ta,tashi yayi cikin sanyin jiki yayi wajan frizer na parlourn buɗewa yayi ya ɗakko gorar ruwa mai
sanyin gaske murfin gorar ya ɓalle sannan ya kafa ta a bakinsa bai ajjiye ba saida yaga ya
shanye ruwan tas sannan ya jefa gorar a tusben,tafiya ya fara cikin isa da taƙama,kana ganinsa
kasan ya cika namiji mai jini a jika,wani irin sheƙi chcolate skin ɗinsa keyi,kyau da kuɗi da huto
da jin daɗi sun gama bai yana a jikinsa,idan ka kallesa ba zakayi tunanin yana cikin damuwa ba
saidai face ɗinsa yayi showing,ƙara sawa yayi part ɗinsa key ya ɗauka ya murza a door ɗin,tana
buɗewa ya faɗa cikin ɗakin,daret bathroom ya nufa rigar cikinsa ya zare sannan ya zare
wandon jikina yayi naked ,tsayawa yayi saki shower a kansa yakai wajan 20minutes ruwa na
sauka a kansa,ajjiyar zuciya ya sauke haɗe da furzar da wani numfashi mai zafin gaske,shower
ya kashe sannan ya ɗaura towel a jikinsa ya fito,gaban mirrow yaje ya daɗe yana kallan kansa
tabbas bashi da wata tawaya,ada yanayin rayuwarsa cikin farin ciki da kwanciyar hankali,amma
yanzo he lost everthing ba yaji rayuwarsa zata dawo dai-dai,sannan bazai iya shiring
damuwarsa da wani ba,bare har asan abinda yake damunsa yasan cewa duk wanda ya faɗawa
damuwarsa babu shakka zai iya ce masa ya haukace,da wannan tunanin dake kwance kasan
zuciyarsa ya gama shiryawa cikin wata ɗanyar shadda getzerna mai kalar sky blue,sai zabga
ƙamshi yake faɗin kyan da yayi ɓata bakine,wayarsa ya ɗauka iphone 7+ pro ya ɗauka ya saka
acikin pocket ɗinsa,harya fita ya manta bai ɗauki key ɗin motarsa ba,dawowa yayi ya ɗauka
sannan ya rufe part ɗin nasa gaba ɗaya,cikin jarumta ta taƙama yake sakkowa daga step ɗin
benen.
Tun kafin ya ƙaraso ƙamshin turarensa ya gama baiyana a parlourn,lumshe idonta tayi tanajin
wani sanyi me daɗi yana rasa dukkan wata kofa ta cikin zuciyarta,ɗagowa tayi a hankali cikin
sa'a idonta ya sauka akansa,baki ta saki gala-gala tana kallonsa,ba ƙaramin kyau M.t yayi mata
ba,cikin sexy voice tace.
"Wow my man kaiɗin na da banne a cikin maza"
duk abinda take akan idonsa,yi yayi kamar baiga abinda take ba,wajan frizer yaje ya buɗe ya
ɗauki gorar ruwa mai sanyi,ɓalle murfin gorar yayi ya kafa a bakinsa bai ajjiye ba saida ya
shanye ruwar tas,harya saka ƙafa zai fita yaji tayi magana cikin cool voice ɗinta tace.
"bro daga nan sai ina kuma?,ko wajan antynmu za'a?"
Wani killer smile ya sakar mata,duk da cewa ba gani take ba,itama murmushi tayi,ƙara sowa
yayi inda take a zaune,dur ƙosawa yayi a gabanta sannan ya kama hannun ya ɗan murzasu
yace.
"Diya zance Papi ya turani ko zaki rakani?" ya tambayeta yana leƙa face ɗinta,dariya tayi har
fararan hakoranta suka bai yana,hannunta ta janye a nasa sannan tasa hannu ta shafi fuskarsa
tace.
"ai biri yayi kama da mutum,nasan wannan wankan ba daimu da muke zaman gida ba saidai
Madam ɗin Bro na"
"Uhm"kawai yace sannan ya kama hannun ya miƙar da ita tsaye yace.
"muje ki rakani kya rage zaman gidan" yana gama faɗin hakan ya riƙe hannunta suka fara tafiya
yana mata jagora,da haka suka isa compound na gidan wajan motarsa ya nufa mai kirar bugaty
key yasa ya buɗe sanyata yayi a gidan gaba sannan ya koma wajan driver ya shiga yaja motar
sai jan bulo.
Tunda suka fita a parlourn take safa da marwa,tama rasa abinda zatai idan har ta bari M.t yayi
aure to zaman gidan da tayi bata ga amfaninsa ba,tsayawa tayi da tafiyar da take tana tunanin
mafita,wannan shegen murmushi tayi na gefen baki sannan tace.
"M.t kenan baka san wace dina ba,amma for now ya kamata kasan dawa kake zaune,ya
kamata ka fara faicing problems naka akaina,zan koya maka soyyayata,zan mantar dakai kowa
da komai,tana gama faɗin hakan ta zari hand bag ɗinta da key din motar ta tayi waje.
Zaune suke a wani tafkeken parlour wanda kana ganinsa kasan an kashe kuɗi wajan
tsarashi,amma duk kyansa bai taka na gidansu M.t ba,shira suke shida Diya wanda ƙarfin
maganar M.t keyinsa dan Diya bata fiye surutu ba musamman inda bata da power,ana haka
tashi M.t yayi shuru kamar baya parlour.
Tunda Ruma ta iso parlour ya zuba mata ido,gaba ɗaya ya kasa ɗauke idonsa daga kanta,ya
rasa bai ya keji a yanzo da yaga Ruma infact zai iya cewa 100 na cikin damuwar to 500 ya
rago,sosai tayi kyau cikin wata dakakkiyar shadda anyi mata ɗinkin duguwar riga,fara ce
sosai,sannan kuma duguwa ce domin tafi Diya tsayi wani ƙamshine katashi lokacin da Ruma ta
gama baiyana a parlour.
Magana take ƙasa-ƙasa Amma ina sam ba yajin abinda take cewa,hannu tasa ta zunguro shi
tace.
"Da alama Anty Ruma ta iso ko" still shuru baiyi magana ba,ji tayi gabanta ya faɗi saka makon
wani abu daya ɗarsu a ranta,ji tayi hawaye na neman zobu mata.
*SAI NA AURETA*
_(luv crises)_
*NA'IMA SULAIMAN*
(nimcy luv)
*19↪️20*
End of free page
*wannan shine page ɗina na ƙarshe a free page,masu tambaya ta prvt kuyimin afuwa ina
cikin busy,inata ganin kuɗinku na siyan book,nagode da ƙauna,matsalar,siyan data,shi yasa
mukace 200 ina gdy sosai da ƙaunarku*
200 naira only 08119237616
Follow me on wattpad
Nimcyluv
_Need ur commets_
Ji tayi hawaye na neman zobu mata,saurin goge hawayen tayi sannan ta jin gina
jikinta a jikin sofar da take zaune,shuru tayi tana tunanin kodai Ruma ba tayiwa yaya M.t bane
shiyasa yayi shuru,Addu'a take sosai a cikin ranta Allah yasa Yaya ya amince da Ruma,bata
gama tunanin dake adda bar zuciyarta ba taji Ruma tace.
"Sannu Diya yaya jikin naki?" murmushi kawai Diya tayi haɗe da cewa.
"Allahamdllilah" wani irin bacci ta keji haka nan,dan haka ta samu gefen sofa ta kwanta tana
jiran Yayan nata ya gama su huce gida.
Ruma ce ta Kalli M.t shima ita yake kallo,baya son koda sau ɗaya wani movement nata ya huce
shi or else akwai problem,kasa tayi da kanta sannan tace.
"ur welcome sir" wani killer smile ya sakar mata wanda ya kosa haukata ta gyara zama yayi
yace.
"Ni banacin miƙe,kin wani tafi wani waje da ban kamar ƴar ƙauye" wasa ta fara da ƴan ya
tsunta,kamar ba zata tashi ba,sai kuma ta miƙe ta ƙarasu sofar da yake zaune ta zauna kosa
dashi,durko suwa yayi wajan face ɗinta har suna iya jin numfashin junansu,kansa ya ɗauke
sannan yace.
"so Ruma what's in ur mind about me?" shuru Ruma tayi dan ba zata iya cewa komai ba,sabida
yadda kirjinta keyi mata wani bugu wanda ba tasan meye dalili ba,jin take kamar a mafarki wai
itace mafarkin ta zai cika,ita kaɗai tasan abinda ta keji game da M.t,ita kawai yake kallo dan ya
nasu yaji amsarta,shurun da tayi ne ya tabbatar masa ya karɓo a zuciyar Ruma,hannu yasa ya
kamo hannunta ya riƙe cikin nasa,baice komai ba ya miƙar da ita tsaye,cikin idonta ya kalla inda
itama shi take kallo,kawar da kansa gefe yayi yace.
"ok mu zamu huce,sai wani time ki kula da kanki" mamakine ya kama Ruma kwata-kwata
yaushe yazo?to mema suka ce da har zai tafi,murmushi ta kallesa ido cikin ido tace.
"Allah ya kiyaye hanya,bari a tashi sister ko?" kallan inda diya take kwance tana bacci yayi,juyo
wa yayi yace.
"No basai kin tashe taba" yana gama faɗin hakan ya durkosa ya ɗauki Diya cak ya ɗora ta a
kafaɗa kamar wata ƴar Beby cikin sassarfa ya fara tafiya har ya isa compoun na gidan,yana
zuwa yasa key ya buɗe murfin motar ya kwantar da ita sannan ya koma wajan driver ya shiga
ya zauna ya rufe motar,kallan yadda take bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi,ganin
ta kwanta ba dai-dai ba yasa ya jawo ta kan cinyarsa sannan yayiwa motar key sai Nasarawa
G.R.A.
wani tsalle Ruma tayi lokacin da M.t yabar parlourn,wani sanyi ta keji yana ratsa zuciyarta,ta
rasa dame zata fasalta farin cikin da ta keji,tabbas tana son M.t ba tun yau ba,ganin baima san
da duniyarta ha yasa ta hakura sai gashi Allah ya kawo mata shi sama taka,dole ta gode
Allah,kuma dole ta zama jaruma kuma ta cire kunyar da take cikin zuciyarta ta riƙi M.t hannu
biyu da wannan tunanin tayi part ɗinta.
Mamu,Payal,Dina suna zaune a parlour suna kallan wani indian series mai suna when all is
gone,M.t yayi sallama gaba ɗaya suka juya suna kallonsa,ganinsa ɗauke da Diya a kafaɗa
Mamu ce tace.
"ita kuma lafiya?ka ɗau kota haka?" baice komai ba saida ya sami sofa ya kwantar da ita,harzai
cire hijab ɗin jikinta sabida yadda take gomi sai kuma ya fasa gudun A.S ya ƙaro sannan ya
ƙarasa wajan Mamu ya ɗora kansa a cinyarta,hannu tasa ta shafi sumar kansa,wani daɗi yaji
yana ratsa shi nan ya fara sauke ajjiyar zuciya,baki ya buɗe ya fara magana cikin slow voice
yace.
"Mamu barka da gida?" kallon Dina tayi yadda ta kasa ɗauke idonta daga kan M.t,sannan tace.
"yauwa,har adawo daga zancan?ita kuma daga rakiya sai bacci?"
"Eh"kawai yace ya tashi ya fara taga step ɗin benen yayi hanyar part ɗinsa.
A 1 week letter
Zuwa yanzo M.t bazai iya faɗin abinda ya keji game da Ruma ba,ya yarda da Auran tane ko zai
daina jin abinda ya keji,amma ina abin yaci tura,saidai yanzo baya bawa zuciyarsa damar
tunani kamar yadda ta keso,shiyasa ya samu ciwon daya keji a cikin zuciyarsa ya rago.
Zaune take a parlour ita da wani matashin saurayi daka ganinsa kasan ya haɗa jini da
sarauta,ita sam bata san shiba,banda Mamu tayi mata faɗa da baza ta zoba,yan zoma shi kaɗai
yake surutunsa,bata cewa komai daga Eh sai a'a,ɗan lan gwaɓar da kai sultan yayi yace.
"haba Diya for now ya kama ta ace kin fahimci sonda nake maki bada wasa ba,ki daina tunanin
wai ke makauniya ce ada ai ba haka kike ba,kuma komai na Allah yana da nasa lokacin,abinda
nakeso ki tsaya ki fahimta yadda nake sonki pls beby"
Shuru tayi babu amsa,sultan ji yayi kamar yayi kuka sabida yadda ya keji game da Diya,hannu
yasa da niyar juyo da fuskarta izuwa gare shi,kamar daga sama yaji an riƙe masa hannunsa..
*wane ya riƙewa sultan hannu?,menene muhimmancin Ruma a zuciyar M.t?shin Auran M.t da
Ruma zai yiwu?*