Showing 1 words to 3000 words out of 3810 words
Chapter 1 - JARABAWAR DA AKAIWA SARKIN BARAYI NOMAU, littafin Magana Jari Ce .pdf
 JARABAWAR DA AKAIWA SARKIN BARAYI NOMAU 
Cigaban Labarin Sarkin Noma da 'ya'yansa. 
 
Littafi: Magana Jarice 2 
Mawallafi: Alhaji Abubakar Imam 
arewanovels.com.ng 
 
Da gari ya waye Sarki ya aika Sarkin Noma ya zo da shi  da Nomau, ya ce masa, “Tun da ka ce 
sata ce ka ke takama da ita, in za ka shiga cikin maneman ’yata, zan jarraba ka da abu hudu. In 
ka kasa ko daya na kashe ka, don fa ka zo yi mini sata ne. Ka yarda?” 
 
Sarki ya ce, “Gobe ka zo ka sace zobena. Ga shi nan zan ajiye shi bisa tebur da rana ana 
fadanci. Ba na ko yarda da a yi layar zana.” 
 
Nomau ya ce, “To, Allah ya kai mu.” Ya yi ban kwana ya tafi. 
 
Mutane suka ce, “Ai ko gobe muna shirin ganin bidiri yadda za a saci zobe da rana gata 
gabammu muna ji muna gani, ba da ko an yi laya ba.” 
 
Kashegari Sarki ya fidda zobe ya ajiye a tebur, mutane suka kewaye ana ta fadanci. Sun 
tabbata zoben ba ya satuwa. Suna nan zaune sai ga wani tsoho da sanho a rike, ya leko 
Majalisan nan, yana bara yana cewa, “Allah ya bu ku na Allah, Allah ya sa mu cikin cetattu.” 
 
Da wani bafade ya gan shi sai ya buga masa tsawa ya ce “Kai, tafi daga nan, ba ka san nan 
fada ba ce? Tsufa hauka ne?” 
 
Sarki  ya ce,  “Kyale shi  ya yi ta yi, ai yanzu shi dai dai  ya ke da yaro.” Sai tsohon nan ya 
kaikaici idonsu ya saki zomo a zauren. Da ganinsa sai fadawa suka ce, “Ihu, ga zomo! Ihu, ga 
zomo!” Sarki  ya ce, “Kai,  ku  kyale shi,  ku lura da abin da ku  ke yi.” 
 
Sai tsohon nan kuma  ya sake sakin gudan.  Fadawa  suka ce,  “Ai, ga wani , ga wani! Ashe 
biyu ne! Ai ko firda-firda ne. Watakila ko da mace da namiji ne, sa yi raha a gwama su da 
naman dajin da Sarki ke kiwo.” 
 
Sarki  ya ce,  “Har yau ko  ban  ta6a  kiwonsu  ba.  Amma  dai kuci gaba da aikinku" tsohon nan 
na nan tsaye na ta bara,  ya  sake sakin guda. 
 
Sarki ya yi wuf ya tashi,  ya  ce,  “Ku  tara  a  kama  su, in gama cikin wadanda nake kiwo.” 
Mutane suka tashi suna bin  zomaye cikin gida su kama,  suka  bar  zobe nan  bisa  tebur. Da  
suke kama zomayen suka dawo. Ko da Sarki ya zo ya duba tebur, sai ya yi salati, ya ce, “Wa ya 
dauki zoben da ke nan yanzu yanzu?” Ba wanda ya amsa. Duk fadawa  suka shiga 
lalabe-lalabe cikin  qura ba zobe ba dalilinsa.
Can  da  azahar   sai  ga  Nomau   ya  zo  da  zoben  Sarki,   ya   yi gaisuwa ya ce,  “Ga   shi, 
Allah ya ba ka  nasara.” 
 
Sarki ya karbi zobe ya duba,  ya ga dai nasa ne,  ya ce, “Karya dai ka ke yi, layar zana ka yi ka 
zo ka dauka, an ko ce ban da layar zana.” 
 
Nomau ya ce, “Ba layar zana na  yi  ba,  Allah  ya ba ka nasara. Ni ne na yiwo shiri kamar 
tsoho, na zo ina bara a wajenku dazun da hantsi, na saki zomaye don ku bi. Wannan ai ba wani 
abu ba ne.  Sai  ka fadi  na biyu.” 
 
Sarki ya huta, ya ce, “To, yau da dare ka zo ka sace gunya din nan nawa Dan-tsito.” 
 
Sarkin Barayi Nomau ya yi gaisuwa ya fita ya tafi gida, ’yan’uwansa suka yi ta yi masa dariya. 
 
Tun kafin rana ta fadi ya je ya sami  tulun  giya  ya sayo ya ajiye.  Da dare ya raba, ya yi shiri  
kamar  ’yar  tsohuwa,  ya  dauki  tulun giya ya nufi gidan Sarki. Kafin  ya  kai  hadarin  ruwa  ya  
taso,  ruwa ya yi ta dukansa, ya isa  gidan  sarki  tsamo-tsamo  yana makyarkyata. Da isarsa sai 
ya tarad da Sarki ya sa dogarai takwas na tsare da Dantsito, ko wanensu ga  baka  da  kwari  
rataye.  Ya tarad da hudu daga cikinsu kowa ya kama qafar dokin nan guda  ya rike. Daya ya sa 
masa ragama ya rike, ga wani can kame da wutsiya, wannan kuwa  ya  kama  dokin  ya  dare.  
Guda  kuwa,  watau babbansu, shi sai kewayar gida  ya  ke  yi  yana  gadi.  Da  ya fito wajen 
zauren barga yana leqe, sai  ya  ga  ’yar  tsohuwa  da kayan tulu duk ta  jika,  sai  makyarkyata  
ta  ke  yi,  haqora  na  qaf qaf qaf, ga ta tsugunne gindin katanga daga  waje.  Sai  ya  fito  ya 
daka  mata  tsawa,  “Ke   tsohuwa,  ina za ki?” 
 
Yar tsohuwa ta durkusa jiki na rawa, ta gigice, ta ce wa dogarin nan, “Na fito kasuwa ne, dare ya 
yi mini, har na sha kashin ruwa, shi ya sa na ra6o in la6e. Giya na kawo kasuwa tun daga 
qauye, ga shi na yiwo dare ba ta sami kasuwa ba.” 
 
Dogari ya matsa ya kwace tulun giya, ya kafa kai kwakwal kwakwal, wai  ya  yi maganin  barci.  
Bai san giyan  nan akwai  banju a ciki ba. Tsohuwa ta ce, “Don Allah yi hankali kada ka fasa 
mini tulu.” 
 
Dogari ya harare ta, ya ce, “Tulun banza!  Wane tulu  ke gare ki?” Ya sami giya ya kyankyama 
dayan cikinsa, sa’an nan ya koma gefe guda ya kishingide, wai ya shakata sa’an nan ya shiga 
wajen aikinsa.  Can   sai  kafirar  ta  fara  dibarsa  yana  tangadi,   kafin  a  yi haka banju ya taso 
ya shiga aikin nasa, sai barci. Tsohuwan nan da ta ga ya yi barci ta tashi sannu kan hankali, ta 
tube rigar dogarin nan da rawaninsa ta sa, ta dauki umararsa ta rike, ta nufi inda dogaran nan 
ke qumun Dantsito, ta ce musu kamar ita ce dogarin, “Ba ku sani ba fa, fitan nan tawa sai da na  
gamu  da ja’irin, na dana kibiya zan dirka masa, ya fadi  yana  roqona  gafara. Tausayi ya kama 
ni na kyale shi, bayan na sa ya rantse ba ya dawowa. Mai so duk ya yi ta barcinsa, ba kome. 
Kuma in wani na tsoron wani abu, ko Sarki ya tambaye ku da safe ku ce ni na ce ku yi. In ko 
kun fi so ku yi ta zama, ku yi ta yi, ni dai don sule ashirin da biyar ba na  wahal da  kaina,  kun 
ga  kwanciyata.”  Sai ya  bingire kamar  yana barci.
Sauran dogarai sun samu babbansu ya ce ko wani abu ya faru  da safe su ce shi ne, to, me ya 
dame su? Sai suka yi ta gyangyadi nan har da minshari. Da Nomau ya ji sun  fara  jan  rago sai  
ya tashi ya fita waje ya dauko kayan da ya hoye, ya sa itatuwa hudu masu gwafa ya gina rami 
ya kafa su, biyu baya, biyu gaba, ya aza wadansu itatuwa bisa kamar masaqa, ya ciccibi wanda 
ke bisan dokin nan ya aza bisa itatuwa, ga shi yana gyangyadi bai sani ba. Ya dauki igiyoyi ya 
daura wa itatuwan nan: Dogarin da ke rike da wutsiya,  da mai riqe da  ragama,  ya ba su suka 
rike igiyoyin  dai dai, suna barci ba su sani ba. Wadanda ke rike kafafuwan ko wanne ya ba shi 
icen nan guda ya rike. Shi kuwa ya kwance dokin, ya daura masa tsumma a kofato, ya ja ya 
surare da shi, ya bar dogarawa nan na ta sharar gyangyadi, Sarkin Dogarai kuwa babbansu na 
kofar gida, giya ta buge shi. 
 
Da gari ya waye Sarki ya bude gida ya tarad da yadda Nomau ya yi wa zababbun 
dogarawansa, abin kuma ya wuce na ban haushi, sai ya bushe da dariya. Ya ra6a ya fita, ya bar 
su  nan  kowa na ta sharar barci, wadansu da ice a hannu, wadansu da igiyoyi sun rike. Ya aika 
aka ta da Waziri, suka zo suka yi ta dariya. Sa’an nan Sarki ya dauki bulala ya yi ta tsala musu, 
’suka farka suna ta zurawa a guje. 
 
Hantsi ya yi sai ga Nomau da Tlantsito yana janye, ya kawo wa Sarki. Sarki ya fusata, ya ce, 
“Yau da dare ka shigo turakata ka sace bargon da na ke kwance sama. Zan hada bindiga, in ka 
zo ko in kashe ka. Yau ko na ke so ka zo, ban ce gobe ba ko jibi. Ba na sa kowa gadinka.” 
 
Sarkin Barayi Nomau ya ce, “Allah ya kai mu.” Ya mike tsaye ya ce, “Sai ni daki bari na Sarkin 
Noma, kushewar  badi  sai  badi!”  Ya sallami Sarki ya tafi. 
 
Magariba na yi ya tafi hurumi, ya duba wani sabon kabari ya tone, ya dauko gawar ya kawo 
gida, ya sami tsani ya gama ya boye. Can da dare ya tashi ya dauki gawan nan da tsanin, ya 
nufi gidan Sarki ya shiga. Ya tasam ma turakarsa ya tarad da  taga bude, ga fitila na ci kamar 
rana. Sai ya jingina tsani daidai taga,  ya dauki gawan nan ya sa6a a kafada ya-kama hawan 
tsani da ita. Can kan gawa ya kai daidai da taga sai Sarki ya gan shi, ya aune shi da bindiga 
kwararam, ya sami gawa a ka. Sai’ Sarkin Barayi ya saki gawan nan kasa tim. 
 
Sarki ya ce wa uwargida da ke nan tare da shi, “Haba kin ji na kashe shi, kowa ya huta. Amma 
fa a ce ’yar cikina ta rasa wanda za ta aura sai 6arawo, ai kin san da sake! Sai ya tashi ya dauki 
fitila, ya biyo matakin soro ya gangaro ya gani. 
 
Sa’ad da yana gangarowa sai Sarkin Barayi ya shiga ta taga,  ya ce wa matar Sarki, “Miqo mini 
bargon nan da mu  ke kwance kai  in yafa, wannan luru bai ishe ni ba, dari! Haba, abu yau sai 
ka ce daren nan jaura ke wucewa.” 
 
Abu cikin duhu, matar na tsammani Sarki ne, ta dauki bargo daga kan gado ta durkusa ta ba 
shi, ta ce, “Mun dai huta da  wannan   qanqama.”
Nomau ya ce, “Da ma daga an kyale shi, ai rashin jini rashin tsagawa.” Yana nan kamar yana 
gyarawa, da ya ji Sarki na hawowa shi kuma sai ya sake bin ta taga ya fita da bargon. 
 
Da Sarki ya hawo da fitila sai ya ce wa matar, “Na kashe shi, amma na ga kamar ba shi ba ne, 
don wannan  har yana da gemu, shi kuwa saurayi ne, bai isa tsai da gemu ba. Watakila  ja’irin 
ne  ya rikide.” 
 
Matar ta ce, “Ya aika.” 
 
Sarki ya duba bai ga bargo ba, ya ce wa matar. “Ina   bargo?” 
 
Matar ta ce, “Wane  bargo kuma  ban da wanda  ka zo ka  karba yanzu?” 
 
Sarki ya ce, “Yaushe na zo na kar6i  bargo?” 
 
Matar ta bayyana masa yadda aka yi. Ko da ya ji haka sai ya yi salati, ya san abin da ya faru. 
Da gari ya waye ya gaya wa Waziri. Suna nan sai ga Sarkin Barayi ya zo da bargo, ya yi 
gaisuwa ya mika wa Sarki, ya yi sallama ya koma gida ya bar su nan suna kakabi.  
 
Suna nan saí Limamin garin da ladaninsa  suka zo gaisuwa. Da suka  ji abubuwan  da  Nomau  
ya aikatawa sarki,  sai .haushi ya kama Liman, ya dubi Sarki, ya ce, ‘“Allah ya ba ka nasara 
wannan labari ai bai kamata mu bari wadansu suji   ba, kada ayi mana dariyar wauta. Abunki ne 
kuke yi kullum ba shawara sai kace wai komai waziri ya gaya maka ya isa. Mutum guda ya ta6a 
shawara shi kadai? Da kun sanad da ni wannan abu, habawa! Nomau din banza, ba cikin ’yan 
shekarun nan muka gama share masa majina ba?” Ya dai sami Sarki nan ya yi ta yi masa 
qanqanci. Ga shi  ya  tsufa,  saboda  haka  Sarki ke  raga  masa, shi ko bai sani raga masa a ke 
yi ba, yana neman ya wuce gona da iri. 
 
Liman ya fita ya bar Sarki  na cizon  yatsa,  sai ga Sarkin Barayi  ya shigo. Sarki ya dube shi a 
fusace, ya ce masa, “Yau da dare ka sato mini Liman, ka kawo mini shi nan gobe da safe! 
Aikinka na hudu ke nan.” 
 
Sarkin Barayi ya ce, “Don wannan  ta  kwana  gidan sauqi,  ni ban ci sarautar 6arayi ba sai da 
na shirya.”  Ya yi gaisuwa ya fice. 
 
Da isarsa  gida ’yan’uwa  suka  ji abin  da  ya faru, sai suka  ce, “Ku  bar shi, ai  ba  hullum  a ke 
kwana a gado ba. Yau  ko shi  ne Gwamnan Barayi, ba Sarkin Barayi ba, ma ga yadda zai yi ya 
saci mutum.” 
 
Sarkin Barayi dai bai ce musu kome ba, sai ya fita bakin rafi da wani sanho, ya yi ta neman 
qaguwa yana kamawa yana zubawa cikin sanho. Da ya cika shi fal da kaguwa sai ya dauko ya 
kawo gida ya boye. Ya tafi kasuwa ya sawo kyandir dauri dauri. Ya kuma sawo katuwar waga ya 
kawo ya gama ya ajiye. Can  da tsakad dare sai ya tashi ya nufi masallaci da kayan nan nasa. 
To, masallacin kuwa yana kusa da gidan Liman ne. Da shigarsa masallacin sai ya yi ta fid da
qaguwoyin nan yana likawa ko wannensu kyandir, yana kunna wuta daga bisa kamar fitila, ya bi  
su duka ya lilliqa, ya sake su nan cikin masallaci suna yawo. Sa’an nan ya tashi ya kama kiran 
salla, bayan ya bi jikinsa ya nade qal da wani farin zawwati. 
 
Da Liman ya ji kiran salla sai ya fito yana tsammani ladan ya rude ne. Da shigowarsa masallaci 
sai ya ga masallacin duk ya haske, ga wadansu halicce-halicce kamar dari sai yawo su ke yi da 
fitilu suna ci bayansu. Ga wani mutum kuma fari fat  yana  jan tasbi. Liman ya ja da baya ya 
buga salati, zai ruga sai Nomau ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, wajenka aka aiko ni, an ce ba 
don kai ba zunubin mutanen garin nan ya isa a kife su. Saboda  haka aka  ce in zo in tafi da kai, 
don mutane su ga misali daga gare ka, su kara lura da al’amarin  addini.” 
 
To, Allah ya ba ka nasara, ban taba ganin jahilin Liman irin wannan ba. Da ma ba Musulmin 
asali ba ne, irin mujusan nan ne da suka tsinci Musulunci da rana tsaka. Sai ya yarda da 
maganar Nomau,  ya durqusa gabansa  ya ce, “To.” 
 
Sarkin 6arayi Nomau ya dauko waga, ya ce, “Ga abin da aka umurce ni in dauke ka ciki, in tashi 
da kai zuwa sama. Shiga ciki ka yi ta salati, in ina tashi da kai.” 
 
Liman na rawar jiki ya kama waga ya shige ya dunqule. Sarkin Barayi ya bi bakin waga ya rufe, 
ya sa igiya ya layyace ram yadda Liman ko ya so fitowa ba ya iya yi. Ya daura wa wage igiya, 
ya yi ta janta ya nufi gidansa kuwuwuwu. Liman tun  yana salati  har zafi ya sa ya kasa. in sun 
fada dutse Liman ya ji bugunsa ya buge sai ya ce, “M.”  
Sarkin Barayi ko sai ya ce, “Yi shiru! Nan sama ta biyu mu ke, mun wuce sama ta daya tuni.” 
 
Da suka fada wani kwari, waga ta birkice, bakin Liman ya bugi kasa qumus, ya ji zafi har ya yi 
kara,  “Wayyo!” 
 
Sarkin Barayi ya ce, “Yi shiru! Yi ta salati mana, mun kawo sama ta hudu.” 
 
Kai, ya Allah ka kiyashe mu da aikin jahilci! Can Nomau na ta tikar gudu da shi wai yana tashi, 
sai suka tarad da wani tabki. Nomau ya ji kwadi na ta kuka kwa, kwa, kwa, cikin tabki, sai ya ce, 
“An kawo sama ta biyar, ka ji ana yi maka maraba. Kai dai yi ta   salati.” 
 
Liman ya taqarqare da sâlati. Can bayan an jima suka isa gidan su Nomau, ya buda sakin 
tattabarunsu ya tura Liman ciki ya rufe. Tattabaru suka yi fafafafafafa. Sarkin Barayi ya ce, 
“Kwanta kurum ka yi ta salati, har Sarki ya ba da izni in isa da kai. Nan inda ka ke sama ta 
bakwai ke nan, wannan motsin da ka ke ji Mala’iku ne masu tashi ke maka maraba. Za ka ji 
suna wani abu bu, bu, ku, bu, bu, irin harshensu ke nan kamar na tattabaru. Ni zan tafi in nemo 
iznin isa da kai.” Nomau ya tafi ya bar jahili nan yana ta salati, shi kuwa ya je ya yi ta shara 
barcinsa. 
 
Da gari ya waye ya taho ya bude dakin tattabaru ya jawo shi, ya ce, “An ce in









