Showing 3001 words to 3810 words out of 3810 words

Chapter 2 - JARABAWAR DA AKAIWA SARKIN BARAYI NOMAU, littafin Magana Jari Ce .pdf

isa da kai. In ka
lura ka ga annuri ya sake, ba kamar na yadda muka baro duniya ba.” Ya yi ta jansa har gidan

Sarki. Ya yi gaisuwa. Liman na ta alla-alla a bude shi ya ga abin da zai gani. Sarkin Barayi ya ce
wa Sarki, “Ga wata ’yar gaisuwa irin tamu na kawo maka. Sai ka buda da kanka ka gani.”

Sarki ya tashi ya buda waga, sai ga Liman ciki ido wuri wuri, da tasbaha a hannu yana salati
yadda Sarkin 6arayi ya ce ya yi. Ko da Sarki ya gan shi haka bai san sa’ad da ya 6arke da
dariya ba. Mutane suka yi kamar za su suqe don dariya. Sarki ya kama Sarkin Barayi, ya
cire hular da ke kansa da rawaninsa ya nada masa, ya ce, “ Na tabbatad da sarautarka ta
6arayi. Batun aure kuma sai mun yi shawara tsakaninka da ’ya’yayenka.” Don kunya
Limamin nan ya kasa fitowa sai da aka kama shi aka kai shi gidansa.

Da aka watse Sarki ya dubı Waziri, ya ce, “To, Waziri, baki fa shi kan yanka wuya. Yaya ke
nan?”

Waziri ya ce, “Ba yadda za a yi sai mu san yadda za mu yi mu rarrashi sauran su dangana, mu
kuwa mu ba Kosau. Don wanda ya gina wannan gida cikin dare guda, ba mai jayayya da shi.”

Sarki ya ce, “Gaskiyarka, sai mu aika Sarkin Noma ya zo da su, su duka.” Da aka zo da su
Sarki ya shiga rarrashin Jimrau da Nomau su yarda kosau ya auri ’yar tasa. Jimrau ya ce ya
yarda. Nomau ya ce shi faufau ba ya yardam masa, sai dai in za a hana shi da karfi a hana shi,
ya san Sarki ya bar batun adalci.
Da Sarki ya ji haka sai ya dubi Waziri. Waziri ya fusata da maganan nan ta Nomau, ya dube shi,
ya ce, “Mece ce sana’arka?”

Ya ce, “Sata.”

Waziri ya ce, “To, kai ko a ranka ka ga ya yiwu a ce ’yar Sarki ta rasa wanda za ta aura sai
6arawo? In dai mu muka haifi ’yarmu, to, mun ba kosau.” Duk fada ta watse. Daga nan aka
tafi aka yi ta shagalin biki.

Da gari ya waye Sarakuna suka taru za a daura aure, sai Sarki ya ce wa Sarkin Gida ya je
taska ya dauko masa kayansa na ado, da lambobinsa na girma. Sarkin Gida ya ruga. Jim ya
dawo a guje, duk ya rude, jiki na rawa, ya fadi gaban Sarki, ya ce, “Allah ya ba ka
nasara, ai duk taskokin nan na tutafi ba sauran ko kyalle yau, sai wannan tsohon bargo da a
ke daure alkyabbu.”

Mutane duk suka yi zugudun suna jin abin mamaki, Sarki zai bude baki ya yi magana sai ga
ma’aji kuma a guje rawani a hannu ya zube gaban Sarki, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ka ji
qaina, na tuba, na bi ka!”

Mutane suka ce, “Me ya faru haka?”

Ma’aji ya ce, “Ai yau baitulmali 6arayi sun yi masa kat, ban da ahu da na tarar bakin qofa ba
abin da aka bari !’

Yana cikin ba da labari kuma sai ga Sarkin Zagi ya zubo a guje ya nufo fada, ba ko wando.
Shantali zai yi masa magana sai ya ga ya durkusa gaban Sarki, ya ce, ,“Allah ya ba ka nasara,
ai barga yau ba sauran doki, duk an sace!”

Sarki ya mike tsaye, sai kuma ga Jakadiya ta fito daga cikin gida, ta durqusa, ta ce wa Sarki,
“Mun taru za a yi wa amarya kunshi, mun duba, qasa da bisa cikin gidan nan duk ba mu gan
ta ba.”

Sai aka ga Sarki ya yi shiru. Can ya dubi dogarawa baki na rawa, ya ce, “Ku yi maza ku zo
mini da Nomau!” Dogarawa suka zuba a guje suka nufi gidan Sarkin Noma. Jim kadan suka
dawo, suka ce, “Ai an ce rabonsa da gida tun jiya da dare.” Sarki ya baza mutane cikin
kasa aka yi ta nema, amma ko duriyarsa ba a ji ba.

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login