Showing 1 words to 3000 words out of 3810 words

Chapter 1 - JARABAWAR DA AKAIWA SARKIN BARAYI NOMAU, littafin Magana Jari Ce .pdf

JARABAWAR DA AKAIWA SARKIN BARAYI NOMAU
Cigaban Labarin Sarkin Noma da 'ya'yansa.

Littafi: Magana Jarice 2
Mawallafi: Alhaji Abubakar Imam
arewanovels.com.ng

Da gari ya waye Sarki ya aika Sarkin Noma ya zo da shi da Nomau, ya ce masa, “Tun da ka ce
sata ce ka ke takama da ita, in za ka shiga cikin maneman ’yata, zan jarraba ka da abu hudu. In
ka kasa ko daya na kashe ka, don fa ka zo yi mini sata ne. Ka yarda?”

Sarki ya ce, “Gobe ka zo ka sace zobena. Ga shi nan zan ajiye shi bisa tebur da rana ana
fadanci. Ba na ko yarda da a yi layar zana.”

Nomau ya ce, “To, Allah ya kai mu.” Ya yi ban kwana ya tafi.

Mutane suka ce, “Ai ko gobe muna shirin ganin bidiri yadda za a saci zobe da rana gata
gabammu muna ji muna gani, ba da ko an yi laya ba.”

Kashegari Sarki ya fidda zobe ya ajiye a tebur, mutane suka kewaye ana ta fadanci. Sun
tabbata zoben ba ya satuwa. Suna nan zaune sai ga wani tsoho da sanho a rike, ya leko
Majalisan nan, yana bara yana cewa, “Allah ya bu ku na Allah, Allah ya sa mu cikin cetattu.”

Da wani bafade ya gan shi sai ya buga masa tsawa ya ce “Kai, tafi daga nan, ba ka san nan
fada ba ce? Tsufa hauka ne?”

Sarki ya ce, “Kyale shi ya yi ta yi, ai yanzu shi dai dai ya ke da yaro.” Sai tsohon nan ya
kaikaici idonsu ya saki zomo a zauren. Da ganinsa sai fadawa suka ce, “Ihu, ga zomo! Ihu, ga
zomo!” Sarki ya ce, “Kai, ku kyale shi, ku lura da abin da ku ke yi.”

Sai tsohon nan kuma ya sake sakin gudan. Fadawa suka ce, “Ai, ga wani , ga wani! Ashe
biyu ne! Ai ko firda-firda ne. Watakila ko da mace da namiji ne, sa yi raha a gwama su da
naman dajin da Sarki ke kiwo.”

Sarki ya ce, “Har yau ko ban ta6a kiwonsu ba. Amma dai kuci gaba da aikinku" tsohon nan
na nan tsaye na ta bara, ya sake sakin guda.

Sarki ya yi wuf ya tashi, ya ce, “Ku tara a kama su, in gama cikin wadanda nake kiwo.”
Mutane suka tashi suna bin zomaye cikin gida su kama, suka bar zobe nan bisa tebur. Da
suke kama zomayen suka dawo. Ko da Sarki ya zo ya duba tebur, sai ya yi salati, ya ce, “Wa ya
dauki zoben da ke nan yanzu yanzu?” Ba wanda ya amsa. Duk fadawa suka shiga
lalabe-lalabe cikin qura ba zobe ba dalilinsa.

Can da azahar sai ga Nomau ya zo da zoben Sarki, ya yi gaisuwa ya ce, “Ga shi,
Allah ya ba ka nasara.”

Sarki ya karbi zobe ya duba, ya ga dai nasa ne, ya ce, “Karya dai ka ke yi, layar zana ka yi ka
zo ka dauka, an ko ce ban da layar zana.”

Nomau ya ce, “Ba layar zana na yi ba, Allah ya ba ka nasara. Ni ne na yiwo shiri kamar
tsoho, na zo ina bara a wajenku dazun da hantsi, na saki zomaye don ku bi. Wannan ai ba wani
abu ba ne. Sai ka fadi na biyu.”

Sarki ya huta, ya ce, “To, yau da dare ka zo ka sace gunya din nan nawa Dan-tsito.”

Sarkin Barayi Nomau ya yi gaisuwa ya fita ya tafi gida, ’yan’uwansa suka yi ta yi masa dariya.

Tun kafin rana ta fadi ya je ya sami tulun giya ya sayo ya ajiye. Da dare ya raba, ya yi shiri
kamar ’yar tsohuwa, ya dauki tulun giya ya nufi gidan Sarki. Kafin ya kai hadarin ruwa ya
taso, ruwa ya yi ta dukansa, ya isa gidan sarki tsamo-tsamo yana makyarkyata. Da isarsa sai
ya tarad da Sarki ya sa dogarai takwas na tsare da Dantsito, ko wanensu ga baka da kwari
rataye. Ya tarad da hudu daga cikinsu kowa ya kama qafar dokin nan guda ya rike. Daya ya sa
masa ragama ya rike, ga wani can kame da wutsiya, wannan kuwa ya kama dokin ya dare.
Guda kuwa, watau babbansu, shi sai kewayar gida ya ke yi yana gadi. Da ya fito wajen
zauren barga yana leqe, sai ya ga ’yar tsohuwa da kayan tulu duk ta jika, sai makyarkyata
ta ke yi, haqora na qaf qaf qaf, ga ta tsugunne gindin katanga daga waje. Sai ya fito ya
daka mata tsawa, “Ke tsohuwa, ina za ki?”

Yar tsohuwa ta durkusa jiki na rawa, ta gigice, ta ce wa dogarin nan, “Na fito kasuwa ne, dare ya
yi mini, har na sha kashin ruwa, shi ya sa na ra6o in la6e. Giya na kawo kasuwa tun daga
qauye, ga shi na yiwo dare ba ta sami kasuwa ba.”

Dogari ya matsa ya kwace tulun giya, ya kafa kai kwakwal kwakwal, wai ya yi maganin barci.
Bai san giyan nan akwai banju a ciki ba. Tsohuwa ta ce, “Don Allah yi hankali kada ka fasa
mini tulu.”

Dogari ya harare ta, ya ce, “Tulun banza! Wane tulu ke gare ki?” Ya sami giya ya kyankyama
dayan cikinsa, sa’an nan ya koma gefe guda ya kishingide, wai ya shakata sa’an nan ya shiga
wajen aikinsa. Can sai kafirar ta fara dibarsa yana tangadi, kafin a yi haka banju ya taso
ya shiga aikin nasa, sai barci. Tsohuwan nan da ta ga ya yi barci ta tashi sannu kan hankali, ta
tube rigar dogarin nan da rawaninsa ta sa, ta dauki umararsa ta rike, ta nufi inda dogaran nan
ke qumun Dantsito, ta ce musu kamar ita ce dogarin, “Ba ku sani ba fa, fitan nan tawa sai da na
gamu da ja’irin, na dana kibiya zan dirka masa, ya fadi yana roqona gafara. Tausayi ya kama
ni na kyale shi, bayan na sa ya rantse ba ya dawowa. Mai so duk ya yi ta barcinsa, ba kome.
Kuma in wani na tsoron wani abu, ko Sarki ya tambaye ku da safe ku ce ni na ce ku yi. In ko
kun fi so ku yi ta zama, ku yi ta yi, ni dai don sule ashirin da biyar ba na wahal da kaina, kun
ga kwanciyata.” Sai ya bingire kamar yana barci.

Sauran dogarai sun samu babbansu ya ce ko wani abu ya faru da safe su ce shi ne, to, me ya
dame su? Sai suka yi ta gyangyadi nan har da minshari. Da Nomau ya ji sun fara jan rago sai
ya tashi ya fita waje ya dauko kayan da ya hoye, ya sa itatuwa hudu masu gwafa ya gina rami
ya kafa su, biyu baya, biyu gaba, ya aza wadansu itatuwa bisa kamar masaqa, ya ciccibi wanda
ke bisan dokin nan ya aza bisa itatuwa, ga shi yana gyangyadi bai sani ba. Ya dauki igiyoyi ya
daura wa itatuwan nan: Dogarin da ke rike da wutsiya, da mai riqe da ragama, ya ba su suka
rike igiyoyin dai dai, suna barci ba su sani ba. Wadanda ke rike kafafuwan ko wanne ya ba shi
icen nan guda ya rike. Shi kuwa ya kwance dokin, ya daura masa tsumma a kofato, ya ja ya
surare da shi, ya bar dogarawa nan na ta sharar gyangyadi, Sarkin Dogarai kuwa babbansu na
kofar gida, giya ta buge shi.

Da gari ya waye Sarki ya bude gida ya tarad da yadda Nomau ya yi wa zababbun
dogarawansa, abin kuma ya wuce na ban haushi, sai ya bushe da dariya. Ya ra6a ya fita, ya bar
su nan kowa na ta sharar barci, wadansu da ice a hannu, wadansu da igiyoyi sun rike. Ya aika
aka ta da Waziri, suka zo suka yi ta dariya. Sa’an nan Sarki ya dauki bulala ya yi ta tsala musu,
’suka farka suna ta zurawa a guje.

Hantsi ya yi sai ga Nomau da Tlantsito yana janye, ya kawo wa Sarki. Sarki ya fusata, ya ce,
“Yau da dare ka shigo turakata ka sace bargon da na ke kwance sama. Zan hada bindiga, in ka
zo ko in kashe ka. Yau ko na ke so ka zo, ban ce gobe ba ko jibi. Ba na sa kowa gadinka.”

Sarkin Barayi Nomau ya ce, “Allah ya kai mu.” Ya mike tsaye ya ce, “Sai ni daki bari na Sarkin
Noma, kushewar badi sai badi!” Ya sallami Sarki ya tafi.

Magariba na yi ya tafi hurumi, ya duba wani sabon kabari ya tone, ya dauko gawar ya kawo
gida, ya sami tsani ya gama ya boye. Can da dare ya tashi ya dauki gawan nan da tsanin, ya
nufi gidan Sarki ya shiga. Ya tasam ma turakarsa ya tarad da taga bude, ga fitila na ci kamar
rana. Sai ya jingina tsani daidai taga, ya dauki gawan nan ya sa6a a kafada ya-kama hawan
tsani da ita. Can kan gawa ya kai daidai da taga sai Sarki ya gan shi, ya aune shi da bindiga
kwararam, ya sami gawa a ka. Sai’ Sarkin Barayi ya saki gawan nan kasa tim.

Sarki ya ce wa uwargida da ke nan tare da shi, “Haba kin ji na kashe shi, kowa ya huta. Amma
fa a ce ’yar cikina ta rasa wanda za ta aura sai 6arawo, ai kin san da sake! Sai ya tashi ya dauki
fitila, ya biyo matakin soro ya gangaro ya gani.

Sa’ad da yana gangarowa sai Sarkin Barayi ya shiga ta taga, ya ce wa matar Sarki, “Miqo mini
bargon nan da mu ke kwance kai in yafa, wannan luru bai ishe ni ba, dari! Haba, abu yau sai
ka ce daren nan jaura ke wucewa.”

Abu cikin duhu, matar na tsammani Sarki ne, ta dauki bargo daga kan gado ta durkusa ta ba
shi, ta ce, “Mun dai huta da wannan qanqama.”

Nomau ya ce, “Da ma daga an kyale shi, ai rashin jini rashin tsagawa.” Yana nan kamar yana
gyarawa, da ya ji Sarki na hawowa shi kuma sai ya sake bin ta taga ya fita da bargon.

Da Sarki ya hawo da fitila sai ya ce wa matar, “Na kashe shi, amma na ga kamar ba shi ba ne,
don wannan har yana da gemu, shi kuwa saurayi ne, bai isa tsai da gemu ba. Watakila ja’irin
ne ya rikide.”

Matar ta ce, “Ya aika.”

Sarki ya duba bai ga bargo ba, ya ce wa matar. “Ina bargo?”

Matar ta ce, “Wane bargo kuma ban da wanda ka zo ka karba yanzu?”

Sarki ya ce, “Yaushe na zo na kar6i bargo?”

Matar ta bayyana masa yadda aka yi. Ko da ya ji haka sai ya yi salati, ya san abin da ya faru.
Da gari ya waye ya gaya wa Waziri. Suna nan sai ga Sarkin Barayi ya zo da bargo, ya yi
gaisuwa ya mika wa Sarki, ya yi sallama ya koma gida ya bar su nan suna kakabi.

Suna nan saí Limamin garin da ladaninsa suka zo gaisuwa. Da suka ji abubuwan da Nomau
ya aikatawa sarki, sai .haushi ya kama Liman, ya dubi Sarki, ya ce, ‘“Allah ya ba ka nasara
wannan labari ai bai kamata mu bari wadansu suji ba, kada ayi mana dariyar wauta. Abunki ne
kuke yi kullum ba shawara sai kace wai komai waziri ya gaya maka ya isa. Mutum guda ya ta6a
shawara shi kadai? Da kun sanad da ni wannan abu, habawa! Nomau din banza, ba cikin ’yan
shekarun nan muka gama share masa majina ba?” Ya dai sami Sarki nan ya yi ta yi masa
qanqanci. Ga shi ya tsufa, saboda haka Sarki ke raga masa, shi ko bai sani raga masa a ke
yi ba, yana neman ya wuce gona da iri.

Liman ya fita ya bar Sarki na cizon yatsa, sai ga Sarkin Barayi ya shigo. Sarki ya dube shi a
fusace, ya ce masa, “Yau da dare ka sato mini Liman, ka kawo mini shi nan gobe da safe!
Aikinka na hudu ke nan.”

Sarkin Barayi ya ce, “Don wannan ta kwana gidan sauqi, ni ban ci sarautar 6arayi ba sai da
na shirya.” Ya yi gaisuwa ya fice.

Da isarsa gida ’yan’uwa suka ji abin da ya faru, sai suka ce, “Ku bar shi, ai ba hullum a ke
kwana a gado ba. Yau ko shi ne Gwamnan Barayi, ba Sarkin Barayi ba, ma ga yadda zai yi ya
saci mutum.”

Sarkin Barayi dai bai ce musu kome ba, sai ya fita bakin rafi da wani sanho, ya yi ta neman
qaguwa yana kamawa yana zubawa cikin sanho. Da ya cika shi fal da kaguwa sai ya dauko ya
kawo gida ya boye. Ya tafi kasuwa ya sawo kyandir dauri dauri. Ya kuma sawo katuwar waga ya
kawo ya gama ya ajiye. Can da tsakad dare sai ya tashi ya nufi masallaci da kayan nan nasa.
To, masallacin kuwa yana kusa da gidan Liman ne. Da shigarsa masallacin sai ya yi ta fid da

qaguwoyin nan yana likawa ko wannensu kyandir, yana kunna wuta daga bisa kamar fitila, ya bi
su duka ya lilliqa, ya sake su nan cikin masallaci suna yawo. Sa’an nan ya tashi ya kama kiran
salla, bayan ya bi jikinsa ya nade qal da wani farin zawwati.

Da Liman ya ji kiran salla sai ya fito yana tsammani ladan ya rude ne. Da shigowarsa masallaci
sai ya ga masallacin duk ya haske, ga wadansu halicce-halicce kamar dari sai yawo su ke yi da
fitilu suna ci bayansu. Ga wani mutum kuma fari fat yana jan tasbi. Liman ya ja da baya ya
buga salati, zai ruga sai Nomau ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, wajenka aka aiko ni, an ce ba
don kai ba zunubin mutanen garin nan ya isa a kife su. Saboda haka aka ce in zo in tafi da kai,
don mutane su ga misali daga gare ka, su kara lura da al’amarin addini.”

To, Allah ya ba ka nasara, ban taba ganin jahilin Liman irin wannan ba. Da ma ba Musulmin
asali ba ne, irin mujusan nan ne da suka tsinci Musulunci da rana tsaka. Sai ya yarda da
maganar Nomau, ya durqusa gabansa ya ce, “To.”

Sarkin 6arayi Nomau ya dauko waga, ya ce, “Ga abin da aka umurce ni in dauke ka ciki, in tashi
da kai zuwa sama. Shiga ciki ka yi ta salati, in ina tashi da kai.”

Liman na rawar jiki ya kama waga ya shige ya dunqule. Sarkin Barayi ya bi bakin waga ya rufe,
ya sa igiya ya layyace ram yadda Liman ko ya so fitowa ba ya iya yi. Ya daura wa wage igiya,
ya yi ta janta ya nufi gidansa kuwuwuwu. Liman tun yana salati har zafi ya sa ya kasa. in sun
fada dutse Liman ya ji bugunsa ya buge sai ya ce, “M.”
Sarkin Barayi ko sai ya ce, “Yi shiru! Nan sama ta biyu mu ke, mun wuce sama ta daya tuni.”

Da suka fada wani kwari, waga ta birkice, bakin Liman ya bugi kasa qumus, ya ji zafi har ya yi
kara, “Wayyo!”

Sarkin Barayi ya ce, “Yi shiru! Yi ta salati mana, mun kawo sama ta hudu.”

Kai, ya Allah ka kiyashe mu da aikin jahilci! Can Nomau na ta tikar gudu da shi wai yana tashi,
sai suka tarad da wani tabki. Nomau ya ji kwadi na ta kuka kwa, kwa, kwa, cikin tabki, sai ya ce,
“An kawo sama ta biyar, ka ji ana yi maka maraba. Kai dai yi ta salati.”

Liman ya taqarqare da sâlati. Can bayan an jima suka isa gidan su Nomau, ya buda sakin
tattabarunsu ya tura Liman ciki ya rufe. Tattabaru suka yi fafafafafafa. Sarkin Barayi ya ce,
“Kwanta kurum ka yi ta salati, har Sarki ya ba da izni in isa da kai. Nan inda ka ke sama ta
bakwai ke nan, wannan motsin da ka ke ji Mala’iku ne masu tashi ke maka maraba. Za ka ji
suna wani abu bu, bu, ku, bu, bu, irin harshensu ke nan kamar na tattabaru. Ni zan tafi in nemo
iznin isa da kai.” Nomau ya tafi ya bar jahili nan yana ta salati, shi kuwa ya je ya yi ta shara
barcinsa.

Da gari ya waye ya taho ya bude dakin tattabaru ya jawo shi, ya ce, “An ce in

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login