Showing 3001 words to 6000 words out of 7944 words
Chapter 2 - DAFIN MACIJI BOOK ONE by Fatima Kas.pdf
Alhaji kabir ne ya katse shirun da cewa. " inde zakiyi aiki yanda ake so kuɗi ba matsala bane ko
nawa kike da buƙata zamu aiko a kawo maki."
A zuciya tace haka nake so dama munafukai ƴan hasara wallahi sai naga bayan ku ɗaya bayan
ɗaya, dama tun da naga Kawu Auwalu nasan ba abin alkairi bane, amma dai shi ke nan a juri
zuwa rahi wata rana tulun zai hwashe.
Tunaninta ya yanke sanda PA Alhaji Kabir ya miƙo mata sabuwar waya dal cikin kwalinta.
Amsa tayi tana zabga uban murmushi na jindaɗi, waya abace da take ɗaya daga cikin mafarkan
rayuwarta idan tayi kuɗi, ko sanda take makaranta ba ta da labari se na idan ta je birni gidan Iya
Abu da waya take jin waƙa ko tayi kallo.
Katsewa tunaninta yayi jin abinda J,B ke fadi.
Zamu dinga magana anan idan buƙatar haka ta taso, kuma idan akwai wani abu wanda bai
maki ba ki karamu kai tsaye. Amma fa ki kiyaye da kyau.
A fili godiya ta dinga jero musu kamar zata taune harshe, amma a zuciyarta tsine musu take ta
na cewa sena tona muku asiri munafukai kawai ƴan iska masu kama da biran jeji.
Bayan angama yi mata gargaɗi sukayi sallami da Kawu Auwalu da ke ta kalle-kalle kamar
tsohon ɓarawo.
Sallama yayiwa Rahane dagwamnatin kai kamar ba ta sanshi ba, ciki-ciki tace Ka gaida mutan
hanya ta yi gaba abun ta zuwa gaban rantsatstsiyar farar motar da aka kawo dan tafiya da ita
gida gwamnati.
Tunda suka dauki hanya jikin rahane yayi sanyi ganin yanda aka baza jami'ai ko ina a hanya
suna ta aikinsu.
Hawayene suka zubo mata ganin yada bawan Allah ya zage yana ta gyara garin Katsina
amma ahaka aka samu wasu mugayen macijai suna saransa da zazzafan dafi a bayan fage.(ni
ko nace haba Rahane miye na kuka tun yanzu ai bakiga komai ba tukun ki bari tafiyar tayi nisa
idan kika shiga gidan gwamnatin sannan.)
Basuyi wa ta tafiya me nisaba suka iso GOVERMENT HOUSE, ruɗewa Rahane tayi ganin irin
tsarin da akayi a ciki, tsoro ne ya kamata ganin irin dukiyar da aka danƙara wajen gina
katafaren gidan gwamnatin.
⭐⭐
⭐ ☀️
✍️✍️
⭐⭐
https://chat.whatsapp.com/F36iTELAmUrLkD3XBti6YZ
https://whatsapp.com/channel/0029VbAho5W8V0tlD03a4Q1g
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=15
96987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattukawaici kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su
sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
300
55997895186
09136291920
7️⃣8️⃣
Rahane ganin wasu jibga jibgan sojoji yasa ta kusa sakin fitsari ganin wani yana ta zare mata
idanu.
Amma da yake ita ma ogar kan ta ca sai ta nuna kamar bata ji tsoro ba.
Da suka shiga ciki sumewa ne kawai Rahane batayi ba wani falo ne ya haɗu iya haɗuwa nan
suka shiga ya Allah ya zan musalta maku haɗu war falon nan wata Matace ta fito daga wa ta
ƙofa tana masu murmushi bayan sun gaisa wanda ya kawo ta yace "inna Lami ga me aiki nan
an kawo".
Matar da aka kira da Inana Lami tace shikenan "zaka iya tafiya."
mu shiga ciki".
Wani ɗan ƙaramin ɗaki ta kai ta tace " wanan shine ɗakin ki kinji".
Tace eh
Inna Lami tace "ya sunan ki"?
"Sunan Rahane".
Inna Lami tace "Ma sha Allah ki ɗauke ni kamar Mahaifiyarki kinji"?tace to.
Tace aikin ki shine "zaki dinga kula da wajan su Haisam anjima zan rakaji ko ina yanzu ki samu
ki huta".
Rahane tace "to Ina makewayi"?
Inna Lami tace "gashinan tace ki shiga yanzu zan sa akawo maki abinci".
Rahane tace "to inna".
Bayan inna ta fita Rahane ta shiga ban ɗaki.
Tana shiga taga bahun wanka ciki da ruwa.
Tace "kai yau burina ya ciki zan higa rahin yan birini".
Tana zuwa ta faɗa ciki ko kaya bata ciri ba takama wanka tana yi tana wata shigiyar dariya can
tace ashi fa wainan yan lawahan sun bani waya.
Rahane tafita da gudu ta buɗe wayan a kwali taga bata san kanta ba tayi tsaki tace "idan na
samu wani ya buɗe min".
Ta koma ban ɗakin sai da tagama shiriritar ta sanan ta fito.
Tana fitowa taga Inna Lami ta ajiye mata kayan sawa da abinci ga lemu me sanyi da ruwa.
Wani ihu ta saki tace oho" ni Rahanen Inna Kande da Malam Tanimu yau nice zan kwashi
wanan garan".
Bayan fitar shi daga gidan Kabir tasha ya wuce bai samu mutar da zata mai dashi garin su kai
tsaye ba sai dai ya hau ta Malumfashi idan yaje can zai samu motan da zata kai shi Yar Mama
sunyi nisa cikin tafiya yan bindiga suka tare su sukayi masu dukan tsiya har zai tafi suka hango
aljihun Awalu yayi tudu suka kuma zasu ɗauka kuɗi Awalu ya riƙe ma wanda zai ɗauka ƙafa
yana ruƙan sa akan yayi haƙuri kuɗin marayune wata dariya ɗaya daga cikin su yayi yace ai
muma marayune suka kwashi kuɗi suka ƙara mai ɗauka gashi sunfi ɗaukan shi haka suka
kama hanya kafin su shiga cikin garin Malumfashi Awalu yaji jiki sosai Dole suka tsaya asibiti
banda sambatu babu abinda Awalu ya ke yi kamar wani sabon kamu haka ya koma.
ℎℎℎℎℎ ℎ ℎ ℎ
Bayan an tafi da Rahane gidan gwamnati Kabir ya kalle J•B ya ce "gaskiya wanan yarinyar
daga ganin ta zatayi mana aiki yanda ya kamata dan haka gobe kaje ka kai ma iyayen ta
miliyan ɗaya hannu da hannu".
J•B yace "gaskiya ne oga dan koni na ya ba da hankalin ta zata iya yi mana duk abinda muke
so fatan muma muyi ƙoƙari mu biya mata ɓuƙatun ta duk abin da tane ma abata".
Kabir yace "tabbas hakane mudai fatan mu burin mu ya ciki".
Daga haka suka rabu.
Muhammad Ƙafur wato gwamnan Katsina.
Zaune suke a falo shida Matar shi Husuna idan ka ganta bazaka ce itace ta haifi Haisam ba
Hajiya Husuna tana da kirki sosai gata da son mutane bata wulaƙanta talaka kamar yanda wasu
masu kuɗin suke ba ita duniya bata dametaba kuma tana ƙarama mijin ta wajin gani ya sauke
haƙin Al'umma da yake kansu.
Fira suke yi sama sama wanda idan bakusa kake dasuba bazakaji me suke cewa ba
Alhaji Muhammad ya kalle Hajiya Husuna yace gaskiya ya kama ta yaron nan ya ƙara aure
kinsan halin da muke ciki badan komai nike so ya ƙara aure ba sai dan wa'inda suka zamar
mun DAFIN MACIJI.
Rahane tana cin abinci tana nishaɗi da suru tanta ita ƙadai.
Ta yago wani ƙaton naman kaza ta kai baki tana ce "indai zan dinga samun kalar wanan garan
meye na damuwa ai ni gaba ta kaini ta ƙara sa maganan tana kwashiwa da dariya".
Inna Lami ce ta shigo tace "yarinyata kin gamacin abincin kizo muji ki gashi da mutanan gidan
dan ki san kowa".
Rahane tace eh nagama suka fita har sun kai bakin ƙofa ta dawo ta ɗauki wayan ta.
Suna fita suka nufa bangarin Hajiya Husuna Matar gwamna.
Suka shiga da salama su duka suka amasa masu salaman suka shiga bayan sun zauna a
ƙasan capet suka gaishe su cikin girmamawa suma suka amsa cikin girmamawa.
Sanan Inna Lami tace Hajiya "me aiki ce aka kawo daga wajan Kabir ".
Hajiya Husuna kallo ɗaya tayi ma Rahane yaji yarinyar ta shiga rainta.
Tace "ma sha Allah ya sunan ki"??
Rahane tayi ƙasa da kai sanan tace "sunana Rahane".
Hajiya Husuna tace "ma sha Allah amma zamu dinga kiran ki da Raihana".
Rahane tace "Raihana kuma".
Hajiya Husuna tace mata "eh ai asalin sunan kenan".
Tace "to Inna inaso Kuma sunan yan gayu ne ko"?
wata dariya ce ta zo ma Hajiya Husuna jin ance mata Inna.
Tace "yarinyar kirki ki dinga kirana da mommy".
Rahane tace "to Mommy".
Alhaji Muhammad dake kallon su yace yace "Raihana daga wani gari kike".
Tace daga "Yar Mama kauyen Malumfashi".
Yace "ma sha Allah ki maida hankali wajin aikin ki idan kina ɓukatar wani abu ki faɗa wa Inna
Lami".
tace "to nagode".
Sukayi yi masu salama suka nufi sashin Haisam.
Sanda suka shiga Haisam kawai suka samu a falo.
Bayan sun gaisa Inna Lami tace " Babana ga me aiki ankawo maku".
Yace to "Inna sanu zakie iya tafiya".
Inna Lami ta kalle Rahane da yanzu ta koma Raihana tace "ga inda zaki dinga aiki idan kin
gama sai ki koma can ki kula kinji yarinyata".
Raihana tace "to inna".
Tasamu waje ta zauna ganin Haisam yana ta kallon wayan shi ga shi tana so tayi mai magana
ta kasa cab dai tace "kai wanan mutumin kana ganin mutane baza kayi masu magana ba ko
ruwa ba sai ka baniba".
A sukwane ya ɗago jin abinda tace mashi ya kalle ta ya maida kanshi kan wayan shi.
Ganin yayi mata banza yasa ta ƙara sa wajan shi tace "tunda baka magana ga wanan wayan
ka sai tamin ita yanda zan dinga kallo da ita kuma ka ɓude min WhatsApp ta gama faɗa yana
dura Mai wayan a Kan cinyan shi".
Yama rasa me zai ce ma wanan yarinyar ganin yanda take bashi umarni kamar wata Mamanshi.
Ya daka mata tsawa yace "ke ni abokin wasan kine"?
Tsawar bata tada mata hankali ba saima hararan shi da tayi tace "idan ba zakayi min ba basai
kayi min masifa ba".
Yama rasa me zai ce mata sai yayi shuru.
Yusurah dake kallon duk abinda duk abin da yake faruwa ta ɗaga hannu ta yi ma Yusurah wasu
zafafan maruka da ya gigita ta
Hummm yanzu wasan ya fara
⭐⭐
✍️✍️
⭐⭐
300
55997895186
09136291920
https://chat.whatsapp.com/F36iTELAmUrLkD3XBti6YZ
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=15
96987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION* ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa
su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
MARUBUTAN
RAYUWR SAMHAT
DAFIN ZUCIYA
AND NOW
DAFIN MACIJI
BISIMILAHI RAHAMANUR RAHIM
Page
9️⃣and
Haisam sandarewa yayi ganan Raihana ta rama marin da Yusurah tayi mata.
Yusurah wani ihu ta saki me tada hankalin me sauraro.
Raihana tace "kan bala'i nan to walahi babu wanda ke duka na na kyale shi bare a mareni naga
alama ke jaka ce baki da ilimi duk ne ilimi ba zai yi mari ba kisani fuska abu ce me daraja so ki
keyaaye ta kai karshin maganan cike da siwa".
she Kam Haisam kalon ɗan ƙara min bakinta kawai yake yi ganin yands take masifa.
azuciyar shi yace tofa wanan yarinyar za aje da ita naga alama amma a haka sai kace batada
ilimi.
Yusurah da gudu ta hau sama ta ɗauki wayan ta ta kira Daddyn ta cikin kuka tace Daddy "Kaine
ka sa aka kawo yar aiki"?? to "walahi saina yi mata abinda sai tayi dana sanin zuwan ta
duniya".
Daddy yace "eh nina sa aka kawo ta me ya faru kuma me tayi maki"??
cikin kuka ta faɗa mashi abinda ya faru sanan ta ɗura da cewa "ina so a wulaƙanta ta da iyayen
ta sanan itama ayi mata abinda baza ta manta ba".
wata tsawa ya daka mata yace "kin kin san wace ita to kibini a hankali dan wanan yarinyar a
yanzu abuce me mahimmanci a wajan mu".
cikin kuka tace "mahimmanci ci fa kace Daddy"?? yanzu har a kwai abun da yafine
mahimmanci"???
Daddy ganin yanda Yusurah ke neman birkita mashi lissafi yasa yace "sorry my dear zamuyi
magana daga baya amma bana so ki kula ta".
Yusurah tama manta da Haisam da yake zaune duk abinda take cewa yana ji amma baya
jin abinda Daddy ya ke cewa.
Haisam wata zuciyar shi tace tabbas sai kasa ido akan yarinyar nan da alama anturo tane.
Yana gama wanan tunanin yayi murmushi a zuciyar shi ya kuma cewa tabbas nayi alkawarin
nida yarinyar da kuka turu mune zamu zamar maku DAFIN MACIJI.
ℎ ℎ ℎ ℎ ℎ
Awalu bayan sun je asibiti aka yi mashi wankin raunika aka bashi magunguna sanan suka kama
hanya koda ya isa gida matan shi da yaran shi nata yi mai magana yayi musu banza sunyi
tambayan har sun haji.
Wata daga cikin yarance tazo cikin rashin tarbiya tace"kai Baba ka bani kuɗi zan je gidan biki".
Wani wawan nushi ya kaimata yana cewa uban "kuɗin zan baki in zama kuɗin ki dauka da me
zanji da asaran da nayi ko da dukan da nasha"??
Matar shi ce ta shigo ɗakin da gudu ta amshi yarinyar. takama "faɗa to mu ina ruwan mu
da abinda ya sameka zaka zo ka sauke fishinka a kanmu".
shedai yayi mata shuru dan ya faɗa duniyar tunani da yarshi ya bada yanzu wacar yar banzar
da yakai ita za taita kwasan arziki babban abin takaicin ma kuɗin da tace akaima mahaifinta
kuma yasan idan kuɗin nan suka je hannu Malam Tanimu ba zai bashi ko sisi ba dan dan
wajan kuɗi baya da wasa.
Kabir bayan sun gama waya da Yusurah J•B ya kira ya faɗa mashi abinda ya faru sanan ya
cigaba da cewa "tabbas wanan yarinyar zata iya abin da suke so yan yana so yaje garin su ya
kaima iyayen ta abin da tanema sanan a tafin masu da kayan abinci idan mukayi hakan zai
ƙara ma yarinyar karfi wajan yi mana aikin mu ko mai take so ayi mata" .
Banji me J•B yace mai ba na daiji ya kwashi da wata uwar dariya warda saida ta tsoratani.
sai kuma J•B yace "zan je zan kai masu sanan dole mu samu wa'inda za su sama na ido
akan ta".
Kabir yace "kayi tunani me kyau bari zan nemi Inna Lami nasan da taga kuɗi zata amince mana
kaga abin ma zai tafi daidai yanda mu ke so tunda shi karan farautar namu sun yarda da ita".
J•B yace "amma kana ganin baza ta bamu Matsala ba"???
Kabir yace " dole ma zata amince idan ba haka ba zata jefa rayuwar ta cikin hatsari".
J•B yace "shikenan sai munyi magana".
ℎℎℎℎℎ ℎ
Rahane ganin Yusurah bata ce mata komai ba yasa tace " tace taƙon tsaƙa dani babu daɗi ki
riƙe girman ki".
A sukwane Yusurah tayo kanta da niyar dukan ga Haisam ya daka mata tsawa yace "kada ki
tsaki ki taɓa ta ba".
Yusurah da kamar bazata haƙura ba ganin yanayin shi ne yasa ta kama hanyar ɗakinta.
Yusurah na tafiya ya kalle Raihana yace "mara kunya kawai".
sai da ta murguɗa mai baki sannan tace "Ni dai mara kunya bace".
yace owk "nima ma yimin zakiyi ne"?
Raihana tace "haba Yaya ni na isa dan Allah ka saita min wayan nan sai ka faɗi aikin da zan
maku".
a