Showing 6001 words to 9000 words out of 129443 words

Chapter 3 - ALKIBLA Complete Book by Safiya Abdullahi Huguma .pdf

Advertisement

godewa Allah dasu abba basu dauko aqidar sai munyi karatu ba
kafin aure,inda haka ne Allah kafin mubar gidan nan saiya sa mana hawan jini" dubanta hafsa
tayi
"Ni kuma kinsan hakan baimun ba,nafison naci gaba da karatu kafin ayimin aure,inda xasu
sauya shawara wallahi hakan yafimin,amma ya haidar kusan yafi kowa na'am da wannan tsarin
tun xamanin su ya khairiyya" hararara zahra ta jefeta dashi tana cewa
"Bakinki ya sari danyan kashi,ni da kike gani na nan ba'a da candy qalilan ce inji 'yan
arabiyya,babu wani karatu da xan tsaya wahal da kaina inayi,me yafi aure dadi?,kaida
masoyinka?,ka samu 'yanci babu me takuraka?,tabdijan,ke ai saikita zama kici takarda da
biron" ta fada tana komawa zuwa kwanciyarta ta daxun.

Dariya hafsa ta saki tana daka mata duka,tana sane ta sako wannan zancan,don duk

cikinsu kowa ya san ra'ayin mahaifansu ya dace da ra'ayin zahran,kuma ita hakan yayi mata dai
dai
"Allah ya shiryeki zahra"
"Amin....ai dan sunna bayaqi sunna ba ko"
"Wannan haka yake malamarmu"
"Kyaji dashi" ta amsa mata tana sake jawo wayarta ta fara buga game,jifa jifa suna hira,tana
kuma dakon daina jin motsinsa a falon hajjan data samu ta fita taci wani abun kafin ta dawo ta
kwanta tadan matse gajiya.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: *KIJI TSORON ALLAH��,KARKI TABA KAYAN
DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*


03


Kusan minti talatin kafin ta daina jin duriyarsa,zuwa sannan bacci ya soma fisgar hafsat,saita
aje wayarta ta miqe a hankali tana gyara daurin dankwalin kanta,ta isa bakin qofar dakinta ta
zura takalmanta sannan ta wuce kai tsaye zuwa falon.


Kyakkyawan matashin saurayin da a qalla bazai wuce shekara talatin bane zaune cikin
falon,saman lallausan center carfet din dake shimfide tsakiyar kujerun,ya miqe dogayen
qafafunsa ya kuma hardesu waje daya yana kadasu a hankali,kallon farko da zakayi masa zaka
fahimci wani irin kwarjini shimfide saman fuskarsa,wanda ke cakude da rashin fara'a da kuma
daurewar fuska,wanda ko a yanzun da yake zaune shi kadai cikin falon wayarshi qirar iphone
12 na tsakiyar tafukan hannayenshi dake saman cinyoyinsa yana amfani da ita fuskarshi a hade
take,da alama gwanin iya tsare gida ne qwarai,gefansa kwanukan abinci ne a jere,bata sani ba
ci zaiyi ko kuma baida niyyar ci ya ajesu ne kuma baxai magantu yace azo a dauke ba.


Kallo daya tayi masa ta tabe baki,duk da bata samu nasarar ganin fuskarsa ba sai
sumarshi dake gyare,ita bamai yawa ba ba kuma saisaye ba,saidai tafi kama da saisayen irin
sama saman nan,tayi wani spring kamar zubin indomie,baqa sidik tana sheqi,da alama ana
bata kulawa yadda ya kamata,don ba qaramin qara masa kyau da kwarjini takeyi ba,ta kuma
dace da kalar kwantacciyar skin dinshi da hausawa ke cewa wankan tarwada,ga duk wanda ya
dubeta yasan ya samu cikakken hutu dajin dadi,duk da kalar aikinsa bawai na hutawa bane
waje daya,saboda aikine na hidimtawa qasa,da bada kariya da tsaro wa dukiyar al'umma da
rayukansu.


SaÉ—af saÉ—af take tafiya saboda bata da buqatar ya ganta,dab da zata gotashi ya daga
kanshi,saida gabanta yayi mummunar faduwa,kallo daya tak ya mata ya maida kanshi ga
wayarshi,kamar baisan Allah yayi wanzuwar wata halitta ba,tilas ta fasa qudurinta na wuceshi

da tayi niyya,ta dawo da baya
"Ina yini yaa haidar" kamar bai jita ba,hakan ya bala'in ɓata ranta,ta tsani wannam halayyar
tasa fiye da kowacce,ita idan zai shekara zaune a waje baiyi magana ba ba damuwarta
bane,amma don me mutum zai gaidashi ya watsar.


Ganin bai amsa ba ya sanyata miqewa donta wuce abinta,sai a sannan ya magantu
"Lafiya.....zoki zubamin" ya fada ba tare da É—ago daga duban wayarshi ba yana mata nuni da
fulasan gefansa.


Kamar tayi tsako don takaici amma tasan bata isa ba,wato saboda tsabar izza yana jiran
wanda zai zuba mishi ne,akan ya zuba da kansa ya gwammaci yayita jira har sai mai zuba
masan yazo,laifin bana kowa bane saina zahra,ita ta batashi,don tana fara zuba abincin ta
tabbatar girkin ma nata ne,ita ta dafa mishi.

Tana wannan tunanin zucin naman data debo a serving spoon daya ya subuce ya koma
cikin miyar,take ta fantsamo man dake saman miyar,ya kuma samu kyakkyawan masauki
saman farar shirt din dake jikinsa.


Da sauri ya daga kai daga danna wayar da yakeyi,ya dubi jikinsa sannan ya maida
idanunsa saman fuskarta,zallar bacin rai ta hanga qarara,ta soma motsa baki da niyyar yi masa
bayani saidai ya rigata magantuwa
"U r very stupid....baki da hankali ne?...."
"Ashsha.....inna wuro garin ƙaƙa?" Muryar hajja ta ratso falon,duk rashin tsoronta amma
sai da taji kamar anyi mata rahama,kafin ta bata amsa ta iso
"Tashi maza ki samo omo da dan toli fefa a goge mishi" tsaki ya saki kawai yana miqewa,ba
tare da yace da kowa komai ba ya soma takawa yana nufar qofar fita
"Ka tsaya a goge maka mana zaki(haka takan kirashi dashi ita da wasu mutanen,sakamakon
sunan mijinta da yaci,bata iya kiran sunanshi)"
"No,barshi kawai"
"Abincin fa?" Ta fada sanda yake gab da ficewa
"Ku amfaneshi"ya amsa a taqaice yana qarasa ficewa.


Bugu hajja ta kaiwa zahra wadda ke tsaye tana yiwa qeyarsa gwalo gamida murguÉ—e
murguÉ—en rawa
"Ja'irah,hala kina sane ko?" Dariya ta saki tana zama gurbin daya tashi,wanda ke fidda qamshin
turarensa ta soma sake bude kwanukan tana baiwa hajja amsa
"Inda ina sane ai da sai abun yafi haka.....arashi aka samu,kuma hakan yamin dai dai"
"Zahra....zahra....kinga ki fita daga idona akan yayanku,kamar ba jininku daya ba"

"To hajja ko kinfi sonsa yanzu a kaina ne?,babu inda nake sakewa fa sai nan,haka kawai sai
nan dinma yazo ya zauna ya hanamu sakewa,idan na koma wajen ummi canma yana nan,da
nayi wani abu itama ta hauni da fada itama,don ya girmemu kawai saiya damemu" daga haka ta
jawo fulasan tahau zubin abinci Abinta tabar hajja da kallon ikon Allah"

"Allah ya shirya" hajjan tace tana sauke ajiyar zuciya kawai,bata amsa mata ba taci gaba
da zurin abincinta.


Salma ce tayi sallama cikin falon tana tsaka da cin abincin,sanye da atamfa dinkin A
shape,sai dan kwalinta data zarga a kanta,hannunta riqe da qaramar wayarta me keyboard
itel,wanda akafi kira da rakani kashi,kusan dukka gidan zahra ce me waya torching,ita dinma sai
da aka hau rimin gafiya kafin a samu lamuncewar oga kwata kwata haidar ya barta da wayar,a
hakanma bisa goyon bayan hajja,saboda abban gwammaja ne ya kawo mata,ita kuma tace
sam ba za'a watsa masa qasa a idanu ba,tunda wayar bawai wata babba bace can,sannan uwa
uba an hanata walwala an dauketa an kaita makarantar kwana aiko ba'a hanata riqe waya ba a
duk sanda tazo hutu,tunda hutun ai baya wuce wata guda kacal,uwa uba kuma ma rashin riqe
wayar yafi riqeta yawa,hakan yasa dole aka barta da abarta.


"Lalalaaaa......lallai zahra.....wannan ba kwanukan da naga yaa xahra nata fadin tashin
hadawa yaa haidar abinci bane?" Sai data kai lomar qarshe na hannunta sannan ta daga kai ta
dubeta
"Sune mana....kema idan xakici bismillah,zoki zuba iya zubunki" kamar wadda ta danawa wuta
a jiki salma ta janye gefe da sauri tana kada hannu gami da fidda ido
"Lalala,bada ni ba saa lallen karya,inason lafiyata wallahi,haka kawai ina lallaba jikina kisa amin
shaidar da xanje kabari da ita,kedai da kika shirya tarar aradu daka"
"Ba zakuci bama,kema wanda kikaci shi kadaine rabonki,tunda kika hanashi ci kema baki
ci,yarinya ta zauna ta bata lokacinta saboda yaro amma a qarshe kuta yiwa aikin,to baku isa
ba,ko ruwan lipto yace ku dafa masa sai kunyi qorafi,kada ma ke inna wuro kiji labari" cewar
hajja,tana kaiwa qarshe ta soma qwalawa gaje kira,zahra ta mele baki "Ko iya haka ma alhmdlh" dai dai lokacin gaje ta qaraso,hajja ta sanyata ta debe kwanukan tana
ci gaba da mita,xahra ta miqe tana kakkabe jikinta
"DaÉ—ina dake hajja baki iya samun magana daya ba.....muje sister ki bani labarin daxu"
"Zakici ƙaniyarki,zaki dawo ki sameni,nasan da wanda zan hadaki" ta fuskanci sarai me take
nufi,amma tasan ba iyawa zatayi ba,don idanma ta hadata dashin ƙarshe sai tafi kowa mita
da jin ciwon hukuncin da za'a matan.


Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta haiqan
"Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci" ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude kadan,ta gane
salma

"Ki saurara min 'yar baqincikin baccin mutum" daga haka ta cusa kanta qasan filo tana gyara
kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu
"Wai kinsan meke faruwa kuwa?"
"A'ah saikin fada" inji zahra
"Sabon kamu fa nayi" sosai zahra ta maida kallonta ga salma
"Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?" Farr tayi da idanunta
"Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman" idanu dukka
zahra ta fiddo waje
"Keee salma.....kiji tsoron Allah,sulaiman din?" Kai ta gyada kai tsaye itama tana dubanta
"Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko yaya?,don kawai
na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk lokacin da aka buqaci na
nuna wanda na tsayar?" Kai zahra ke kadawa kawai dama da hagu cikin nuna zallar jimami
"Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba".


Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita tana duban
zahra
"Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da muka
sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce miki akayi idan
don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu wata.....idan bake ba sai
rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da gaske har a badininsa?,bance miki
fau fau ba'a samun wanda hakan bane.....amma sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata
ne,maha'inta ne,basu da *ALƘIBLA* qila kece ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya
nima bazanyi saki na dafe ba,na laru dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata
da gangar jikina ba.....na shafa rana guda naji wayam" ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.


Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar salma bata
samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa kai mafaka,banda
haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu tattareshi dashi koda sau
daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum soyayyarsu qara gaba
take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda da zancan salma 'yar tamore
"Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba" zahran ta amsa mata bayan takai qarshen nazarinta
tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi
"Eh....kekam taki zuciyar na daÉ—e da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne dakkan
yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan har matan"
kusan hirar da suka dinga yi kenan a tsakaninsu,wanda har ya kusa kaisu ga musu.


Saidai basu ja da yawa ba dakin ya soma cika da 'yammata,hakan ya sauya akalar hira
suka shiga hirar sabgogin da suka shafesu,kamar qawayensu na unguwar dana islamiyya
wadanda aka kawowa kudi da wadanda aka sawa rana,jarrabawar qualifying da suke
fuskantarta,candy da zasuyi nan gaba da kuma aurensu da sauran hirarraki da ba'a raba

'yammata dasu.


Duk da wannan hirar da ake amma hankalinta nakan wayarta lokaci lokaci,tana tsumayin
nuraddeen kowanne lokaci,amma saidai har suka tasamma watsewa saboda lokacin É—ora
girkin dare yayi a kowanne sashe,kasancewar kowaccensu duk da akwai masu aiki É—ai É—ai
a kowanne sashe amma ba'a barsu sun zauna sun ta'allaqa komai a kansu ba,babu nuradden
ba duriyarsa,don haka ta jawo wayarta ta miqe da ita tana tunanin zuwa wajen yaa zahra ta tura
mata updated watsapp,don nata yayi expair.


Ci gaba da hayaniyarsu ta hira suke har suka zo zasu gifta ta ma'ajiyar motocin gidan.


Dukkaninsu sun hangeshi,duk da cewa bayanshi kawai suka hango amma babu wanda bai
ganeshi ba cikinsu,saboda haka kowacce taja bakinta ta saisatashi gami da rage sautin
muryarta.


Sanye yake da wata farar riga ƙal me gajeran hannu,wanda hakan ya baiwa
murÉ—aÉ—É—en dantsensa damar bayyana,sai dogon wando shima fari gamida wani farin
booth dake qafarsa,daga inda kake wucewa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa da iska
ke kwasowa tana bazashi ko ina,ba kayan dazun bane a jikinsa,da alamu ma wanka yaje ya
sake ya sauyasu saboda miyar data batashi,waya yake amsawa,kallo daya zaka masa kasan
cewa yes!,aikin da yake yayi matuqar dacewa dashi,ko shafawa kayi kasan cewa shi din SOJA
NE.


ƙasa ƙasa zahra taja tsaki cikin ranta
"Da wannan kayan yafi kamata ma ace jikinsa ya ɓaci dazu naga ta qaryar gayu da
ƙyanƙyami" ta qarashe maganar tana fitar da tsakinta a sarari dai dai sanda ta hangi ya
musty na qarasawa inda yake tsayen bayan ya baro wajen me gadi wanda da alama wani saqo
ya bashi.

Suna gab da rabuwa kowa ta shige sashensu ba tare da sun ankara ba sukaji muryar ya
musty na nufosu yana fadin
"Yaa haidar na magana fa 'yammata" dukkansu babu wadda cikinta bai murÉ—a mata ba,yusra
da tafi kowa tsoro cikinsu cikin rawar murya tace
"Wa yake kira a cikinmu?"
"Dukanku" ya bata amsa yana qunshe dariyarsa,don basu ba,hatta su da suke maza ba kasafai
kiran haidar ke musu daÉ—i ba.

Junansu suka kalla,yusra ta sake cewa cikin qas qas da murya don kada ya jisu
"Amma me kuma muka yi masa ya musty don Allah?"
"Idan kunzo kwaji" daga haka shima ya juya abinsa don kada yayi laifi.


"Kome zai mana ai bazai rabamu da numfashinmu ba ko?,kuzo muje" inji hafsat qanwarsa
wadda suke uwa daya uba daya,zahra ko tabe baki tayi,duk da cewa ita dinma a tsorace
take,haka suka nufeshi sum sum kamar waÉ—anda suka É—auko gawa.


Gaba daya su bakwai din suka zube gabanshi,yayin dashi kuma ke tsaye abinsa yana
latsa waya kamar baisan An haliccesu wajen ba.


Saida suka tsammaci ya manta dasu a wajen,sannan ya buda baki kamar wani saraki ya
jefo musu tambaya yana ci gaba da latsa wayarsa
"Wace inna wuro a cikinku?" Tambayar duk saita zo musu wani banbarakwai,tunda sunsan dai
duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya san me sunan,hakan yasa suka kasa amsashi suka
hau kallon kallo.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 04

*KIJI TSORON ALLAH������,KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI
BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
___________________________

*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kintaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace
data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren
fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped
action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba
duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da
turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma
zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me
bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram*
*@turare_by_awwaba mungode*
_______________________________



Sake maimaita tambayar yayi a karo na biyu dai ba tare daya kallesu ba,sanin hali yasa
suka fara yunqurin nunata kawai,saidai basu kai ga aikata hakan ba tsawarsa ta mamayesu
wanda ta rudasu,ba shiri kuma suka nuna zahra dake tsakiyarsu.

A hankali ya dora birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza a kanta
na sakan daya kana ya janye yana cewa
"Itace ta dawo yau daga boarding ba?" Haushi tambayar tasa ta bata fiye data dazun,baqo ne
shi,ko yau ya soma zuwa gidan nasu,tuni suka amsa masa da eh
"Good" ya fada yana kashe wayarsa ya zurata a aljihun wandonsa na baya,idanunsa dake
ladabtar da mutum na bisa kanta.


"Daga dawowarki yau shine kikeson maida mana qofar gida tasha?" Ya jefa mata tambayar
da batasan amsarta ba,hakan yasa tayi shuru tana nazari,tare dason gane me yake nufi da
hakan
"Am asking you!" Ya kuma fada cikin tsawar data dan razanata,wannan karon bai jira amsarta
ba ya dora da
"Wato kaiko boarding da akayi baisa komai ya canza ba ko?,su samarin da sukazo suna son
mana tumasanci qofar gida duka ina kika sansu kina kulle cikin makaranta?,koko malaman naki
ne soma biyo sawunki?,duka duka shekarunki nawa?tun baki tafasa ba zaki qone?,to i wil deal
with u,bazan dauki wannan iskancin ba tun baki riqa ba,ba zaki fi qarfinmu ba,ki gayawa
kowanne shashasha duk randa ya sake zuwa qofar gida ya mana fada saina masa daurin da
za'a kasa ganeshi,ba gidan 'yan iska bane nan,hope kin haddace abinda nace?" Tuni hawaye
ya soma ambaliya saman fuskarta saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa
mishi,har sai daya maimaita mata cikin tsawa
"Kinji ko bakiji ba?"
"Naji" ta amsa cikin muryar kuka
"Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!" Ya kuma fada cikin tsawar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login