Showing 114001 words to 117000 words out of 129443 words

Chapter 39 - ALKIBLA Complete Book by Safiya Abdullahi Huguma .pdf

Advertisement


Kwanaki biyu kenan da dawowarsa,qarfe sha daya saura na safe ya shigo sassan hajjan,a
lokacin abba babba abba yusuf da abban tsakiya duka suna falon hajjan,zahra na kitchen tana
wanke kwanukan data hada musu breakfast,don tun safe sukazo suna ta lissafi,na haqqin Allah
da za'a fitar cikin kudin hajja da ake juya mata,lokacin fiddawa yayi.

Tunda ta gama ta zuba masa nasa a fulasan da ake zuba masa kamar koda
yaushe,kwanaki biyu kenan tun randa ruwan saman ya tareta hajjan bata sake bari taje din
ba,saidai ta bayar a kai masa kamar yadda ya fada,ita kam zahra nata idanu ne,saboda tasan
halin hajjan,katafila ce sarkin aiki,takan kowa take bi idan aikinta ya tashi.

A ladace ya cire takalmansa ya qaraso gabansu ya tsugunna,daya bayan daya ya
gaidasu,yaji dadin samunsu a tare,tunda yaje bai samesu a sassansu ba dama
"A kawo maka abincinne?" Hajja ta tambayeshi,tunda ta lura kwana biyu wani shareta yake,tun
ranar nan,itakam ko a jikinta,tunda tasan koma meye qarshe shi zaifi kowa mora
"A'ah...zanyi magana idan za'a kawomin din....magaa nakeso muyi dama" abbansa ne ya daga
kai ya dubeshi yana ninke takardar daya gama rubutu akai,abba yusuf ne ya amsa
"To Allah yasa lafiya" qasaitaccen murmushin nan nashi na gefan baki yayi sannan yace
"Lafiya lau abba.....cikin yarjewar ubangiji inason satin nan da zamu shiga in sha Allah mu wuce

umara,nida hajja da abba na.....da kuma mama" Wani farinciki ne ya bayyana sosai saman
fuskar hajja,burinta a duniya kenan ta koma qasa mai tsarki,duk da cewa taje har sau biyu,hajji
daya umara daya,amma wajene da babu musulmin da bazaiso ya dawwama ma a can ba,lallai
ba shakka haidar din wata kyautar Allah ce cikin iyalinta,soyayyar da yake mata mahaifi da
mahaifiyarsa kai dama ahalinsa gaba daya abarso a sameta ce cikin zuciyar kowanne daga
cikin dangi,don samun dorewar qaunar juna da danqon zumunta.


Kowanne a parlour din son barka yake gami da sanya masa albarka,tare da yaba wannan
namijin qoqarin sa yayi
"naso ace na qara da abban tsakiya da abba yusuf,to amma kudin hannuna sun qare,ba zasu
isa ayi komai na mutum biyu ba,amma in sha Allah sune a lissafina na gaba" nunawa sukayi
babu komai,su da dan uwan nasu duka abu dayane,sannan suna da yaqinin da yardar Allah shi
mai kai kowa ne cikin dangi idan da halin yiwuwar hakan.

Sun dan jima anan suna tattaunawa cike da farinciki,kafin daga bisani suyiwa hajja sallama
kowa ya nufi wajen neman kudinsa,sai falon ya rage daga hajjan sai haidar din,sai kuma zahra
dake kitcehn tana dora abincin rana kawai don idan ta zauna ta huta gaba daya,inna gaje ciwon
qafa ya hanata zuwa aiki tun shekaran jiya.

Kira hajjan ta qwalawa zahra tace ta fito da abincin haidar,ta zata kai masa za'ayi,batayi
tunanin yana falon ba don haka ta fito gaba gadi haka abunta,wata straight gown ce a
jikinta,wadda tayi mata das a jikinta.


Da kallo ya bita bayan ta gaidashi ta aje masa abincin ta koma,suna hada ido da hajja ya
hade rai tsam sannan yace
"Yanzun haka take yawo anan?"
"To uban mutane,sai akayi yaya?ni bama wannan ba,tafiyar nan da zahra'u ya dace ayita,don
baka je dakin Allah haka ziqau ba,kabar kyautar da yayi maka a gida ba" kallonta yayi ya soma
zuba abincin yau da kanshi ba tare daya nema wani ya zuba masa ba
"Yanzu dai babu kudi hannuna,saidai nan gaba idan Allah yayi" hade ranta tayi sosai
"Eh na sani ai ubana.....ni zan biya mata da kaina,saboda haka a sama mata komai da
komai,idanma za'a dage tafiyar sai lokacin data samu to a dage din" baice mata komai ba,dama
kuma tasan halinta ba zaya tanka ba,don haka taci gaba da sabgarta kawai,tana ta kiran 'yan
uwa daya kamata su sani tana gaya musu batun biya mata umarar,abun mamaki kuma don iya
qarfa qarfa irin na hajja sai take hadawa da zahra kan harda ita za'a tafin,shidai yana zaune
yana cin abinci yana kuma kallon ikon Allah,zahra kuwa na kitchen bata ma san wainar da ake
toyawa ba.

Sai da ya gama cin abincinsa sannan ya miqe ya fice,dole zaiyi maganin hajja,zai kawo
qarshen wannan mulkin mallakar nata,zata ga nasa qarfin ikon akan aurensa,don haka tun a
motarsa driver na jansa ya kira anty alawiyya.


Bayan sun gama gaisawa tayi masa godiya da addu'ar qaruwar aziqi kan umarar da ya
biyawa iyayensu saiyayi mata maganar da ita ta sanya ya kiratan
"Kaya nakeso a hadamin,irin wanda ake hadawa amare a akwati" dariya ce taso kubce mata
amma ta danne,don kada tayi dariyar ta jama kanta jagwal,duk da cewa ita ke gaba dashi
"Ohkey.....lefe kenan....kaman na nawa?,kuma akwati nawa?"
"Akwati bakwai is okey,nayi hidima da kudaden hannuna....amma banison kaya low quality
please,designers kumadd high quality"
"In sha Allah babu matsala"
"Please su zama ready kafin na dawo"
"To shikenan....babu damuwa" saiya yanke wayar ya aje gefa,ya maida idanunsa kan titunan da
suke wucewa.

40


Wayar ya sake jawowa,wata number ya sake laluba,wanda suke masa aikin ginin filin da ya
siya a nan,yadan jima da siyan filin,tun farkon fara aikinsa ya hada albashinsa ya siya,hakanan
da kadan da kadan ake aikin gininsa,yadda zaifi masa sauqi bazai wahala ko ya kashe kudi
masu yawa ba lokaci guda,zuwa yanzu ginin yayi nisa qwarai,don abinda ya rage ma sauran
abubuwan da ba'a rasa bane,da farko yayi niyyar ma ya kammala gidan ya saida,amma da yayi
tunani sai yaga,bashi da mazauni kenan duk sanda yazo ganin gida saidai a cikin
gidansu,auren da aka daura masa da zahra yasa ya fasa saidashin kwata kwata,saboda koba
zahra ba dama dole zaiyi aure,idan kuma yayi auren zai dawwama zuwa gidansu ya
zauna?,dole yana buqatar muhalli.


Da kamfanin yayi magana,ya shaida musu abinda yake da buqata cikin gidan,suka gaya
masa kudinsa da zaya bayar,yayi musu alqawarin turawa zuwa qarshen wata,a sannan suna
can basu dawo ba kenan a yadda ya lissafa,yana saka ran kuma kafin su dawo din an kammala
komai,saiya aje wayarsa yana ci gaba da lissafe lissafensa cikin ransa,zuciyarsa fes,yana jin
wata nutsuwa da sukuni suna ratsashi.


******** **** ********


Bai sakewa hajja zancan tafiyar zahran ba,kamar yadda bai amshi kudinta ba,tayi tunanin
waskewa yakeson yi,saita matsa da mita da qorafi,sai ranar daya sameta zaune ya miqa mata

komai da komai na tafiyar zahran da aka kammala bayan an dage tasu tafiyar da sati daya.


Kwalla ce ta qwacewa hajjan,abinda bai taba zaton gani daga idanunta ba,duka shida
zahra dake zaune a gefanta suka zuba mata ido,jikinsu duka yayi sanyi
"Allah yayi maka albarka,ubangiji yaci gaba da gin riqo da hannayenka,Allah ya kula maka da
rayuwarka,yadda kake taimakon al'ummar annabi kake kula da iyayenka da 'yan
uwanka....Allah yayi maka kyakkyawan sakamako,haidar....kaida zahra Allah shine shaida....kaf
cikin jikokina babu wadanda suka shiga raina kamar yaku,hakan ya sanya nan duniya tun kuna
da qanana bani da burin daya wuce Allah ya hada kanku kuso juna ku zama miji da mata,sai
wani al'amari me daure kai ya soma gudana a tsakaninku,amma hikima ta ubangiji da baya
maida addu'ar bawansa,sai gashi ya kawo hadin aurenku ta fuskar dani kaina ban tsammata
ba.....haidar....ga zahra nan,a yau zan baka amanarta...ka riqe amanar zahra,kai da ita duka
nasan halayenku...hakan ya sanya nake da yaqinin dukkanku kun dace da junanku,zaku
gasgata abinda nake fada din,zahra,haidar yayanki ne kuma mijinki,ki bishi ki masa biyayya,ki
masa biyayya kamar yadda musulunci ya tanada,Allah ya albarkaci rayuwarku" cikin sanyin jiki
dukkansu suka amsa da amin,saita miqawa zahra passport din hannunta
"Zaki tafi umara tare damu,mijinki ya biya miki" kamar a mafarki taji fitar furucin daga bakin
hajjan,saita daskare a zaune tana jujjuya passport din,yau itace zata qasa me tsarki ta
qarqashin ya haidar din?,mutumin da take masa kallon mara qaunarta,wanda bayason yaga
suna farinciki da walwala?,mutumin da take kiranshi da mara ALKIBLA?,mai baudadden
hali,wanda sam ALKIBLARSU bata zo daya ba,ashe ta sanadinsa zata je taga ma'aiki?sai
qwalla ta cika mata idanu,ta sake matsawa kusa dasu muryarta na rawa saboda farinciki
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi,ya qara budi,ubangiji ya biya da jannatulfirdaus" idanunsa ya
lumshe yana jin dadin muryarta hade da dadin addu'ar data yi masa ya amsa da
"Amin".


"Wannan kadanne daga alkhairinsa,alkhairin nasa kuma da zaya shiga rayuwarki matuqar
kika ci gaba da bin maganar magabatanki,matuqar kika ci gaba da daukar zancansu da
muhimmanci,na taba gaya miki,haidar ba irin sauran maza bane gama gari,tun a shekarun
quruciya na gama karantar halayyarsa tsaf,tun kafin na haifeki nake sha'awa inama ina da diya
da idan ya girma zan bashi ita?,yana da boyayyun nagartattun halaye da dabi'u,yana da sauqin
kai da sanyin hali,yana da tausayin mace.....amma dukka ba kowa ke iya karanta da gane
hakan ba,saboda matuqar zaka mu'amalanceshi daga nesa,to tabbas zaka masa fassarar mai
ra'ayin riqau,mai kakkausan hali,mara tausayi ne,mai zafi da saurin fushi,eh aliyyu yana da
ra'ayin riqau akan gaskiya,yana da kafiya kan abinda yasan shine dai dai,yana da fushi idan
yasan an sabawa dai dai ko doka,yana da rashin tausayi akan azzalumin mutum mara
imani,amma matuqar baka da irin wadan nan siffofin,zakaji dadin zama da haidar fiye da
kowane dan adam.....zan baki tips na zama da haidar din,a matsayinki na diyata,ni kuma uwa a
gareshi da tasan halayyarsa,ba don ki mallakeshi ba,sai don ki masa biyayya ku samu zaman
lafiya da qauna me dorewa" wadan nan sune lafuzzan umminta a sanda take shaida mata
batun tafiya da ita bayab ta miqa mata passport dinta ta sanya masa albarka,zama ummin tayi

ta dinga zayyana mata abubuwa masu matuqar amfani a rayuwarsu,har zahran ta dinga
mamaki da kunyar hakan,saidai ta lura ummin ko a jikinta,saboda ta sani tana gyara rayuwar
diyarta ne,tana kuma inganta rayuwar haidar dinta,aikine da takejin ya wajaba a kanta a
matsayinta na uwa

*_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT KANO_*


Da motoci hudu duka aka dunguma aka tafi rakiyarsu filin jirgin saman don wucewa qasa
me tsarki,suna ajesu sukayi bankwana dasu aka maida motar gida,dama daya ta abba yusuf
ce,daya ta abban tsakiya,zasu wuce kuma kasuwa ne abinsu,sauran biyunne na
haidar,mustapha yaja daya,ya shamsu da suke tare da ya sadiq sukaja daya suka koma gida da
sauran yaran gidan da aka taho dasu.


Gaba daya wani irin nauyi takeji,surukutar abba babba da mama takeji tana mamayarta,ko
hira ake bata iya magana cikinsu,dama shi haidar din ba wani gwanin magana bane,sau tari
wayarsa tana hannunsa ne yana faman danne danne,wanda baya wuce duba labarai,ko duba
saqonni da suka shafi aikinsu.

Yana ankare da yadda ta kasa sakewa din,nutsuwar data sakeyi ta bashi mamaki,kusan tun
tale tale yasan zahra cikin yaran gidan,tayi shuhura wajen aikata laifi da samun kariya daga
wajen hajja da a wancan lokacin yake ganin daure mata qarqashi kawai takeyi,abinda ya janyo
rashin jituwarsu kenan,yaci alwashin shi bazai bari ta buwayi kowa ba,duk da girma ya sake
canzata qwarai,amma a yau din ta sake canzawa,wata kamala ta musamman ke kwaranya tun
daga fuskarta zuwa jikinta.


Qafarshi daya dora daya kan daya ya sauke bayan ya gama karantarta,ya duba agogon
hannunsa,akwai sauran lokaci kafin a nemi passingers din,don haka ya miqa a nutse yana
daukar hularsa dake ajjiye gefe ya soma takowa inda suke.


Ita ta fara ganinsa,a sace take kallonsa,tunda suke da shi ba zata iya tuna sau nawa ta
taba ganinsa da qananun kaya ba,yau sai gashi sanye da wata dakakkiyar shadda gezner gray
colour,sabuwar dal,sai maiqo take da daukar idanu,wani irin annurin kyau yake fitarwa na
musamman,gaba daya kamanninsa sun canza kamar ba Aliyyu haidar sojan nan ba,batasan
yaganta,batasan tunda ta fara kallonshin ya ganta ba sai da yazo dab da ita,ba tare da su abba
suna gani ba yadan ranqwafa ta gefan kunnenta kamar xai dauki wani abu
"Idan kinaso kawai kice kinaso,kada ki wani damu da jan ajin nan naki" saiya miqe ya barta
daskare cikin tsananin jin kunya da nauyi,yayin daya bar mata sauran turarensa tana shaqa

wanda ke qara sanyata cikin wani yanayi nason kasancewa dab dashi
"Waini babu inda zan samu ruwa ne,ishirwa fa nake ji tunda muka fito daga gida" hajja ta
fada,sai haidar din yace
"Akwai.....muje a duba mata" yayi maganar yana duban zahra,a hankali ta miqe,tayi gaba yabi
bayanta.


Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare mata kallo yake
tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya cimmata,saiya jera da ita,suka ci
gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar wadansu masu shirin film,lokaci lokaci saisu
waiga kallon juna,kowanne saiya kama dan uwansa,sai kuma kowa ya dauke kansa,saidai shi
haidar yana maida kansa gefe daya ne ya murmusa,komai nata ya gama fallasa kanshi,wai
amma dole saita ja masa aji?,saiya samu kansa da wassafa yadda zai qure jan ajinta da kuma
kunyarta,qaramar dariya ta kubce masa.


Kafin su qarasa provision din haushi duka ya cikata,ta dinga jin ba dadi saboda yadda ake
binsu da kallo,abun haushinma yadda duk 'yammatan da zasu gifta sai taga sun bishi da
kallo,yau aiport din a dan cike take,alamun akwai yawan matafiya kenan a ranar.


"Kai....nasma,kinga sojan nan,wanda ke zuwa gidan general hamza" daya daga cikin
fararen 'yammata uku sanye da baqar abaya ta fada qasa qasa tana tabo ta kusa da ita,wanda
hakan ya faru a kunnen zahra wadda ke tsaye daga qofar provision din tana jiran fitowar haidar
da ya tsaya biyan kudin ruwa da lemon da suka siya,wani abu ne ya takore wuyanta,ta juya a
hankali tadan kallesu,dogaye ne don sun fita tsaho,hakanan farare ne ba kamar ita da take
chocolate ba,hannun kowacce tsadaddar waya ce,wadda aka kira da nasma ta bada attention
dinta inda haidar din yake tsaye,saita fidda ido
"Wow....wallahi shine,don Allah heedaya,yau ko ya za'ayi mu samu number dinsa please" daya
ce ta zaro idanu
"Waye zai tunkari wannan?,ban taba gaya miki yadda muka taba yi dashi ba,tsinannen girman
kai ne dashi,kulashi shine great mistake da zakuyi,ku nema number dinsa dai ta wata hanyar
daban,koda cikin gidan general ne"
"Gidan general ba kowa sai matarsa,duka yaransa sunyi aure,ita kuwa ban tsammanin tana da
number dinsa"
"Quiet sis....gashinan fitowa fa" dayar ta fada,duk sai sukayi shuru har zuwa sanda ya fito din,ya
qaraso inda zahra take,wadda kishi ya cikawa qirji,ranta ya dinga suya.


Jerawa yayi da ita,kuma ta tabbatar yammatan nan sun bisu da kallo,a hankali ta saka
hannunta ta lalubo nashi,saita hade tafukan hannunsu waje daya ta matse gam,taqi kuma
duban fuskarsa.

Mamaki ya kamashi dajin faruwar hakan,saiya bi hannuwan nasu da kallo,laushi da dumin
tafin hannunta yana ratsashi,ya dinga qoqarin lalubar qwayar idanunsa taqi bashi dama,har sai
da sukaje kusa da inda su hajja suke sannan ta fara qoqarin zame hannunta,shi kuma yace
baisan zance ba,hakan yasanya ta dakata da tafiyar da sukeyi,ta juyo tana dubansa,matsowa
yayi gab da ita zai hade tazarar dake tsakaninsu,taja baya da sauri,cikin salon marairaicewa ta
shagwabe masa tana masa inkiya dasu hajja da ido
"Idan kika sake lasa min zuma a baki ko?hmmmm....." Saiya gyada kao ya zare hannun nasa a
hankali,ya soma yarfar dashi,kamar wanda wani abu ya maqale masa.


Cikin jirgi ta kasa ta tsare,saboda ta lura ashe jirginsu daya da 'yanmatan,number din set
dinsu dama daga nashi sai nata,don haka harda qirqirar baccin qarya saman kafadarshi.


Bai fahimta meke faruwa ba sai daga baya,cikin ranshi ya dinga dariya sosai,shikam zuwan
yammatan ma kamar taimakonsa yayi,saiya tallafeta sanda take kwance kafadar tasa yana
tayata,ta dinga zare ido a boye tana tsoron kada fa ta wuce gona da iri.


Hotel me kyau suka sauka,dab da harami,don daga window dinsu suna iya hango
masallaci,su shida harda wata 'yar qawar hajjan da suka hadu a jirgi,itama umara ta kawota
"Daki daya mas'ud da halima su zauna daki daya,daki daya kaida zahra,nida rabi mu zauna a
daki daya" hajja ta tsara yadda zasu zauna,duk da mama najin nauyi amma haka suka
amsa,hakanan itama zahran nauyinsu takeji,ga haidar kuwa sai yaji nutsuwa,yaji har ransa
hakan yayi masa,amma saiya basar bai nuna ba saboda yasan tsiyar hajjan,don haka kowa
shida kayanshi ya wuce dakinsu.


Dakine madai daici mai kyau,wanda yake dauke da duk abinda xasu iya buqata a
kwanakinsu,itace qarshen shigowa don tuni haidar shi ya shigo,tana ajjiye qaramar jakar
hannunta taji ya riqe mata hannu,dubansa tayi,ya kafeta da idanunsa har wani lumshewa
sukeyi,saiya matsa hannun da qarfi har sai data dan saki qara "Badon hajja tace haka ba,da bazaki ce komai ba kenan ko?,saiki bita gotai gotai ki dinga
kwana a bayanta?" Kasa amsa masa tayi,saboda wani nauyinsa kunya da qimarsa data dadu a
idanunta,da kansa ya sakar mata hannun yadan ja da baya sannan ya dauke idanunshi,order
din abinci yayi musu sannan ya wuce bandaki.

Cikin kwanaki biyu suka gama ibadar umara,sai sauran ziyarce ziyarce da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login