Showing 27001 words to 30000 words out of 85584 words
Chapter 10 - Gidan Rina Book by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
K'afarshi sanye da fari sandal kanshi ba hula amma ya gyara sumar kanshi ta kwanta luf-luf
gwanin ban sha'awa.
Hannayenshi zube ciki aljihun wandonshi ya nemi sofa da ke facing d'inta ya zauna ya yi
crossing legs d'inshi, sai wani shan k'amshi yake.
"Sai lokaci ta d'ago ta d'an zame daga kan kujera, cikin muryarta mai d'and'ano gaske ta ce
ina kwana?"
"Saida ya k'are mata kallo ta k'asan ido a zuciyarshi yana yaba tsananin kyau da tayi, cikin
k'asaita ya amsa da lafiya qalau kintashi lafiya?"
"Lafiya qalau Alhamdulillah!
Ta amsa mishi, komawa tayi ta zauna daga haka ba Wanda yasake cewa da d'an uwanshi ci
kanka.
Ita tana operating phone d'inta shi Kuma yana girgiza k'afarshi a hankali, knocking d'in k'ofa
akayi ya yi kamar bai ji ba, cigaba da knocking akayi da d'an k'arfi still ko motsawa bai yi ba
balle tasa ran zai tashi, kallonshi tayi a tsanake, taga tabbas ba shida niyar tashi gani yadda ya
kwanta akan kujera hadda su lumsashe idanuwa.
"Ta6e baki tayi kafin tace Yalla6ai ana knocking.
Shiru bai amsa ba sake mai-maitawa tayi cikin d'aga murya Yalla6ai ana knocking.
"Bud'e idanuwanshi ya yi ya zuba su akan fuskarta ya d'age girar ido, kasa jure kallon eye's
ball d'inshi tayi ta kauda fuska, ya yatsine fuska yace wai waye da wannan sanyi safiya zai nemi
ya takurawa mutane?"
Nifa Allah banaso damuwa mtsss....yak'arasa magana da jan tsaki.
"Saida ya gama jan ajinshi kamar mace sannan ya mik'e ya nufi k'ofar yayin da barrister A ta
rakashi da idanu, Kai wannan guy akwai yanga kalli yadda yake tafiya tafad'a a k'asan
zuciyarta.
"Yana bud'e k'ofa yaci karo da Isah direba tsaye dauke da basket da warmer a hannu, barka
da asuba maigida"
Cewar Isah direba yana murmushi.
Harara ya zuba mishi maimakon amsa gaisuwar tashi, cikin shan k'amshi ya ce Isah banaso
tsohon iskanci, gidan bak'onka ne da za ka tsaya kana min knocking?"
"Allah ya huce zuciyar maigida gani nayi bai kamata na shigo gaba gad'i, a gidan ma'aurata
ba izzini amma tuba nake yi ayi min afuwa.
"Shiru ya yi yana kallon Isah kafin ya ta6e baki ya ce dallah malam wuce ciki banaso iyayi
tsiya.
Ya wuce gaba Isah yana biye da shi ina kwana amarya?"
Cewar Isah yana washe hak'ora.
Cikin fara'a ta amsa da lafiya qalau ta mik'e ta kar6i warmer d'in hannunshi, ta nufi dining area
yayin da Isah ya bita rik'e da basket.
Ta ajiye warmer akan dinning table ta kar6i basket d'in had'e da furta sannu da k'ok'ari an gode.
Yauwa amarya!
Isah ya fad'a had'e da juyawa ya koma parlour, cikin girmamawa ya ce maigida ko kana da
buk'atar wani abu na tsaya?"
"Girgiza Kai ya yi na barka lafiya Isah ya fad'a had'e da nufar k'ofar fita.
Saida ta dauko plate da mugs had'e da spoons a kitchen, sannan ta shiga bud'e warmers d'in ta
farko wainar shinkafa ce tayi laushi har ta gaji ta bud'e ta biyu miyar taushe ce taji tantakwashi,
k'amshi ya buge hancinta, sai guda d'aya mai dauke da chips da fry plantain sai sauce d'in
Koda da hanta ya ji karas da cabbage, sai flakes mai dauke da kunu gyad'a yaji Madara fari
kal....da shi ga Kuma farfesu kayan ciki da na cow tail ta gyad'a kai ciki da yabawa, dole ta
koma parlour domin ta Kira d'an iko nata ya zo ya yi breakfast.
"Yalla6ai nayi arranging table ka zo kayi breakfast.
"Saida ya yi mata kallo na nashi na d'age girar ido kafin ya gyad'a kai, tsaye tayi tana jira ya
tashi Saida ya gama jan ajinshi sannan ya mik'e tabi bayanshi, da sauri ta jawo mishi kujera ya
kalleta ya yatsine fuska da sauri ta kauda nata fuska, ya zauna ta dauki plate batare da ta kalle
shi ba ta ce akwai waina da chips wane za'a zuba maka?"
"Bana cin abinci mai nauyi.
Ya fad'a batare da kalleta ba.
Na zuba ma chips kenan?"
Ya gyad'a kai.
Ta zuba ta ajiye a gabanshi.
Ki je store ki dauko kayan tea ki had'o da nessacoffe.
"Yana gama magana ya koma jikin kujera ya lafe, ya Kuma yi folding hannayenshi a kirji.
Mamaki ne ya lullu6eta gani yadda ya yi mata magana cikin izza da gadara, bata ce komai ba
ta tafi store ta dauko abinda ya buk'ata tea za'a had'a maka?"
"Coffee!
Ya fad'a a takaice.
Ta shiga had'awa za ta zuba sugar ya ce bana shan sugar, honey za ki zuba.
"Shiru tayi na seconds kafin ta ce ina zuma yake?"
"Ki je store ki duba.
"Dole ta koma store da kyar ta gano idan Zuma yake ta dauko, ta zuba tea spoon uku ta juya ta
ajiye mishi.
Na waye?"
Ya furta can k'asan mak'oshi.
Me kenan?"
Tafad'a tana kallonshi.
Coffee!
Ta hadiye yawu kafin ta ce naka ne.
Humm.... barrister bana Shan zak'i sosai Zuma da ki ka zuba ya yi over.
Yanzu kam sosai taji ranta ya6aci ya fara kaita bango da reni wayonshi, da kyar tayi control
temper ta ta ce Yalla6ai miyasa tun farko da nake had'awa ba ka fad'amin adadin Zuma da zan
zuba ba?
Ya d'ago idanuwanshi Yana kallonta gira d'age yayin da ta kauda fuska.
Ya ce had'a coffee yana miki wuya ne?"
Girgiza Kai tayi.
To sake had'a min wani banaso musu.
Batare da ta ce komai ta dauki wani mug ta sake had'awa, ta kalle shi ta ce spoon nawa zan
zuba na honey?"
Yatsanshi guda ya d'aga ta6e baki tayi ta d'an juya coffee ya rage zafi ta ajiye mishi, sannan tayi
serving kanta waina ta zuba ta ci ya rigata tashi duk da ta lura bai wani ci abinci kirki ba.
Tana kammalawa ta kwashe plates d'in suka yi using ta nufi kitchen ta wanke, sannan tadawo
parlour Koda ta shigo Yana waya Yana gama waya ya mik'e ya dubeta ya ce ni zan fita.
Muryarta asanyaye ta ce adawo lafiya.
Har ya juya ta ce Yalla6ai karka manta ajima around 9:00 o'clock za mu tafi dinner da abokan
aikina suka shirya mana.
"Ya juyo ya k'ura mata idanu kamar mai nazari, ta sunkuyar da Kai k'asa.
Wai ke har yanzu bidi'o'i naki ba su gadi k'arewa bane?"
Yalla6ai ba wani bidi'a abinci ne kawai za'a ci a wuri, don Allah ka taimaka min mu je idan ba
mu muje ba zasu ga kamar na musu wulak'anci.
Ta k'arasa magana kamar za tayi kuka.
Batare da ya ce da ita zai je ko ba zai je ba yai tafiyarshi, ranta ya sosu ba kad'an ba saidai
batada yadda zata yi ta zuba tagume ta afka tunanin irin zaman da za suyi domin tun tafiya bata
yi nisa ba tafara gajiya da halaye Aliyu.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*Haske writers association*
*GIDAN RINA*
_this page is for you Rahinerth alk'aluma shidda suna jin dad'in comments d'inki keep its up
dear!_
*18*
Zuwan barrister Z gidan ya rage mata tunanin Aliyu, nan take ta bata labarin yadda tayi da shi.
Karki damu bebs ko wancan karon haka ya yi mana kamar ba zai je ba, sai gashi duk events
d'in da akayi ya yi attending.
"Ki saki ranki inshallah ko wannan zai je, Aliyu bahagon mutum ne ba kasafai ake gane idan
ya dosa ba.
Yakamata ki jajirce zama da irinshi sai an shirya.
"Talla6e kumatu tayi tana kallon barrister Z kafin ta ce ni zan gayamiki bebs yau da safe wurin
breakfast kawai saida ya haddasa min headache, labari abinda yafaru ta shiga gayawa Zarah.
Dariya sosai barrister Z taci tabbas bebs Aliyu ne dai-dai ke kina tak'ama miskilanci sai gashi
kin had'u da Wanda yafi ki.
Bari kawai bebs na had'u da gamo na.
Gaskiya kam bebs kin had'u da gamonki sai hak'uri.
Dariya suka yi daga bisani suka mik'e suna zagaya gidan, yayin da Barrister Z sai yaba kyau da
tsarin gidan take.
*****""'***""******
Tun misali k'arfe 7:00pm wacce za ta yi wa barrister A makeup d'in zuwa dinner ta zo, kuma har
zuwa lokaci Aliyu bai dawo gida ba.
Saida ta sallaci sallar isha'i aka fara tsantsara mata makeover, black gown tasaka aka nada
mata bride turban White colour, tayi kyau na ban mamaki saidai duk zuciyarta a chakud'e take
sakamakon rashin sani manufar angon nata.
Sai k'arfafa mata gwiwa Barrister Z take duk da haka hankalinta bai kwanta ba.
Lokaci sai ta tafiya yake dole tafito, barrister Z na biye da ita har suka iso parking lot, da sauri
Isah direba ya bud'e mata mota kirar jeep Volkswagen farar tass....da ita tana danna kanta ta
gashi zaune ya yi relaxing sai faman operating wayarshi yake, k'amshi perfume d'inshi ya cika
motar. Batasan lokaci da tasaki ajiyar zuciya ba.
"Batare da ya kalleta ba ya ce barrister ga ki da son bidi'a amma bakida kama jiki, almost 20
minutes ina zaman jiranki har nafara tunani ko kin fasa zuwa dinner ne, na kama gabana.
Saida ta zauna kusa da shi ta kuma k'are masa kallo, sannan ta ce lamarinka sai kai Yalla6ai
tunani bai bani za ka je dinner ba.
Sai gashi har zaman jiranki nayi.
Ya karasa magana yana ta6e baki tare da cewa wai Isah me kake jira ne da ba za ka ja mota
mu tafi ba?"
Umarninka nake jira maigida.
"To na ba ka umarni sai ka ja motar mu tafi, kana k'ara 6ata mana lokaci.
A tunaninta idan ya gama magana da Isah zai kulata sai taga sa6ani hakan.
Don haka ita ma taja bakinta ta tsuke Bata k'ara cewa uffan ba har sanda suka iso hall d'in,
suna fitowa ya rik'o hannunta suka k'arasa ciki hall, dinner ta k'ayatarda Aliyu matuk'a a cewar
shi duk events d'in suka yi ba wanda ya burge shi irin dinner d'in, saboda ba hayaniya sai slow
music ke tashi anci ansha anyi couples dance sai kusan 1:00am aka tashi kowa ya kama
gabanshi.
"Tun a mota tafara bacci har suka iso gida bata saniba, tasheta Aliyu ya yi ta hanyar cewa
barrister ki tashi mun iso gida.
ko motsawa bata yi ba ji ya yi zai iya tafiya yabarta anan, har ya bud'e mota ya fita ko me ya
tuna sai dawo gefen da take, ya shiga bubbuga hannunta da k'arfi bugu d'aya zuwa na biyu ta
bud'e idanunta masu cike da bacci.
"Fahimta abinda ke faruwa tayi shiyasa bata furta uffan ba tafito tana rangaji tana had'a hanya
ta nufi cikin gida, dai-dai k'ofar shiga main parlour ta kusa fad'uwa da sauri ya tarota ya rik'o
shoulder ta, ya d'an rungume rabin jikinta yayin da ya sak'ala d'ayan hannunshi akan waist
d'inta. "Wani irin kunya taji ya lullu6eta sakamakon yadda ya rungume waist d'inta nan take ta
wartsake daga baccinta, a haka suka cigaba da tafiya har zuwa bedroom d'inta.
A gefen gado ya zaunar da ita ya kalleta ta k'asan ido ya ga yadda take lumshe ido alamar
bacci bai gama sakinta ba, ya ce kiyi k'ok'ari ki rage kayan jikinki za ki fi jin dad'i kwanciya.
Daga haka ya juya har ya murde handle ya d'an juyo cikin wani irin murya ya furta "Good night!
Murmushi tayi kafin ahankali ta ce "Good night!
Haka kawai ta tsince kanta cikin nishad'i marar misaltuwa, umarninshi tabi ta hanyar sauya kaya
zuwa sleeping dress.
****""***"""'*****
Washe gari!
Kasancewar gajiya tayi musu yawa hakan ya basu damar yin bacci, Kuma da yake daga gidan
Daddy ake kawo musu abinci.
"A kwana na shidda da bikinsu tana zaune a falonta tana tunani fara girki a yau, saidai batasan
miye favorite d'inshi ba.
Gani za ta wahalada kanta a banza yasa ta mik'e ta nufi falonshi da ke upstairs, ta tura k'ofar ta
shiga da sallama zaune ta sameshi yana aiki a system.
Jin motsi bud'e k'ofa da kuma k'amshi fitinane turareta ya bugi hancinshi, yasa d'ago da
kansa ya kalleta sai kuma kauda kai ya cigaba da aikinshi.
Cikin tattausan lafazi ta ce barka da hutawa Yalla6ai!
Saida ya6ata almost 20 seconds kafin ya amsa da yauwa ya akayi ne?"
Yalla6ai dama zuwa nayi na sanarda kai yau inaso nafara girki da kaina, saidai bansan abinda
ka fi so ba.
"Uhm!
Ke nan kin iya girki ne?"
Bata yi mamaki tambayarshi ba saboda tasan fiye da hakan ma, zai iya aikatawa.
"Ba laifi ina k'ok'artawa.
Uhm!
Ba ki iya ba kenan?"
Sai an bani dama anan za'a gane iyawa na.
Ki yi hak'uri da girki nan har mu je Abuja, tsananin dad'ewarmu a garinan ba zai wuce 7 days
ba.
Shikenan tunda haka ka za6a na barka lafiya, takarasa magana had'e da ficewa.
Bayanta ya bi da kallo kafin dawo da ganinshi akan system.
Haka zamansu ya cigaba da kasancewa kowa yana sha'anin gabanshi, tun abin yana damunta
har ta zo tafara sabawa dama tasan baya sonta, bata tunani zai so ta koda zuwa gaba ne.
Shiyasa tayi hak'uri da yadda ta tsince kanta aciki, ko ba komai ta fitarda iyayyeta kunya, ta
kuma yi musu biyayya dama kuma ance bin na gaba bin Allah.
***'"***'"***'''***
Da misali k'arfe 5:00pm na yammacin ranar tana zaune a falonta, Indian series take kallo, text
ya shigo wayarta a zatonta ko alert ne.
Saboda tana expected d'in wasu kud'ad'e da azama ta dauki wayarta, ta shiga inbox *ki shirya
za mu je ki yiwa su momma bankwana tomorrow morning za su wuce Abj ki shirya yanzu nan
karki 6atamin lokaci*
Murmushi tayi had'e da girgiza kanta ganin yanzu nan ya wuce ta, amma tsabar ya tsaneta ba
zai iya yi mata magana ba shine yake turo mata text.
"Ta tashi jiki asanyaye tashiga bedroom d'inta ta canza kaya zuwa wata French gown,
maroon colour tayi rolling da white scarf, tasaka takalmi heel tafito rik'e da 'yar k'aramar purse
d'inta a hannu sai zuba k'amshi take.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*19*
A main parlour ta tararda shi tsaye yana jiranta, yana sanye da fari material na maza wanda ya
yi masifar k'ara fitowa da kyakyawar halittarshi, tana fitowa yafice zuwa parking lot.
Tabi bayanshi tuni Isah direba ya jawo mota, ya fito ya bud'e musu k'ofa suka shiga yaja motar
suka fice daga gidan.
K'amshin perfume d'inshi ya garwaye da nata ga kuma sanyi Ac motar, ya had'e ya bada wani
daddad'an k'amshi mai tafiyar da ruhi da gangar jiki.
"Tafiyar kurame ce ake yi daga shi har ita ba wanda ya furta uffan, afakace ya sace kallonta
ya dauke fuska.
Gani ba girmanshi bane satar kallonta yasa ya fito da wayarshi ya kira wani business partner
d'inshi.
"Hakan yasa ta mayarda hankalinta ga kallon gefen titi.
Koda suka iso gidan ya wuce gaba ta bi shi abaya har zuwa sitting room d'in gidan, anan suka
iske momma zaune da alamar tasan da zuwan nasu.
Barrister A ta durk'usa har k'asa gwiwa biyu-biyu ta gaidata.
"momma wacce ke hakince akan two sitter tana shan k'amshi wanda atsawon rayuwarta ba'a
ta6a gaidata haka ba.
"Kauda fuska tayi tana wani yatsina, ta bud'e baki da kyar ta amsa da kina lafiya?"
"Lafiya qalau!
Cewar barrister A da yake ita ba k'aramar yarinya bace, ta hango tsan-tsan kiyayyarta a kwayar
idon momma.
Shi kanshi Aliyu bai ji dad'i yadda momma tayi mata ba, shine ya yi k'arfin hali cewa tashi ki
zauna akan kujera.
"Girgiza kai tayi ta gyara zamanta akan rugs carpet ta sadda kai k'asa, girls d'in momma na
shigowa falon suka yi arba da ita suka sa ihu, har rige-rige zuwa wurinta suke.
"Hatta Teema da batada lafiya dariya take tana tafa hannayeta, tana jujjaya kanta alamar
tana farin ciki ganinta.
"Sai lokaci ta d'an saki jikinta, tana murmushin yak'e, hannunta Teema ta k'ank'ame sai faman
lek'e fuskarta take tana dariya.
"Sosai haushi ya turnuk'e