Showing 54001 words to 57000 words out of 85584 words
Chapter 19 - Gidan Rina Book by Hauwa Shehu Aliyu.pdf
samu matsala ta dalilin aikinki. Ya karashe magana yana wani k'ara daure fuska.
"Murmushi tayi mai sautin gaske ta ce "Yalla6ai kenan har yanzu kana da saura sani wacece
Barrister Amina Abdallah Barkid'o, shiyasa har kake wannan tunani akaina anyway zan kiyayye
kaman yanda ka fad'a.
"Haka ya kamata ki fad'a ba wai ki ce ina da sauran sani akani ba.
Murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take yi, lokaci kwanciyarsu bacci ya yi yau ma a
dak'inshi suka kwana saida ya, ya motsata son ranshi sai dai bai yi mata komai ba sannan suka
yi bacci.
Washe gari kasancewar Juma'a ce k'aramin lokaci ne yasa ta tashi da wuri ta had'a mishi
breakfast kaman yanda ta saba, bayan ya kammala ta raka shi sai dai yau iya k'ofar fita main
parlour ta tsaya, ya bata goodbye kiss sannan ya nufi flat d'in momma koda ya shiga bedroom
d'inta tana wanka, sai kawai ya wuce na Daddy cikin tsananin damuwa ya tararda Daddy, sosai
Aliyu ya tsorata da gani mahaifin nashi cikin wannan yana yin.
"Jikinshi ya yi matuk'ar sanyi ya nemi kusa da Daddy ta yadda zai fuskance shi da kyau ya
zauna.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:18 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*30*
Saida ya k'arewa Daddy kallo kafin ya ce "Don Allah ka daure ka gayamin abinda ke damunka,
bana jin dad'i ko k'adan idan naganka cikin dumuwa.
"Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya shafi gemunshi cikin rauni murya ya ce Sultan ni kaina ba
zan iya fad'ar takamame abinda ke damuna ba, saidai inaji kaman narasa wani gurbi a jikina.
"Aliyu ya yi shiru yana nazarin maganganu Daddy, kafin ya nisa ya ce "Daddy na fahimce ba
kaso ka sanarda ni damuwarka, amma koma menene ka rage tunani kada ya shafi lafiyarka.
Shikenan my boy zan yi amfani da shawararka sai abu na gaba ina tunani lokaci ya yi da zan
fita da Maryama abroad a duba lafiyarta, ko Allah zai sa adace ni sai nake mamaki meyasa duk
tsawon lokaci da Maryama ta dauka cikin rashin lafiya na kasa bata kulawa yadda ya dace.
Sultan ina zargin kaina da rashin yi ma rayuwar Maryama adalci, musanmman idan na tuna da
irin hallaci da ta yi min.
Rashin lafiyar Maryama tana d'aya daga cikin abinda ke adabar ruhi da gangar jikina, a duk
kwana duniya sai nayi yunk'uri shiga flat d'inta na dubata sai naji na kasa.
"my boy ka sakani a addu'a Allah ya yaye min wannan matsala, inajin tsoro na mutu a wannan
yana yin tabbas ubangijina zai tuhume ni akan rashin adalci da na shinfid'a a gidana.
Tsawon shekara 28 da nayi watsi da rayuwar Maryama ban kuma sake waiwayarta ba, abin
takaici mu kwana mu tashi a gida d'aya.
"Lokaci ya yi da zan gyara abinda na 6ata banaso na mutu da hakki Maryama.
Ya karashe magana hawaye na zuba daga kwarmin idanuwanshi.
Naunayyar ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya gyara zamanshi ya rik'o hannun Daddy na dama ya
had'e da nashi, ya sanyayya muryarshi ya ce "Daddy ka daina blaming kanka is not your fault
musanmman idan akayi la'akari da yana yin aikinka wasu abubuwa ba za ka iya gudanarda su
da kanka ba, in fact Daddy naga momma tana kula da ita sosai. Ajiyar zuciya Daddy ya yi ya ce "please.....Sultan idan ina magana ta arziki ka daina sako min
mommanka, wallahi ko sunanta banaso ji.
Cike da mamaki Aliyu yake kallon mahaifin nashi kafin ya nisa ya ce "Daddy kun sami matsala
ne da ita...?
Ba ko d'aya kawai dai banaso zancenta mu ajiye shi a gefe, muyi wani.
Shikenan Daddy wane country kake tunani a fita da ita sai na nemo muku visa....?
Nayi magana da Dr Williams ya ce akaita Indian saboda suna da kwararun likitoci kwakwalwa.
Ba matsala Daddy yaushe kake so tafiyar...?
Nan da two weeks shima a dalilin inaso naje Lagos, da na dawo sai muyi tafiyar.
Ba damuwa ka barmin komai a hannuna.
Cewar Aliyu yana mai mik'ewa tsaye ni zan wuce Daddy daga nan suleja zan wuce na kwana
biyu banje gidan gona ba, jiya ma Abbas ya kirani yana gayamin abincin kifi ya k'are.
Allah ya tsare ya kai ka lafiya.
"Amin Daddy ka kula da kanka banda yawan tunani.
Murmushi kawai Daddy ya yi yana jin k'aunar d'an nashi na yawo a sassan jikinshi.
Abinda Daddy baisani ba tun daga lokaci da suka fara magana momma tana la6e, duk firar da
ta wakana atsakaninshi da Aliyu akan kunnenta saida taji motsin fitowar Aliyu ta ruga da gudu
ta 6oye cikin curtain saida yafita sannan tafito daga ma6oyarta.
***----*****-----****
Barrister A tana dawowa daga raka Aliyu ta tattara plates d'in da suka yi amfani ta shiga kitchen
ta wanke, tana kammalawa ta zari Hijabinta tafito compound adaidai baranda da tasaba
tsayuwa tayi tsaye tana kallon shige da fice na mutanan gidan can ta hango Sa'eed yana ba
flowers ruwa, wani gajere tunani tayi ta nufi wajenshi yana ganinta ya runsuna ya gaidata ta
amsa tana d'an siriri murmushi "Sa'eed idan ka kammala aikinka ka sameni a garden I have
some important matter to discuss with you.
Duk da ya tsorata da jin farucinta bai bari fuskarshi ta nuna hakan ba, sai cewa ya yi okay
ma'am.
Ta juya ta nufi garden ta zauna tana jiran zuwanshi bata jima da zama ba sai gashi ya zo,
kujerar da ke facing d'inta ta nuna mishi please have a seat!
Ya zauna yana d'ari-dari ka saki jikinki Sa'eed tambayar da zan maka tana da matukar
muhinmmanci.
To ma'am Allah yasa ina da amsar tambayar naki.
"Amin!
Tafad'a had'e da yin shiru na wani d'an lokaci ta nisa had'e da cewa Sa'eed I trust you
completely shine dalilin da yasa na kira ka anan.
Sa'eed!
Yes ma'am!
me kasani akan mahaukaciyar da ke cikin gidanan....?
Wacece ita menene matsayinta anan gidan?
Shiru ya yi na few seconds saboda haka barrister A bata katse mishi shiru nashi ba, sai ma tayi
amfani da shiru nashi tana karantar yana yinshi.
"Asanyayye Sa'eed ya d'ago saida ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "ma'am gaskiya ba
komai nasani akanta ba zan ba ki labari iya abinda nasani, saboda ban wuce ten years da fara
aiki a gidanan ba wani abu yafaru akan idanuwana wani kuma nasamu labari daga bakin wasu
ma'aikata da suka rigani zuwa gidan "Kaman yanda nasamu labari Hajiya Maryama ita ce uwargidan Alhaji M Ardo, tsawon
shekaru 28 kenan da ta had'u da wannan lalura, doka ce agidanan ba'a bari ma'aikaci ko d'aya
ya kusancin koda baranda flat d'inta ne, duk yawan mutane da ke gidanan idan kika cire Hajiya
Zaituna ba wanda ke shiga wurinta. Ni kaina ina mamaki wane zunubi ta aikata da yasa mijinta ya wofitar da ita har haka.
"Abinda zai ba ki mamaki ma'am tsawon shekaru goma da nayi agidanan banta6a gani wani
ko wata daga danginta ko na mijinta da suna ya zo ganinta ba.
"Barrister A ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta talla6e kumatunta da hannayenta, ta ce "Sa'eed
anaka hasashe me ya kawo wannan rashin kulawa da Maryama take fuskanta daga bangare
biyu mijinta da danginta...?"
Meyasa kuma iya Momma ce kadai ke shiga flat d'inta...?
"Sa'eed ya nisa had'e da juyawa ya kalle hagu da damarshi saida ya tabbatar da ba wani ido,
sannan ya ce ma'am maybe yana da alak'a da labarin da maigadi Daniel ya ta6a bani.
"Wane irin labari....?
Cewar barrister A cikin k'osawa.
A yanda Daniel ya labarta min ya ce Hajiya Zaituna asiri tayi ma Alhaji M Ardo shiyasa baya
kulawa da Maryama kuma yana zargin ita ce silar haukacewa Maryama, saboda akwai wata
rana da nurse d'in da take kula da Maryama ta zo dubata ya yi la6e ta window ya ga lokaci da
nurse d'in take yi ma Maryama wata allura wacce ba ko shakka batada nasaba da ciwonta, ya
ce lokaci da aka yi mata allurar yana kallon yadda ta dinga gurnani tamkar ranta zai fita, daga
bisani tayi bacci ma'am duk yadda kike tunani wannan murd'ade al'amari ya wuce da saninki
gidanan tamkar gidan Rina ne komai nashi ya sha bamban da sauran gidaje.
"Shiru barrister A tayi kanta ya dau zafi ba k'aramin rud'ani ta shiga ba ta sauke ajiyar zuciya
yafi a kirga da kyar ta k'irk'iro murmushin dole ta ce "Sa'eed nasan za ka yi mamaki yadda nake
maka wad'annan tambayoyi na yarda da kai Sa'eed shiyasa na za6e ka don ka warware min
wannan al'amari, idan har da gaske momma ce silar haukar Maryama ni kuma na dau alk'awali
sai nayi silar dawowa da ita cikin hankalinta, kuma sai na daidaita tsakaninta da Daddy wannan
alk'awalina ne.
"Nima ina goyon bayanki hundred percent ma'am idan kina buk'atar wani taimako daga gareni
ashirye nake da na taimaka.
"Nagode Sa'eed indan buk'atar hakan ta taso zan nemi ka kuma wannan ya zama sirri
atsakaninmu.
"Karki damu ma'am insha Allah ba wanda zai ji wannan sirri daga gareni.
Cewar Sa'eed yana mai kallon fuskar barrister A.
Shikenan Sa'eed za ka iya tafiya.
Nima nagode ma'am ya karashe magana had'e da mik'ewa tsaye ta bishi da kallo har ya
6acewa ganinta sannan tayi ajiyar zuciya, ko ta wane hali dole ta nemi Baaba laraba tasamu
wasu information daga gareta.
"Mik'ewa tayi ta koma flat d'inta da zumar daga baya zata nemi Baaba laraba.
A bangaren momma kuma tana gani ficewa Aliyu ta koma bedroom d'inta ta kira Jarumi a waya
ta bashi labari abinda ke faruwa, sosai ya harzuk'a har tana jiyo hucinshi kaman zai kama da
wuta.
Ranshi a 6ace matuka ya ce "Abinda nakeso da ke Zaituna ki bi kowace irin hanya ce ki
hanawa barrister A shiga flat d'in Maryama, shigarta wurin zai iya 6ata mana plans da sauri shi
kuma M Ardo ki barni da shi ni nasan ta yanda zan bullo mishi.
Bai tsaya jin ta bakinta ba ya yi hanging up.
***"""***"""****
Around 9:20pm Aliyu ya shigo gida Saidai fuskarshi ahad'e ba fara'a ko k'adan ba kaman yadda
ya fita da safe ba.
Tana mishi sannu da zuwa ko inda take bai kalle ba, balle ya amsa mata ya ra6a ta gefenta ya
haura sama, ta bishi da kallo baki sake tayi shiru tana tunani laifi me tayi mishi da zai mata
haka, iya saninta har suka rabu batasan ta mishi wani laifi ba ko bayan tafiyarshi ya kirata a
waya kuma ko awayan lafiya qalau suka rabu. "Maybe ko awaje ne aka 6ata mishi rai to ni miye laifina da laifin wani zai shafe ni..?
Tafad'a a k'asan zuciyarta har tayi niyyar ta share shi sai kuma tafasa, ta haura steps tanufi
bedroom d'inshi ta murd'a handle had'e da sallama ya amsa mata adak'ile shima ya amsa ne
saboda sani darajar sallama da ba zai amsa mata ba, ko inda take bai son kallo don haka ya
juya mata baya yana cire kayan jikinshi da sauri ta nufi bathroom ta dauko mishi bathrobe ta
mik'a mishi mtsss....ya ja mata tsaki had'e da ra6ata ya shiga bathroom sai kuma ya lek'o da
kanshi sounding very angry ya ce "kada ki kuskura na fito na sameki a d'akina daga haka ya
rufe k'ofa, ya barta tsaye turuss...tana kallon k'ofar bathroom jin saukar ruwa yafara wanka yasa
tafice for the first time da taji tausayin kanta ya lullu6eta da ta tuna da irin zazzafar soyayyar da
take mishi bata ankara ba taji saukar hawaye akan kumatunta, da saurinta ta sauka k'asa ta
shiga kitchen ta jingina bayanta a kitchen cabinet tasa kuka mai cin rai she is totally confused,
me tayi ma Aliyu zai mata wannan wulak'anci.
Da ada ne zata iya daurewa a yanzu kam ba za iya ba, saboda yariga ya saba mata da
kulawarshi da soyayyarshi, idan ya ce zai juya mata baya ba ko shakka zata iya susucewa ko
kuma tayi 'yar k'aramar hauka.
"Ta kasa jurewa ta share hawayenta tafito ta zauna a dining table, tana jira ya fito cin abinci
tafi 10 minutes a zaune amma ba Aliyu babu labarinshi, tana gani haka tagano nufinshi ko
abincin nata ba zai ci ba.
Zata iya jure komai daga gareshi amma ba zata iya jure ya kwana da yunwa ba ta tashi da sauri
tanufi upstairs.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:18 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*31*
Ahankali ta murd'a handle k'ofar ya bud'e ta danna kai, ta hango shi zaune akan resting chair ya
lankwashe k'afarshi d'aya akan chair d'in, yayin da d'ayan k'afar take k'asa ya saka laptop
atsakiya yana operating bud'e k'ofar da tayi yasa ya d'ago afusace ya ce "whats the hell are you
doing in my room...? Banace banaso ganinki ba me ya dawo da ke...?
"Tuni idanuwanta suka ciciko da hawaye she can't take its anymore ji take kaman ta d'ora
hannu bisa kai ta dinga ihu, cikin rawar murya mai dauke da alama so yi kuka ta ce "Yalla6ai I'm
sorry...ni bansan laifi da nayi ma, ba don Allah daure ka fad'amin laifi da nayi maka na rok'eka
gafara.
"Ke dallah rufemin baki I can't wasting my precious time akanki don haka kifita ki bani wuri.
Kuka ta fashe da shi tana fad'i "Ba zan fita ba koda za ka kasheni Yalla6ai haba don Allah
meyasa za ka dinga treating dina haka..?
Cikin muryar fushi ya ce "Duk wannan kuka da kike yi na munafuci ne you really disappointed
me Amina, me nayi miki da za ki za6a ki wulak'anta min mahaifiya...?
"Kukanta ya tsaya cak...tasaki baki da hancinta tana kallonshi wato tanan momma ta 6ullo.
Ba shakka kuwa tayi nasara amma zata tabbatar ta rusa nasararta ta.
Da sauri ta durk'usa daf...da shi ta rik'o soft hand d'inshi ta matse anata tana massage palm
dinshi ahankali, hawaye na kai da kawo akan kumatunta ta tausassa muryarta, ta ce "Kada
Allah ya kawo min wannan bak'ar rana arayuwata da zan wulak'anta koda 'yar aiki mahaifiyarka
ce Yalla6ai balle mahaifiyarka. Idan har ni Amina zan iya wulak'anta mahaifiyarka to ashe kuwa zan iya wulak'anta tawa
mahaifiya.
"Tun daga lokaci da tafara magana jikin Aliyu ya yi sanyi, shiru ya yi yana tuno wacece
momma tun yana cikin zani goyenshi zai iya bada labarin halayyata, yafi kowa sani makircin
mahaifiyarshi musanmman da ya tuna bataso aurenshi da Barrister A saboda haka zata iya bin
kowace irin hanya don ta kawo 6araka atsakaninsu. "Cikin sanyi murya ya ce "Mekika je yi flat d'in Maryama...?
Ba komai Yalla6ai kawai naga anbar flat d'in da dirty shine nasa housemaid su tsaftace, ni kaina
bansan hakan zai jayomin laifi awurin momma ba.
To amma ni ba haka momma ta gayamin ba.
"Zaro idanuwa tayi tare da fad'i na shiga uku me ta ce da kai Yalla6ai...?
"Murmushi ya yi had'e da d'ago ha6arta yana kallon cikin idanuwanta, ya ce manta kawai
banaso maimata zance, ni kaina banaso ki sake zuwa flat d'in wannan matar she's very
dangerous zata iya cutar min da ke ba zan manta ba lokaci da ina k'aramin yaro na ta6a shiga
flat d'inta kinsan me ya faru...?" Cike da zumud'in son jin labarin ta girgiza kanta.
A wannan lokaci rufeta kawai ake yi a d'akin kwanata, tsautsayi yasa ni shiga wurinta tana arba
da ni ta k'ank'ameni a jikinta kaman zata mayarda ni cikinta, ga wani irin gunji kuka da take yi
da kyar aka cireni daga jikinta, tun daga lokaci momma ta hanani shiga wurinta da yake nima na
tsorata matuk'a shiyasa har zuwa yau da nake ba ki labari k'afana bai sake shiga wurinta ba. "Tagwaye ajiyar zuciya ta sauke ta rangwad'ar da kanta tana kallonshi ta ce "gaskiya Yalla6ai
matar nan tana da ban tausayi ya kamata ku taimaka mata, tsawon shekara 28 tana rufe ba fa
kwana 28 bane shekaru ne masu yawan gaske don kawai Allah yasa tana da saura kwanaki a
duniya da tuni an shafe babinta a duniya. Ta6e baki ya yi yana fad'i a kwananan Daddy zai fita da ita Indian, insha Allah zata sami lafiya.
"Yauwa Yalla6aina tashi mu je kaci abinci.
Mik'ewa ya yi yana murmushi suka sauko downstairs hannayensu sark'e da juna, suka nufi
dining area d'aya daga cikin kujerun dining table taja mishi ya zauna ta dauki plate tayi mishi
serving, sannan taja kujerar da ke facing d'inshi ta zauna tare da serving kanta, ahankali suke
cin abincinsu ba ka ji komai sai k'arar spoons suna kammala cin abinci