Showing 1 words to 3000 words out of 42614 words
[7/31, 10:34 PM] +234 814 290 6707:
*AL'AMARIN UBANGIJI.*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W.*
*Mmn Abduljalal.*
1-5.
*Domin Nishad'inku masoya.*
مسب* الله نمحرلا *ميحرلا
*"D*addy, gaskiya wnn qauye ya min,
ya ban sha'awa ba kad'an ba, har naji kamar na dawo nan da zama.
"D'an nema, tun yaushe nake binka mu zo tare da kai kana qi, an gaya maka ni d'in a banza
nake son zuwa qauyennan ne.
Duk lokacin da na ziyarci qauyennan nakan samu nitsuwa ,kwanciyar hankali da nishad'i.
Snn yakan tuno min da abubuwa da dama wad'anda suka shud'e, shi yasa kaga bana jimawa
ban leqo ba."
"Gaskiya daddy, nima ai yanzu na gane, tare zamu riqa zuwa."
Kallon shi na d'an lokaci daddy yayi.
"Kai Habibullah, wato babu maganar karatu a agender ka ko, har yanzu baka shiryawa tafiyar
ba kenan kake ikrarin zamu rika zuwa nan tare.
Shafa kanshi Habibullah yayi yana neman abunda zai cewa daddy.
Isowar wata 'yar yarinya da gudu ya ceceshi dan ya rasa excuse din da zai bawa daddy.
Yarinyar tayi butu butu da ita, uniform dake jikinta duk yasha qura, gaba daya jikinta datti ne.
Kafa gwiwowinta tayi a kasa dab da tabarmar da suke zaune a kai, tana washe kananan fararen
hakoranta, tana kuma haki, alamar taci gudu.
Idonta kan Daddy tace "Lah, baba Alhaji, yaushe kazo."
Shima kallonnata yakeyi da murmushi d'auke a fiskarsa, kafin daga bisani ya kawar da fiskarshi
alamar fushi yake da ita.
"Nayi fushi 'yar Baba, tun jiya nazo garinku amma ban saki a ido ba sai yanzu."
Karyar da kanta tayi tace "Ayya, yi haquru Baba alhajina, bansan kazo ba."
Sai kuma ta rike baki "Lallai Innata da mugun hali take, yanzu a ce kazo tun jiya bata fad'a min
ba."
Kallonta yayi yace "Um, um Bintu kada ki sake fad'ar haka, uwa bata mugun hali watakil dai ta
manta ne."
Turo d'an qaramin bakinta tayi tace "Ba wani mantuwa da tayi, yoo in ba mugun hali ba baba
Alhaji mai zai sa ma ta manta da zuwanka."
"To ko dai wani laifin kika mata 'yar baba?"
Gyara zama tayi nan kasa ta ce "tsaya babana in lissafa maka abunda nayi jiya ta rika make ni
kamar na mata wani laifi.
Kaga da na tashi da safe, fitsari naje na fara yi, snn nayi alwala nayi sallah, na na wanke
bakina, na tafi karatun allo, da na dawo sai hararata takeyi wai ina wasa a hanya na dad'e zanyi
lattin Makaranta Ka ji d'aya.
Gyad'a kai yayi yace "Naji Bintun baba.
"Ban kulata ba, naje nayi wanka naci d'umame na na wanke hanu da bakina na na shirya na tafi
makaranta.
Da na dawo ban san hawa ba ban san sauqa ba sai kawai naji dundu a bayana wai nayi datti
da kayan makaranta na, ni qazama ce.
Kaji biyu.
Ta fad'a tana d'aga mishi yatsunta guda biyu.
"Naji Bintuna."
"Na uku kuma bayan naje islamiyarmu na dawo naci abinci nayi sallah, me ya rage?"
Ta tambayeshi tana waro mishi madaidaitan fararen idanunta.
Biye mata yayi da cewa "babu yar baba."
"Yauwa baba alhajina kana ji?"
"Ina jinki."
"Tunda babu abinda ya rage sai na fita na biya gidansu Indo muka tafi dandali muka warwasa ."
Tana fad'an warwasan tana girgiza jikinta irin ansha rawa d'innan."
"To meye laifina anan, kuma na manta ban fad'a maka ba dana dawo daga islamiyarmu ma
saida ta rankwasheni da zata aikeni wai saura kuma naje na zauna.
Kaji Uku.
"Duk fa nayi haquri na kyale shine kuma dan naje dandali ta kama ni ta zane ta kuma fad'awa
baffana ya min fad'a, dan Allah baba wnn ba mugun hali ba?"
Ta tambayeshi tare da kureshi da ido ita a dole amsa takeso ya bata.
"Bintu na kenan, ba mugun hali bane ,yar baba, tana yi miki hakane sbd ki zama ya ta gari, ki
zama mutuniyar kirki kinji ko?"
Gyada kanta tayi tace "naji baba alhaji. "
"Yauwa Bintun baba, daga yau idan an tura ki karatu ko aika ki rika dawowa da wuri ,ki daina
tsayawa wasa a hanya, kuma ki daina zuwa dandalinma kinji ko?"
Zaro ido tayi waje kamar an fada mata wani mummunan abu.
"Babana to rawanfa?"
"Kiyi a gida ."
Ya bata amsa a takaice.
Watsa hannayenta tayi tace "Ai gidanmu ba kid'a."
"To ki haqura da rawan ai ba dole bane, kuma ma karatu ya kamata kiyi ba rawa ba."
Ba tare da ta amsa ba ta maida kallonta kan Habibullah, da shi dinma ita yake kallo da
mamakin yawan surutunta ba ko gajiyawa.
"Lah baba, ina ka samo dan Hindiyawa?"
Ta tambaya tana dubanshi sama da kasa.
"Yayanki ne, yarona ne shima Bintu."
"Tabd'ari amma aradun Allah, yayi bala'in kama da Hindiyawa."
Dariya yayi yace "A ina kikasan su."
"A TBn gidan kansila nake ganinsu."
Zuba mishi ido tayi ba ko kiftawa kamar yanda shima bai daina kallonta ba.
"Kai babana yaronnan akwai ruwan kyau."
"Kema ai kina da kyau Bintuna."
Farfara ido tayi tace "Allah, Baba Alhajina, to dani dashi wa ya fi kyau."
Qasa2 tayi da murya "Allah yasa yace nafi shi kyau aga ruwan yanga a garinnan."
Dariya dukansu biyu suke mata dan sunji abinda tace.
"Bintuna ai kinfi shi kyau, ya isa ma ya had'a kyanshi dana 'yar Babanta."
Wani murmushi jin dad'i ta saki tana kara qarewa Habibullah kallo.
Matsawa tayi kusa da shi tasa hanunta kan dimple d'inshi.
"Kai baba alhajina yaronnan gasa yake so yayi dani, kaga tayani kyaunshi irin nawa."
Dariya Daddy ya kuma yi "Ai naki ya fi nashi kyau."
Cire hanunta tayi daga fiskarshi ta mayar kan fiskarta tana shafawa "Ni kodai kama mukeyi da
shine, ko da yake ma Baba yace nafi shi kyau, shi dogon fiska ne dashi ni kuma nawa bai kai
nashi tsawo ba."
Suna kallonta tana ta zuba shirmenta sai kuma ta mike da sauri "Baba alhajina Barin je inyi
fitsari."
"To 'yar baba, daga nan kici abinci duka."
Kafin ya karasa tayi nisa dan ba karamin gudu ta kwasa ba.
Cikin nitsuwa ta fito tamkar ba itace ta gama zuba rawan kai awanni da suka shud'e ba.
Sake take da atamfa riga da zani sai d'an madaidaicin hijabi da ta saka light blue. Kafarta sanye
da takalmin rubber.
Hanunta rike da 'yar ledar litattafan islamiyanta.
Tsaf tsaf da ita kamar ba ita ce tayi butu butu d'azu ba.
Nan inda ta bar su ta dawo ta samesu, kasan bishiyar mangoro, saidai ya ba suturar d'azu bane
a jikinsu dukansu biyu.
Kusa da Daddy tazo ta rusuna "Baba alhaji na d'azu na manta ban gaisheka ba , ina wuni ?"
"Lafiya lau 'yar baba mun sameku lafiya."
Ba tare da ta amsa ba tace "Baba alhaji sai yanzu na samu na fito nan ma sbd zanje islamiya
ne, ina fad'a maka innata ta b'aci da mugun hali kaqi ka yarda gashi ai ta fara nuna maka, daga
barin je inyi fitsari in dawo ta rike ni ,saida naci abinci nayi wanka nayi sallah, ta kuma hana ni
fita saida na kuma wani sallar kafin ta bar ni na fito."
"Bintuna ki daina cewa innarki tana yi miki mugun hali so take ki nitsu, ki rika hutawa , yanzu
baki ga yanda kika fito fess dake ba, kinga kyaun da kika qara kuwa?"
Juya ido tayi "Allah babana?"
"Sosaima kuwa, yanzu dai tashi maza ki tafi islamiya idan kika dawo sai muci gaba da hirar mu
ko?"
"To babana."
Ta fada tare da mikewa zata tafi.
"Baba alhaji sai na dawo, yaron baba alhaji kaima sai na dawo."
Habibullah dake kishingid'e ya mike ya zauna "Tsaya in rakaki islamiyyar."
[7/31, 10:35 PM] +234 814 290 6707:
*AL'AMARIN UBANGIJI*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W*
*Na Mmn Abduljalal.*
*5-10*
*G*aba tayi yana binta a baya har sukayi nisa.
Can ta juyo ta kalleshi taga da rata tsakaninsu.
D'aga muryarta tayi tace "Kai yaro, kayi sauri idan ba haka ba tafiyata zanyi in barka."
Sai kuma ta sauke murya tana cewa .
"Hmmm, idan kayi wasa idan ban barka ka bata ba, babanka yayi ta nemanka babu abinda ya
shalleni.
Har ya iso kusa da ita mita take ta zubawa danjin haushin ya b'ata mata lokaci.
"Kaga yaro, wlh yanzu kam idan bakayi sauri ba tafiyata zanyi, kasan abinda nakeso inyi ne
kafin na isa islamiyyar, ko so kake yau ma a tareni latti."
Ta karishe maganarta tana zumburo baki tare da fara tafiya.
Kamo hanunta yayi, "Wa kike cewa yaro?"
"Kai mana, to nasan sunanka ne, ba Babana yace kai yaron shi ne ba?"
"Idan ni yaronshine sai kema in zamo yaro a gunki, ganki yar mitsitsiya dake sai raini."
Kallonshi tayi fiska a daure, ganin shima nashi fiskar a daure tace " to aini bansan sunanka
bane."
"Sunana Habibullah."
"Tabb, Habibalah."
Tace tana rike baki.
"Habibullah akace."
Ammafa sunan yaso yayi kama da na Abulahn gidan malam lawwalli."
D'aure fiska ya dad'a yi "Ke kika kuma b'ata min suna saina fasa bakinki."
"Yi haquri, kiran sunan ba dole bane, kuma ma naga bani na tambayeka sunanka ba, kai ka
fad'a ko?"
Ta karishe da alamar tambaya.
"Ko ba ke kika tambaya ba sai kin fad'a daidai, dan bazan zuba miki ido kina cemin yaro ko bata
min suna ba.
Suna ci gaba da tafiya tace "To kawai nace maka biba mana tunda sunan da tsawo, ni kuma ba
iya wa zanyi ba."
Matse hanunta yayi da dan k'arfi har ta yi qara, "Kice Habi."
"Habi."
Tace da sauri.
Ya karasa da bullah."
Nanma ta maimaita.
To had'a ki fad'a muji."
Saida ta d'an d'au lokaci kafin tace "Bibillah."
"Ina kikabar harrufa biyu na farko, anya keko baffa ba asarar kud'in tara yakeyi ba?"
"Cabb, aka fad'a maka kud'in kirki yake ban ne balle yayi asara? Naira biyar ce fa, sai nayi sa'a
ya bani goma wollah."
"To lissafa min, a sati nawa yake kashewa."
Shiru tayi nad'an lokaci daga bisani tace idan lissafin biyar biyar za'ayi a sati ishirin da biyar ne,
idan goma ne kuma ishirin da biyar sau biyu, kuma ai ba kullum yake bani goman ba nace
maka."
"Na wane ishirin da biyar sau biyu?"
"ishirin da biyar da ishirin da biyar."
Ta bashi amsa da full confidence dinta.
"Idan an had'a goma da goma fa?"
"Goma sha goma."
Nanma ta bashi amsa.
Nawa wnn?
Ya tambaya yana nuna mata gudan ishirin.
"shine ishirin din ai."
"To idan an had'ashi da wani ishirin d'in fa?"
"Ishirin da ishirin mana."
"Idan an had'a da goma fa?"
"Ishirin da goma."
"Gyara dai."
"To goma sha ishirin."
"Ammafa ke d'innan wawiya ce ta gaske."
Fizge hanunta tayi daga rikon da yayi mata "Kai Bibilah ni kake cewa wawiya da girmana?"
Duk da baiso yin dariya ba saida ya dara "Wai da girman ta."
Ya fad'a ranshi yana kuma murmushi.
"Yi haquri babba, muje kada kiyi latti."
Gyara tsayuwa tayi tana fiskantarshi "Bibi, ai, Habi, ba nace maka akwai in da zanje kafin na je
islamiyyar ba?"
"Ina ne?"
"Can gurin bishiyoyin yazawan (cashew) nan ka gansu can a jere, sai na cira zan isa islamiya
raka ni muje kaji."
Har wani langabe kai takeyi ita gata mai wayo.
"Babu inda zaki sai kin iya kiran sunana."
"Na shiganga."
Ta fada tare da d'ora hanu a kanta."
"Yanzu duk kokarin da nayi baka gani ba? To qara fad'in sunan yanzu zan haddace."
"Ha.bi.bu.llah."
Ya fada mata daddaya.
"To me zai hana nace maka habu tunda yafi sauqi."
Zare mata ido yayi "Kinji nace miki Habu ne."
Kanta ta girgiza a tsorace tayi shiru kamar mai nazari, can tace "Habibi, dan Allah mu barshi
haka ka rage min tsawon sunan.
Maimaita Habibi yakeyi cikin ranshi can kuma ya kalleta "Sake fad'a muji."
"Habibi nace."
"Yauwa barshi haka ma yayi."
Da sauri tace "To zamu je? Sai ka hau ma ka cire min na huta hawa, ko mai shi yazo yau bazan
gudu ba dan nasan kana da karfi, ka jibgar min shi sosai fa, dama haushinsa nakeji kullum
mutum yaje ciran yazawa idan ya ganshi sai ya mishi masifa, hhhh, yau kam zaka jibgu Baba
audu." Ta fad'a har da d'an tsallenta.
"Ta ina ne islamiyarku?"
Ya jefo mata tambayar.
Kaga wancan hanya? Da mun yanki kwanar can zakaga islamiyar an kewayeshi da karare."
Tana gama fad'i ya sunkuceta ba tare da yayi magana ba ya sab'a ta a kafad'arshi yabi hanyar
da ta nuna.
"Kai, Habibi saukeni kada ka cuce ni, yau idan ban sha yazawan nan ba bazan ci tuwo ba."
Ko kulata baiyiba, ya ci gaba da tafiya.
Wuntsila kafafunta ta shigayi tana zamowa daga jikinshi.
A haka yaci gaba da tafiya tana ta zille zille da surutai har ya gane islamiyar.
Kofar islamiyar ya sauke ta ya had'e rai, "Maza shiga ciki kafin na kira malamanku su zane min
ke."
Cuna bakin tayi ta shiga ji take kamar ta cijeshi ko zata huce takaicin da ya tura mata.
Zama yayi a kan wani gungumen itace kusa da islamiyar yana ta kalle kalle, har suka tashi.
mantawa tayi da cewa tare da wani take suka fito suna ta tsalle tsalle da qawayenta.
"Indo Innarki tayi gullun suwa?"
"Eh tayi anjima zan kai dandali."
"Muje ki ban rabona."
"Ki bari mana bintu saimun fita dandali."
"Allah yanzu zaki bani , ai kinsan ba ko yaushe nake zuwa dandaliba idan innata ta ganni
hanani takeyi, jiya ma fa saida na sha duka da zagi da harara da rankwashi, ke innata muguwa
ce fa."
Ta karasa tana rike hannun Hali dake gefen hanun hagunta.
"Hali ke kuma me innarki tayi?"
"Hana baba tashi."
Hadiyar yawu tayi tace "Yauwa indo mu fara zuwa gidan su Hali muci hana baba tashi kafin mu
wuce gidanku.
Dadai sun karyi kwana zasu shiga lungun gidan su Hali taji an dawo da ita baya.
A tsorace ta kalleshi ta waro idanu "Dama baka tafi ba, me kake jira ?"
Bai tankata ba yaja hanunta suka fara tafiya.
" Mun shiga uku turawa sun shigo gari sun fara satar mutane, wayyo Allah."
Indo ta fad'a da k'arfi.
Had'a baki sukayi dasu Hali suna kwala ihu "Jama'a ku zo ,ga bature ya saci Bintu."
Juyowa tayi tana dariya "Ku, kubari Habibi ne fa yaron Baba Alhaji, tare muka zo dashi yasin."
Jin ta fadi haka sukayi shiru suna kallonsu har sukayi nisa.
"Nifa yau kana ta cutata, ka hanani shan yazawa, kace d'aya."
Biye mata yayi yace d'aya."
"Ka hanani shan gullu suwa, kace biyu."
"Biyu ."yace
"Yauwa ka hana ni cin hana baba tashi, uku kenan ko? "
Tun bata ji abinda zai ce ba tace "Dan Allah baka cuce ni ba Habibi."
"Ban cuceki ba ke dai kika so ki cuci kanki, dan nasan idan kikayi dare duka zaki sha gurin
innarki."
Dariya ta kwashe dashi "Kai yaro, ai Habu, wai, Habibi, ni fa bana cutar kaina da wayo na
wlh, cin dad'i nakeyi son raina aradun Alla."
"Meye ma sunanki."
"Baka ji Babana yana ce min bintu ba."
"Banda shi fa?"
"Na ainihin kakeso in fad'a maka?"
"Eh."
"Na aininhin ainihin?"
Ta kuma tambayarshi."
"Eh, shi d'in."
"Fad'imatu ko Fatsuma amma fa bintu ake kirana."
"To ni Islam zan kiraki."
Wani wawan birki taci kamar wacce taji abunda ya tsoratata tace "Me? Islam, ban tab'a ji ba
tunda innata ta haifeni, kuma itama tunda innarta ta haifeta bata tab'a ji ba nasan da ta fad'a
min yasin."
"Ba sai kin taba ji ba ni hakan zan kiraki wuce muje."
Cigaba tayi da tafiyar tana mita a hankali "A a ba Islam ba idan yaso islamiya, haka kawai ka
qala min sunan da ban taba jiba, kamar ma ba sunan mutane ba."
Sai kuma tace "Amma dai sunan Hindiyawa ne ko?"
" Ba a koya muku addini a makarantarku na boko?"
"Ana koya mana mana."
"To ya kuke kiran subject din?"
"I R K."
Ta bashi amsa."
"Menene full meaning na IRK."
"Ni nasan maka wani pulmin, zaka ta min yaren hidiyawa ance maka ina ji ne?"
Dariya yayi kadan yace "Turanci ni na miki ba indiyanci ba."
"To mu ba'a koya mana ba."
"Kina so na koya miki ?"
"Sosai ma , haba da anga ruwan yanga a garinnan wlh, yaro, au, Habibi sai wanda na ga dama
zanwa magana aradu."
Dadai isowarsu kofar gidansu, ta fiskanceshi "Zaka koya min yanzu."
"Shiga gida Islam maghriba ta gabato sai mun samu lokaci."
Ya fad'a yana duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hanunshi."
Turo baki tayi ta juya tayi hanyar shiga gida," islo," tace tana mai jin haushin sunan da ya qira ta
dashi.
Har ta shige gida yana tsaye yana kallonta yana murmushi.
Gidansu da suka sauqa ya