Showing 1 words to 3000 words out of 9240 words

Chapter 1 - Dame Ake Ado Book 2 By Fauziyya D. Suleiman .pdf

Unknown   

08 Jul 2025

1387

DAME AKE ADO

BOOK 2

1⃣ DAME AKE ADO 2 Uban waye yagaya muku wane munafuki ne yasanar daku wannan
magana Umma tafadi ahasale batabar sunce komai ba tadora da masifa to duk wanda
yagayamuku karya yake yi hassada ce kawai nice nahaifi Ahmad nice uwarsa Afusace take
maganar Daya daga cikinsu takuma amshewa haba baiwar Allah kiyi hakuri munriga munji
komai zance duniya fa baya buya Idan har danki ne mai yasanya aka cireshi daga lissafin
sunan yayan gidan kinada Auwalu da sani da rabi'u yaya akayi shi yafita daban? Mu kinga
yansako ne kiyi hakuri sai anjima tadire kudin sadaki akan kayan suka juya suka nufi kofar fita
Umma tabisu dasauri tana fadin don Allah kudawo nayi muku cikakken bayani don Allah
kudawo Basu saurareta ba suka nifi kofa suna ficewa suna ganin Ahmad suka kalleshi suka
wuce kawai Umma data biyosu da sauri arude taci karo da Ahmad tsaye ta yi turus cike da
tsanani tashin hankali tana kallonsa Ahmad yana tsaye idonsa yana zubda hawaye cikin
muryan kuka yake fadin kirabudasu Umma ki kyalesu gaskiya suka fada munyi laifi dabamu
gayamusu gaskiya tun farkoba wannan wace irin masifa ce wane irin cin mutunci ne wannan
don cuta sai da muka gama komai harmun raba katin biki zasuzo mana dawannan maganar
wane irin Abin kunyane wannan shikam tsananin tausayin Umma yafi komai yawa aransa wane
irin so ne wannan baiwar Allah take yimasa ina ma itace tazo a matsayin mahaifiyarsa inama
ana komawa baya asauya Uwa daya koma yafita daga cikin mahaukaciya yakoma cikin
Ummansa mlm sulaiman dake sallama yashigo da hanzari jin kuka matarsa a rude yake yakalli
deeje dake kuka yakalli Ahmad cikin tsananin damuwa yace lfy deeje meke faruwa haka kike
kuka subhanallahi Dahannu ta nuna masa tulin kayan lefe dake jibge yakallesu yadawo da
kallon kanta yakuma shiga rudu kansa ya kulle yace banfahimta ba deeje ? Cikin kuka tace
daga gidnsu Ummi wacce Ahmad zai aura waisun fasa auren ...... Takuma fashewa dakuka
yawaro ido waje da wata irin kidima mara fasaltuwa gabadaya jijiyoyin jikinsa sun janye saiji
tamkar yadaskare dakyar ya iya karfin halin kakalo wani zancen bangane sunfasa Auren ba
wani abu akayimusu tadansausata kukan tana goge hawaye
2⃣ tace ba.ayimusu kome ba mlm saidai munafukai sun shiga ciki lamarin anje angayamusu
Ahmad wai shege ne ba shida uba banda wulakacin mai yasanya tunfarko basu ce haka ba
saida aka kammala komai malam yayi shiru yama rasa abinda zaice domin iliminsa da
tunaninsa suntsaya gabadaya na wucin gadin Lami dake labe tana jinsu tadaka tsalle cike da
tsananin murna har da daga hannu sama ta fadi Alhamdulillahi da.anayimin wata fuffuka kullum
yaro yana shiga manyan riguna shiga masu gida daman nafadamasa ba da riga ake ado ba da
uba ake ado ehe! Takuma zuro kanta tana jiran jin abin da mlm din zaice tasami nadorawa sai
jiyo shi yana fadin kunga kuwuce ciki muyi maganar kantabarma suka zauzzauna mlm
yadubesu da damuwa yace duk Abinda Allah yakaddara babu makawa sai ya sami bawa
daman can Allah baikaddaro ummi matarka bace Ahmad don haka babu yanda za.ayi ka aureta
Umma tace Amman mlm baka ganin anbata masa suna kana ganin ko wata diyar yaje aure
zata yadda ta aureshi malam ? Ahmad yadafe kai yana kallon umma tausayinta yana kuma
karuwa aransa da kyar ya iya bude baki saboda nauyinda yayi masa yace Umma kiyi hakuri kiyi
hakuri .......kuka yaci karfinsa malam yadube shi da tausayawa wato Umman yake baiwa hakuri

Umma tace Ahmadu kai ya dace mu baiwa hakuri tunda mun kasa kareka daga wannan suna
mummuna mun kasa cire kalmar shege daga jikinka Balaifinku bane ba Umma bakuda laifi
kunyi duk wani yunkuri na boye wannan mummunan suna daga gareni Amman Allah yakaddara
sai najishi Umma idan wanka ba.aboye cibifa malam yakalleshi da hanzari yace kaga tashi
kawuce dakinka zansan yanda za.ayi idan takama aje a sulhunta nema zanyi zannemeka
yamike dasauri yana tangadi iska naneman kayardashi saboda juwa akarshen kwanar gidan
yaci karo da Lami tana lekensu takalle shi da hanzari saita juya tayi cikin gidanta yabita ka llo
cike da mamaki mai tsanani bai san abinda yayima matar nan ba tasanyashi agaba yanufi
gidansu Ummi yayi shiru yana tunanin idan yacemata shine zata iyakin fitowa kokuma iyayenta
suhanata don haka yace da yaro kace Abdul ne bayan tafiyar yaron da kamar sakan talatin
saigasu tare da Ummi fuskarta dauke da tsananin mamaki waye kuma Abdul yake sallama da
ita mamakin ta yadada karuwa sanda takula bakowa bane sai Ahmad tsaye ya hade hannuwa
akirji gabanta ya yanke yafadi tayi dan dum dum kamar zata koma sai kuma ta dake ta bata rai
tace gani yaya akayine ? Tana magana babu ko fara.a
3⃣ tsananin mamaki yacika Ahmad yau Ummi ke masa haka yadaure da kyar yace Ummi babu
gaisuwa kenanko? Takara hade rai tana fadin baikamata nagaida mayaudari ba kacuceni
matuka Ahmad kasanya nabata lokacina daduk wani tunanina akanka Ashe kai shege ne
bakada Asali maganar tadakin kirjin kwarai dagaske idonshi yakuma cikowa da kwalla kamar
zaifashe da kuka yakwantar da murya cikin lallashi yana fadin
Ummi yanda muka gina soyayyarmu cikin aminci banyi zantan dan Abu kalilan irin haka zai iya
mana itaba...... Takalleshe afusace tana fadin Au kai agurinka wannan yar karamar matsalace
kenan amman ka bani mamaki matuka to idan kai ta zama karamar matsala a gurinka kana
ganin doka kasance shege bawani abu bane to nikam Allah yasani babbar matsala ce bazanso
nahaifi ya ya adinga cewar Ubansu shege ne mara asali ba maganar mungina soyayyarmu
kuwa daman can akan tubalin toka da karya muka ginata don laillai dana san kai shege ne da
banta lokacina akanka ba na soka Ahmad ashe kai mara asali ne ka boyemini kacuceni wlh
kayaudaran .... Saita fashe dakuka 4⃣ DAME AKE ADO ....... Ahmad yaji duk yatsani kansa da
rayuwarsa tabbas Ummi tayi gaskiya waye zaiso hada zuri.a da shege mara.asali hawaye
dayake ta hadiyewa suka ci gaba da biyo kuncinsa yakasa cewa komai domin bashida sauran
abinda fada din Ummi ta kalleshi afusace tace idan abinda ya kawoka kenan nizan koma domin
inada abinyi a gida yayi dum yana kallonta da tsananin mamaki da damuwa jiyake kamar ya
bita yakamota shikenan Ummi tayimasa nisa haka yajuya yanufi gida baisan yanda akayi
yajeba yasandai Allah ne yakaishi Acikin gidama duk wanda akasanar da shi abinda yafaru
cikin yan uwansa sai hankalinsa yatashi abinda suke tambaya shin Uban waye yaje yafada duk
yanda sukaso ganin Ahmad sulallasheshi abin yatura don ya kargame kansa acikin daki Malam
sulaiman kam yajima yayi shiru akan dakali yana tunanin mafita har zuwa lokacin da ya cimma
burin tunanin nasa yasanya yaro yakira masa dan uwansa mlm jibril bada jimawa ba ya fito ya
zauna kusa da yayansa yace malam gani naji ance kana kira na yakalle shi tsahon lokaci
sannan yace kaji abinda yafaru da Ahmad kuwa? Dasauri yace naji wlh dazu na shiga gida
Lami take sanar dani Abin kam baiyi dadi ba mlm sulaiman yanisa yace tunda abin nan yafaru
nake tunanin mafita har Allah yasanya tunanina yafado kan diyarka Raliya da hanzari
yadubeshi yace Raliya kuma mlm yagyada kai yana fadin ita kuwa kamar yanda kasani nima
nasani Raliya tazama gagararriya wacce duk wani kokari namu dana yan uwanta yagagara

gyara ta saidai addu.a gashi tayi girman daya dace ace tafidda miji amman anrasa wanda
zaifito dagaske yace yana sonta saboda sanya shashanci datayi agabanta hakan nakeganin
abune mawuyaci Raliya tasamu miji nutsattse don haka tunani yasanarda ni mezai hana tunda
anyi haka amaida ranar auren Ahmad kanta kada acanza komai ayinan da wata gudan amman
kai yakagani domin ka fini hakki akanta yayi shiru tsawoh lokaci yana nazari can yadaga kai
yakalli yayanasa yace yaya duk abinda kayanke yayi saidai kana gana ganin Ahmadu bashida
wata illah da zata iyayiwa rayuwar Raliya illah ? 5⃣ mlm sulaiman yaduberhe da sauri yace kada
kace mini kacikin mutane masu jahilci dakama wani da laifin wasu wlh bagori zanyiwa kaina ba
Ahmadu yafi duk yayanda muka haifa nagarta balle Raliya da kai kanka kasan irin abubuwan
kunyar da ta daukowa gidan nan auren nasu shi zai zama rufin Asirinsu baki daya jibril ya
girgiza kai yana fadin wannan haka yake to Allah yasanya Alkhairi mlm sulaiman yayi murmushi
cike dajin dadi yace Amincewarka tafi komai agareni kuma koda hakan batafaruba kayan dakin
raliya daman akaina suke tunda dai nine waliyinta dahaka suka rabu ran malam yahaskake
yasan yana da damar kara kyautatawa Ahmad da mai dakinsa Adaki yatta Umma tana lazimi da
alama addu.a take yiwa danta yasami guri yazauna yana murmurshi yace Allah dai ya.amsa
Addu.arki saiki kwanta ki soma bacci Umma tadubeshi damamaki
Fuskarta babu yabo ba fallasa tace malam kenan kana zaton hankulanmu zasu kwanta cikin
sauki kuma wannan kankanin lokaci ? Yakuramata ido yana karantar yanayinta yace Amman ai
tunda abin nan yafaru Allah muke gayawa ba kyazato zai kawo mana mafita cikin gaggawa tayi
saurin yadda da batunsa har daga fuskarta yafimci hakan ta hanyar yin murmushinta tana fadin
duk abinda da akace Allah magana takare Amman taimakeni sanar dani wannan Abin dadin
yayi dariya yana kokarin tattaro farin cikinsa suyi rabonshi tare yace danki dai yasami matar
aure kuma awannan rana za.ayi bada fashi takalleshi datsananin murna da mamaki wacce
tagaza boyuwa akan fuskarta tace najima banji labari mai dadin wannan ba dan Allah mlm
wacece dan Uwanane ya.amince da baiwa Ahmad auren diyarsa Raliya kinga Asiri yarufu ko ?
7⃣ DAME AKE ADO Anacigaba dagudanarda sha anin biki Abba duk yaraba iv ga dangi da
abokansa abin mamaki har sanarwa yasa agidan radio itama Umma tadauki dukanin burinta
tasanya akan bikinnan hakanne yasanya yadanne zuciyarsa da damuwarshi ake gudanarda
komai cikin farinciki duk da bahakanne akasan ranshiba Abinda yabashi mamaki da tsoro ya
kuma sanya Raliya tafita daga ranshi baiwuce rashin mutunci datayi mashi cikin soron gidanba
malam yayi matukar kokarinsa domin shine yayi duk wasu kayan daki na Raliya akaje akayi jere
hatta kayan daya dace ace uwa tayi shine yayi domin lami cewa tayi Auren da akayiwa diyarta
na dole ne donhaka ko tsinke bazatayi ba wadanda suka haka suzasuyi komai saidai mutane
dayawa sungane borin kunyane domin babu tsiyar dataaje domin Auren diyarta tuncan baya
kudinta wurin bin malamai yake karewa balle yanzu datake iyakacin kokarinta na wannan Auren
baitabbataba domin acewarta diyarta kalar masu kudice da Asali ba kamar Ahmad fakiri ba
Ranar kamu amarya ba yabo ba fallasa tayi kwalliya kamar gaske koda yake yayyanta sunyi
mata fada harda mahaifinta da Abban duk da Ahmad duk da Ahmad bahalarta wurin kamun ba
yayi farinciki kwarai dagaske da lbr dayaji gurin yara na yadda Amarya ta cashe rawa
------>DAME AKE ADO part 5.
8⣠DAME AKE ADO Karfe biyar daidai motonci daukar Amarya suka iso Raliya tayi wanka duk
da batayi wata kwalliyaba amman tayi fes domin wata yayar Lami takama fada tanafadin tunda
akadaura ya kamata su watsarda makaman yakinsu surungumi kaddara yaushe za ace akai

amarya haka wannan yasanya tadan kimtsa idonta kemadagas babu alamun kunya itakadai
tasan tanadin datayiwa Angon nata narashin mutunci buhu buhu haka akawuce gidan mijinta da
ita saiwajen karfe 9 nadare Ahmad yagama kammala shirya kayansa tsaf cikin jakarsa don
haka rataya kawai yayi yanufi gurin Ummansa tana zaune arumfa dasauran yan biki basu
watseba yadurkusa yanagadin Umma zanwuce inabukatar Adduarku idan nayimuku wani abu
kuyafemin don Allah yasunkuyarda kansa jin muryansa tana rawa tamkar zaifashe dakuka
idanuwan Ummansa sunciko da kwallah tanajin kamar zata rabu da dantane har Abada Allah
yajarabeta da tsananin son Ahmad bata son Abinda zainisantasu saigashi yau Aure zairabasu
tayi shiru tsawon lokaci sannan tadaga kai ta kalleshi yana tsugunne kan kafafuwansa Kansa
yana kasa Tunda nake dakai banta ganin wani abu na ashsha kona kaico agarekaba nasan
Raliya zata iyayin komai domin ta tunziraka ta kuma hasalaka banason jin komai daga gareka
sai alkhairi kada kayadda wani abu nabacin rai yafito daga wurinka kayi komai domin
kafarantawa" babanka rai kiyayyar mace takaitacciya ce wata rana zata daina ranar daza awayi
gari kunfara tara zuria shikenan komai yazama tarihi Allah yayimaka Albarka idanuwansa suka
dinga zubdaí ½í¸­ inama yanda yake da iyaye nagari sukai masa fada yaji Raliya ma tanada su
da Aurensu yazauna lfy daga can saman kansa yaji umma nafadin tashi kaje kada dare yayi
Allah yayi maka Albarka yamike sumu sumi yana fadin Amin yawuce shikenan kyau zai bar
gidansu zai bar cin abinci Ummansa ya isa kofar gidan nashi da babur dinsa yasauka yatura
kofar ga mamakinsa sai yaga kofar abude take donhaka yatura babur dinsa yashiga tundaga
tsakar gida yafara jiyo kugin radio ankure wakokin turawan zamani mamaki yacika shi domin dai
daga dakin dake kulle wakokin suke fitowa yasan wannan dakin baccin Raliya ne yakada kai
yanufi dakinda aka jera kujeru aciki domin yasan dakin da raliya take bazaisamu damar kwana
acikiba ko bata rufo kofarba balle dakin abame yake ma har ya kwanta akan kujera yaga
dacewar yakoma shagon gidansa kawai da kayansa ya zauna nanne dakinsa da asuba yatashi
ya nufi masallaci tayi sallah yadawo yafara lazimi kamar yanda yasaba daman baisanya ran
raliya zata tashi tayi sallah ba domin yasan batada wannan tarbiyar sai wajen 10 nasafe take
tashi ai kuwa yau dinma hakane saida rana tatake sannan tatashi lokacin tuni yadade da
karyawa domin flask yadauka yaje yasiyo musu shayi dayasha yabar mata nata aflask duk da
yanacan daki yana hangota ta windo yaga tafito amman abinda yabashi mamaki har karfe goma
raliya bata fitoba kuma gidan ba irin na yangun nan bane mai bandaki aciki balle yace tayi
Alwala aciki can saiyajiyo sautin radio ansa kidan jiya naturawan zamani yaso yashareta
amman sai yatuna yanzu hakkin raliya da tarbiyar ta duk suna kanshi dole yatunatar da ita
gaskiya don haka yamike yanufi dakin nata yatura kofa dasallama tadaga kai cike da tsananin
mamaki tana dubansa shikam yanayin daya taddata ne yasanyashi tsananin firgita da rudewa
domin wata yar figigiyar rigar bacci ce ajikinta dukkan surarta tana waje jikinnan nata yayi jajur
tasha man kanti gashi tana kan kurciyarta saiwani sheki da sulbi fatarta keyi 9⣠DAME AKE
ADO Wani abu yadinga jin yanaimasa yawo cikin kanshi saboda baitaba baitaba ganin wata
mace cikin irin wannan yanayiba yayi masa wani kallon banza sama dakasa tana yatsina fuska
tace inazaton kayi batan kaine ko malam yanayin yanda tayimasa maganar yayi gaggawar
dawo dashi cikin haiyacinsa yayi kokarin tattaro jarumtakarsa da nutsuwarsa yasanya akan
fuskarsa duk da zuciyarsa tayi kokarin bijirema hakan sannan yayi kokarin zakulo abinda
yakawoshi inatasau raren ganin kinfito kinyi sallah asuba saikuna naji kin kunna radio ma
alamar bakida niyyar gaida ubangijinki Tayi dariya tayi shewa tayi masa irin kallon da akeyiwa

yantasha Au ashe fa Ustazu aka kakaba mini ko? Wai kayi zaton zuwa nayi zama agidanka dan
Allah dubeni kadubi fatata aikasan banyi kalar dazan iya zama acikin wannan gidan kirar
talakawaba talauci yahaifeni nakuma yadda nazauna natayu acikinsa amman bazan yadda na
dauwama har nakare rayuwata acikin saba batun sallah kuwa kada ka matsamini domin ba
kabarinmu dayaba bakuma bazo zama bane jira nake kashigo kabani red card dina Ransa
yabaci ainun banda kaddara me ye hadinsa da Raliya komai jahila bata iya komaiba sai wauta
amman ace itace matarsa takuma zage tana zaginsa haka yayi kamar yakara magana saiyaga
rashin dacewar hakan danhaka yajuya da zummar ficewa saiya jiyota daga bayansa tana fadin
malam fitafa bata kama kaba gwara kasallameni tunban yagama rigar mutuncinkaba
baikulataba yafice domin tunaninta irin na dabbobine idan yaci gaba dajinta komai na iya faruwa
kawai sai yafice daga gidan yaukam abin yafi najiya domin tundaga kofar gida akejin sautin kida
yashiga da sallama badon yasan zatajiba sai domin mutanen boye abin mamaki saiya hango
takalmi barkatai na mata dakuma hayaniyarsu anata shewa ga tukwane da kwanuka Nan anyi
girki anbata gidan yayi faca faca harda garar abban

DAME AKE ADO part 7.
duniya tayi mata yanda takeso kenan tsawon sati guda kenan anazaman yan marina agidan
babu wani da Raliya dakeyi na zaman Aure hatta shara shiyakeyinta wanke wanke kawai take
yi shima dan ita take bata kwanikan da kawayenta dake wuni kullum agidan dayafita aiki
sukuma zasu dira basu barin gidan sai dare zuwan Lami nafarko kuma nakarshe shiyakara
dagula komai suna daki ita da diyarta sunata kulle kullensu ya iso gidan agajiye yake tubus
domin yau bai tsaya hutawa ba kamar yanda yasaba yana rashi daga aiki yayo gida kawai kai
tsaye yashigo da babur dinsa gidan Dai dai lokacin da yaji Lami tafito daga dakin Raliya nabiye
da ita furucinta nakarshe ne ya doki dodon kunnensa 1⃣2⃣ DAME AKE ADO 2 Yayi tsai yana jiyo
ta tana ta habaici da zage zage dukkan kalamanta bakomai bane illa tunin kalaman da
mahaifiyarta kegaya masa sanda yana yaro har ya girma bashida abinyi bayan neman tsari
daga shaidan dan kada yatunzurashi ya aikata abinda zaisanyashi dana sani agaba yana jin
kiran sallah magriba yayi sauri yafice dan bada farali acan masallaci ya zauna yana lazimi har
akayi sallar isha I yayi sannan yanufi wani gidan Abinci namasu karamin karfi yaci yakoshi ya
jima agurin yana tunane tunane domin yarage dare fatanshi sanda zai isa gidan Raliya matar
jaraba tayi bacci don haka sai wajen karfe shadaya yanufi gidansa ya tura kofar a hankali ya
shiga yamaida kofar yarufe cikin gida yawuce yadauro Alwala domin dai yau daren jumua ne
waton ranar Alhamis daren da Allah kanyi saurin amsar Addua bayinsa don haka yayi Alkawarin
kaima Allah kukansa shima yau yazabamasa Abinda yafi Alkhairi yana sallah yajiyo bugun kofar
raliya kamar zata balle masa kofar abinda yabashi mamaki biyu ne na farko kofar abude take
amman taketa dukanta nabiyu kuma me yakawota dakinsa saidai yakula bazata barshi yayi
sallah nan idan har baikulataba dan da karfi take bugun kofar tayi kokarin yin sallam yanufo
kofar yadubeta sanda take kallon sa tadaina dukan kofar cikin tsananin mamaki yace lfy
takalleshi araine tayi wani tsaki zuwa nayi Amsar sallamata domin nagaji dazama wannan
akurkin naka nakula bakada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login