Showing 6001 words to 9000 words out of 9240 words
kwana ita kadai adakiba idan tana gida tana makale bayan ummanta har bacci
yadauketa sai cikin dare umma ke zamewa tagudu dakin maigidanta da anyi kiran sallar farko
tadawo takwanta amakaranta kuwa dakinsu su goma shatara ne don haka bata taba kwana
itadaya ba ta mike dasauri tana waigen dakin tome yakamata tayine shin yayanta yakamata
takira kokuma rufe kofa zatayi harta kama kofa zata tura saitaji kamar anmata kuwwa cikin
kunnen ta danhaka tafito daga cikin dakin dasauri danma dahasken wutar nefa tajima tsaye
atsakar gidan tana sakawa da kwancewa tarasa madafa saitaga kamar gidan yana yimata gizo
dan haka tayi soro dasauri yayi sa a kofar dakin nasa abude take dan haka tasamu guri ta
tsuguna tanannade jikinta cikin hijab tamkar maijin sanyi ahaka har bacci yafara daukara
2⃣0⃣ DAME AKE ADO 2 Ahmad yanaciki baisan abinda kefaruwa asoronba tunda yazauna
yakasa motsawa yarasa abinda yadace yayai tsawon lokaci yana awannan halin hardare yafara
ja saiyaga dacewar yatashi yadaura Alwala yayi sallar isha'i sannan yanemi yardar Allah da
amincinsa bisa wannan auren dayazomasa bagatatan yamike yanufi kofar dakinsa yayi baya
tsorace yana ambatan sunan Allah domin karo dayaci da ma'u wacce keta shirgan baccinta
haikan babu wata fargaba saida yanutsu sannan yasan itace mamaki yakoma kamashi yamatsa
kusa da ita yanakallonta meyakawota nan meyasanyata bacci ahaka cikin daga murya yafara
ambaton sunanta domin yaga alamar batasan dashi agurinba tafarka afirgice cike da tsananin
tsoro dafirgita tana waige waige yadurkusa agabanta nine nana kwantar da hankalinki
meyakawo ki nan kina bacciya yafada cikin rarrashi domin yakula duk akidime take tayi narai
narai da idonta domin tana tsoron kar yadaketa Allah yaya tsoron dakin nakeji sai naji kamar
anamotsi abayan kyauren yayi murmushi yace nana haryazu ke sokuwace ko? Tomeyasanya
baki sanar da niba tasunkuyarda kai tanasosa keyarta cike da tsananin kunya yakula tunda
suka iso gidan ma 'u kejin kunyar hada ido dashi shima nauyinta yakeji kwarai dagaske jinbata
niyar cewa komai yasanya yamike yakama hannunta yanafadin taso muje ki kwanta kada kikara
kwanciya anan bamusu tabishi amman hankalinta amman hankalinta yatashi saboda rikemata
hannu dayayi saiya sanya tsikar jikinta tashi ahaka harsuka isa dakin yazaunarda ita gefen
gado yanafadin to kwanta bari nakwanta akasan yadauko filo daya daga kan gado yajefar kan
tayal yakwanta yajuyamata baya Umma tana kwance datsananin damuwa idonta nazubda
hawaye batasan sheshshekar kukanta yabaiyanaba malam yamike zaune yakunna fitilar dakin
yakalleta duk da tajuya masa baya yasan ba bacci takeyiba cikin raunanniyar murya yakira
sunanta khadija kitashi nasan ba bacci kikeba tashi kisanarda ni dalilin kukanki tsoro dafargaba
suka kamata ashe kukanta yabayyana har malam yajiyota tashiga ukku meyadace tayi yanzu
nace kitashi muyi magana khadijah tsawarshi tasanyata mikewa dasauri jikinta yana rawa
domin takula ran malam yabaci yatsareta da idonshi wanda yakada tayi jajir kisanardani abinda
keranki khadija kigayamini komai da bakinki cikin rawar murya tace wlh malam bakomai araina
karya kikeyi akwai abinda keranki deeje mutum bayayin kuka kawai saida damuwa nalura dake
tunda nasanar dake auren ma'u da Ahmad yanayinki yasauya furkarki tanuna bakiji dadin
hakaba shinkina kyamar Ahmad dan bayada ubane kece kike nuna jin haushin abinda wasu
kemasa kamin wannan lokaci deeje baibarta tabada amsaba taci gaba dafadansa idan harkikayi
haka kinbani kunya kinkuma ci Amanar ahmad Ahmad zaitabbatar da lallai bashida uwa
bashida galihu kowa yana kyamarsa yakarasa maganar da kunci dazafin zuciya tadaga kai
tanafadin kodaya malam wlh abinda kake zato nahaka bane bantaba kin Ahmad ba
2⃣1⃣ DAME AKE ADO 2 Bantaba danasanin kasancewarsa tare daniba bantaba danasanin
zamanshi danaba haka banajin komai game da aurensa da ma'u kukan dakaga inayi banakin
aurensu bane illah tausayinsu gabadaya Asma'u yarinyace karama bata iya komaiba saiwauta
da tsiwa bankoyamata komaiba na rayuwar aureba nayi sakaci bantaba bata lbr meye aureba
shikuma Ahmad yarone dabaisan komai gameda rayuwar aureba shin yaya zai kalli ma'u da
halayenta inatsananin jin tausayin ma u dakewarta wlh wannan shine kadai abinda ke damuna
amma har abada bazantaba dana sanin hada auren nan da akayiba nayi mamakinma da
wannan zargin yazo ranka malam takarasa maganar datsananin damuwa yayi ajiyar zuciyar
cike dagarinciki acikin ransa yana godiya ga Allah dayasanya ba abinda yake zargibane aran
deejen ba yakalleta yayi murmushi Amman shirmenki yayi yawa waton har abada mace bata
girma danwannan abinne kawai yasanyaki damuwa kodayake nasani harda soyayyar ma u
dakukan rabuwa da itako yakarasa maganar da zolaya tasunkuyar dakai tana murmushi kasa
kasa malam yaci gaba dajawabi kikwantar da hankalinki daga Ahmad har ma'u duk rainonkine
watakima ahmad yafiki sanin halayen ma 'u dan haka babu wani abu dazaibiyo baya insha Allah
sai Alkhairi nayi imani zaikoyarda ita komai tunda kinkoyamasa kokin manta da dannaki ya iya
girki kala kala ne? Yakarasa yana dariya abinda yasanyata darawa itama ya dinga zolayarta
haryasamu ta sakko Suka fahimci juna sannan suka kwanta baccinsu sunawa yayansu addua
tunda asuba yatasheta tayi sallah shikuma yawuce massalaci bayan yadawo yazarto dakin
yazauna yacigaba da lazimi itakam baccinta takara komawa aranta tanaganin babu abinda yafi
gadonta dadi kamar wacce akatasa karfe bakwai tafarka ta tadda yayan nata har lokacin yana
lazimi tamike tsam tanufi kofa ya bita da kallo kamar zaiyi magana saikuma yafasa don yayi
zaton bandaki zatashiga itakam kicin tawuce tayi zaune tanasakawa da warwarewa akan
abinda yakamata tayi domin sanda yatafi masallaci umma takira wayarshi tadauka umma tace
waye tace nice tace yauwa daman kedin nakeson kidauka domin nasan yanzu Ahmad yana
masallaci kinaji idan gari yawaye kishiga kicin ki girkamuku abinda zaku karya sannan kishare
gidan kigoge ko ina nasan kin iya shara daguga dan kinayi amakaranta ko dasauri tace eh inayi
tace to kitabbatar kinyi kinjiko?
2⃣2⃣ DAME AKE ADO 2 Takoma amsawa da to shine yanzu tana tsaka da bacci maganar Umma
tatasheta tadauko doya tafara ferewa bayan takammala tayankata gutsi gutsi kamar zatayi faten
doya sannan tadauki kwai ukku tafasa akan doya ta kunna risho tadora mai kozafi baiyiba
takama kwan da doyar ta zuba tana jiran su soyu daga can acikin daki yafara jiyo kauri dasauri
yamike domin zuciyarsa tabashi ma'u ce yanufi kicin din dasuri saiyaga doya da kwai da mai
sunata zabalbala yarike baki damamaki yana fadin Nana mezakiyi? Mekike dafawa? Tayi firgigit
ganin kallon dayake mata tace doya da kwai zanyi sai akacemiki kuma haka akeyi waye
yasanyaki girki kuma baki iyaba cikin zafin rai yake maganar tayi kwal kwal da ido tana jada
baya domin tana gudun kada yadoketa tace Umma ce tace nayi abincin Kari
kuma............kuma..........yadoka mata tsawa get out mekika iya bayan shirme yadauko kaskon
suyar daga kan wuta yayi waje dashi sukaci karo abakin kofa tana tsaye tana gunguni yayi baya
dasauri dan sauran kiris yakifamata yakoma kuluwa yace Amman bakyajin magana nana bance
kibar gurinnanba dasauri tawuce tabar wurin takoma gefe tatsaya yanufi gindin rariya da abinci
yasamu kwano yazuba yasanya ruwa yawanke kaskon sannan yanufi kicin din tana tsaye tana
kallonsa yadauki wata tukunya yazuba ruwa yadaura shayi duk tana tsaye tana hangensa
yanata kaiwa da komowa acikin gida harya kammala dafa shayin yajuye aflask yanufi kofar gida
tana ganin yafice tanufi kicin Don ganin abinda yayi bata hango komaiba tafara bubbude
kwanika cikin tsautsayi bataga flask din yazuba shayinba tabangaje yafado jikake tush flask din
yafashe shayin yazube atsakar kicin din tarike baki cike da tsoro dafargaba saita kasa gaba
takasayin baya kamar ancilloshi yashigo gidan tundaga nesa ya hangota akicin yakarasa da
sauri yana fadin nana meyakawoko kicin dinnan bance kada kisake kishigaba tayi tsuru tsuru
daidai lokacin daya karasa yadauki dogon salati sanda yaga flask din shayi duk kwance akasa
yana ambaliya ya kalleta yama rasa abinda zaice cikin rawar murya tace Allah yaya bangani
bansan da flask agurinba yayi ajiyar zuciya yayi kokarin hadiye fushin shi domin ma'u yargaban
goshin shice duk da banzan rawar kanta yanunamat kofa zokiwuce daki maza tataho tana
rakube rakube tana goge ido tana gudun kada yadoketa har ta isa bakin kofa data samu tafice
ta falla da gudu saida tadire acikin daki sannan tazaya tana haki da dariya wai Allah nagodema
da yaya Ahmad ya mini irin ko rankwashinsa ne aida naga takaina tarike haba tana haki shi
kam kada kai yayi da takaici sannan ya shiga yashare kicin din yakara dora wani shayin
yazuzzuba akofi yakaimata nata hardaki ta amsa tana fadin nagode yaya
2⃣3⃣ DAME AKE ADO 2 yadaga kai kawai sannan ya zauna yafara shan nasa ma'u tadubeshi
yana shan shayin tace yaya don Allah zankoma makaranta kaga ranar monday za afara
jarrabawa kuma Abba yace saikayadda zankoma yadaga kayi yakalleta saiyaga ikacin
gaskiyarta take maganar babu wani bayani dazaiyi uagamsada ita saiyace aibazakiyi wannan
jarabawarba kihakura kawai tawaro ido cike da fargaba yaya kanufin nadaina karatu kenan
kainefa kace zanzama likita yajijjiga kaida damuwa ma'u tayi kankanta da Aure tayi kadan
dafuskantar irin wannan matsalolin donhaka gara yasanar da ita gaskiyar komai yadubeta da
nutsuwa yace nana kinsan yanzu ke matar aure ce ko? Tadaga kai alamar eh yagyara zama
yauwa kinga ai makarantarku ta yanmatace babu matan aure ko? Towannan dalilin yasanya
bazaki kara komawaba kinkammala makarantar kenan yanzu zakizauna zaman aurenki kinemi
Aljannarki tamike atsorace cike dafaduwar gaba yaya zakace haka yaya Ahmad shikenan
niyanzu bazankoma zuwa ko inaba sainan gidan kuma bazan zama likitaba......yaya bakayin
karya amman yanzu kayi meyasanya tambayar tacazamasa kwakwalwa harya rasa amsar
dazaibata saiyasake hade ransa yace kincikani dasurutu nana tashi maza kiyi wanka kishare
gidan kiwanke kwanika tayi narai narai da ido domin tana matukar son karatunta tace amman
yaya...............yadaka mata tsawa isaid get out ma'u jikinta yadauki yadauki rawa hawaye
yamakale ido yafara tafice dasauri ta
nagoge idonta tana aiki tana kuka yanajiyo sautin kukan nata bashida zabi babu yanda zaiyi
abba yagama yanke hukunci daga karshe ma saiyayi wanka yafice yabar gidan wannan shune
yakara dagamata hankali saitaji gidan yakara mata girma tazauna tsuru babu abinyi sai tsoro
yafara shigarta tamike tanufi soro takama leken waje tana hango mutane dake kaiwa da
komowa saitaji sanyi aranta donhaka saita zauna akofar gidan tana kalle kalle dakaramin hijab
akanta idan taga abin dariya tayi idan taga abin mamaki tayi mutane suna wucewa suna
kallonta babu wanda yayi zaton matar gidance domin komakota basusan ankawo amaryaba
sunyi zaton Raliya ce itakuwa daga yanayin kawayenta da gantalin datake fita kullum yasanya
suka gano bamatar arzikiceba donhaka babu wani wanda yarabeta tsawon lokaci tananan
zaune tana cike da nishadi shikam Ahmad gidansu yanufa kaitsaye yatadda yan uwansa sunzo
dayake ranar assabar din karshe sati ce anata cafta saiyazauna anatayi dashi Umma saishige
dafice takeyi wurin ganin takammala kirkin rana kunya da nauyi sunhana ta tambayi ma'u takula
shima Ahmad kunyar yimata maganar ma'u yake amman daga yanayinsa talura babu wata
matsala anan sukaci abinci lokacin da inna tazuba abincinne ma yatuna da ma'u da abinda
zataci saidai Allah yataimakeshi umma tacika flask din da dambu datayi tadire tace gana yar
gidanka Ahmadu yaji dadin hakan danyana kammala cin abincin yadauki flask yahaye babur
dinsa yanufi gidanshi abinda ybashi mamaki da tsoro baiwuce hangon ma'un shi zaune akofar
gida daramba tana hirarta da wasu yara da alama yayan makota tasamu tabiye musu
yanacigaba da karatowa mamakinsa nakara linkuwa harzuwa sanda ya iso indatake da babur
dinsa tadaga kai takalleshi saitadan firgita masamman yanda yanayinsa yacanza lokaci guda
takalli yaran dake gabanta tayi duru duru sai tamike ta shige cikin gida dagudu batayi birki ko
inaba saibayan gado tana huci talabe cankurya tana maida numfashi yashigo gidan ransa yana
suya ya iso harbayan gadon yajawo kunnenta tafasa ihu jikinta naci gaba da bari dan Allah yaya
Ahmad kayi hakuri Uban wa yace kifita waje kizauna komunkoya miji wannan tarbiyar agidane?
Cikin sheshshekar kuka tace A ah gidan ne shiru ga tsoro shine naleka waje don Allah kayi
hakuri tafashe dakuka yadunkule hannu ya rankwasheta yana fadin koda zanhakura saikinji
ajikinki kifita kofar gida kizauna kamar wata sokuwa inakikakai aurenki yakoma rankwashemata
kai kwas akanta takuma sanya ihu saida yajeramata guda hudu sannan yasakarmata kunne
takuma fashewa dai kuka lokacin yafice daga cikin dakin yanufi shago domin yasanya uniform
dinshi yatafi wurin aiki saidai yanashirin kukan ma'u yana dukan zuciyarshi tuncan baya
bayason bacin ranta yakanyi komai dankar abatamata rai balle dayaji sunan mahaifiyarsa ne
akasanya mata hakan yakara soyayyarta acikin zuciyarsa yanzu kuma gashi tazama matarsa
wato yanzu soyayyarta agareshi hawa ukku ce don haka dole intana kuka yarikaji harcikin
bargonsa da kyar yakammala shirinsa yanufi soro da zummar yafice saikuma yaga rashin
dacewar hakan dan haka yajuya cikin gidan yanufi dakinta tana rakube a inda yabarta abayan
gado tana kuka ya isa inda take tahada kai da gwiwa tana sharbe yakira sunana tadago
takalleshi dafaduwar gaba don batasan yadawo dakinba tayi zaton kara dukanta zaiyi donhaka
tafara ja dabaya tana sharbe majinarta tana kuka
DAME AKE ADO part 11.
2⃣4⃣ DAME AKE ADO 2 Dan Allah kayi
hakuri wlh bazan kara fitaba
nadaina..........yakada kai yana karemata
kallo wlh da Abba yayi shawara dashi
dazaice abar ma'u takammala karatunta
tazama cikakkiyar mace kafin ayimata
wannan auren yarinya ce tsaba yanzu
tafara kirgen dangi irin namata baikallonta
da komai haryanzu sai kanwarsa ihunta
yadawoda shi hayyacinsa yace kinga
badukanki zanyiba cewa zanyi kidaina fita
waje idan nafita zanturo miki yaran
sudinga tayaki hira kinjiko? Tadaga kai
dagamsuwa tanacew to tuni kukun nata
yakoma ciki tafara dariya gawannan idan
kinason cin wani Abu kisaya gakuma abinci
can aflask Umma tace akawomiki ta amsa
hannu biyu tana godiya yakada kai yafice
tabishi dasaikadawo yaya kamar yadda
tasaba yimasa agida ya amsa da Allah yasa
yafice takalli dari nan tadaka tsalle cike da
murna waiyau itace keda dari duk tatace
lallai Allah yasanya yara sushigo su
siyomata agwalima yayi sa akuwa yan
yaran dayatadda azaune dasu har lokacin
sunanan zaune suna wasansu don haka
yace maza suje sutayata hira dahanzari
suka shige gidan suna murna sallamarsu
tatsinkayo acikin gidan tayi waje dagudu
cike da murna sai alokacin tahango flask
din abinci tashiga kicin tadauko faranti
tadebi nata suma tazuba masu nasu suka
zauna sunaci suna hira itakuma tana
kwasar dariya tundaga wannan rana gidan
nata yazama gidan yara domin ance laifi
yaro kiwa laifin babba rowa Asma'u kam
hannunta asake yake akwaita da kyauta
Ahmad hankalinsa yakwanta shike
hadamusu abinci dazasuci dasafe darana
da dare saidai idan yasan yanada aikin
safe tun asuba zaidora kirkin rana yazuba
aflask ya ajiyemata da daddare kuwa
yazomata da ( take away ) domin yace
batayi wayon dazatayi girkiba harta kunna
risho ba aikinta kawai wanke wanke da
shara ko wanki shine kemusu sanda
yakeda lokaci saidai yanashan fama da
kurciyar ma'u da shirmenta yautunda safe
yakammala girkin yazubamata aflask
yarufe harya kammala shirinsa tana gindin
Tv tana kallon NTA muhawarace akeyi da
daliban makarantarsu dana wata
makaranta cikin harshen turanci tanajin
kamar tatsallake tafada cikin tv idan anyi
tambayar dayan makarantar suka kasa
amsawa tasani saitayi karaf tace dan Allah
kazane kuce kaza ahaka ya isketa tsahon
zamani yana kallonta batasan yazoba
tausayinta yakamashi ma'u tanason karatu
kwarai shima yanason tayi karatun saidai
yanada tsananin kishi bazaitaba yadda ace
matarsa tanazuwa makaranta kullumba
dama dai ace takammala karatunta akayi
aurensu dayaga batada niyyar dawowa
hankalinta yakira sunanta tawaiga dasauri
tace la yaya harka gama shiri zo dan Allah
kaga wadannan sokayen sunkasa amsa
tambayoyo nafi sauki kumafa sinio
dinmune a school yayi murmushi yace
nana nidake sauri zantafi aiki inanakeda
lokacin kallo amshi Nan yamikamata kudin
tasanya hannu ta amsa yaci gaba da
magana zanwuce sainadawo akwai abinci
aflask banason barna dawarkai kada
kilalata komai kinjiko idankuma andauke
wuta kikashe kayan kallo duka dan kada
akawo wuta sulalace ta amsa dato tana
cigaba da kallonta haryakai bakin kofa baiji
tace saikadawo ba yawaiga yakalleta yace
yauba babu adawo lfy kanwata dasauri
tace lah yaya namanta adawo lfy tana
fadin haka tamaida kanta wurin kallonta
yayi dariya yafice baijima dafitaba kuma
nepa suka dauke wuta bakinciki kamar
yakasheta domin taso taga karshen wasan
takoma kan kujera takwanta tafara tunane
tunanen duniya kwatsam yayarta kuma
kishiyarta tafadomata saitaji gaba daya
ranta yabaci saidai abinda kedauremata
kai baiwuce rashin zuwa gurinta da yaya
Ahmad keyiba ko maganarta ma bayayi
sam tanason tatambayeshi amman kishi
da haushi raliya yahanata don haka tabar
abin cikin ranta tana kwance tana sakawa
da kwancewa har kawayenta suka fara
shigowa tamike tafita suka fara lido A'ilo
daya daga cikin yaran ta kalleta tace waike
ma'u bakyayin sabon girkine kullum saidai
naga kindebo acikin flask ma'u tatabe baki
da damuwa ban iya girkinba yayana ne
yakeyi yazuba acikin flask A'ilo tace
cabdijan to idan bakya gwalgwalawa yaza
ayi ki iya kinganni bankai girmankiba har
wake dashinkafa nake dafawa babanmu
arisho bama da murhuba mamaki yakama
ma'u tace ke A'ilo koni danagirmeki
ummana bata bani girkina saitace
kazantane saidai kawai na izamata wuta
amman kice harwani girki akebaki A'ilo ta
tafa hannu tadoki cinya shekarata shabiyu
amman wlh ina girki tambayi kanena ma
sale idan yashigo saiga sale yashigo da
gudu tamkar yasan nemansa ake A'ilo
tace yauwa sale zo dan Allah banayiwa
ummanmu girki sale yatsaya yana haki
kinayi mana ranar har danwake
kikayimana ma'u tafe kirji danwake lallai
kin iya girki daman inason na iya don allah
ya akeyi A'ilo tayi murmushi dadai akwai
fulawa ne dasai nanuna miki yanda akeyi
ma'u tace bari naduba inada yake ajiye
kayan abincin nasa Allah yasanya da
fulawar daman nagaji dacin shinkafa da
miya ko dafaduka shikenan fa abinda ya
iya tanufi dakin taduba ga rashin sa arta
bata tadda fulawaba amman saitace ga
kudi asiyo gwangwani ukku nafulawa su
kwaba dadi ya cika yaran suna murna
yauzasuci girkin amarya ihu suke yi tamkar
ranar sallah nandai sale yafalle dagudu
yasiyo fulawa aka kwada aka kunna risho
aka fara kokarin saka danwake gabadaya
akaduru akicin din sugoma A'ilo ce agan
risho tun ruwan bai tafasaba akafara saka
danwake duk sanya daya sai anyi ihu tafi
ahaka akammala sakawa aka koma gefe
anajiran yatafasa gabadaya danwake ruwa
yahadu ya cakude ahaka akafara kokarin
saukewa anduba babu tsumman da za
asauke ma'u tace bari tasauke bakin
zanenta takama tana kokarin saukewa
ashe zanin yalaso wuta zafin wutar
dayatabota yasanya tafasa ihu tasaki
tukunya da zaninta dayakama da