Showing 114001 words to 117000 words out of 139785 words
Chapter 39 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
abun arzikin da mijinki ya kawo maki, yshe yana sonki har haka? Tab irin wannan mota danƙareriya." Kallonta kawai Rahama takeyo da ido dan tun lokacin da Imran Matawalle ya saka ƙafa yabar cikin parlorn gidan su taji gabaki ɗaya an kwace mata duk wani jin daɗi da walwalar duniya. Ummi har part ɗin Hajja ta sameta da trolley ɗin kayanta wanda take amfani dasu sanda tana gidan wanda mafi yawancin kayan sababbi ne, saboda Rahama na son ɗinka kaya a rayuwarta, dan a yau idan taga atamfa tayi mata kyau sai ta matsawa Ummi ta siya mata ko kuma Abbanta. Hakama dogayen riguna. Sannan duk da hakan Ummi ta faɗa mata zatayi magana da Kausar akan ta kira Imran ya kwaso mata kayanta na can gidan. Yadda Ummi ke lallaɓata yasa zuciyarta ta ɗan yi sanyi ko babu komai tana tare da Ummi zata samu sassaucin abunda takeji a zuciyarta. Wata Turkish abaya ta fiddo ta saka a jikinta kalar ash mai ratsin baki ajikinta. Vesiline ta murza kaɗan sai taji ta tsani kamshinsa haka kurum taji kamshinsa nayi mata wani iri har yana hautsina mata zuciya lokaci ɗaya. Gefen gado ta kwanta tana sauke numfashi a hankali jin wani irin amai nazuwar mata babu shiri ta nufi toilet da gudu sai ƙakarin amai take wanda babu komai a cikinta. Haɗe kai tayi da bango tana jin kanta na wani irin juyawa, bata kara sanin inda kanta yake ba sai dai ta buɗe ido ta ganta akan bed ɗin Hajja da drip a hannunta. Hajja na zaune a gefenta ta zuba tagumi tana sharar kwalla. Ganin ta buɗe ido da sauri yasa Hajja ta riqota ta rinqe yi mata sannu "Meke damunki yanzu?" Da sauri Rahama ta shiga girgiza mata kai hawaye na cika idonta lokaci ɗaya. Hajja ta kalleta tana girgiza kai tana faɗin. "Kina jin yunwa?" Da sauri Rahama ta ɗaga kai jin tayi babu komai cikinta haka tamkar zata mutu haka takeji. "Me zakici?" Hajja ta faɗa da murna tana riƙe da ɗayan hannunta. "Koko..!" Ta faɗa murya can ƙasa. Da sauri Hajja ta saki hannunta ta nufi kitchen ɗin tana faɗin "Toh bari naje na haɗo maki." Bin Hajjan tayi da ido tana lumshe ido Imran kawai ke cikin ranta batasan wane hali yake ciki ba yanzu, tasan yana can a buge babu wanda ya damu dashi haka babu wanda zai tambayesa meke damunsa. Yanzu kam tana so ta kirashi tana son taji muryarsa sai dai bazata iya taka dokar mahaifinta ba, gashi wayarta ta hannu ya karɓe ya bata wata ya saka mata sabon sim card. Duk da tana da lambar Imran akanta sai dai bazata iya kiransa ba. Cikin minti goma Hajja ta kawo mata kokon mai shegen kauri tamkar ta zuba madara a cikinsa yayi wani kalan fari. Hajja ta taimaka mata ta tashi zaune ta miqe zaune Hajja ta ɗora mata kan bedside drower, ta kalli agogon bangon ɗakin kusan sha biyu da rabi na rana tace. "Hajja ina son na shiga toilet na wanko bakina." Numfashi Hajjan taja tana faɗin. "Toh ni ban san ya ake cire wannan karfen da aka sargafa maki a hannunki ba, amma bari na kira uwar taki ita da ta saka maki sai tazo ta cire miki ki saka wani abu acikin ki." Hajja ta ɗaga waya ta kira Ummi ba'a daɗe ba Ummi ta taho ɗakin Hajja ta cirewa Rahama drip ɗin da ya kusan karewa. Hajja ta riqata zuwa toilet koda suka fito babu Ummi a ɗakin, zama tayi a gefen bed ta ɗauki mug ɗin ta fara shan kokon daɗi ya kama Hajja ganin yadda taga tasha kusan rabi "Ko a saka maki madarar ruwa?" Rahama ta girgiza kai tana faɗin. "Yafi daɗi a haka Hajja." Sosai kokon yayi mata daɗi haka ta faɗawa Hajja shi zata sha da rana, wani daɗi Hajja taji aranta.
***************
Yana kwance cikin royal bed ɗinsa ya dunkule kansa cikin duvert wani irin kalan ciwon kai ke damunsa, kiran Matawalle ne ya shigo wayarsa dakyar ya ɗaga wayar da sanyi murya ya gaishe da Matawallen "Lafiyanka ƙalau kuwa Imran?" Matawalle ya faɗa cikin sanyi murya, ya lumshe ido a hankali kafin ya buɗe can ciki yake faɗawa mahaifinsa lafiya lau. "Owk ka zama cikin shiri jirgin karfe biyu zamubi zuwa Abujan." Sai da ya cije lips kafin ya iya amsawa. "Owk Daddy." Haka kawai ya faɗa ya kashe wayarsa, wani iri Matawalle yakeji aransa dan yasan Imran ɗin na cikin damuwa sosai. Wannan karon ya kamata ya zama namiji yasan cewar ba komai ne kakeso ya zama alkhairi acikin rayuwarka ba. Kiran Aunty Kausar ne ya shigo a wayarsa ɗagawa yayi yana yi mata sallama, suka gaisa ta faɗa masa sakon Ummi na bada kayan Rahama tareda ɗora nasiha a sama. Godia yayi mata, ya faɗa mata yanzu idan zai fito zai baiwa maigadi kayan ya kawo musu. Godiya yayiwa Aunty Kausar ɗin. Sakkowa yai daga kan bed ya shiga haɗawa Rahama kayan, kusan trolley huɗu ya haɗa na kayanta, karfin hali kawai yake akan komai. Kusan 1:00pm ya shiga ɗakin Humaidah Itama tana kwance cikin bed dinta kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai, ya aje mata 100k akan mirror ya faɗa mata cewar zaiyi tafiya shida Daddy idan tana buƙatar wani abu tayi amfani da kuɗin. Fatan sauka lafiya tayi masa har ya fice daga ɗakin idonta na kansa, lokaci yayi da zata bar cikin rayuwar Imran Matawalle duka, dan bata cancanci ta zama matar auren sa ba, yanzu koda ta zauna dashi bazai fasa yi mata gori ba koda kuwa ta canja halinta ne na bin mazan kan titi, ita kam ta tsani gori a rayuwarta, kuma tayi imani da cewar Imran baya cikin kaddararta zata nemi ya rabata da wannan auren dan ko kaɗan bata waji enjoying ɗinsa. Drivern gidan Matawalle ya lodawa kayan Rahama a motar gidan ya kai gidan su Rahaman, nan ma ƙin yarda akayi ya shiga gidan Galadanci sai da Ummi ta fito sa'annan aka bar motar ta shigo. Kai tsaye ɓangaren Hajja aka kai kayan, Hajja ta ɗauka ma kayan lefene sai da akayi mata bayanin kayan Rahama ne na sakawa Imran ya aiko dasu. Baki Hajjan ta buɗe tana kallon uban kayan wai duk na Rahama ne. Rahama na zaune a parlor bin bags ɗin kurum take da ido tana jin zuciyarta na wani irin matsewa da wani sabon ciwo da take yi mata. Ya tabbata kenan Imran ya rabu da ita tunda ya fara tattaro mata kayanta. Sai da sukayi lunch tareda Daddy zuwa 2:00pm suka nufi airport matawalle na kula da yaron nashi ko acikin jirgi baya wata walwala. Nan da nan yaji garin Kano na fita daga ransa ahankali. Tabbas dole yayi wani abun da zaisa yabar garin Kano na ɗan wani lokaci kuma daman akwai wani course da zaiyi a ƙasar India na tsawon watanni tara yanata baya-baya da tafiyar sabida baya so yayi tafiyar da zai sa yabar Rahama, shi kuma baya so ya ɓata karatun ta. Amman wannan karon yaji yana son yin tafiyar zaiyi magana da Daddynsa yasan kuma Daddyn zai goya masa bayan tafiyar sai dai ya zaiyi da Humaidah? kwata-kwata baya sha'awar zama da ita a matsayin matar aurensa.
Karfe biyar na Yammah
(MARCORIONO CHINESE RESTAURANT ABUJA)
Yana ganin yadda Khalifa Turaki yake hargitsa kyakkyawar sumar kansa mai kama data Larabawan madina. "Kasan cikinka yana manne a mahaifarta shine zakayi wannan ganganci? Are you mad Imran?" Khalifa turaki ya faɗa a tsawace yana kallon Imran Matawalle da kyawawan fararen idanunsa. Imran ya girgiza kai yana faɗin. "Saboda farin cikinta nayi hakan, Khaleefa kasan duka auren mu babu wani walwala da farin ciki a cikin sa kuma duk ta sanadiyar iyayenta da basa so, idan banyi abunda mahaifinta keso ba haka zamu cigaba da tafiya tana yi min kallan mugu tunda ni ina yiwa nawa biyayya. Kawai na bashi lokaci da fili ne yayi yadda yake so da yarsa saboda tun ranar dana saki matata na qara maida auren mu.!" Da wani irin yanayi Khalifa Turaki ke kallonsa yana girgiza kai, da mugun mamakinsa yake cewa. "Ka sanar da daddy hakan?" Imran Matawalle ya girgiza kai yana kallon Khalifa da idonsa da suka gama juyewa yake faɗin. "Na saketa da ta haihu mahaifinta zaiyi ƙoƙarin aurar da ita ga wani ba sai naga ta yadda zai ɗaura aure kan aure ba, babu wanda ya isa ya auri Rahama idan har ina raye a duniyar nan saboda itace kaddarata." Kalaman Imran na karshe sun tsayawa Khalifa Turaki arai. "So sai kayi ƙoƙarin ka faɗawa Rahama cewar har yanzu akwai sauran aurenka akanta kar taje ta kwashi wani zunubin." Imran Matawalle ya kwantar da kansa cikin seat ɗin da suka kawata wajen yake faɗin. "Da wace wayar zan faɗa mata hakan? ta riga ta yanke duk wata alaqar mu tun ranar da na rubuta mata takarda da wannan hannun nawa." Ya faɗa yana buga hannayensa akan desk ɗin wajen. A mota Khalifa ya saukar da glass ganin yadda Imran ɗin ya cika musu mota da hayakin sigari. Yana mamakin yadda Imran baya gajiya da durawa cikinsa hayakin sigari, kuma yasan irin illar da takeyi ga lafiyar ɗan Adam. Tamkar yasan tunanin da Khalifa keyi sai yayi murmushi yana faɗin. "Don't worry my friend zan daina wata rana." Khalifa bai ce komai ba ya mai da hankalisa kan tukin da yakeyi, can kuma damuwace a kasan zuciyarsa wacce take neman yi masa yawa duk adalilin Rahama. Yaji labarin soyayyar dake tsakaninta da Imran Matawalle duk a bakin Maheera Matawalle daga lokacin da yaji irin soyayyar dake tsakanin Imran Matawalle da Rahama Galadanci ya tsayar da soyayyar da yake yi mata acikin zuciyarsa da karfin Allah da karfin addu'a. Ko Ammi da Khalifa ya faɗa mata ta daɗe tana jimamin al'amarin. kwana biyu sukayi a Abuja shida daddy suka nufi Kaduna a gidan Aliyu Matawalle wannan karon tafiyar mota sukayi, akan hanyarsu ta zuwa Kaduna yake faɗawa Daddy tafiyarsa course ƙasar India. Daddy yayi murna sosai shima ya faɗa masa zaiyi maganar matsalarsa da Aliyu Matawalle haka Daddy ya bashi shawarar ya sauke komai da yakeji akan Humaidah ya karbeta a matsayin mata yayi tafiyar nan da ita zata taimaka masa sosai. Shi dai shiru yayi bai faɗawa Daddy hukuncin da ya yanke akan hakan ba. Kusan karfe 3:30pm suka shiga garin Kaduna Aliyu Matawalle yayi murna sosai da ganin ɗan na shi. Hakama Yusoof Ali Matawalle wannan karon shima ya shigo gari yayane a wajen Imran Matawalle. Wanka sukayi aka gabatar masu da lunch. Suna gamawa Imran da Yusoof suka fice daga gidan cikin motar Yusoof ɗin. Anan ne kuma senator Bashir Matawalle ya samu damar fayyacewa yayan nasa komai akan matsalar Imran ɗin da mutuwar aurensa da Rahama. Sosai mutuwar auren ta tsayawa Aliyu Matawalle dan sosai ransa yai zafi kuma ya baiwa kanin nashi shawara akan su cigaba da addu'a idan Rahama alkhairi ce acikin rayuwarsa zata dawo, haka yayi mata fatan ta haihu lafiya cikin aminci. Ya ɗora da faɗin zaiyi magana da babban malaminsa zuwa bayan magrib zai ɗauki Daddyn suje suyi masa bayanin matsalar Imran ɗin. Nan ma sai da Matawalle ya kara baiwa ɗan uwansa hakuri akan kin bin maganarsa da yayi a baya na matsalar Imran din, idan ya tuna Mommy ce ta basa shawarar kin yarda da shawarar Ali Matawalle tun a baya sai yaji wani kunci a ransa. Tun daga ranar da Mommy ta yiwa Imran gorin shaye-shaye ya kaurace mata a komai. Itama Mommy sosai abun ke damunta har ta gaji da barar da kudinta a wajen malam mai tasiri dan duk maganin da yabata akan Matawalle da yaronsa baya wani tasiri a kansu. Komai ya tsaya mata cak. Kallo ɗaya zakayiwa Mommy kasan tana tattare da damuwa. Malam Hussain ya dubesu dukan su ya tabbatar masu da cewar shaye-shayen Imran yana da alaqa da asiri dukansu sai da suka shiga shock ya tabbatar masu da Imran sai ya tsani giya baya so yake shanta, duk wani abu na maye baya so kawai yana aikatawa ne badan ransa yana so ba. Da kansa zaiyi masa rubutu yasha na tsawon sati biyu kuma zasuyi masa saukar alkur'ani na sati biyu insha Allahu zai dawo dai-dai. Wani irin abu ya riqa tsayawa maigirma Matawalle a zuciya. Sosai yayiwa malam Hussain alkhairi da godiya haka ya tabbatar masa Imran ɗin zai xauna a Kaduna na tsawon sati biyun. Suna dawowa Aliyu Matawalle ya kira Imran a falonsa ya shaida masa zai tsaya Kaduna na sati biyu. Har zaiyi musu Bashir Matawalle ya ɗaga masa hannu yana faɗin. "Uncle ɗinka ya gama magana Imran.." Babu yadda ya iya dole yai shiru. Washe gari Bashir Matawalle yabar jihar Kaduna, Imran kuma ya zauna a ranar da Matawalle yabar Kaduna a ranar Imran ya fara shan ruwan addu'arsa....
(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida Makarfi
#Khalifa Turaki
#Team Albi
#Haske Writers Association....
[12/13, 10:17 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya na MTN. Ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
49........
Wani irin canjawa jikinsa ya dinga yi sannu a hankali, canzawa yake a duk lokacin da yasha ruwan maganin sai yaji jikinsa yayi wani kalar canjawa, haka indai yasha sai yayi amai sosai, ta sanadiyar hakan sai da ya kwanta a gadon asibiti na tsayin kwanaki uku, nan ɗin ma malam ya yiwa Ali Matawalle bayani akan babu komai duk hanyar samun sauqi ne. Wata irin rama Imran ɗin yayi taban mamaki a cikin sati biyu, yayi wani irin fayau dashi tamkar wanda yai azababben ciwo, gashi bai ƙara bari ya rasa jam'i ba, a gefe guda kuma Yoosuf Matawalle yana ƙara sanarda shi muhimmanci yawan yin azkar da kuma amfanin yi shi. Bayan cikarshi sati biyu a garin Kaduna suka koma wajen Malam Hussain inda ya yiwa Imran ɗin tambayoyi kuma duk ya faɗa masa baya jin komai sai yawan ciwon kai, anan ma sai da ya riƙe kansa ya shiga yi masa addu'o'i haka ya bashi wasu addu'a na tsari da zai riqa yiwa kansa a koda yaushe. Ranar Friday shi da Yusoof Matawalle suka sauka a garin Kano. Sosai Bashir Matawalle yayi murna daganin yaron nashi, sai dai yayi rama ba yar kaɗan ba, Yusoof ɗakin Imran dake cikin gidan su anan ya sauka. Yayin da Imran kuma ya nufi nashi gidan da ɗayar motar Matawalle da yake amfani da ita. Sai kusan magrib ya sauko ƙasa da car key a hannunsa da kuma farar takarda, kai tsaye ɗakin Humaidah ya nufa, wannan karon kwance take cikin soofa tana danna waya kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai, ta miqe zaune fuska babu walwala take faɗin. "Ashe ka dawo?" Ɗaga kai kurum yayi batareda yayi magana ba. "Daman ina son muyi magana." Ta faɗa tana kallon sa, gyaran murya yayi yana gyara tsayuwarsa yake faɗin "Ina saurarenki." Ji tayi harshenta nayi mata nauyi haka zuciyarta na wani irin bugawa, tana kaunar Imran, Amman ya zama dole tabarshi da wani irin yanayi cikin muryarta haka muryarta na rawa sosai take faɗin. "So nake ka datse igiyoyin aurenmu." Baki ya buɗe yana kallonta da shock a fuskarsa, bai taɓa tunanin Humaidah zata iya faɗa masa haka ba, sai dai wani sashe na zuciyarsa yaji wani irin tausayinta ya cika masa zuciyarshi. Takowa yayi zuwa gabanta, samun kansa yayi da zama gefenta wanda space kaɗan ne a tsakaninsu, sosai takejin kusancinsu na kara jefata cikin muguwar kaunarsa. "Nasan bani da kirki, na wahalar dake a auran nan Humaidah kiyi hakuri ki yafe min, ba laifina bane laifin zuciyata ne da taki karbarki a matsayin abokiyar rayuwa." Wani murmushi yayi tare da kamo hannunta na dama ya riqe cikin hannunsa, da wata irin muryarsa dake ƙassara duka gabobin jikin Humaidah yake faɗin. "Some one rules my love and life. love is fire very, very fire Humy." Ya faɗa sounding so very hurt cikin muryarsa. "Bazan barki a cikin rayuwata ki cigaba da wahala ba, gashi a kwanan nan zan bar ƙasar nan duka, dan haka na yanke igiyoyin aurenmu ga takardar sakin ki Humaidah Allah ya baki wanda ya fini, wanda zai kula dake fiye dani." Ya faɗa yana damka mata takardar cikin tafin hannunta. Kallonsa take tana jin wani irin a zuciyarta, lokaci ɗaya kuma hawaye suka wanke mata fuska hawayen da bata san dalilin zubar suba. Hannu yasa yana ɗauke hawayen gamida girgiza mata kai. Ɗayan hannun ya damka mata car key. "Ga sabuwar mota Humaidah kiyi maneji, haka nayi maki transfer na naira miliyan 3 a account ɗinki, ki kula da kanki dan Allah, and please be a good girl!" Ya faɗa yana ɗan jan kumatunta. Ɗaga masa kai tayi tana sakin murmushi, lokaci ɗaya kuma tayi hugging ɗinsa hawayenta na sauka akan bayansa. Sun ɗauki mintuna a haka kafin ya cirota daga jikinsa, da haka ya fice daga ɗakin.
Kifa kanta tayi cikin soofa ta fashe da wani irin kuka mai sosa rai tana jin wata sabuwar soyayyarsa na samun wurin zama acikin zuciyarta. Damke takardar tayi acikin hannunta ji tayi duniyar na juye mata a hankali, gashi ta tsani Aunty sosai take jin tsanarta aranta, saboda da ta bata tarbiyya ta gari da ta tabbatar Imran Matawalle zai sota zai darajata tamkar yadda yake yiwa Rahama Galadanci... Kallonsa kurum Al'ameen keyi da sabon yanayin da yake hangowa a tattare da Imran Matawalle, wai yau Imran Matawalle ne zaiyi rejecting ɗin shan beer. Sai kusan 10pm na dare yabar cikin club ɗin wanda yaje ne kawai dan tunanin Rahama yabar zuciyarsa ta huta. Sunyi waya da Yusoof da kuma Daddyn shi akan bazai samu shigowa ba sai zuwa safiya yanzu dare yayi. Sosai Rahama ta murje tayi qiba dan Hajja na kula da ita sosai, hakama iyayen nata idan Abba da Ummi suka fita suna dawowa da kayan kwalam irin na masu ciki su bata, sannan Abba yana shigowa sashen Hajja idan yana gida yana ɗan yin hira da Rahama duk dan ta cire