Showing 12001 words to 15000 words out of 149432 words
Chapter 5 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
ne a hasale ya bude baki zai yi magana, Mummy ce ta dakatar dashi ta hanyar masa gargadi da idanunta. Shiru sukayi suna kallon Gwaggon, don inda sabo sun saba da Halin tsohuwar da rigimarta, shima Muhdeen din Abunda ya Kara 'bata masa rai shine kalmar karuwar da ta kira matar da zai aura dashi. Ita kanta Sumayya hawayen da ya cika mata ido ne ya samu nasarar zubowa, ranta ya baci matuka tsanar tsohuwar ce tab a cikin zuciyarta. Muhdeen ya je har gida ya dauko ta don tazo ta gaisar da kakarsa amma tazo gaida tsohuwar amma sakayyar da tayi mata kenan kalmar karuwa kawai take ta maimaitawa a cikin zuciyarta.
Mikewa tayi aguje ta nufi kofar fita, Muhdeen ne ya bi bayanta yana kwala mata kira,
"Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!"
Amma Ina ko kallonsa batayi ba ta ta ci gaba da gudu dai-dai takai bakin gate ne tana kokarin fita ya samu nasarar rike hannunta, kokarin kwatar hannun tayi ta kasa, hakan yasa ta fashe masa da kuka tana fadin
"Ka sake ni na tafi dama ka kawo ni nan ne dan a tozartani? kukanta ne ya tsananta, bai san lokacin da ya janyota jikinsa ya rungume ta yana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, Don ya rasa abunda zai ce.
Dai-dai lokacin ne Gwaggo ta fito daga kofar falon tana fadin "ba dai bin ta yay...
Turus ta tsaya ganin Muhdeen rungume da Sumayya.
Salati ta saka tana tafa hannu cikin Al'ajabi tace
"Inalillahi wa'inna ilaihir rajiun ni 'yar Sulaiman yau naga tashin hankali ganin ido na, lallai iskancin ku ya girma, rashin kunyar ku ta balaga, to wallahi ba a gidan d'ana zaku janyo masa masifa da bala'i da ransa ba, ban san yaushe Muhammadu ya lalace haka ba Amma zanyi maganin ka wannan yarinyar mai kai kamar na jemage ba matar aurenka ba ce".
Muhdeen ya janye ta daga jikin sa ganin tayi shiru ta daina kukar sai hawaye dake bin idanunta, dama ita bata raina abun kuka, hannunta ya rike suka nufi wurin mota da kansa ya bude mata motar ta shiga, Shima ya zagaya ya shiga ya tayar da motar Malam Ibrahim dake kallonsu ne ya wangale masa gate din ya fice.
Gwaggo dake sake da baki tana kallon ikon Allah tasa kai ta shiga falon yadda tabar su haka ta same su, zama tayi tana kallon Inteesar da tayi shiru tana tunani.
Nuna ta Gwaggo tayi da yatsa tace
"To ita wannan yarinyar da na gani wallahi na dauka ita ce matar da zai aura, saboda sun dace da juna sosai, wallahi it ace ta dace dashi ba waccan tambad'ad'd'ar karuwar ba.
Mummy ce ta kalle ta tare da cewa,
"Gwaggo wannan fa zargi kikeyi baki da masaniyar cewa karuwa ce, zato kike kuma kin san ance zato zunubi koda ya kasance gask..."
Bata karasa ba Gwaggo ta nuna ta da yatsa tana fad'in
"Ke Fatima a hir dinki ki fita a idona na runtse, idan ba karuwa ba wace ce ita? Ki nuna uban irin kayan da tasa gaba daya surar jikinta a bayyane suke wannan suturar dake jikinta marabar ta da babu kusan daya ne, hata kirjin ta kusan rabinsa waje suke, ga uban gashin dokin da aka kara mata kamar na sabuwar mahaukaciya ga wani kwalliya dake fuskarta kamar na aljannu".
Mufida ce tayi dariya tare da cewa
"Ke Gwaggo Ina kika taba ganin kwalliya Aljannu"
Harara Gwaggo ta watsa mata tare da cewa,
"Ke kiyi mani shiru ba dake na ke yi ba da uwarki gata nan zaune, da ita nake".
Sannan ta ci gaba da magana tana cewa,
"Yanzu na fahimta wato duk isakanci da suke aikatawa da daurin gindiki suke aikatawa, ni dai bazaku jawo wa dana masifa da bala'i yana zaman zamansa ba".
Murmushin takaici tayi sannan tace,
"To ni meye nawa a ciki me sukayi na daure masu gindi Gwaggo?"
Jinjina kai Gwaggo tayi tare da cewa
"Lallai ma zaki ce me sukayi? Yanxun ganin idona na gansu nike da juna kamar zasu shige jikin juna kafin yasa ta a mota suka fita. Allah ya dawo da ubansa wannan kama bata dace da matar da yakamata a aura ba"
INTEESAR ce ta Mike tare da cewa,
"Mummy bari na tafi dama aiki nakeyi nace bari nazo mu gaisa da Gwaggo".
Gwaggo ce tayi saurin janyo hannunta tace "Allah sarki 'yar nan kin tafi bamu gaisa ba?"
Durkusawa tayi cikin girmamawa da sanyin muryarta tace
"Ina wuni?"
Washe washe baki tayi kamar ba ita ta gama sababi ba, tace,
"Lafiya kalau 'yar nan, ya kike?"
"Alhamdulillah", Inteesar ta amsa Mata.
Gwaggo tace
"Masha Allah. ya sunan ki?"
"Sunana Inteesar"
Shiru Gwaggo tayi tare da cewa
"Too wannan sunan naki da wahala wai isitas"
"Ba Inteesar kadai ba hatta Mummy da Mufida sai da sukayi dariya, Mufida harda kwanciya.
Sakin baki Gwaggo tayi tana kallonsu
"To meye nayi na dariya da zaku tasa ni gaba daga nayi magana kamar mahaukaciya".
Mufida ce tace
"Gwaggo ba fa isitas aka ce ba Inteesar"
Tabe baki Gwaggo tayi tace
"Ni kam bazan iya ba"
Daga nan Inteesar ta tafi gida.
Gwaggo ta kalli mufida tace
"Ita wannan yarinyar daga Ina take?" Mufida ce ta bata labarin Inteesar tun daga ranar da direban Mummy ya kade ta da mota har rana irin ta yau.
A b'angaren Muhdeen da SUMAYYA kuwa suna cikin mota duk yadda yayi kokarin rarrashin ta kin sauraren shi tayi a haka har suka isa gida nan ma haka yayi ta bata hak'uri amma ina bata saurare shi ba, dole ya kyaleta idan ta sauka zuwa gobe zai dawo ko zata saurare shi.
A can b'angaren Gwaggo kuwa Dady na dawowa ko ruwa bata bari yasha ba, ta Fara basa labarin irin abunda idanunta suka gane mata, ta kara da cewa "sai dai Muhdeen ya fasa Auren Sumayya".
Dady ne ya numfasa yace
"To Gwaggo meye hujjar ki da kike kiranta karuwa? kin ganta a wani wurin ne, ko kuma kallon da kikayi mata yasa kika gane cewa karuwar ce?"
Gyara zamanta tayi akan kujera sannan tace,
"Ahaf na nawa kuma? yarinyar da kayan jikinta kusan tsirara ne ko idonta a tsatstsaye alamun na rashin kunya da rashin sanin darajar mutane, da kake tamabaya ta ko na ganta a wani wurin ne to a cikin gidan ka suke badalar su ganin idona na gansu nanike da juna kamar zasu shige jikin juna, yadda na gansu Allah yasa naga annabin rahama, ko mai gadin gidan nan shaida ne, saboda haka ban yarda ka aurawa danka wannan yarinyar mai kama da busasshen crayfish ba".
Shiru Abba yayi tare da ciro wayarsa number Muhdeen ya lalubo ya kirasa, bugu biyu ya daga.
"Assalamu alaikum"
Daddy yace
"Wa'alaika Salam kana Ina ne?"
Shiru Muhdeen yayi kafin yace
"Ina hanya"
"To idan ka iso ka sameni a falona". Daga nan ya katse kiran tare da aje wayar.
Muhdeen ne jikinsa yayi sanyi don ya san tabbas wannan kiran bai rasa nasaba da Gwaggo.
*KUYI HAK'URI DA WANNAN*🙏ÀFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.
Page 11
_________Cikin sanyin jiki ya fito daga cikin motar kamar wanda aka zarewa lakka a jikinsa.
Kai tsaye part din Dady ya nufa, inda ya tarar da Dadyn da Mummy da kuma Gwaggo, da sallama dauke a bakinsa ya shiga falon, Dady da Mummy ne kadai suka amsa masa sallamar ya yin da Gwaggo ta ta'be baki tare da cewa,
"Ga iya sallama rangada sallama kamar na Allah, ya yin da Allah kadai yasan barnar da ta'asar da yake aikatawa a bayan idon al'umma, ka dai dinga jin tsoron Allah ana tunawa da mutuwa yara sai shegen jarabar tsiya".
Harara ya gallawa Gwaggo tare da Jan tsuki
Cikin daga murya Gwaggo tace,
"Bani kayiwa ba uwarka kayiwa gata nan zaune".
Ta karasa maganar tana nuna Mummy da yatsar ta manuniya.
Ko kallon ta bai yi ba ya karasa gabansu ya zauna kan center carpet din falon, ya kalli Dady yace
" Ina wuni Dady?"
"Lapiya qalau"
Ya amsa
Sai ya kalli Mummy zai bud'e baki ya gaisheta kenan sai ta daga masa hannu alamun dakatarwa.
Sunkuyar da k'ai kasa yayi yana jiran mai zasu ce masa yana fargabar abunda zai biyo baya, tunda Gwaggo tayi masa mugun fahimta kuma Don tun kafin ya bar gidan ya ji sallallami da kalamanta.
Muryar Gwaggon ne ta katse sa daga tunanin da ya ke yi,
"Kada Allah yasa ka gaisheni Mana, wadan da suka haifeka sun gaishe Ni d'an banza mai jajayen kunnuwa".
Shi dai bai tanka Mata ba, saboda idan suna gaban Dady da Mummy bai cika kula ta har ya bata amsa ba.
"Muhammad mai kake aikatawa ne haka? Wani irin labari naji Gwaggo Tana fada da yasa raina ya sosu, ahe kai mutumin banza ne ban sani ba eye?"
Dago Kai yayi ya kalli mahaifin nasa ya Fara magana kamar haka
"Amma Dady wallah..."
Dakatar da shi Dady yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yace,
"Kai ma kasani Gwaggo ba za ta yi karya ba, idan har bata ganku ba ba za ta fada ba".
Gwaggo tace
"Da karyatani za ka yi? mutumin banza da idona na ganka manne da kuna ka rungume ta kana sumbatarta Amma zaka karyatani, to uwarka ka karyata bani ba".
Muhdeen da ransa ya gama baci da abunda tsohuwar ke fada ya kalli Dady cikin rawar murya yace,
"Dady Don Allah ka bani dama nayi magana kafin ka yanke hukuncin da zaka yanke.
Zuba masa ido yayi na d'an lokaci, domin shi ma kansa yasan irin tarbiyar da su ka yi wa 'ya'yansu ba tarbiyar banza ba ne, sannan baya jin d'an nasa zai aikata kazamar dabi'a, ga gefe daya kuma ya san Gwaggo mahaifiyarsa ce ba za ta yi masa ƙarya ba, cikin sanyin murya yace,
"Ina Jinka Muhammad Fadi abunda kake son fada",
Muhdeen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ba wa Dady labarin duk abunda ya faru tun daga kiran da Gwaggo tayi masa Yana office tace kar na dawo gida sai yazo Mata da matar da zai aura, da yadda ya d'auko ta da irin cin mutunci da Gwaggo tayi mata.
Shiru yayi kafin ya cigaba da fadin,
Kuma Dady wallahi tunda nake a rayuwata ban taba rike koda hannun wata mace wacce ba muharrama ta bace, ko ita Sumayya da Gwaggo take magana akan ta na rungume ta yanayi ne yasa haka, ganin irin kukan da takeyi na d'aukota har gida na kawo ta anci mata mutunci har da Mata kazafin karuwanci, gashi ranta ya 'baci ta fita tana kuka taki ta saurareni ne sai na d'an rungumeta da sigar Rarrashi kamar yadda kasan Ina rarrashin Asiya da Sumayya idan suna kuka ina son na rarrashesu to hakan ne ya faru tsakanina da ita, kuma maganar cewa na sumbaceta ba sumbatar ta nayi ba rarrashinta nakeyi ta hanyar fada mata kalamai masu sanyaya rai a cikin kunnenta, wallahi Abba ban taba sunbatarta ba".
Shiru Abba yayi Don ya fahimci Dan nasa, cikin sanyin murya Abba yace
"To shi ke nan naji Amma ka kiyaye kada makamancin wannan ya sake faruwa".
Jinjina k'ai yayi tare da cewa "insha Allah"
Mummy dai shiru tayi don bata da ta cewa.
Dady ne ya kalli Gwaggo yace "to me kike son ayi yanzun?".
Gyara dan kwalin ta tayi sannan tace,
"Ni dai ban yarda ya auri wannan tambad'ad'd'yar yarinyar ba ehe, sai dai ya nemo 'yar mutunci yo wannan wace tarbiyya zata ba yaran da zasu Haifa? Don ko ita tana bukatar tarbiyya".
Wani irin kallo Muhdeen yayi wa Gwaggo, ya bude baki da nufin zai maida mata martanin maganarta, Mummy ce ta yi masa kallo mai cike da gargadi hakan yasa yayi shiru ba tare da ya furta kalaman da yayi niyyar fada ba.
Dady ne yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli Gwaggo cikin girmamawa ya Fara magana
"Yanzun haka Gwaggo idan kika ce fasa Auren nan bayan ni da Yaya Adam da Aminaina mu ka je har gidan iyayen yarinyar nan muka nema masa Aurenta, sun girmamamu da mutuntawa suna muna kallon dattako da kamala, suka dauki 'yarsu suka bawa d'anmu anyi komai an saka rana nan da watanni biyu masu zuwa sannan yanzun muje muce mun fasa aurawa d'anmu 'yarsu munyi masu adalci kenan?".
Gwaggo dai ta'be baki tayi tare da cewa;
"Uhum".
Abba ne ya ya cigaba da maganar da ya ke yi;
"To idan sun tambaye mu dalilin fasa Auren Mai zamuce masu?meye dalilin da yasa muka fasa?Babu hujjar da zamu basu, sannan yarinyar nan da kika Kira da sunan karuwa bakida hujjar kiranta da sunan Don baki ganta Tana karuwanci ba ko wajen da karuwai suke zuwa, sannan maganar rashin tarbiyya da kika fada bazaki tabbatar da hakan ba don baki zauna da ita ba, sannan Ana sanin mutum ta hanyar zama dashi da aiyukan da mutum yake aikatawa ba ta suturar da yake sakawa ba, ni dai Don Allah na roke Alfarma a wajenki da ki bari ayi bikin nan kada mu zama kananun mutane".
Gwaggo tace
"Shi ke nan tunda haka kace, daga kai har matar ka kun goyi bayansa ai shi ke nan tunda haka kuka gani duk abunda dan ku yake so shi kuke so idon ku ya rufe baku hango abunda nake hangowa a tattare da ita ba shi ke nan ai"
Daga nan ta mike zata bar falon sai ta tsaya bakin kofar ta dawo ta kallesu tace;
"Ba mugun baki nayi ba, amma ku sani akwai ranar da ku da kanku zaku tuna da cewar ni na hana auren saboda akwai abunda na hango, lokacin da zaku gano abunda na hango kuma lokacin kun riga kun makara aikin gama ya riga da ya gama amma lallai sai tazo, Muhammadu ka rubuta ka ajiye duk sai kun yi nadama".
Abba ne ya budi baki yace
"Gwaggo Don Allah ki daina fadin haka Addu'ar ki kadai muke bukata da Sanya alkhairi".
"To shi ke nan ina maku addu'a kowa ne rana, biki kuma Allah ya sanya alkhairi".
Tana gama fadar haka ta sa k'ai ta fice.
Abba ne ya kalli Mummy da Muhdeen yace
"Kada ku damu komai zai tafi dai-dai da yardar Allah".
Mummy dai shiru tayi ta wuce b'angaren dama ba wai Tana son Auren Muhdeen da Sumayya ne ba, Amma ba yadda ta iya tunda ya nace ya ji ya gani ita ya ke so.
Mikewa Muhdeen yayi jin ana kiran sallar magariba, Mummy ma mikewa tayi tabi bayansa ya yin da Dady ya nufi bedroom din sa Don doro Alwala ya nufi masallaci.
Wata Rana bayan Inteesar ta gama yiwa umman ta aiki kamar yadda ta saba.sai ta shigar dakin ta ta kwanta bisa 'yar katifar ta Tana Jin alamun zazza'bi na damunta, wayarta ne tayi ringing ta duna taga sunan Mufida ce ke kira, daga wayar tayi tare da yin sallama.
Mufida dake zaune akan kujera Gwaggo na tsaye akanta Tana Mata fadar cewa me yasa har yanzun Inteesar Bata zo ba kuma Bata Kira ta a waya ba? Ita wallahi bazata ci Abincin Mummy ba sai dai a Kira Inteesar tazo suyi girki.
Jin Inteesar ta daga wayar ne yasa mufida cewa
"Inteesar Don Allah ki zo ko wannan rigimammiyar zata Bari nasha ruwa".
"Gaky Mufida gaskiya bazan samu zuwa yanzun ba don har na d'an kwanta anjima zan shigo"
Sai ta d'an yi shiru sanin cewar idan har Bata tafi ba Gwaggo zata hana kowa sakat a gidan Nan idan Bata ga Inteesar ba.
"Ko kuma kice mata gani nan zuwa yanzun nan insha Allah"
Daga Nan ta katse kiran ta Mike tsaye tare da daukar wayarta da Hijab dinta, bayan saka Hijab din ta kai tsaye dakin mahaifiyarta nufa, zaune ta sameta bakin gado Tana ninke kayan wankin da Inteesar ta wanke mata.da sallama ta shiga dakin,Umma ta amsa Mata Tana sakin murmushi cikin son d'iyarta d'aya tilo da Allah ya Bata.
"Umma dama zan je gidansu Mufida ne, Gwaggo ce take son wai na je muyi girki tare"
Jinjina Kai Ummu tayi
"To ke da kika ce bakida lafiya kina jin ciwon k'ai da zazza'bi? tunda kin sha magani kamata yayi ki kwanta ki sanar dasu baki Jin dadi"
Ta karasa maganar Tana tausayin 'yarta.
Murmushin karfin hali tayi tare da cewa,
"Umma baki San Halin Tsohuwar Nan ba wallahi idan ban je ba zata addabe su ne musamman Mufida"
"To shi ke nan Allah ya baki lafiya ki gaishesu"
"To za su ji"
Daga nan ta fice ta nufi gidansu Mufida lokaci zuwa lokaci takan zubar da yawu a bakin ta kamar wata mai ciki, dama haka zazza'bin ta yake saboda bakinta ba taste bata iya had'iyar yawu.
Tana isa bakin kofar gidan ta gaida Mallam Ibrahim Mai gadi, sannan ta nufi cikin gidan dai-dai lokacin da ta karasa kan barandan kafin ta shiga falon sai ta juya ta zubar da yuwun bakin ta, kwatsam ta ji ance "keee!" da sauri ta waiga ganin Muhdeen zaune akan kujera Yana kallon yawun da ta watsa masa a Riga.l, cikin kad'uwa ta zaro ido Tana kallonsa kafin ta ankare ya sauke Mata tagwayen maruka biyu, cikin azaba ta kwalla kara wanda ya ja hankalin jama'ar gidan.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne,ban Rubuta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba .Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
Page1️⃣2️⃣
Cikin azaba ta kwalla Kara Wanda yaja hankalin jama'ar gidan.Mallam Ibrahim Mai gadi da yunusa Mai bawa fulawa ruwa da sauran ma'aikatan gidan cirko-cirko sukayi suna kallon ikon Allah. yayinda Inteesar ke durkushe dade da kuncin ta Muhdeen kuwa na tsaye akanta Yana huci, dai-dai lokacin Mummy da Mufida da Gwaggo suka karaso wajen,ganin Inteesar durkushe Tana kuka yasa Mummy cikin sauri ta karasa tare da mikar da ita tsaye,ganin sawun kumatunta sunyi jajir ga sawun yatsu biyar da Muhdeen ya Mata ne yasa hankain tashi cikin tsananin bacin Rai Mummy ta Fara magana.
"Yanzun son Kaine ka daga hannayen ka akan fuskar yarinyar Nan ka mare ta akan meye? Yarinyar da ba ruwan ta Mai gudun 'bacin ran mutane zaka mare ta?"
Yana huci ya Fara magana
"Mummy baki ga abunda tayi Mani bane,yawun bakin ta ta watsa Mani a jikin Ka..."
Kafin ya Karasa maganar sa ne Gwaggo tayi saurin cewa,
"To shugaban mugaye na Duniya sai me idan ta watsa maka yuwun bakin ta?ko yawun najasa ne da zaka kama 'yar mutane daga zuwan ta ka Fara dukan ta kamar