Showing 3001 words to 6000 words out of 38686 words

Chapter 2 - GAYYA CE! COMPLETED by Fatima Alaramma Alaramma-1.pdf

24 Jul 2025

979

ba mahaifin jalila ba ne,

Wanda ake kiran ta da bebyn papy shiɗin mahaifin ne ga jawad,

kuma shikadai-ne dansa a duniya,
Ammy ita ce mahaifiya ga jawad itama shine ɗa ɗaya da allah ya bata a duniya,


papa shi ne mahaifin jalilah wadda ake kirah da bebyn papy, ana masa alkun yane da bebyn papy,

amma azahirin gaskiya Al-Hassan shine mahaifin ta,

ita kuma mamy ita ce mahaifiyar jalilah,

dayake tafi rayuwa gidan su jawad shiyasaka ake kasa ban-bance iyayen su,

Bayan jawad ya gama aikin sa misalin karfe biyar na yamma ya fito zuwa office din papa saboda yun
wa yake ji sosai,

ga kuma ga jiya atare dashi.
da sallama ya shiga office din ran-nan nasa a hade,
sai da ya basa izzini sannan ya shiga.

gaida papa yayi cikin Kasai tacciyar muryar sa maikama da busar sarewa,

bayan ya amsa ne yake tam-bayar'sa ya aiki?

" dama papa na gama aikin'ne, i
zan koma gida shine nazo na gaya maka ko zamu tafi yanzu?"

Yakare maganar da yanayin tam'baya,

" ohhh jawad kaje kawai akwai wani aiki da nake so na karasa idan na kam-malah zuwa mag'riba zan
dawo insha allah,"

" tom shikenan a tashi lpy papa,"

" insha allah jawad papa ya fada yana murmushi,

Sosai jawad yayi farin cikin rashin tafiyar papa yan'zu, saboda sam baya san tafiyar dasukeyi a tare,

kai tsaye wayar sa ya ɗauka ya kira Adamu direver.
kafin ya karasa bakin parking space Adamu direver ya karaso.

Labaran dake gefe ne ya bude masa mota ya shiga.
Adamu yatashi motar bai tsaya ko ina ba sai cikin gidan su.

farking yayi Daya daga cikin ma aikata ya budewa Jawad . Fitowa yayi cikin tafiyar'sa ta zaratan mazan
da suka am-sa sunan su Maza ya shige gida,

tare da dagawa Adamu hannu alamar godiya,

Kai tsaye ban daki yashiga yasakar-wa kan'sa ruwa bayan yashiga Hadadden dakin'sa dayagama jika
da kayan mure rayuwa,

Saida yashare sama da mintuna talatin aban dakin yafito jikin sa na figar ruwa.

Shirya jikinsa yayi cikin kananan kayanda suka matukar kar-bar farar fatar'sa,


kai tsaye babban falo ya nufa inda ya tadda Ammy zaune da alama wani take jirah,

karasawa yayi ya gaida ta cikin ladabi. Fus'karta dauke da fara a ta amsa tare da yimasa sannu da
office,

"Jawad!"

" na am Ammy."


"wai bana fada maka ka dinga dariya ba?"

"a ce shi mutum kullum fuska a haɗe kamar Wanda aka aikowa sakon uwar'sa ko uban'sa sun rasu?"

"haba mana Jawad manzon Allah cewa yayi murmushima sadakace."


"nikai-na da nake mahaifiyar ka har na fara manta kalar dariyar ka haba jawad."

" kiyi hakuri insha allah zaa kgarah."

"Allah ya sa."

" kullum haka kake fada ai."

"papy nake jirah ya fito muyi dina. tun da naji ankirah sallah nasan sai an jima,"

jawad ya faɗa yana mikewa daga kan table din.

"zakaje masallaci ne ko?,"

"eh."

kawai yace mata tare da tashi yafita zuwa masallacin ,
dama da alwalar sa,

"Allah dai ya shirya mun kai jawad."

"Ammy tayi maganar tana kallon'sa cike da so.

Bayan sun dawo masallaci ne suka ran kayo zuwa gida,

kai tsaye daining suka zarce.
Zaune suka Sami Ammy da bebyn papy saboda daman in dai papy na gari to bata zama a gidan-su har
sai ran da papy yayi tafiya,

Dinar suka farah bayan Ammy tayi sarving din su, sosai abincin yai'musu Dan dano a Baki,

Bayan jawad ya gama ne ya jawo fulas din shayi ya farah zuba wa a cup,

duk abin da yake akan idanun bebyn papy.

ta rasa ta in da zata tsokanesa nan fa taji wani mugun dadi ganin zai zuba tey tasan ko ba komai ba
sugar a wajen dole zai mata magana,

be ga sugar ba ya juyo ya kalleta fus'ka adaure yace..

"daukon sugar,"

bata ce masa kala ba ta mike ta shige kicking da mur-nar ta,

wata farar ruba tadauko ta aje gaban'sa sanan takoma ta zauna,
idanu ta zuba masa ganin ya fara zubawa.
sosai sobida shi mutum ne mai san zaki sosai,

ita kuwa tana gefe tana murmushin mugun ta.

bayan ya gama ne ya ɗaga cup din yakai bakinsa. Baiyi tunanin komai ba Dan haka ya kurba da yawa,

ai baisan sadda yayi saurin fesar-waba.

sabida yan'da yaji wani azabar gishirin daya kusa cire masa har-she kan tsabar kaifinsa,

cikin tsananin bacin rai ya kalli Jalilah tare dayin kwafa,

Tsaki yayi ransa idan yayi dubu abace yake.

Ammy da papy ne sukashiga tam-bayar'sa ko lafiya?

kasa magana yayi sabida tsananin bacin rai,

idanun-sa sun kada sunyi jajir, makoshinsa har daci yakemasa tsabar takai-ci,

baice kala ba ya mike ya bar fallon.
Binsa sukayi da kallo cikin mamakin ko lpy?




*GARIN KADU NA*



"Jawahir! ki fito haka mana kafin dare yayi kin san fa bana san ki dinga kaiwa dare suyar Awarar nan
ko?"


"ganinan mama azkar din nan nake son na karasa kafin na fito."

" kuma insha Allahu zata kare da wuri, "

"insha Allah." cewar mama,
Kyakykyawar datti juwar-da aka kirah da mamace na kallah,
bawata babbar mace bace dan ashe karu bazata Fi 40 da haihuwa ba,

amman kana ganin ta kasan akwai wahalah a tattare da ita,

ga kuma wata rama dan abushe take sosai zanin jikin'ta duk yabi ya kode ya jeme,

mataccen gida ne mai daki biyu da wani gajeran ban daki idan kafiye tsayi ka shiga wanka tsab Wanda
kekusa zaigan'ka,

Tsakar gidan bayada Fili kokadan . duk ya farfashe dagani kaga gidan talaka wanda kekar-bar rayuwa,

"Jawahir!".

"gani mama."

"haba ki fito mana zaman ya isa haka,"

" gasu SANI sun kai maki kayan suyya tun dazu kilama man yayi zafi,"

" dan nasan SANI zai hura wutar",
"kifito dare fa yanasakeyi,"

mama ta kare zan cen cikin gajiyawa da surutu.

"To mama gani nan."
Kyakykyawar budur war da mama kekira Jawahir tafada,

"yauwa fito haka",

mama dake wanke wanken tayi maganar.

"yauwa mama gani zan tafi kiyimin addu a",

"Tom Jawahir Allah ya tsare ki a kula dan Allah ki kama kan ki kinji?"

"sabida shi talauci ba hauka bane kuma ki ƙara kula sosai Allah yayi maki albarka,"

addu,ar da mahaifiyar ta ta kemata a kullum idan zata fita suyya kenan Kuma tana matukar tasiri
aran'ta,



Lokacin da nakarewa Jawahir kallo Saida Al kalamina yakusa faduwa domin-ko batada ban-banci da
bebyn Papy,

Komai Nasu iri dayane tamkar an tsaga Kara.

KUBIYO NI DAN JIN WACECE WANNAN DAKE MATUKAR KAMA DA BEBYN PAPY ??????

INA GODIYA SOSAI MASU BIBIYAR WANNAN LITTAFIN

TAKU HAR KULLUM
FALARAMMA


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•






Typing

GAYYA CE!
*Free page*




*Written by*

*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*



https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ



Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun
Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.



✨✨✨

Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda
ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da
kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges
nagode.







PG5⃣&6⃣

Tabbas wannnan ba bebyn papa bace to maima zai kawo bebyn papa nan. Ita kuwa jawahir sakai tayi
tafita wani karamin mataccen soran su wanda ko rufi babu asaman shi. Kai tsaye bakin yar kasuwar dake
gefen gidan nasu ta tsaya ta zauna kan kujerarta ta suyya dan kuwa tayi sa,a man yayi zafi sosai ta farah
zuba awarar, nan da nan aka farah siya Alhmdllh. misalin takwas da rabi na 8:30pm suka gama ita da
sani suka haɗa kayan zuwa gida.
Da sallama ta shiga ɗakin mama ta zauna gefen wata lametsatsiyar katifa yar bodin, "mama na dawo"
"sannu da dawowa jawahir ya kasuwar? Alhmdllh sai godiya, "ma sha Allah cewar mama tare da karɓar
kudin da jawahir ɗin ke miƙomata tafarah irgawa nairah dubu goma ne da ɗari biyar da hamsin kudin, "
mama ce ta kalli ƴar tata tace Allah ya maki albarka tashi kije ki kwanta sai Allah ya kaimu kiyi addua
kafin ki kwanta" idan kuma zakiyi wanka ga ruwan zafi can, "banajin daɗine kai na ke ciwo, "to mama
Allah ya baki lpy sannan ta fice abunta tare da taisayawa mahaifiyarta ta wannan kenan.
Yau ne ya kama ranar monday ranar da bebyn papa zata farah zuwa company dan aiki da ɗan,uwan ta
Jawad. Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa da kalar pinky mayafinta da jakarta duk pinky tayi kyau
sosai dan bebyn papa kyakyawace ta ajin farko. A babban falo tayiwa kanta masauki dan jiran fitowar
papa, batafi minti 2 a wajen ba papa ya fito riƙe da jakar shi a hannun Ammy, cikin farinciki beby ta
ƙarasa gaban papa ta rungume shi tana mashi barka da fitowa "Kallanta yayi cikin farinciki sannan yace
bebyn kinyi kyau sosai fa", mushi mushi tayi tace ngd papana. "sannan ta kalli Ammy tace sorry Amma na
ina fatan kin tashi lpy, "Dariya Amma tayi tace wato sai yanzu kika ganni ko" Dariya bebyn papa tayi tace
kinsan babu wani abun gani muddun papana na kusa dani wannan kenan.

Kai tsaye bakin motar papa suka tsaya, yayin da beby tuni ta shige papa kuma sukayi sallama da
Ammy sannan suka ɗauki hanyar (J. U. J) company beby ce a gyefen papa tana ta zuba mashi surutu can
kuma tace papa na, tafaɗi cikin wata murya, "kallanta ya ɗago yayi dan ya fahimci magana zatayi yace
na,am bebyn ya akayi" Papa wai maiyyasa yaya jawad bazaiyi aure ba?, papa akwai ƴan mata da dama da
suke san yaya jawad fa, kuma ayanzu yaya jawad yanada shekarun daya dace yayi hakan, musamman
idan kafahimci yadda bayasan yawan shigarsa jama,a papa a tunani na ya kamata asamu wadda zata saka
yaya jawad farinciki koyaya ne ta ƙare maganar tana kallan papa, wanda shima ita yake kallo" "Tabbas
wannan maganar taki akan gaskiya take beby Amma matsalah guda ɗaya ce wacce zata iyya zama da
jawad a irin halin nan nashi yaro saiya wuni baice kallaba, ya ƙare zancen cikin jimami" haka ne papa
amma wllh nasan za,asamu sbd yaya jawad ne mutum ne na musamman ga addini da sanin ya kamata"
Tom shikenan beby in sha Allah za,asan yadda za,ayi yawwa beby yau da safiyar nan mrst Obey ya kirani
za,aje garin kaduna dan tabbatar da wannan yarjejeniyar ta haɗa kwangilar mu dasu amma inaso keda
jawad kuje tare nan da sati ɗaya dan ni bazan samu dama ba", Ba damuwa papa na Allah ya nuna mana
lokacin, daidai nan kuma sukayi parking harabar company.

"Mom na faɗa makifa ni makaran tar da yaya yusuf yake koyarwa nake so a kai ne haba Jamlah wllh
bana so akai ki makarantar da yusuf yake wllh sbd takura ma shi zakiya sam bakiji wllh nifa mom indai ba
canba na fasa, aa aa meyake faruwa a falon nan haka wani matashin dattijo yafaɗa, "yauwa Dad kwarah
da kazo mom ce wai baza,a kaini makarantar da yaya yusuf ke koyarwa ba, ta ƙare maganar cikin
tsagwaɓa, mom dake zaune tace wllh kasani dad indai aka kai jamlah makarantar da yusuf ke koyarwa an
ɗauki hakkin shin sbd sam jamlah bataji sai dai shirin Allah, " zama yayi kan kugerar gefen shi sannan ya
jawo jamlah jikin shi yace mamana ki kwantar da hankalin ki, yau da safiyar nan natashi da canjin wajen
aiki an maida ni kaduna kuma nan da kwana uku zamu koma da izinin Allah sannan akwai wani
makaranta a kaduna dana sama maki zaki farah zuwa na kuma siya maki motar d za,adinga kaiki
makaranta da itta dan banason kina driving,"cikin farinciki Jamlah ta rungume mahaifina nata tace dad
nagode fa sosai ta kuma fashe da kuka tace dad ubangiji ya maka abunda kamana Allah yasaka maka da
mafifincin Alheri ina sanka my dad, "ya ƙara rungeta jikin shi yace nima hk my jamlah, daga nan zance ya
ƙare wannaan kenan.
Da misalin ƙarfe biyar na yamma jamlah tafito dan zuwa wajen gidan yayan mahaifin nata wato
gidan su yaya yusuf a bakin kofar gidan ta tsaya tana kallan ko inna kafin daga bisani naga tayi murshi ta
ɗibi ƙasa tashiga gidan bakin ta ɗau ke da sallah ma tayi kuwa sa,a babu kowa a tsakar gidan dan hk tasa
kai zuwa ciki kai tsaye har zata shiga falon taji ana buɗe kofar banɗaki tayi saurin tsaya wa yaya yusuf ne
yafito da alamar wanka zanyi harya shiga ya manta wani abu sai ya fito, kai tsaye ɗakin shi ya faɗa ko
kulah ta ɓeba sbd sanin hali. Tana hangar haka tayi sauri komawa da baya ta shige ban ɗakin ta juye
wannan ƙasar ta hanunta a cikin ruwan wankan shi sannan ta fito da sauri ta faɗa falon mama, kan
kugera ta zauna ta kalli mama tace mama ina wuni mama "lpy lau jamlah ya mom ya kuma sanyi sanyi
dama lokacin lokacin sanyi ne, " mama duk lpy suke sanyi kuma Alhmdllh", amma mama naji gidan shiru
ina safiya ne" " ohhhhh safiyya taje gidan yata ne may be anjima ki ganta", yayan ku kuma ya shiga
wanka" haka dai suka cigaba da hirar su, sbd ita mama mutumce ta jamma,a gashi kuma Allah yasa tana
san jamlah, bayan misalin mintina 15 sukaji an bugo ƙofa a ɗan tsorace mama ta ɗago tana kallan yusuf

dake tsaye bakin falon ransa amatuƙar ɓace," ya fara magana wai maiyasa jamlah kin rainani ne
arayuwarki kin hanani jin daɗin rayuwata kullum acikin haduwa da ƙalubalen ki nake haba jamlah," "
mama wai yusuf mai yarinyar nan ta maka ne daga shigowar ta gidan nan gaba ɗaya ka takurah mata
meta maka?" " mama sai da nakai ruwa na zan shiga wanka fitowar da zanyi naga jamlah dama duk jikina
yayi sanyi sbd ganin yarinyar nan ba alkairi bane a gare ni, nashiga wanka na farah kenan naga ruwan
nawa duk ƙasa gashi nariga na saɓe jikina haka na watsa na fito gashi babu wani ruwan zafin ga sanyi ta
kyauta min kenan?" "yaya yusuf nifa ban san ruwan ka bane nashi banɗaki wanke hannu na amma bada
ganganba" "mama tom kaji dai abinda ta faɗa bada niya tayi maka hakan ba sai kayi hkr" yajuya zai fita
tayi mashi gwalo nan mafa rashi ya ƙaraɓaci, kaɗan daga takurar da jamlah kewa yusuf kenan, wanda ya
kasance ɗan wan baban ta.
Cikin ikon Allah dad ya gama shirya komi nashi yau ne zasu koma garin Kaduna dan cigaba da aikin shi,
mom ce abakin mota ita da dad sai jamlah dake gefenta idon ta cike da kwallah gefe safiyya ce ƙanwar
yusuf sai yusuf wanda murmushin kan fuskar shi ya kasa ɗaukewa, yayin da yake tayiwa su mom fatan
nasarah, mom tuni ta shige muta yayin da Dad ke jiran jamlah, " jamlah ki ƙarasa mana ki shiga mom na
jiranki fa, ta tsinci muryar Yusuf na faɗa mata, fuska dauke da murmushi, kallan shi takeyi sai kuma ta
fashe da kuka tace nasan yaya yusuf daɗi kakeji sbd zan tafi, Ummm jamlah kenan ba haka bane yaza,ayi
da abinda Ubangiji ya tsarah, amma gaskiya jamlah naji matuƙar farincikin tafiyar ki duk da bazanyi
kewar ki ba. ya ƙare maganar yana murmushi", wannan magan ganun duk yana yinsu ne yayin da yazu
daidai kun nan ta, tafaɗa mutar tacigaba da kuka yayin da dad ya jah mutar suka bar layin yusuf yanata
ɗagawa jamlah hannun fuska ɗauke da murmushi.
"Dad mom

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login