Showing 1 words to 1722 words out of 1722 words
Chapter 1 - Kundin Tsatsuba Book 8 By Abdulaziz Madakin Gini .docx
Kundin Tsatsuba 8
Littafin Yaƙi
By Abdulaziz Sani Madakin Gini
yanzu na duniya. A halia yanzu shekarata dubu tamanin da uku a duniya. Abin arzikin da ka yi mini kuwa shi ne, wata rana ka shiga jejin Zabas kana neman saiwar bishiyar Lukis don hada wani sirihi, sai ka ga wata barewa kwance a kas tana numfashi sama-sama, sakamakon barbin ta da a ka yi da kibiya mai dafi. Take tausayin barewar ya kamaka ka je gare ta ka cire mata kihivar, kuma ka sa mata magani wanda ya kashe karfin dafin kibiyar. Kana kallo barewar ta mike ta shiga cikin jeji abinta. To ka sani cewa wannan barewa ba dabba ba ce face 'yata Zarina. Wannan harbi da a ka yi mata kuwa, wani manemin aurenta ne ya so ya hallaka ta, saboda an hana shi ita. Tun daga wannan lokaci na dauki alwashin sai na saka maka da abin da ya fi wanda ka yi mata."
Sa'adda aljana Hammatul Luhurus ta zo nan a zancenta, sai tayi shiru tana dubana, ni kuwa tsananin mamaki ya sa nayi shiru ina juya alamarin cikin Kwakwalwata. Daga can sai Hamantul Luhurus ta yi mini ban kwana ta bace. Wannan shi ne usulin zamana a nan, yanzu ga shi kun zo mini da abin da zai wanke mini bakin cikin rayuwata.
Lokacin da Boka Hafsil Habar ya zo nan a zancensa, sai Jafar ya dube shi ya ce "Ya kai wannan Boka, hakika mun ji labarinka mai ban tausayi da al'ajabi ne, amma ka sani cewa idan ka raba mu da wannan littafi ba ka yi mana adalci ba, domin mun sha wahałar gaske kafin mu zo nan ma. Zai fi kyau ka biyo mu mu tafi tare izuwa jejin Kalkim don mu dauko takobin Sarjis, sannan mu wuce birnin Teheren mu sato aljani Markahul Sabus, wanda zai iya samo
mana kubar Muftahul Zarbil domin mu bude wannan littafi da ita,"
Ko da jin haka, sai Hafsil Habar ya ce "Wannan ai zancen banza kenan, ya za ai na tafi yawon banza na Bata lokacina, alhalin ga abin da nake jira shekara da shekaru ya zo bannuna? Sai dai ku jira ni na fara zuwa birnin Mazdur tare da Kundin Tsatsuba na dauko fansar abin da Sarki Zurkilu yayi mini, sannan na dawo muku da littafin, ku ma ku je ku aiwatar da taku bukatar."
"Haba, haba, ai wannan ma renin wayo ne. Ya za ai ka ganmu da abinmu, kuma ka ce zaka nuna mana fin karfi. Gaskiya ba zamu amince da haka ba." Jafar yayi wannan furuci cikin fushi.
Kafin ya gama rufe bakinsa, tuni igiyar nan ta karfo ta sake kanannade su shi da Yelisa tana tamatse su, suka fara ihu. Ba zato sai Hafsil Habar ya ga igiyar karfen tasa ta karkatse, kawai sai ga Gimbiya Sima da Waziri Kaddaru sun bayyana a gabansa. Kaddaru na dane da kwari da baka, ita kuma Sima na rike da takobi ta ja layi tana jiran ya motsa ta afka masa.
Cikin fusata Flafsil Habar ya dube su ya ce "Ku kuma su waye?"
"Sanin ko mu su waye bai taso ba, abin da na ke bukata da kai kawai, ka baiwa yaran nan littafinsu su tali. idan kuma ka Ri yanzun nan zan hallaka ka." Gimbiya Sima ce ta yi wannan bayani cikin gadara.
Hafsil Habar ya tuntsire da dariya ya ce "Ina ganin kuna da karti, mai zai hana ku jarraba karbar littafin ku ba su? Na rantse da darajar tsafi zan yake ku ba tare da na yi
amfani da shirin tsafi ba, domin na raina ku, na raina isarku. Yanzun nan zan yi gunduwa-gunduwa da wannan kyakkyawar surar ta ki. Kai kuwa wannan dan guntun, duk dai da ka fi ni tsawo, sai na rugurguza ka kamar yadda kura ke ruburbushe naman a baki."
Yana gama fadin haka a daga hannu sama, sai ga wata zabgegiyar adda ta dira a hannunsa. Addar ta fi shi girma da nauyi, amma sai ya shigakaiwa su Sima sara da ita, yana sarrafata kamar wanda ya rike tsintsiyar laushi. Nan fa wuri ya yamutse aka fara dauki ba dadi. Ba shiri Kaddaru ya yarda kwari da bakansa ya zaro wani mashi da ke daure a bayansa, ya ci gaba da kaiwa Hafsil Havar suka, kuma yana kare saransa. Nan fa Hafsil Habar ya zame musu alakakai ya takure su ya hana su sakat, ma'ana yai ta kai musu sara ba Rakkautawa.
Jafar da Yelisa kuwa sai suka zama 'yan kallo, Yelisa ta dubi Jafar ta ce "Kai amma gaskiya kyakkyawar budurwar nan ta burge ni, dubi yadda ta iya fada, wannan ai ko a fagen yaki sai ta yi barna.
Jafar ya ce "Gaskiya ne, amma ni guntun mutumin nan ya li burge ni. Ga shi tsoho tukuf amma sai kokarin tsiya, ki dubi yadda ya addabe su shi kadai."
"To yanzu kai shi kake so yayi nasara ko su?"
"Haba kawata, ya zan yi na so yayi nasara, alhalin ya raba mu da Kundin Tsatsuba? Ai ni takaici na shi ne rashin iya yakina. Da na iya fada da makami, ai kin ga da sai na taimaka musu.
"An gaya maka ana koyon fada ne a baki, ai sai da jarrabawa. Ga wata takobi can dauki ka je ka jarraba.
Ko da Jafar ya waiga ya ga takobi ajiye a kas, saiya ruga ya dauka, sannan yayi kururuwa ya alkawa Hafsil Habar. Da zuwa Hafsil Habar ya sa kafa ya mangare shi, sat ga Jatar yai sama kamar an cilla kibiya ya kuwa fado kasa a sume daf da inda Yelisa ke tsaye.
Ko da Yelisa ta ga abin da ya same shi, sai dariya ta Kwace mata la ce "Lallai Jafar ka cika sakarai, kawai daga na zuga ka sai ka yi wauta. Ina kai ina fada da wancan tsobon mayakin?"
Jim kadan sai Yelisa ta ga ko motsi Jafar baya yi, nan fa hankalinta ya tashi ta fara jijjiga shi tana kıran sumansa. Jafar dai bat motsa ba. Cikin rudewa la cire wata karamar alkyabba da ta yafa a jikinta, ta rinka yi masa fifita da ita. Nan take Jafar ya farfado cikin ajiyar dogon numfashi. Har yanzu a na ta badakala tsakanın Boka Hatsil Habar da su Gimbiva Sima. Abin mamaki shi ne, duk cikinsu babu wanda aka yiwa rauni, ga shi suna yin lada ne cikin zafin nama ko alamar gajiya babu a tare da su.
Ba zato ba tsamamni sai aka ga waya iska mai Karti ta daga Boka Hafsil Habar ta fyada da kasa, take ya sume.
Iskar ta rikide ta zana Nagaz da aljani Gulzum. Cikin sauri Gulzum ya daddaure Hatsil Habar da wata igiyar tsafi. Shi kuwa Nargaz ya tafi izuwa inda aka ajiye Kundin Tsatsuba. Da zuwa ya Isaya ya karanta wadansu kalmomin tsafi, sannan ya dauki Kundin Tsatsuba salin alin ba tare da wani abu ya mase shi ba. Nargaz ya matso gaban Jatar ya mika masa Kundin Tsatsuba, shi kuma ya karba.
"Ku zo mu tati kada wankin hula ya kai mu dare. Babu irin neman da ba mu yi muku ba muka rasa a inda
kuke, ashe ku nan cikin karkahin kasa." Nargaz ne yayi wannan batu, a sannan ne kuma ya sami damar yiwa su Gimbiya Sima kallon tsaf.
"Wadannan kuma su waye? Meye gaminku da su?" Aljani Gulzum ne yayi wannan tambaya.
Jafar-yayt farat ya ce "Na san su, domin na taba ceton rayuwarsua wancan jejin da muka yada zango. Yanzu kuma su ne suka ceci rayuwata da ta Yelisa a nan. Lallai ba abokan gaba ba ne. A wancan karon wannan kyakkyawar tayi mini bayanin cewa ita ce Gimbiya Sima mai mulkin birnin Laharim, amma ba ta gaya mini dalilin da yasa ta baro kasarta ba."
Ko da jin haka, sai aljani Nargaz ya ce "Haba, ni na san biri yayi kama da mutum. Lallai wadannan ne masu biye da mu a baya, kuma tabbas ba su kenan ba akwai abokin tafiyarsu wanda ya kasance aljan ba mutum ba
"Daina zargin komai gani nan, ni ne abokin tafiyar ta su, lallai ba ka yi karya ba" Aljani Durfus ne yai wannan jawabi, yayin da ya bayyana tsulum a gabansu.
A daidai wannan lokaci ne Boka Hafsil Habar ya farfado daga suman da yayi sakamakon mugun kayen da ajani Nargaz yayi masa. Ko da ya kyallara ido ya gan shi a daddaure da igiyar tsafi, kuma ya ga Kundin Tsatsuba a hannun Jafar, sai ya raina kansa, nan take ya fara tuba, yana mai rokon alfarmar a tafi da shi izuwa jejin Kalkim da fadar sarki Lu'umanu, kuma ya ce ya amince sai bayan an gama karanta Kundin Tsatsuba sannan an ba shi ya tafi birnin Mazdar daukar fansa a kan Sarki Zurkilu.
Yayin da Jafar ya ga Boka Hafsil Habar ya saduda, sai ya bushe da dariya ya ce "Lallai in ka ji ki-gudu, sa-gudu ne bai zo ba."
Jafar ya juya ya fuskanci Gimbiya Sima ya ce "Ya ke sarauniyar kyawawa, sanar da mu dalilin da ya sa kuke biye da mu sau da kafa."
Ba tare da wata gardama ba, Sima ta kwashe labarinta tun daga lokacin da ta aika aka kirawo Waziri Kaddaru ta sanar da shi bukatarta, kawo izuwa lokacin da Boka Sulbaini ya hada su da aljani Durfus suka yi wannan tafiya. Bayan ta kare wannan jawabi, sai kowa yayi shiru yana jinjina al'amarin.
Daga can sai Jafar ya mike tsaye ya daga Kundin Tsatsuba sama ya ce "Yanzu dai na fuskanci cewa duk rigimar duniya a kan wannan littafike yinta. Gaba dayanmu nan akan abu guda muke, saboda haka îña son mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinmu guda, Ina son yanzu mu dunguma mu tafi izuwa jejin Kalkim mu dauko takobin Sarjis, sannan mu tafi birni Teheren mu shiga kurkukun Sarki Lu'umanu mu sato aljani Markahul Sabus. Ku sani cewa, wannan aljani ne kadai zai iya zuwa bangwayen duniya guda uku ya dauko mana sassan kuban Muftahul Zarbil, wacce da ita ce kadai zamu iya bude Kudin Tsatsuba har mu sami damar karanta shi. Kun amince da wannan shawarar, ko kuwa akwai mai korafi?"
Gaba dayansu suka yi shiru, aka rasa wanda zai ce wani abu. Kawai sai Jafar ya kama hannun Yelisa suka dane bayan aljani Gulzum, shi kuma Gulzum ya haye bayan Nargaz
08137237071