Showing 3001 words to 6000 words out of 17850 words
Chapter 2 - ZUCIYA DA KWANJI 3 Hausa Novels by MAIMUNA IDRIS SANI BELI .pdf
"Ah! To ki
zauna
mana kin yi faman tsaiwa ne kamar mai shirin
shekawa a guje?" Ta harera kujerar da ya nuna
mata sannan ta mayar da ganinta gare shi.
"Zan
ci gaba da tsaiwar ne dan idan abin gudun ya
taso ba sai na nemo ta ba". Ya kare mata kallo
tsab cikin nazari,ya tsayar da kallonsa a fuskar
ta
lokacin da tasa fuskar ta dan canja ta hanyar
rahe annuri. "Ya kamata tuntuni mu hadu dan
tattauna abin yi da abdullahi, ragoncinki ya
hana
na ga kuma idan na ci gaba da zama a haka
zamu mutu Abdullahi na nasara a kanmu. Shi ya
sa na dauko batutuwa dankam na tahi inda
kike,ina saka ran za ki cire duk wani tsoro mu
tattauna hanyoyin da za su kai mu rayuwa
tare".
Ta kara gyara tsayuwarta,yanzu fuskar babu
tsoro ko jarumta. Ta ce,"ina jin ka". Ya kara
kare
mata kallo ya ce. "Da gaske ne kin bawa
abdullahi kanki har kina dauke da juna biyu
fatima?" Ba tare da fuskarta ta canja ba ya
dubi
laila sanan da dube shi. "Idan ka sha sauraron
karya daga bakin da ya fada maka. Sai ka zuba
maganar a akwatun shakka,idan kuma daga
amininka ka ji to gaskiyar ke nan.sai kawai ka
yankie min hukuncin da ya dace dani" Ya
sassauta murya da rarrashi. "Duk fa lamarin bai
kai zafin haka ba,ni ko a ya ya kike ina sonki,in
ma cikin ne ki zauna don Allah mu tattauna
yadda za a yi kada ki bari yaron nan ya yi
nasara
a kanmu. Na rantse miki babu abin da ba zan iya
ba a kanki,ban taba tanadin rayuwata da wata
mace bayan ke ba fatima, ban taba kwatanta
cikar kyawun gidana idan babu ke ba....
Like · React · Report · May 18, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
Ke in miki ta mahaukaci,ni wallahi ban zan iya
zaman aure da kowace mace idan ba ke ba,na
san duk yadda yaron nan yake yaudararki ba
zai
ko kwatanta miki a farin cikin da nake jiyar da
ke
ko nake kara tanadin jiyar da ke ba,ki taimake
ni
fatima kar ki goyi bayan abdullahi ya yi sanadin
karewar numfashina....." Yanzu dukkan jikinta
ya
yi sanyi,kuma duban tausayin nan na Alh da ke
dankare a kirjinta ya motsa yake kuma tuna
mata
da gaske ne babu namijin da ya cancanci ya
dore
da ita a duniya sama da Alh,wanda girma da
dukiyarsa ba su taba sauke matsayin ta a idonsa
da zuciyarsa ba. Sai dai wannan tausayin bai
hana ta tuna abubuwan uku da watakila sune
gibi
wajen cika burinkansu,sune kawu Abdullahi
kuma
wata baragurbin dangantaka da Alh ya kulla da
laila. Yanzu ma kallon banza ta ke wa
laila,sannan ta kalli Alh muryarta na rawa ta
ce.
"Daga yammacin jiya zuwa yau,na fara
rinjayar da
tunanina cikin zabin ci gaba da zama da
abdullahi
da dalilan da kusan duk kai ka kirkire su. Bani
da
lokacin dogwayen wasu zantuka a halin yanzu,
duk yadda na kangarewa iyayena ban kai
kangarar da za ka kawo min wannan kwadon
ba,bisa wacce hujjar za ka wanko kafa ka zo
gidan mutum? Kuma dan keta haddi har cikin
dakin matarsa......" Ya yi hanzarin tare da a
firgice. "Matarsa? Yanzu zara'u kin amince
cewa
ke matarsa ce, kin min adalci kuwa idan kika
furta hakan a kunne na.....?" Ita ma ta tare
shi
tana nuna laila. "O.k ba matarsa ba ce? Irin
rayuwar da kake da wannan banzar mu ke? In
irinta muke na tabbatar baka da wani bukatar
jiran ya sake ni ka aura." Yanzu ya fara gane
inda
gizo ya yi sakar saboda haka ya sassauta murya
cike da nuna nadama ya ce mata. "Au baki
yarda
cewa mun je farm fresh dan samun nutsuwar
tattauna halin da muke ciki ba? Yanzu fatima
kina tsammamin akwai wata mace da za ta sha
gabanki a wajena.laila yi mata bayani saboda
Allah. A sanyaye laila ta dago za ta yi magana
da
sauri kuma cikin fishi fatima ta tare ta. "Kar ki
sake ki fada min komai laila, ni tsakanina da ke
sai dai in kai wa Allah kararki,kar ki yi
tsammanin
za ki iya binne ni kamar yadda kike binne Alh.
Akwai tazara mai kima tsakanina da shi, ni ba
za
ki amfane ni da komai ba bare in ji dadin
bakinki
saboda kar in rasa. Sannan ban runtse idon da
zai janyo min gigitar zabubbukan haram in
juyar
da halak ba, ina girmama iyayena ina kuma
gudun dukkan abin da zai janyo duniya ta zage
ni. Saboda haka nake shawartar ki iya takun
ki,idan ba haka ba wallahi kwanan nan za ki
ballowa kanki ruwan da zai shanye miki kai".
Laila shiru, Alh sai faman kallon ta yake yana
kifta idanunwa. Tuni ya san fatima sa dama
birkitaciyya ce, in ta kulla kudurinta sai an sha
faman gaske ake kwance shi. Dubi dai yanzu ta
ki
kwata kwata ta saurare shi bare su warware tarin
matsalolin da suka kuduire musu. Ya muskuta
cikin rashin abin cewa ya ce. "To yanzu ya ya za
ayi? Tunda kin kushe ziyarar da na kawo miki
sai
ki daure ko satar ido ne ki yi ki zo mu tattauna
abin yi,in kuma kin ki haka labudda ba za ki
gako
da ganina a gidan nan ba, idan ba ki yi wasa ba
har dare zan iya kawo ziyara. Ni ba tsoron uban
kowa na ke ba, idan yana takamar shi dan
zamani ne tudu biyu nake ci, nawa zamain da
nasa. "Allah ya ba da sa'a". Abin da ta fada ke
nan cikin daure fuska,ta kuma ciri hijabin jikin
kujera ta zira ta kama hanyar fita daga
falon,ta
fice ta zagaye baya cikin matsanancin dukan
zuciya ta nemi kujera ta zauna,fargabar
duniyar
na ta cika ranta. Abdullahi ya shigo ku kuma ya
samu labarin Alh ya shigo masa gida, tabbatar
da
yadda yake da kawaici da daga mata kafar laifi
ba zai shafi zuwan Alh gidansa ba,kila kuma ya
ki
karbar hanzarinta har maganar ta fasu a
dangi.
Tana nan zaune hindatu ta cimmata,da sakin
fuska ta ce. "Kar dai kin manta da bakinki?
Yanzu
suka fito suna duban ki suka fice". Fatima ta yi
sakare tana kallon hindatu cikin tsoro,sai dai
Hindatu ba ta fahimci komai ba tunda ta saba
da
halayyar fatina ta shan kamshi,idan batu ba ya
bukatar amsa ta kan ja numfashi kafin ta
amsa.
Yanzu ma haka ce ta faru, cikin dawurwura ta
lalibi abin cewa mara hikima. "Mun yi sallama
babu sabo tsakanina da mijin nata da ta kawo
min ne, shi yasa na zo nan na zauna". Hindatu
ba ta zargi komai ba, dan ita kanta ta yi
mamakin katon mutum kamar wannan zai debo
kafa ya shigo gidan mutane haka gidan ma irin
na
Abu turab da ke iya rintse ido ko 'yan 'uwa
maza
ya ce ba ya son zuwan su bare wani mijin kawa.
Hindatu ma ta nemi kujera ta zauna suna dan
hira sama sama wadda hindatu ta kirkiro ta
hanyar tambayar ta yadda ta kara ji.
1 · Like · React · Report · May 18, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
Abdullahi na kan hanyarsa ta dawowa gida aka
kira shi a waya da bakuwar lamba,ya yi bismillah
ya daga cikin shiri domin tsammanin Alh ne. Ai
kuwa ko sallamarsa Alh bai amsa ba cikin
kaushin murya ya ce masa. "Abdullahi kana da
lokacin sauraroma ko kuwa baka da shi? Duk
wanda ka zaba ni dai dai ne a wajena saboda
na
shirya masa". Abdullahi ya rage gudu yasa
signal
yana amsawa cikin jarumta. "Idan kana
tunanin
sauraron naka zai amfanar damu me zai hana
in
saurare ka? Ni fadace fadace ne kawai bana so
shi yasa idan na jika nake kashe wayar. Ya
saukar da. Motar gefen titi ya tsayar da ita
yana
sauraron Alh da ya hadiye fushinsa, cikin murya
cike da gadara ya ce. "Yaushe ka shirya sakar
min mata?" Ya dan cije lebe saboda mugun
zafin
da kalaman suka yi masa, amma sai ya hadiye
da murya a sake ya ce. "Kar ka yi sabo
ALh,matarka kuma?" Cikin zafin rai ya ce.
Abdullahi ya tabe baki ya ce. "A'a,taka ce,
kuma
ni kake jira in sakar maka ita,ni ban gane
wannan
hausar ba...." Alh ya tare a kule. "Kar fa ka
nemi
ka zage ni" Kai tsaye Abdullahi ya amsa. "Ba za
sage ka ba, mu yi maganar da ka kira ni a
kanta.
Alh ya ce. "Ai shine na ce yaushe za ka sakar
min mata?" Cikin tsaurin ido ya ce. "In kuma
na
ce maka ban san ta hanyar da wani ke sakin
matar wani ba, yaushe za ka sakar min mata?
Dole sai ka gyara hausar nan zamu fahimci
juna".
Mamaki da takaici ya lullube Alh,ransa ya dinga
yi masa kuna saboda haka numfashi sarke ya ce.
"Ni kake wawantarwa haka Abdullahi? Na
amince
da kai sai ka ci amanata in dogara da kai sai ka
nemi rusa ni, daga sati biyu ka rike min mace
tsahon shekara? To yanzu sai ka fada min abin
da kake nufi dani, Allah bashi ni kuma ka ji irin
nawa kamun ludayin. Abdullahi ya dora da
jarumta a muryarsa da zuciyarsa ya ce masa.
"Har yanzu ba ka ce komai ba Alh matukar za ka
dinga ambaton fatima da sunan matarka,to
wallahi zan kwanan dubu ina ban fahimce ka
ba".
Shima Alh ya fara tanado. Dakewa wadda a
ka'ida dama shi ya cancance ta ya ce. "Kar ka
yi
tsammamin ina binka yadda kakeso ne dan
tsoro,albarkacin fatima dake karkashinka nake
daga maka lafa,saboda zabin da ta yiwa kanta
na
boyewa kanta abin tir! Ba dan haka ba da tuni
ka
tsuka da tashen tsaurin ido. Ba tare da nuna
damuwa ba abdullahi ya murje ya ce. "Ai bisa
wannan dalilin za ka kira fatima a karkashina?
Matar taka ce ke karkashi na?" A fusace Alh ya
ce. "Kai ka sani karamin mara kunya".
Abdullahi
ya yi wata siriryar dariya ya ce, "to don Allah
mu
takaita gwamawa juna numfashi mana, mu bar
wannan tashe tashe hankulan dai da kake yana
nuna ni ke da matar kuma yanzu zan takaita
maka dogwayen hange da saka rai. A taikace
ina
son matata,kuma in mutu ba zan sake ta
ba,wanna alkwarin na yiwa kaina, kai ma ka
zama shaida,in kana da abin cewa ina jinka,
idan
kuma matakinka zan gani ina jiranka". Sai da
Alh
ya daure jirin da ke dibansa sannan ya yi
magana
cikin fishi ba tare da tauna ba. "To ai da mugun
sauki abdullahi in dai zuwa har ta ka mutu ne
ba
za ka saki fatima ba, ba tare za ka mutu da ita
ba.wata kila ni kuma hukuncina shine mutu ka
bar tan kamar yadda na fada maka,har kisa
zan
iya na dukkan halittar da ta shirya yi min
katanga
da fatima". Abdullahi ma ya tare shi cikin fishi.
"Idan raina a hannunka yake don Allah kar in
sauke wayar nan, wallahi a dauki niyyar zame
maka katuwar katangar karfe da fatima,in ka
so
hukuncina ya ninka kisa sau daya....... Mts! Za
ka bata min lokaci da shirme a soyayar
duniyarka. Bai jira cewar Alh ba ya kashe
wayar,kuma cikin karfin hali ya tashi motar ya
hau tiri,sai dai a karfin halin ya tsaya
kafatanin
ransa a jagule yake a kuma dan wani abu daga
tsoro. Bai yaudari kansa cewa Alh ba zai iya
neman ransa ba, in kuwa haka ne a haka ne ya
kamata ya dauki matak
Like · React · Report · May 18, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
Bai shawara da kowa ba ya juya mota ya nufi
gandun albasa gurin wani abokinsa lauya mai
suna sagiru Ahmad Suka yi tattaunawa ta fiye
da
awa biyu, ban da sauran lokutan sallah da na cin
abinci,duk ya kwashe masa adananiyar hirar da
suke shan yi da Alh, wadda yake adanawa a
wayarsa. Sannan suka rabu a kan wahsegari zai
dawo masa da dukkan wani abu da ya karba da
Alh,a goben su kara tattaunawa in hali ya bayar
su yi kokarin shigar da kara. Bai nemi gidans ba
sai goma, zuciyarsa cike da makakin takaicin
sadiya kuma makare da tausayin fatima wadda
Doctor ya yi umarni kar ta yi ayyukan wahala,
amma ya kore umarnin Dr sannan yana ji yana
gani ya bar ranta a dugunzume, wadda dukkan
hakan zai iya zama matsala a tare da ita. Yana
shiga tsakar gidan dukkan hankalinsa na kan
dakin sadiya da dokin ya ga ta doka yaji,haba
masifarta da bala'inta ya ishe shi. Amma sai
murnarsa ta koma ciki domin ya hangi haske a
dakinta,kuma da karar T V sama sama.haka.
Yasa ya ransa ya yi mugun baci,ya yi daki ya
wuce daki abinsa. Ya yi wanka. Cike. Da kunci
sannan ya zauna a falo yana. Kulla wadda za ta
fisshe shi. Akwai dolancin ya fita. Ya ga
fatima,amma ya hade masa da dolen adalci
zuwa
wajen sadiya. Da ta cancanci. Zuwansa a
yau,kuma. Ko kadan ba ya kaunar dora ido a
kanta,dan haka ake neman yin biyu babu.
Like · React · Report · May 18, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
Haka ya tashi ya tura ya zauna ya nashe
abinsa,dama ya shigo da nono mai kyau da
kudurin ko ya tarar sadiya ta dawo abincin ba
zai
ci ba,shi yasa ma ya zage ya take cikinsa a
gidan
sagiru. Yana zaune Hindatu ta kwankwasa
kofa,ya yi kicin kicin fa bata rai saboda
tsammanin sadiya ce,amma yana ganin Hindatu
dole ya kori bacin ransa ya amsa sallamar ta
cikin walwala a fuska kuma ya yi mata izinin
shiga. Ta nemi gurin zama suka gaisa,ya yi mata
tayin fura cikin zolaya. "Ai ke matsalarki ba a yi
miki tayin fura yanzu sai ki wawashewa
mutum...." Ta tare shi cikin barkwanci. "Dama
abin da ya kawo ni ke nan, ka shigo na ji shiru
ba
ka miko komai ba, ban ko yi girki ba dan bani
tare da yunwa". Ya nuna mata fridge yana
cewa.
"Ban shigo da komai ba sai nono, dauko shi ma
ki raba muku". Ta dan yi dariya ta ce. "A sai na
tsaya damawa?" Shima ya yi dariya ya ce. "Sai
in
dama miki". Ta wuce tana cike da nazarinsa
tana
cikin mamaki, babu shakka babu kunci babu
fargaba irin wadda yake ji idan sun kebe a
girkin
sadiya. Ta tabbatarwa kanta bango ya fara
kaiwa
da masifar sadiya. Ta nufi fridge din ta fito da
nonon a bokitin roba,ya dan daga murya. "Ki zo
mu shanye wannan ina tsammanin ta yi min
yawa, sai ki taho mana da ludayi". Duk mamaki
ya cika ta,har ta je ta dawo da ludayin ya sakko
kasa suka zauna suna sha a kwarya daya, suna
dan hira sama sama. Can a sanyaye ya ce mata.
"Ya ya jikin fadima ko yau ba ki ganta ba?"
Muryarta a sake ta ce. "Da sauki dan dazu da
zama ma har azahar muna tare a bayan muna
hira". Ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya mika
mata
ludayi ta kama,sai da ta hadiye wadda ta zuba
a
bakinta sannan ta dago a sanyaye ta ce.
"Gaskiya Abu turab ba neman wani abin na zo
dakin nan b*, na zo na akan matsalarka da
sadiya...." Ya yi saurin yamutse fuska tare da
tarar numfashinta muryarsa cike da bacin rai ya
ce. "Hindatu na gaji da halin sadiya wallahi
kwannan nan idan ba ta bi a sannu ba zan yi
mata abin da take so wato saki,sai ta je can ta
ci
gaba da rashin tarbiyyar da ta tsotsa". Da sauri
ta tare shi fuskarta na bayyana jimami. "Haba
abu turab,ni ba abin da na zo ji ke nan ba. Yau
gidan ne gaba daya ba na jin dadin sa,kai babu
dadi matan gidan babi dadi. Da shekarun ku da
komai abu turab,duk yadda kake hayaki ai ba a
kara tura shi ba, ni dai in za ka ji shawarata to
zan shawarce ka ci gaba da hakuri". Duk a
maganar ta abin da ya tsanata shine. ....."Kai
babu dadi matan gidan babu dadi...." Wato a
babu dadin har da fatima? To ta wacce sigar?
Cikin dabara ya ce mata. "Matan gidan babu
dadi,to mene ne babu dadin a fatima? Ni babu
abin da ya hadanni da ita,fatima fa ba ta da
matsala Hindatu,ko ban ce ta kai ki kawaici ba
tana sauraron fada idan na yi,kuma ta kan
kokarta ta kiyaye. Amma sadiya duk wani abu
da
zan yi wanda bai yi dai dai da tsarinta ba,to
zata
dauke shi kiyayya ta kuma tirke ni da masifa
kamar haifata ta yi, shi ya sa na barta ta
huta,in
ta ga dama ta canja ni kamar yadda ta yi
ikirari.
Tunda Hindatu ta ji Abdullahi na fasa mata
cikinsa tsakaninsa da sadiya ta tabbatar ba
karamin laifi ta yi masa ba, dan haka ta fara
ba
shi hakurida kalamai na grimamawa. Ta tashi ta
raba musu nonon ke nan sadiya ta kwankwasa
kofa ta shigo, abdullahi na ganinta ya yi wani
mugun hade gira,ya kuma kawar da kai.
Hindatu
ko ta firgita, ta amsa sallamar ta ci gaba da
sabgarta. Mugun kallon da Abdullahi ke wa
sadiya ya sauke katon farashin masifarta, ta
kwaso kafa ne bayan ta ji bugun zuciya na
neman kashe ta saboda shigowar Hindatu dakin
Abu turab a girkinta. To ga shi a gaban hindatu
ya nuna kamar ya ga mutuwarsa. Ta kokarta ta
zauna tana ce masa. "Sannu da zuwa. Shima ya
kokarta ya amsa a ciki "yauwa'. Ya kawar da kai
yana kallon hindatu data sunkuya tana rabon
nono ya ce mata. " Na ji kamar nonon nan da
dan tsami ko?" Ta kada kai. "Ba kama ba
ce,akwai tsamin ma, amma kuma ai yana da
dadi". Ya dan yi tsaki ya ce. "Mts! Anya? Kawai
kar ki raba da fatima ita ciwon ciki bai kamata
ta
sha abu mai tsami ba". A ladabce hindatu ta ce,
"haka ne". Ko banza ta fara ganin sakayyayr
ladabi da rashin daukar dumi irin na tukunyar
kasa. Ta raba ta mayar masa nasa