Showing 42001 words to 45000 words out of 111068 words
Chapter 15 - THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt
daining ɗin.
ZARINA dake ƙwance ta kasa tashi kawai saita fashe da kukan baƙin ciki,tayi imanin da a gidansu take sai abinda ta keso za'ai mata.
Mai babban ɗaki ce ta kalli wani gefen wanda tunaninta ya bata a nan SAIFU yake a zaune,bata san yama daɗe da barin wajan ba,ya nufi wani ɗaki nada ban,cikin ɗan ƙasa da murya tace.
"Soja maza taimaka mata ta miƙe tsaye tasha kunu koza taji ƙarfin jikinta"
Cikin shagwaɓa da sangarta Zarina tace "Ammi ya daɗe da barin wajanfa"cikin jarumta ta rarrafa tare da ƙarasawa wajan daining ɗin,a kasalance ta kama hannun kujerar ta miƙe tsaye tare da zama kan kujera wacce take ɗaya daga cikin kujerun dasu kaiwa daining ɗin ƙawanya.
Saifu kam ƙara gyara tsaiwarsa yay yana bin maka-makan photo nan da suke manne cikin ƙayataccen bedroom ɗin,wani photo ya tsorawa idanu domin duk yafi jan hankalinsa akan sauran,photo'n ɗauke yake mutane biyu mace da namiji,sai kuma wani ɗan ƙaramin beby boy cikin kayan na jarirai an rufesa da showel,idanunsa ya manna akan magidancin namijin wanda yake sanye da Alƙyabba ruwan ƙwai tare da rawani mai kunnuwa guda biyu irinna manyan sarakai,Fuskarsa ɗauke da wani ƙawataccen murmushi wanda ya bayyana asalin ƙyansa da ƙwarjinsa,Gefensa wata kuma ƙyaƙƙyawar matashiya ce,itama sanye da kayanta irin nasu na Igbora ta ɗura Alƙyabba a jikinta irin tasu ta mata.
Lumshe idanunsa yay yana jin kewan Mamynsa na ratsa zuciyarsa da sassajan jikinsa,ware manyan idanunsa yay tare da saukeso akan fuskar mutumin dake sanye da kayan manyan sarakai.
Jiki a mace ya juya zuwa babban parlour'n dake cikin sashin nata.
Sa ɗan sassarfa ya ƙarasa wajan daining ɗin ganin lkc na neman ƙurewa,kujera yaja ya zauna,yana zaman Hadima Kaltume na shiguwa bakinta ɗauke da sallama.
Tana zuwa ta fara sarving ɗinsu na abin buɗe baki,ZARINA kam sai yanzu ta samu nutsuwa jin hanjin cikinta ya warware nutsuwa ta ziyarceta.
A hankali ya ɗauki dabino guda ya sanya cikin bakinsa tare da fara taunashi cikin nutsuwa,a hankali yake cin dabinon har yaci guda baƙwai,a kasalance ya lumshe idanunta tare manna glass cup ɗin da aka zuba masa kunun gyaɗa saida yasha fiye da rabi kana ya ajjiye,gorar ruwa mai sanyi ya ɗauka tare kafawa a bakinsa,wani sanyi yaji yana ratsa cikin jikinsa da jijiyoyin dake jikinsa.
Ƙara lumshe idanunsa yay ƙana ya taune jajayen laɓɓansa cikin daddaɗar murya mai taushin gaske yace.
"ZAHABAZ ZAM'U WABATALATUL U'RUF WASABATIL AJJIRA INSHA ALLAH"
JIJIYOYI SUN JIƘO,ƘISHIRWA YA TAFI LADA TA TABBA GA ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI.
Mai babban ɗaki ya kalla wacce take sanya ƙosai cikin bakinta yace "Ammi barka da shan ruwa ƙishi ya tafi ko?"
"yawwa barka dai soja kasha ruwa lafiya?"lumshe idanunsa yay yana jin nutsuwa na saukar masa tare da wata kasala,a hankali ya ware idanunsa tare da saukeso bisa kanta,tana zaune tana shan haɗin fruit ɗin da tayi ɗazu wanda yaji ƙanƙara,taɓe baki yayi cikin ƙasa da murya dai² kunanta yace "Acici"
"SAIFUDEEN ka barmin yarinya tayi buɗe baki cikin nutsuwa,na lura idan ta ganka duk kiɗimewa take,ki daina tsoransa kinji Zarina"
Baice komai ba ya miƙe har yaje baƙin ƙofa sai kuma ya tsaya yace "Allah yasa na dawo daga yarinya zaune babu sallah taga yadda zanyi filla-filla da wannan jikin kamar an fige kazar hausa"yana faɗin hakan ya fice daga cikin sashin yana jinsa wani fresh tabbas Azumi na musammanne wani murmushi ya saki lokacin data faɗi ƙasa sabida tsabar wahalan data sha.
Da manyan idanunta ta bisa da kallo,ganin ya ɓacewa ganinta ya sanya taja ƙaramin tsaki cikin zuciyarta tace "Ɗan iska"a fili kuma ta kalli Mai babban ɗaki tare da turo baki gaba ta ƙwaɓe fuska tamkar tana kallonta tace "Ammi kiyimin iyaka dashi walahi na tsaneshi,zuciyata na zafi da raɗaɗi idan ganshi,dan Allah Ammi kice masa kada ya sake zuwa"ta ƙare maganar idanunta na zubar da hawaye.
Mai babban ɗaki data lula duniyar tunani taja dugun numfashi kana ta lalubi hannun Zarina tace.
"kin taɓa tunani menene ya sanya kuke da zobe iri ɗaya kuma a yatsa ɗaya?kin taɓa tunanin menene yasa kuka samu kanku a masarauta ɗaya?kin taɓa tunanin menene ya sanya kuke tare dani kuma inuwa guda?"girgiza kai tayi a sanyaye tace "A'a"
"Good girl dalilin shine “ƘADDARA”tabbas zanan ƙaddararku ɗaya ne,kuma ko duka kuna rayuwa sabida dalili ɗaya,haka nan zuƙatanku duk abu ɗaya suke gaya maku,kamar yadda yake nuna ko in kula a kanki,haka kema yanzu kike jin tsanarsa,idan kin tunanin ƙwanakin baya ba haka kike ba,kene da kanki kike kuka akan rashin magana da yake dake,shin baki tunanin aƙwai dalilin daya sanya kike jin tsanar tasa?,ƙwarai ƙarfin ƙaddararsa tafi taki girma,amma kece mahaɗin tashi ƙaddarar,bansan mene a zuciyoyinku ba,amma wata rana zaki gane,ranar da babu ni,ranar daza ku tsinci kanku matsayin abu guda kuma ƙarƙashin inuwa ɗaya"tsura mata idanu Zarina tayi tana son ta gasgata maganganu Mai babban ɗaki amma taki yarda,sosai abinda yay mata yake taɓa masa zuciya,banda Allah yasa ta farka daga baccin daya ɗauketa mekenan zai faru da ita?lumshe idanunta tayi tana jin wani iri a zuciyarta haka nan ta samu kanta da son ganin Lil Prince.
Hadima Kaltume ce tazu ta kama Mai babban ɗaki tare da shigar da ita toilet ta ɗaura mata al'wala,paryer mat ta shimfiɗa kana ta sanya mata hijab,cikin nutsuwa Mai babban ɗaki ta fara gabatar da sallah,Hadima Kaltume itama fita tayi domin ɗaura al'wala..
Sosai ta zurfafa tunanin akan maganganun Mai babban ɗaki amma ta gagara fahimtar komai,daddaɗar muryarsa ce ta sauka cikin kunnuwanta,yadda yake karatu yana fidda ƙira'a tare da baiwa ko wanne harafi haƙƙinsa,sosai karatunsa cikin speaker'n masallacin bilhas ya ciki masarautar lungu da saƙo.
Lafewa tayi jikin kujerar tana sauke numfashi,sosai muryarsa tayi mata daɗi a kunne,a hankali ta miƙe tare da shigewa cikin bedroom ɗin Mai babban ɗaki domin gabatar da salla'n Issha'i da ashan..
A can sashin kuma Lil Prince ne zaune gaban kayan da aka haɗa masa na buɗe bakin da aka ajjiye masa,shuru yay tare da zubawa ƙaramin table ɗin idanu,shi duk basu yake buƙata ba,Zarina yay missed ita idanunsa keson gani.
A hankali ya miƙa hannu tare da jawo shishar dake gabansa ya fara sha,saida ya cika cikinsa da shishar kafin ya soma kaiwa cikinsa ruwa.(buɗe baki da shisha🤔).
Yana gama cin white rince and egg soup with salad ya miƙe tsaye tare da faɗawa kan bed yana tunanin yadda zai yaga Zarina a wannan lokacin ko yaji daɗi a ransa,sosai zuciyarsa ke azabtuwa da rashinta.
Yana jin Masallacin Bilhas na kiran sallah amma yay banza tamkar ba wanda yakai Azumin Ramadan bakinsa ba.
Some hours yana zaune yana faman tunanin yadda zaiga Zarinansa,hannu ya sanya tare da ɗauko wayansa ya kira Yazeed ringing ɗin farko ya ɗaga tare da faɗin.
"Allah ya taimaki magaji ya Azumin,Allah yasa dai kayi dan nasan hali?"tsaki Lil prince yay kana yace.
"damn you, idan banyi azumi ba ai sai zunubin yaymin yawa,now kana inane"ya ƙare maganar yana shafa mararsa wacce yaji tayi masa sama,sbd tsananin feelings ɗin da yake ciki.
Wata dry Yazeed yay cikin dakiya yace.
"for now dai ina gida na gama buɗe baki,but anjima zanje Hotel wajan wata ɗanyar yarinya danai mata al'ƙwarin zatai past na exam ɗinta idan ta amince min"
Murmushi Lil prince yay kana yace "ohh samamin wata baby'n nima,yau dai na ƙarasa cika umarnin Mai martaba wanda boka ya bashi,ina tunanin hakan shi zai bani damar mallakar Zarina as my wife"
Tsaki Yazeed yay daga cikin wayan kana yace "kana da damuwa Lil mene yasa ba zaka cika burinka akan ita Zarinan ba?"
"kaji wawa! Cewa nayi ina sonta fa,bawai irin son da nake amfani dashi akan sauran matan ba,banjin zan iya cutar da ita,aduk lokacin da nayi niyar hakan kaina na matsanta ciwo,gaba ɗaya jikina ya zama very weak,i think aƙwai kariya jikinta,any way dai zamu haɗu a hotel za kaji alart a wayarka"daga haka ya kashe wayar ya faɗa toilet,a gaggauce yay wanka ya sanya Al'ƙyabba ruwan powder,kana ya nufi sashin Uwar suro.
A zaune ya samu Uwar suro kuyangunta suna gefenta suna yi mata fita,da murmushi fuskarta tace.
"A'a yau kuma Magaji ya tuna da zamana a masarautar bilas maraba lale"ta faɗa tana ɗan miƙewa daga kishin giɗan da tayi bayan ta idar da salla'n isha'i,zama yay a gabanta tare da faɗin.
"Kawai dai aikine yay yawa,yaya azumi?"
"Allahamdulillah,aiki kafara yine babu labari ne?"
Shuru yay domin yasan babu wani aiki da yake,kawai Fulani kilishi ce ta hanashi zuwa,sabida rashin jituwar da suke,Inibin daya gani cikin fruits ɗin dake gaban ya sanya hannu ya ciri guda ya sanya cikin bakinsa.
Fulanin sura ce ta gyara zama tare tacewa "wai sai yaushe ne zaka fito da Kulsum daga ɗakin duhun daka saka aka kaita,how long zata kasance a ciki,baka tunanin haƙƙinta zai kamata NAJEEB?ɗago kai yay jinta ambaci real name ɗinsa wanda aka daɗe ba'a kirasa dashi ba,wannan dalilin ya sanya yake ganin girmanta,jinjina kai yay kana yace.
"wlh na manta fa,bari naje nasa Sarkin tsakar gida ya fito da ita"yana faɗin hakan ya miƙe tare da fita waje.
A can harabar Masarautar ya nemi Sarkin tsakar gida akan ya fito da Kulsum,yana faɗin hakan ya hango Saifudeen yana tafiya a hankali cike da nutsuwa suna tafe suna magana da Waziri ƙasa-ƙasa,tsaki yaja kana ya shige cikin motarsa yay waje da gudu.
A hankali Saifu ya sanya hannunsa tare da murɗa handle din ƙofar sashin nasa,yana shiga direct bedroom yay,kana ya nufi bathroom tare da cire kayansa ya saƙale kan hanger,shower ya sakarwa kansa tare da lumshe idanunsa yana jin yadda ruwan shower ke sauka akan fresh skin ɗinsa,duka hannayensa ya sanya ya dafe bango ruwan yaci gaba da saukan a gadon bayansa,lumshe idanunsa yay tare da fesar da wani numfashi mai zafi,a hankali kuma ya buɗe idanunsa sabida ƙyaƙƙyawar fuskarta data fara bai yana cikin eyes ball ɗinsa.
Ƙara runtsa idanunsa yay yana jin wani iri a zuciyarsa,tabbas idan abinda ya keji a zuciyarsa da kuma ganggar jikinsa gaskiya ne,tabbas ƙaddara batai masa adalci ba,banyi tunanin hakan ba,kuma bai shirya hakan ba sam.
A sanyaye ya sanya hannunsa ya shafi mararsa wacce yaji tayi masa sama,da ɗan mamaki ya waro idanunsa tare da sunkuyar da kansa ya zubawa wajan idanu,a karo na biyu ya ƙara sanya hannu ya shafi saman mararsa,hannunsa yabi da idanu ganin ya shafo wani kalan ruwa wanda bai taɓa ganin irinsa a jikinsa ba.
Zubawa marar tasa idanu yay ganin tana halbawa tare da ɗan mimmiƙewa,lumshe idanu yay tare da langwabar da kansa gefe guda cikin yanayi na kasala da kuma shagwaɓa,ya ɗan turo bakinsa gaba tare daya mutsa fuska can ƙasan maƙoshi yace.
"Abin harya kai haka?yaushe hakan ya faru?"pouting ɗinsa yay yana ƙara tunanin yadda ƙyaƙƙyawar fuskarta ke bai yana cikin ƙwayar idanunsa,wani halbawa mararsa tayi tare da ɗan ƙara miƙewa.
Da sauri ya sanya hannu ya riƙe cikin sexcy voice yace.
"Auchiiiii Wayyooo Abbuna marana"ya ƙara maganar ya shafawa da sauri kuma ya saki yana faɗin.
“Astagafirullah”a zuciyarsa,a sanyaye ya ƙarasa wankan tare dayin brush ya ɗaura al'wala kana ya sanya bathrope a jikinsa ya fito.
A sanyaye kuma a kasalance ya ɗan murza body lotion saman fresh chocolate skin ɗinsa,yana gamawa ya fesa body spray mai ɗan sanyi a jiki,wani pech ɗin boxer ya ɗauka sanya wanda ya kama jikinsa,sosai halittarsa ta bayyana,tsorawa ƙwantaccen gashin dake ƙwance saman ƙirjinsa yay,jarumta da kuzari ya aro ya sanyawa kansa kana yaja ƙafafunsa zuwa mamaken royal bed ɗinsa ya ƙwanta,pillow ya jawo ya rungume,wani murmushi ne ya ɗan subuce masa wanda ya fidda tsantsar ƙyau da ƙwarjininsa,ɗan rolling eyes ɗinsa yay kana ya tura ƙaramin yatsansa zuwa baki tare da fara tsotsa a hankali, a sonsa najin abinda ta keji idan tana tsotsan yatsan nata,ƙwaɓe fuska yay tare da lumshe idanunsa,cikin wata iriyar ƙasalalliyar murya yace.
"Ni banji komai ba"da wannan tunanin bacci yay gaba dashi.
_Washe gari_
Misalin 6 na yamma a hankali take ƙwaso foodflast ɗin daga kicthen zuwa daining area,cikin sanyin jikinta take ai watar da komai ita da Hadima kaltume.
Bayan sun gama jera kayan buɗe bakin, ta buɗe cikin bedroom ɗin mai Babban ɗaki tana zuwa ta ganta zaune bisa dadduma tana lazimi,da ɗan sassarfa ta ƙarasa inda take zaune tana zuwa tace.
"Ammina barka da hutawa zo muje lokaci ya kusa fa"murmushin jin daɗi Mai babban ɗaki tayi kana tace.
"Ɗiyata baki gajiya da aiki,yau kam ina Soja ne shuru najisa?"ta ƙare maganar tana neman sandan dogarawarta.
"Uhmm ban sani ba nima"shine kawai abinda tace,kana ta kama hannun Mai babban ɗaki suka nufi waje.
Suna fita ana kiran salla'n magrib kiran salla'n kuma shine yake nuni da lokacin buɗe baki yay bisa tsari na addinin musulunci.
Kujera taja mata tare da zaunar da ita kana itama ta nemi wajan zama,a hankali ta ɗaga idanunta ta zubawa kujerar daya zauna jiya akai,lumshe idanu tayi tana tunanin inda ya shiga,murguɗa baki taya tare da faɗin.
"mene nawa ni"
"da akai me?"cewar Mai babban ɗaki "babu fa"Zarina ta bata amsa a taƙaice.
Har wajan isha'i suna jiran zuwansa amma shuru babu shi.
Misalin ƙarfe goma ya shigo,cikin shigarsa mai ƙyau da tsari wacce ta amshi chocolate skin ɗinsa,cikin zazzaƙar muryarsa me daɗi yay sallama.
"Wa'alaikassalam da Soja"Mai babban ɗaki ta amsa masa tana mai sakin murmushin jin daɗi sabida daman shi take jira taƙi tafiya ɗaki.
Saukar muryarsa cikin kunnanta ya sanya gabanta faɗuwa,curewa tayi waje guda ta soma fidda wani numfashi sabida daɗin turarensa daya daki hancinta wanda yake barazar sauya mata lissafi ya tilasta mata tura fuskarta cikin tafukan hannunta,t wani magaɗisun abu ne ke ɗibanta,sosai idanunta da zuciyarta sukai kewansa na tsayin yini guda harta kasa jurewa.
Tsanar da tayi masa ta sanya sam ba zata iya ɗaga idanu ta gansa ba.
SAIFUDEEN dake bakin ƙofa ya janye idanunsa daga gareta tare da ɗan jan tsaki kaɗan,kana ya nufi wajan Mai babban ɗaki dake zaune bisa wata lafiyayyiyar kujera mai ƙyan gaske.
Yana zuwa ya zame ƙasa tare da ɗora kansa bisa cinyoyinta ya soma sauke ajjiyar zuciya kamar wanda ya shekara yana kuka.
Hannu tasa ta fara bubbugawa bayansa na tsayin wani lokaci, ɗan gyara zama tayi kana tace.
"Har yanzu dai?"kai ya girgiza tare da faɗin "ba wannan ba"
"uhmmm ok me?"miƙewa yay tare da faɗawa jikinta ya rungometa sosai yaci gaba da sakin ajjiyar zuciya ajere-ajere.
"shuru ya isa haka nan"jinjina kai yay cikin ƙarfin hali da juriya yace.
"Ammi zani wajan Abbuna nayi kewansa ban iya jurewa"
"ohh shine na kuka kuma"pouting lips ɗinsa yay ba tare da yace komai ba,can ta nisa tace.
"yaushe ne?"
Ware idanunsa yay kana ya saukesu kan Zarina wacce tayi lamo tana sauraren abinda suke faɗi,ɗauke kai yay kana yace.
"Yanzu insha Allah,jet ma ke jirana"da mamaki tace "yanzu kuma gidanku Soja kamar ana kurarka"ɗan murmushi yay yace "Eh fa Ammi"
"to sai zuwa yaushe ne zaka dawo?"ɗan girgiza kansa yay cikin sarewa da maganar yace.
"bana ce ba"jinjina kai Mai babban ɗaki tayi kana ta shafa kansa tace.
"Masha Allah SAIFUDEEN Allah yay maka albarka amma kada ka manta da shuka bata taba yiyuwa babu mahaɗi,kamar yadda mutum bazai taɓa rayuwa babu iska da ruwa ba,haka kuma kamar yadda mutum baya rayuwa saida ƙaddara a jikinsa All the best Sweethreat"lafewa yay jikinta yana sauraran abinda take faɗa,haka kuma yana ji kamar ya haƙura da tafiyar amma sam bazai iyaba,yakai matakin da idan baiga Abbunsa ba zai iya samun matsala.
Hadima Kaltume yaywa nuni ta miƙa Mai babban ɗaki zuwa bedroom ɗinta,haka kowa akai cikin hikima da lallashi ta nufi ɗaki da ita.
Miƙewa yay a hankali cikin isa da izzah ya nufi inda take ƙwance,a gefenta ya zauna tare da zuba mata fitinannun idanunsa.
Yadda zuciyanta ke gudu very past,da yadda jikinta yaɗan fara rawa ya tabbatar mata yana kusanta,sosai ta kejin idanunsa a jikinta.
Numfashi mai zafi ya fesar tattausan hannunsa ya sanya bisa ƙafafunta ya jawota zuwa inda yake zaune,ƙara runtsa idanunta tayi sosai tana jin wata far gaba da musamman na shigarta,ganin yadda ta kulle idanunta da kuma yadda jikinta ke rawane ya sayashi ware laɓɓansa tare da faɗin.
"kee! Open your eyes"girgiza kai tayi,wani tsaki yaja tare dasa hannu ya dalle mata baki,cikin dakakkiyar murya yace.
"look at me"mai makon tayi abinda yace kawai saita fashe da kuka tare da cure jikinta wace guda.
Duk yadda yasu danne abinda yake zuciyarsa kasawa yay,yana jin wani iri a ransa,sosai kukanta ke takura zuciyarsa,yaje matakin ƙarshen da bazai iya danne abinda yake ransa da zuciyarsa ba,yasan yana da juriya da kuma danne abu a rai,amma wannan ba yajin zai dannu cikin ransa,sosai yaje matakin ƙarshen da bazai iya haƙura ba,koda yay shuru babu shakka zuciyarsa da kanta zata fallasa abinda ke ransa.
A kasalance da kuma yanayin sabon mood daya samu kansa,ya sanya tattausan hannunsa ya jawota jikinsa gaba ɗaya tare da matse bisa faffan ƙirjinsa.
A tare suka sauke ajjiyar zuciya,lallai suna rayuwa ne ƙarƙashin abu guda,kuma dalilin abu guda,kuma su nawa kansu “SO”wanda basu san da hakan ba,bawai SO kawai ba,gaba ɗayansu suna rayuwa da tunani da kuma ƙaunar junane.
Jinta a faffaɗan ƙirjinsa ya sanya taci gaba da kuka tare da ƙoƙarin ƙwace jikinta,a wannan lokacin da zaka tambayeta kukan me take? Ita kanta bata da wannan amsar,sabida bata son ta ƙamaimai kukan mene take ba.
Cikin sabon shauƙin daya samu kansa ya ɗura tattausan laɓɓansa misa kunnanta tare da sauke mata wani zazzafan numfashi,haɗi da ɗan bubbuga bayanta alamar
"Rarrashi"
Can ƙasan maƙoshi yayi amfani da wata sassanyar murya yace.
"Ƙin tsaneni ko?"shuru tayi babu alamar zata bashi amsa,a karo na farko yaji haushi shurunta,runtsa idanunsa yay tare da tsune laɓɓansa,ƙara tura laɓɓansa yay cikin kunanta cikin murya mai amo da ɗan sauti yace.
“RINA..”sai kuma yay shuru yana ƙara ɗan matseta ajikinsa yana jin kamar bazai iya faɗin abinda ke zuciyarsa ba,lumshe idanunsa yay yace.
“RINA I LOVE YOU”
Tsayawa da kukan tayi sabida saukar maganarsa da taji kamar ruwan sama,sosai maganar tazu mata a bazata,kaita ɗaga tare da zuba masa idanunta wanda sukai jaa,hannu ya sanya ya lakaci hawayen tare taune lips ɗinsa yace.
“I LOVE YOU RINA WITH ALL MY HEART bansan SO ba dan hakan bansan tayaya ne zan ƙwatanta maki shiba,bansan yaya ne zan faɗa maki abinda yake rai da zuciyata ba,dukkan abinda ke zuciyata yafi ƙarfin ƙwatance,amma ki sani kuma ki amince da cewa SAIFUDEEN BILYAM LOVES YOU RINA" ya ƙare maganar yana sauke wani wahalallan numfashi,sabida tsayin