Showing 75001 words to 78000 words out of 111068 words
Chapter 26 - THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt
kana tace.
"aƙwai ƙofa ta baya tanan zaki bi kada ki juyo kawai ki tafi bakinki,kina fita ki samu mai napep kice ya kaiki tasha a nan zaki samu ta garinku daga nan ai zaki gane gida ko?"
Kaita gyaɗa mata kana tayi mata gdy harta fita tayi saurin dawowa ta tsurawa wannan sashin kallon wanda kullum saita leƙa ta window,hawayen daya zubu mata ta goge kana ta murza zoben hannunta ta ɗaga hannunta tayiwa wajan bye bye,tana yin hakan ta juya da saurin ta fice a part,duk ƙwatancen da Falmata tayi mata shi tabi harta fice daga gidan sarautar tana fita ta samu mai napep tace masa "tasha" umarnin shiga ya bata tana shiga yaja napep ɗin da sauri sai...
THE NEW IS NOT FREE IS FOR SALE 200 NAIRA ONLY 08119237616
*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
*61-62*
Sai tasha,sauka tayi ta sallami mai napep ɗin,cike da tsoro take wurga ƙwayan idanunta cikin tasha musamman tarin jama'ar data gani sunyi masifar yin yawa,idan ba zata manta wannan shine karan farko na rayuwanta daza tayi ta fiya ita ɗaya.
Lumshe idanunta tayi tana jin zuciyarta na bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito,wanene shi? Mene haɗinta dashi?mene yasanya tunaninsa ya addami zuciyarta har yake nema yay mata illah?yadda fuskarsa ke mata yawo cikin eyes ball ɗinta ya sanya take tunanin kamar ta sanshi but where? Shine abin tunanin kuma tayi imanin babu wanda yake da amsar tambayarta,hawayen da take ɓoyewa ne tun ɗazu suka sami damar sakkowa ta cikin idanunta zuwa kan farar fatar fuskarta.
Zoɓen hannunta ta ƙara damƙewa domin shine kaɗai yake sanyawa taji daɗi da kuma sauƙin abinda ke damunta cikin zuciyarta.
Babban yatsanta ta sanya cikin bakinta ta fara tsotsa wajan 2minutes ta fara sauke ajjiyar zuciyar mai ɗan ƙarfi,a hankali ta ware manyan idanunta jin ana faɗin.
"saura 1 passinger motar kogi"
Da ɗan raguwar ƙarfin daya rage mata ta ƙarasa wajan motar tare da tsura drever'n idanunta,kasa cewa komai tayi sabida dama magana ba aikinta bane,zuwa yanzu ta dawo Zarina ba fake Zarina ta masarautar bilhas,maganar drever'n ce ta dawo daga ita daga tunanin data tafi da yake cewa.
"yarinya maza shiga kada waje ya cika,tubarkallah ƙarama dake amma kin iya zuwa waje mai nisa har haka,ko dake yaran yanzu aƙwai so da wayo,kema fuskarki kawai zata nuna ƙuruciyarki sai sakalci amma ba dai jikinki ba maza shiga kinji"
Da idanu kawai take kallonsa,zuciyarta kuma zallar mamakin mutumin take,daga ganin mutum lkc guda saika hau surutu ratatata kamar ako,raguwan kujerar da yay saura ta shiga ta zauna tare da lumshe idanunta,tana shiga drever yaja motar suka fara tafiya.
Saurin leƙa kanta tayi ta ƙofar motar tana jin kamar tayi mantuwa ne,hannunta tasa saman ƙirjinta tare murza saitin zuciyarta cikin siririyar muryarta tace.
"Ya rabbi see this innocent Zarina i don't understand anything"
Ta faɗa cikin very slowly voice tamkar zatai kuka,komawa tai ta jingina jikin kujerar idanunta na zubwar da ƙwalla,dwon hrt ɗinta kuma cike yake da zallar ƙaunar hrt drm ɗinta,wanda a kullum take ƙwana tashi take tashi dashi,dukkan wani hope da wish ɗinta gaba ɗaya sun tattara garesa ne.
Bata da burin daya huce ta gansa cikin rayuwarta koda sau ɗaya ne,ƙara ware manyan idanunta tayi a karo na farko taji tana son zamanta masarautar bilhas saidai bata san kowa ba,hasalima bata san yaya akai ta tsinci kanta a cikin masarautar ita dai tana bin kowa da idanune,yayinda komai ya gaza ɗaukan brain ɗinta saita zamana kamar statue.
A haka motarsu taci gaba da sharara gudu saman ƙwalta...
Da sauri yake taka ƙafafunsa yana tafe yana gyara zaman alƙyabbar jikinsa,duk surutun da Meera take masa sam baya gane mene take faɗa,gaba ɗaya hankalinsa yana kan Zarina wacce a yau yake saka ran zata zama matarsa ta har abada,wani ƙawataccen murmushi ya saki yana raya irin casun da zaiyi a night club ɗinsa.
Saida ya kusa zuwa sashin Fulani kilishi yace.
"jirani nan cimgum"
Yana faɗin hakan ya shige cikin part ɗin,a zaune ya samesu gaban kilishi,tana zaune saman wata lafiyayyiyar kujera ta sarauta,gefe guda kuma Chiroma ne da Galadima sai kuma Waziri wanda bara zanar kilishi ya sanya yazu waja bawai a son ransa ba.
Yana zuwa suka miƙe tsaye gaba ɗayansu,saida ya zauna sannan suka zauna ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu yana zuwa kan Waziri ya tsallake sabida harga Allah jininsa bai ɗaya danashi ba.
Gyaran murya kilishi tayi tace.
"Bana son a ɗauki dugun lkc ba'a aiwatar da abinda nakeso ba,ina son ɗaurin auren ya kasance kafin a fiddo da wancan yaran mai ƙiran samudawan farko ba,haba jiki duk a murɗe,sannan bana son wata matsala ta faro,a yau basai gobe ba ina son a ɗaurawa magani aure da farin cikin ransa,lallai hakan shine zai tabbatar mani kuna ba yana a koda yaushe kuma a ko wanne lkc,ina son burin Magaji ya cika da ƙarfin mulkin wannan masarautar,ina son na nuna ikona da kuma izzata a wannan lkc'n,ina son aikata abinda babu wanda ya isa ya aikata shi a wannan masarautar ko a tarihi,barin Mai martaba yasan da wannan maganar ƙwarai babban kuskure ne dan haka a kiyaye faruwan hakan,bana son magana biyu kuma bana son jin kuskure koda wasa"
Ta ƙarasa maganar tana sauke numfashi,Galadima ne ya numfasa yace.
"Babu wata matsala da zata faru maganarki kamar umarnine a wajena,daman yadda muka tsara abun nizan zama waliyin ita yarinyar yayinda kuma Waziri zai zama waliyin angon,sai kuma Chiroma da liman su zama shida akan hakan"
Wani murmushin gefen baki tayi ƙwarai taji daɗin abinda Galadima ya faɗa,kallon Waziri tayi taga yadda ya ɗauki abun sai dai ba taga komai ba,kasan cewar ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Waziri kam jin maganar yay daga sama tayaya zai karɓawa yaron da bai san darajarsa aure?tayaya zai zama waliyi ga yaron da baishi da ɗigon mutunci bare biyayya,shi kam harga Allah an shiga haƙƙinsa domin bashi da niyar hakan bare ra'ayi.
"kada lkc ya huce muje a fara gabatar da shirin ɗaurin auren,alrdy nakai katan ɗin alawa da kuma huhun goro"
Gaba ɗaya suka jinjina kai alamar gamsuwa kana suka miƙe tare da fice waje,Lil primce na fita Meyrah ta ƙarasu wajansa tare da fakar idanun jama'a ta rungomesa haɗi da jan marars,ƴar ƙara ya saki kaɗan tare da faɗin.
"kema yau zaki huta domin zan kasance matata kuma sabuwar hannu zan huta sosai abuna kuma na ƙwashi garata hankali ƙwance"
Dariya Meyrah tayi tace.
"Ohh idan ita sabuwar hannuce kai kuma fa?"
Dariya yay sosai sabida shikansa yasan yayi ta'asa wa ƴar ƴan mutane,tabbas da tarayyar da yake da ƴar ƴan mutame yana kaisu ga haihuwa da babu shakka zai tara yara sama da ashirin ko fiye da hakan.
Ganin yay shuru yana sakin murmushi ya sanya Meyrah faɗin.
"a dadisu bazai lissafuba ko?"
Ta faɗa cikin muryar raɗa,dariya yay kasan cewarsa mutum mai saurin dariya kana ya saki wani killer smile a saman fuskarsa yace.
"Only God know"
Kafaɗa ta ɗaga sama tare da warewa irin ko a jikinta ɗinan tace.
"whatever dai today you going to be groom finally kana da mai ɗauke maka buƙata tunka saika daina bin yaran mutane,nima kaga na huta na koma gidanmu"
"eh ƙwarai zaki tafi gida but not now,kisan inajin daɗin tarayya dake,batun na daina ɓata yaran mutane kuma sam bai tasu ba,wannan a jinin jikina yake kuma ya zama rayuwata,dukkan abinda aka haɗa da rayuwar mutum kinga ya zama jigon rayuwar gaba ɗaya kenan"
Prince ya faɗa yana gyara zaman alƙyabbar jikinsa tare dayin gaba,taɓe baki tayi haɗe da girgiza brest ɗinta wanda ya sanya yay saurin runtsa idanunsa sabida wani halbawa da mararsa tayi sanadin hakan da tayi,cikin muryar raɗa tace.
"God forbid"
Tana faɗin hakan ta juya zuwa sashin domin samun hutawa kafin ya dawo.
A can yankin Kogi.
A tashar garin motar ta tsaya mutane suka fara sauka,saida aka gama sauka bafa fito ba,muryar da taji a kanta ne ya sanyata buɗe manyan gajiyayyun idanunta wanda suke cike da gajiya,sakalcin,shagwaɓa,uwa uba kuma kewa.
Tana jin kamar ta rasa wani jigo na rayuwarta duk da kasan cewar bata da kowa a inda ta tsinci kanta,amma hakan baisa ta manta da garinba bare kuma masarautar.
Mutum ta zubawa idanun a zahiri su take tayi magana amma yadda laɓɓanta sukai mata nauyin gaske ya sanya dole tayi shuru ta hqr da faɗin abinda tayi niyar faɗa.
Santala-santalan ƙafafunta ta zura waje daga jikin motar kana ta gyara zaman mayafin jikinta,babban yatsanta ta tura cikin bakinta ta fara tsotsa.
Lumshe idanunta tayi sabida wani daɗi da kuma sanyi daya saukar mata a zuciya,tabbas komai daɗin waje bazai taɓa daɗin garinka kuma mahaifarka ba.
"Yarinya baki bada kuɗin motarki ba?"
Ɗan ware idanunta tayi tare da juyashi a saman fuskarsa,jiki a sanyaye ta zare hannunta daga baki cikin ƙaramar murya mai ɗauke da zallar shagwaɓa tace.
"ayya afuwan i almost forget"
Ta faɗa tana ciro rabin kuɗin hannunta ta bashi,amsa yay yana irgawa kansa ya ɗago ya kalleta yace.
"kuɗin sunyi yawa sosai ai"
Lumshe idanunta some minute ta waresu a kansa kana ta cije lips ɗinta tace.
"ka riƙe sabida darajar Allah,sannan kuma ka tayani da addu'a ubangiji ya bai yanamin abinda yake buɗe kana kuma ya biyan buƙata ta"
Murmushi yay cike da jin daɗi yace.
"Hajia wacce buƙatar naki domin nasan kalan addu'ar da zan maki?"
Ya faɗa yana washe bakinsa domin sosai yaji daɗin ƙyautar da tayi masa.
Girgiza kai tayi tace.
"Ubangiji ya sanya mafarkin Zarina ya zama gsky,idan ka faɗin hakan shima ya wadatar"
"insha Allah ubangiji ya shige maki gaba"
Murmushi kawai tayi domin taje gejin da bazata iya magana ba.
Kamar daga sama taji wata murya tana faɗin "little sis, little sis"
Da saurin ta juya ihu tayi tare daka tsalle sabida ganin Tupic da tayi.
A guje ta ƙwasa tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da ganƙamshe ta fashe da kukan murna.
Shikam Tupic zuwansa keman tasha karɓan sako wajan wani mutumi da Abba ya sashi ya karɓa.
Kamar a marki ya ganta mai tabbatar ba saida yaga ta juya yaga gefen fuskarta,shine ya girta domin ƙara tabbatarwa,sai gashi bisa mamakinsa ta amsa kiransa.
Rumgometa yay sosai a jikinta,tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi Allah ya sani su kaɗai suka san soyayyar da sukema tilon ƙanwar tasu.
Sosai yay murna ganinta jikinsa ya janye taki sakinsa sabida gani take yana matsawa kamar wani zai ƙara ɗauketa.
Da ƙyar yaja hannunta zuwa cikin mota sam yama manta da abinda ya kawoshi.
Cikin motar ya shiga bayan ya zaunar da ita shima ya zauna,revers yaywa motar kana ya jata da wani irin spend yabar wajan.
Yana zaune yana kallon gabans idanunsa a lumshe a wannan lkc shine kaɗai yasan abinda yake damunsa a zuciya.
Duk yadda yaso ya danne abinda yake damunsa ya gagara,sosai rauninsa keson fallasa asirin zuciyarsa.
Yana jin wata faɗuwar gaba da musamman wacce bai taɓa samun kanshi a cikinta ba.
Ƙwarai idanunsa na ƙwaɗai tuwa da son ganin ƙyaƙƙyar fuskarta da kuma surar jikinta,yana jin ɗumin jikinta a wannan karan yana son ya raɓeta ne matsayin mata bawai budurwa ba.
Tabbs hqrinsa ya fara gazawa ya tabbatar a koda yaushe zai iya samun matsala a mararsa zuwa cikinsa.
Ako wanne lkc kuma a ko wanne second da minutes baya hucewa saida tunaninta,amma a wannan karan kuma a wannan lkc tunanin yazu masa ba'a yadda ya saba yi ba,ya samu kansa ciki fargaba da kuma zullumin abinda zai fita ya tarar idan ta fita.
Bai taɓa farin ciki da zuwan wata huɗun nan ba,sai yanzu domin zuciyarsa nason gasgata masa cewa something bad gonna happen "ya rabba help me"
Ya faɗa yana lumshe idanunsa.
Turo ƙofar ɗan ɗakin akai wajan kusan mutane biyar ne suka shigo,kallo ɗaya yay masu ya ɗauke kansa.
"Captain Saifudeen now you are free"
Ɗaya daga cikin masu tsaron ƙofar ya faɗa yana mai yin baya wajan ƙofar sabida zafi da tiririn ɗakin daya daki fuskarsa.
Jaramta da kuzari ya aruowa kansa ya miƙe tsaye tare da sanya hannayensa duk biyun cikin aljihun wandonsa.
Cikin taƙama da kuzari haɗi da zallar izza wacce take bai yana cikar haibarsa da kuma tsarin halittarsa ya sanyo kansa waje tare da fitowa.
Lumshe idanunsa yay tare da fesar da wata zazzafar iska daga bakinsa,gyara tsaiwrsa yay tare da ware laɓɓansa yace.
"Allahamdulillah bi rahamatika Allahkulli halin"
Taɓe baki Lil prince yay cike da tsana yake bin Saifu da kallo yace.
"Ina maka murnar fitowa daga kurkuku,sannan ina mai tayaka baƙin cikin rashin abin ƙwanarka,nasan labarin dazan faɗa mai dai² yake da bugawar zuciyarka but i don care abinda nasu shi nake,kuma damuwar wani bata taɓa zama tawa,lallai kayi gangancin haɗa kishi dani,kayi wawtar sanya zuciyarka abinda nakeso,amma a wannan karan ka zama lozer baka da nasara nine mai nasara a koda yaushe,babban tagai cikina yadda ɗan talaka dakai zaka dinga haɗa inuwa da jinin sarautar wanda daga nan zuwa gobe ko jibi labarin zai sauya daga ɗan sarki zuwa Sarki,babban farin cikin kuma a ranar zan haɗa shimfiɗa da guda da sanyin idaniyar taka kuma..."
Saurin dagatar dashi Saifu ta hanyar ɗura hannunsa akan lips ɗinsa ya ɗan motsa laɓɓansa kaɗan yace.
"shiiiit pls,zama ɗan Sarki baya gabana,wannan kaiya shafa, and ƴan uwanka masu jinin sarauta zaka faɗawa ba Saifudeen Bilyam ba,then ka faɗi abinda kakeso faɗa ka cikani da magana akana faman tufan yawo"
Wani Fadane yay saurin dakawa Saifu tsawa tare da faɗin.
"ƙarya kake ɗan talakawa gyara bakinka Magaji mai jiran gado ne a gabanka"
Maimakon Saifu yaji tsawar da akai masa saima gyara tsaiwa yay tare da miƙa hannusa ga wani mutum yace.
"wayana?"
Da sauri mutumin ya miƙa masa wayoyinsa tare da key ɗin part ɗinsa.
Lumshe idanunsa yay ya fara tafiya cike da nutsawa yana tafe yana bada faɗin haɗi da buɗe faffaɗan ƙafaɗunsa.
Hannu ya sanya ya ɗan janye ƙaramin hannun rigarsa zuwa sama sabida wani zafi hannun yake masa,dalilin yawan ƙwanciyar da yake a ƙansa.
Tashi hankali kenan,da wani irin gigitacciyar murya prince yace.
"Wait ina ka samu guron masarautar bilhas har yake manne a jikin damtsen hannunka...
_THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE IF YOU NEED CONTACT ME 08119237616 200 NAIRA ONLY_
*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
THE NEW EMIR
BY
NIMCYLUV🤏🏼🔥
*63-64*
Gayamin inaka samu wannan gurun dake jikin hannunka..
Lil prince ya ƙara faɗa cike da tsantsar mamaki da kuma tunanin inda Saifu ya samu gurun.
Duk ihun da yake koda sau ɗaya Saifu bai ɗaga kai ba,bare ya saka ran zai jiyo ya kallesa harya amsa masa tambayarsa.
Cikik nutsuwa da kamalar data gama ratsa jikinsa yaci gaba da tafiya,duk inda ya keta barori da kuyangu ne suke ta faman kai kawo cikin harabar masarautar.
Cikin izza da taƙama yake taka sahunsa har zuwa ƙofar part ɗinsa,lumshe idanunsa yay tare da fesar da wani huci ta cikin bakinsa,a kasalance yasan key ɗin a jikin ƙofar ya buɗe tare da murɗa handle ɗin ƙofar ya tura kaɗan.
Idanunsa da suke a lumshe ya buɗesu tare da tura kansa cikin ƙaramin parlour'n da cikin ma dai² cin part ɗin.
A hankali yake juya ƙwayar idanunsa cikin parlour sosai yay mamakin ganinshi fess babu ƙura bare datti,direct ƙofar da zata kaishi bedroom ya nufa,yana zuwa ya juya wayoyinsa a charge kana ya sutale kayan jikinda tare da turasa lugun wardrope ɗin side ɗin datti clothes,saida ya rage daga shi sai bozer kana ya sanya kansa cikin bathroom sai ya tsina fuska yake,da alama ƙyanƙyamin jikinsa yake,yana shiga ya nufi jakuzzie ruwan zafi ya haɗa kana ya zuba bathparfume cikin ruwan wankan cikin sanyi jiki ya zare bozer ɗin jikinsa ta saƙale saman hanger.
Taune laɓɓansa yay sabida ƙartawar da cikinsa yake masa alamar jin yunwa,ƙyawawan ƙafunsa wanda suke ɗauke da zara-zaran gargasar jiki da sukai lub lub saman chocolate skin ɗinsa.
A cikin jakuzzie'n ya sauke ƙafafunsa tare da zama cikin jakuzzie'n lumshe idanunsa yay tare da fesar da numfashi kana ya soma sauke ajjiyar zuciya a jajjera,ƙara nutsewa yay cikin ruwan sabida daɗinsa daya keji,tattausan tafin hannunsa ya ɗura a saitin zuciyarsa wacce take bugawa da ƙarfin gaske,ƙwaɓe fuska yay tare da langwaɓar dakai gefe guda,sosai yake jin yanayin jikinsa na sauya zuwa bad mood ba tare daya san dalili ba,ware idanunsa yay tare da sanya hannunsa akan gurun hannunsa tare da murzawa kaɗan,sai yanzu maganganun Lil prince suke dawo masa ka.
"inaka samu gurun masarautar bilhas?"
Shine maganar data faɗu masa,ɗan tsaki yaja kaɗan tare da lumshe idanusa haɗi da ware cinyoyinsa ruwan yaci gaba da ratsa masa saman mararsa.
Shine ina yasan wata bilhas infact ma baisan shi kansa garin bilhas ɗin bai san dashi ba,haka bai taɓa zuwa cikinsa ba sai wannan karan,bashi da kowa cikinta mezai saka yasan da zamanta,rayuwarsa Cameroon kawai ya sani a nan ya tashi a nan yay wayo,a nan yasan kansa,maganar wani guru kuma su suka sani domin ko za'a ɗaura masa wuƙa a wuya bashi da tarihinsa da kuma dalili da yake a cikinsa.
Lumshe idanunsa ya ƙarayi tare da ƙara nutsewa cikin ruwan har saida rabin fuskarsa ya shige ciki ruwan zafin.
Taune laɓɓansa yay a hankali romantic mood ɗinsu ya shiga dawo masa cikin brain ɗinsa,duk da yanzu wajan wata huɗu da faruwar hakan amma yana ji tamkar yanzu abun yake faruwa,tsigar jikinsace ta soma mimmiƙewa wani sihirhirtaccen sanyi ya fara ratsa saman fatarsa zuwa cikin naman jikinsa.
Ƙara shigar da fuskarsa yay tare da shaƙar numfashi wanda ya haddasa tafiya da ruwan zafin cikin hancinsa,runtsa idanunsa yay da ƙarfi sabida wani zafi da raɗaɗi haɗi da yaji daya shigar masa har cikin ƙwaƙwalarsa,hakan kuma bai saka ya ɗago da kansa ba.
"A ranar zan haɗa shimfiɗa da sanyin idaniyarka"
Shin hakan na nufin zaiyi rayuwar auratayya da ita ne ko mene? Ko kuma haka na nufin zai aikata mata ta ƙarfin tsiya ne? No! Hakan bazai taɓa faruwar ba,ƙwarai da yaga wannan ranar gwamma yaga ranar mutuwarsa,babu wani ɗa namijin daya isa ya shigar gonar da yake sakaran zata zama mallakinsa harya bata yabanya kuma ta fidda ƴar ƴar harda iri.
Sosai maganar Prince tayi ta siri cikin zuciyar Saifu hakan ya haddasa masa wani ƙunci da kuma baƙin ciki a ransa.
Wani damuwa ne ya shiga cikin zuciyarsa,hakan ya sanya yaji ƙansa na sara masa tamƙar zai rabe gida biyu.
Sannu a hankali ruwan zafin ya fara shigewa cikin hancinsa sabida yadda fuskarsa ta nutse a cikin ruwan jakizzie ɗin.
A hankali idanunsa suka fara lumshewa yayinda gangar jikinsa ya saki gaba ɗaya, idanunsa sukai sama hakan ya sanya tsaiwar numfashinsa..
da idanu lil Prince ya bishi duk yadda yasu ya danne abinda ke damunsa kasawa yay, zaman alƙyabbarsa ya gyara tare da fara tafiya cike da izzarsa ta ƴar ƴan sarakai,domin kallo guda zaka masa kasan jinin sarauta na yawo a jikinsa.
zuciyarsa fal tunanin yadda akai wannan gurun yazu wajan Saifu har yake manne