Showing 1 words to 3000 words out of 20315 words
Chapter 1 - BEELAL BUK BOOK 2 COMPLETE BY MAMAN AFRAH.txt
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦💦
*FCW* 💛
Book 2
Page1️⃣➡️2️⃣
*LAGOS*
Tun da suka sauka a garin Lagos a tasha, Idrisu ke tsangwamar Beelal saboda wai ba ya sauri kwata-kwata bai duba larurar da ke tare da yaron ba, ta nakasarar, da ke tare da shi ba, haka kawai yake jan hannunsa ƙiii suna keta mutanen da ke cikin tashar motar da aka saukesu. Babu wani wanda ya lura da su kowa sabgar gabansa yake, Beelal kwa banda hawaye babu abin da ke zarya a fuskarsa ga wata azababbiyar yunwa da yake ji. Sai da ya samu machine suka hau Beelal ɗin ne ya fara hawa sai shi ma ya hau bayansa haka suka zo unguwar da Idrisu ke zaune. A ƙofar wani shago da ke wurin aka ajiyesu ya fitar da kuɗin mai machine ɗin ya biya.
" Kai gurgun mage ka ga inda nake kwana dan haka ba wai a kyauta nake zaune a ciki ba biya nake dan komai da kake gani a Lagos na kuɗi ne ba kamar can gida bane inda muka baro fa, a can ne wani ma zai iya bada kyautar shago dan kawai mutane su zauna a sadaka wasu har gida suna iya bawa mutane su zauna kyauta" Cewar Idrisu yana yiwa Beelal wani kallo.
"To Baba zan ...
"Ko da wasa kar in ƙara jin ka kirani da wannan sunan dan ni tuni na daɗe da barwa uwarka Fatima kai, dan haka zamu zauna ne a nan a matsayin masu taimakon juna idan ka taimakawa kan ka ka nemo kuɗi yadda ya kamata to zaka samu abinci idan kuma baka nemo ba to ka kwana da sanin da yunwa za kake zama"
Hawaye sun riga buɗewar bakin Beelal zubowa, saboda ganin irin rayuwar da zai gudanar mai cike da uƙuba a birnin Lagos, an rabo shi da wajen mahaifiyarsa mai so da ƙaunarsa wacce duk runtsi duk wuya sai ta nemo masa abin da zai ci ko da a ce ita ɗin ba za ta samu ta ci ba to ta gwammace ta samo masa idan ya ci sai ta yi farinciki. An kawo shi inda bai san kowa ba sai wanda ya kawo shi wanda ke ƙyamatarsa ba ya ko ƙaunar ya kira shi da sunan mahaifi saboda nakasar da Allah ya halicce shi da ita.
"Za kake nemowar kuwa? Duk da wasu na cewa wai zafin nema baya kawo samu, to ni dai na ƙaryata haka, sai dai in mutum bai dage ba, dan da ya dage dole ya nemo, sannan ka bar zubo min da wannan hawayen munafurcin dan taimakon ka na yi kar kasa wasu su zargi satoka na yi, to shin ma
in ba barar ba menene ya dace da mutum irinka, mai irin suffarka, mai ɗauke da nakasa kamar kai" Ya faɗa yana hararar Beelal.
Hannu ya sanya ya goge hawayen duk da ba wai kukan nasa ya tsaya bane, kai kawai ya sunkuyar yana jin ba daɗi har cikin rai da zuciyarsa, dan baya so ake kiransa da nakasashshe duk da yana ɗauke da nakasa in aka faɗa masa dan a muzanta masa sosai yake muzanta, sosai yake jin babu daɗi a cikin ransa dan yana gani kamar mutane na ganin shi ya yi kansa a haka suna manta cewar Allah ke halittar mutum a yadda ya so a kuma lokacin da ya so.
"Wuce mu je ai dai ka ji abin da na ce in kuma ka ƙi to jiki magayi, dan ni idan ma baka kula ba ko a jikina wai an tsikari kakkausa" Cewar Idrisu yana yin gaba ya nufi shagon, cikin sanyin jiki Beelal ya bi bayansa tunanin mahaifiyarsa cike da zuciyarsa yana tuna irin tsantsar kulawarta garesa dan duk abin da uwa take yiwa yaro yana nan zaune daram da ƙwaƙwalwarsa in ma mai kyau ko akasin haka, Allah ba mu ikon tarbiyantar da ƴaƴanmu kamar yadda ya ɗora mana nauyin hakan amin .Suna zuwa Idrisu ya tura ƙofar da take a kare.
"Wane ɗan iskan ne zai turo ƙofa babu neman izini" Aka faɗi hakan daga cikin shagon tare da ɗura wani zagi mai gunna.
"Kai dalla can ni ne, kar ni ma ka harzuƙa ni yanzun nan mu hau sama mu faɗo" Shi ma Idrisun ya faɗa yana lailayo nasa ashar ɗin, tare da bankaɗe labulen shagon ya shige ko sallama babu.
"A ah shegen ashe kai ne" Cewar Imran da ke ringishe a kan katifa yana zuƙar sigari.
"Dallah can wai har ni kake yiwa wani eya ne" Cewar Idrisu yana miƙa wa Imran hannu ya bashi sigarin da yake zuƙa shi ma ya kai bakinsa sai da ya mata zuƙa biyu ya fesar sannan ya zauna a gefen katifar.
"Ai na ɗauka wani ne, da ban zai kawo min raini"
"Kai dai ka sani to ya ake ciki ne"
"Kai dai bari Baaba wallahi al'amura duk sun caɓe babu wata hanyar samun kuɗi yanzu, ni machine ɗin ma da nake ja na mayarwa mai shi saboda sai in wuni ina yawo amma ba na samun fasinja wai sai a yi ta cewa a buge nake" Cewar Imran yana kallon Idrisu.
"Da gaskiyar su ai"
"Au haka ma za ka ce"
"To ai kai ɗin ne ya za a yi ka shayu ka yi tatul kuma ka ce wai za ka samu fasinja, tsakani da Allah waye zai yarda ya hau bayan bugagge wataƙila ma duk kana warin sholi"
"Dalla can rufe mana baki, ai duk kanwar dai ja ce daga ni har kai waye gwara, kai ma warin sholishon ai ko jikinka ba ya bari" Cewar Imran yana kai wa Idrisu wani uban duka a baya.
"Kai maida wuƙar Malam na zo mana da hanyar samun kuɗi yanzu cikin sauƙi, duk da dai dama ba wai ba ma sakun kuɗin ba kawai dai suna ƙarewa ne a wajen siyan kayan maye da neman matan banza, amma dai yanzu ga wata haja da nake ganin za mu buɗe...
"Kai rufa ni ka saya ni wallahi duk iskancina bai kai nan ba" Imran ya katse Idrisu yana wani harararsa.
"Kamar ya? Kai fa matsala gareka, ai ka bari na mutu ma kafin ka binne ni"
"Haba Idrisu daga tafiya gida wajen bushashshiyar matarka ko za ka samo mana kuɗaɗen da kake zato yayarta ta kai mata, kuma kawai sai ka saro mana hodar iblis ka ce mu buɗe haja, son kulawa su yi ram da mu, azo ana A'i ina indo"
Wata irin dariya Idrisu ya ƙyalƙyale da ita, yana nuna Imran da yatsa.
"Ka fi kowa sanin ba na son rainin hankali"
"Ai Baaba dole na yi dariya daga ambaton haja sai ka ce hodar iblis ce bari ka ga hajar da nake nufi, mai lasisi ce, kuma hajar mai jini ce" Cewar Idrisu yana buɗe murya ya shiga ƙwalawa Beelal kira da ya daka ta a ƙofar shagon bai shiga ba amma yana jiyo duk surutan su.
"Kai gurgun mage, gurgun mage!!" Ya shiga ƙwala masa kira kamar wani makaho.
"Na'am" Cewar Beelal ya shiga share hawayen fuskarsa. Sannan ya ja ƙafarsa marar lafiyar ya tunkari shagon gabansa na dukan tara-tara.
"Gurgun mage kuma waye ka samu haka ko shi ne ka baiwa ajiyar hajar tamu da kake ta faɗa" Cewar Imran yana son jin amsar sa daga wajen Idrisu.
"Assakamu alaikum" Cewar Beelal daga ƙofar shagon amma ko labulen bai ɗaga ba yana jiran sai ana amsa sallamar tasa an bashi izinin shiga sannan ya shiga, kamar yadda Mamarsa ta koya masa.
"Kai ba zaka shigo ba" Idrisu ya faɗa yana kwararo wani uban ashariya.
Labulen ya buɗe a hankali ya miƙa ƙafarsa cikin shago ransa cike da tsoro fal dan gabaɗaya ma sai ya ji yana matuƙar tsoron su.
"Kai amma kai dai Allah wadaranka Idrisu, ya za ka kirawo mana almajiri bayan ka san mu kan mu muna da buƙatar abinci"
"Kai dalla sakarai ni ne kake cewa Allah wadaraina, to sai dai Allah wadaranmu baki ɗaya saboda suk kanwar ja ce, to wannan da kake gani tun daga arewa na taho da shi kuma shi ne hajar da nake baka labari yanzu"
"Kana da hankali kwa Idrisu wannan abin ne haja? Ko dai ka samu taɓi ne bayan barinka garin nan"
"Na manta kan ka na kwakwa ne, gabaɗaya ya zama dusa ba ya ja ko kaɗan to bari na maka gwari-gwari, wannan ɗan gidan wannan matar ne wacce take zaune da sunan wai tana aurena, to yadda ka ganshin nan a haka ta haifeshi shi yasa na sallama mata shi, duk da ma ba wai na san ɗawainiyarsa daga shi har ita bane, sai dai wannan zuwan na yi tunani zai mana mugun amfani a garin nan shi yasa ma na sato shi ba tare da ta sani ba na taho da shi"
"Ikon Allah na zaune ya faɗi, kai yanzu wannan in banda dai wahala mai ka ɗakko mana yaro hannu a ƙame ƙafa a shantale to ma uban me wannan zai mana" Imran ya faɗa yana aikawa Beelal da mugun kallo dan shi gabaɗaya ma kallo ɗaya ya yiwa yaron ya ji ya tsane shi, ganinsa ma yake kamar aljani.
"Maida wuƙar tukunna in faɗa maka manufata a taƙaice, daɗina da kai baka cin ribar zance, to wannan yaron na ɗakko shi ne dan yake bara yana samo mana abubuwan da muke buƙata, kama daga abinci kuɗi da dai sauransu" Idrisu ya faɗa yana wani murmushi tare da wani karkaɗa kai na jin daɗi.
"Shegen ina yinka nawan wallahi ai kai fa kan ka na ja ba kamar nawan ba amma in jika, gaskiya ka mana babban kamun da za mu daɗe muna mora tabbas wannan duk inda ya shiga zai samo sadaka, baka ma ganin yadda tsofaffi wanda ma basu da nakasa suke samo sadaka irin waɗan da ke zuwa neman kuɗi daga arewa da sunan bara, ka ga tsohuwa ta takarkare tana zabga waƙar bara ƴar jagora tana mata amshi kuma fa ita ba gurguwa ba, ba makauniya ba babu wani ɓangare na jikinta da yake a nakashe amma kuma sai ta maida hakan hanyar samun kuɗi, kuma wallahi sosai suke samun kuɗi, ka gansu idan suka tashi tafiya gida arewa sun koma da maƙudan kuɗin da ba lallai ne wanda suka zo nan ɗin da sunan neman kuɗi ba su samu ko da rabin hakan ne"
Imran ya kai ƙarshen maganar yana kallon Idrisu.
" Kai ai sai yanzu nake jin mugun daɗi da na taho da yaron nan, dan na san tsuntsunmu zai kama tarko"
"Sosai ma kuwa"
"Kai gurgun mage ƙaraso ka zo nan" Idrisu ya faɗa yana kallon Beelal da ya takure daga wajen ƙofa ya ƙi shigowa cikin shagon.
Haka ya janyo ƙafarsa ya ƙaraso wurinsu, ga ɗakin ban da warim sigari baka jin komai.
"Kai idan za ka saki jikinka ka saki jiki, dan nan fa shi ne garin da za ka cigaba da rayuwa a cikinsa, idan kuma ba haka ba za mu ladabtar da kai ta ƙarfi da yaji" Imran ya faɗa yana yiwa Beelal wani kallo na tsana da tsangwama.
Beelal dai kansa a sunkuye yana durƙushe a gabansu.
"Ka ɗago ka bamu amsa mu ba ma son wannan munfurcin sadda kan irin na uwaka" Idrisu ya faɗa cikin ɓacin rai.
"Zan yi Bab...
"Ba?" Cewar Idrisu yana kallon Beelal da mamaki, dan ya san dai ɗazun nan ya gargaɗesa a kan kiransa da suna Baba .
"Gaskiya da sake abokina ya ma za a yi wannan abin yake kiranka da Baba son ya ja ake kallon mu ai wannan abin kunya ne wallahi" Cewar Imran
"Ni ban san ya zan ke kiranka ba, ba zan iya faɗar sunanka ba" Cewar Beelal yana hawaye ganin duk sun tsare shi da ido.
"To haɗi garemu dan ka kirani da sunana ni fa na faɗa maka na janye dukkan alaƙa d dangantakar tsakani na da kai" Cewar Idrisu.
"Kawai yake ce maka Alhaji, ko da wani ya ji ya kiraka da hakan zai ɗauka taimakonsa yake kuma wannan suna ne mai ɗaga daraja kawai yake kiranka da haka" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu.
"Amma na ji daɗi da ka samo min wannan suna to kuwa ba ni kaɗai zai ke faɗawa ba kai ma haka zai ke kiranka" Cewar Idrisu yana murmushi.
"Kai tanƙwashen kifi faɗi mu ji, dan yadda ƙafa da hannun nan naka suka sha kwana sai suka min kama da kifi tanƙwashe" Imran ya ce yana kallon Beelal.
"Alhaji" Cewar Beelal ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa.
Hahahahaha gabaɗaya suka ƙyalƙyale da wata irin dariya kamar mahaukata sabon kamu.
MMN AFRAH 09030283375
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦
NA
MAMAN AFRAH
Book 2
*FCW*💛
Page3️⃣➡️4️⃣
"Yanzu ka san me za a yi abokina?" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu.
"Sai ka faɗa"
"Ka san akwai keken guragu a cikin wancan rufeffen shagon na wannan gurgun da suke zaune a cikin shagon da ya mutu, sauran ma suka fasa hayar shagon to tun da ba wai so ake ba shi za mu ɗakko shi wannan sai yake hawa"
"Kamar ya yake hawa, bayan yana tafiya gani nake duk inda zai je kafin ya je a keken ya je a ƙafa, kuma ma so kake ka sauƙaƙa masa tafiyar ya zama yana yin barar yana samowa a ɓagas ba zai san zafin nema ba kenan? Ai gwara dai yake yawo da ƙafafunsa duk da dai ba wata tafiyar kirki yake ba sai ka je wuri sau goma ka dawo ka tarar da shi yana hanya bai je ba"
"Haba ka gane mana ba wai dan ya samu hutu za a bashi keken ba ka san yanzu idan aka ganshi zaune a keken kuma hannu da ƙafa a lanƙwashe za a ɗauka gurgu ne a haka sai ya fi samun sadaka, a kan a ce da ƙafarsa aka ganshi"
"Shege Baaba wallahi kwanyarka na ja amma a wajen son samu fa" Idrisu ya faɗa yana baiwa Imran hannu suka kashe.
"Wallahi nake faɗa maka ko kaɗan ni ma kawai jin maganar na yi ta sauka a kwanya ta ba tare da dogon nazari ko tunani ba na ce bari dai na faɗa maka tun da dai na san ai ni da kai bata ɓaci"
"Ai tuni ma an gama yanzu je ka fito masa da keken ya hau ya fara fita tun yanzu ka san da zafi-zafi a kan daki ƙarfe"
"Kai Idrisu wutar cikin naka ta yi yawa yanzu daga zuwanku kake cewa ya tafi bara ko hutawa baku yi ba kuma bai samu komai ya ci ba, kuma ma na ɗauka sai an ɗan nuna masa wajejen zuwa tun da ba inda ya sani kar ya je ya ɓata a shiga tara" Imran ya faɗa yana kallon Idrisu.
"Kai ka jika da wani zance, to me ma za a bashi ya ci ai sai ya nemo mu ma za mu ci, kuma da kake cewa daga zuwanmu, zai fara fita to ma wai shin mai za a fasa mutuwa ko hisabi? Kuma zancen ɓata a shiga tara ai ko uku ba za mu shiga ba dan ya ɓata Allah raka taki gona gaba ta kaini gobarar titi na huta da yiwa gyatumarsa bayanin dalilin da ya sa na tafi da duk da dama ba wai tsoronta nake ba, shi idan ya ɓata sai na nuna ba ni ne na tafi da shi ba"
"Ni fa ba wai rasa shi ne tarar da za mu shiga ba, to in dai zai ke samo mana kuma a rasa shi dole mu shiga tara tun da haryar samu ta toshe mana"
" Kuma fa haka ne, amma yanzu idan ya hau keken mu za muke tafiya yana bin mu a baya sai mu kai shi inda za a fi samun sadaka muna daga gefe a tsaye kamar ba tare muje d shi ba idan muka ga ya tara mana abin da muke so sai mu dawo" Idris ya faɗa yana dariya. Shi dai Beelal yana nan durƙushe bai ce komai ba kansa sunkuye a ƙasa yana sauraren duk abin da suke cewa.
"Bari na ɗakko masa keken" Imran ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Zan yi a hakan ba sai da keken ba" Beelal ya faɗa cikin in'innarsa.
"Kai dalla rufewa mutane baki, kai har wani zaɓi ne da kai, wato kai ma duk a yadda kaken nan a nakashe ta ko ina har kana ƙyamatar hawa keken guragu dan kar a kiraka gurgu ko?" Idrisu ya faɗa yana hararar Beelal da kansa ke sunkuye.
"Ba haka bane Alhaji, ni da a ce ma bani da nakasa ba na jin zan ƙyamaci kowane irin halittar Allah kawai dai tun da Allah ya mini ni'imar samun ƙafa ina tafiya bai kamata in hau keken guragu ba, in ɓata ni'imar da Allah ya mini ta ƙafafu bayan ni ba gurgu bane saboda kawai in samu abin duniya sai na butulcewa baiwa da ni'imar da Allah ya mini" Ya faɗa cikin in'innarsa yana ɗago kansa a karo na farko ya sanya idanunsa cikin idanun Imran.
Wani uban haushi ne ya turnuƙe Imran cikin zafin nama ya ɗaga hannu ya kaiwa fuskar Beelal wani gigitaccen mari, Beelal ma cikin sauri ya duƙar da kansa ƙasa, Imran ya mari iska, ganin iska ya mara bai samu fuskar Beelal ba daga Imran har Idrisu suka tsaya kallon -kallo da mamaki.
"Kai har ni ka ɗaukewa kai na mari iska" Cewar Imran cikin ɓacin rai.
"Ni ma mamakin da ya kasa barin raina kenan" Idrisu ya faɗa cikin mamaki.
"Ai ban yi laifin da za a mare ni ba" Beelal ya faɗa cikin in'innarsa.
"Lallai ma yaron nan, kai da kake a ƙarƙashinmu sai yadda muka yi da kai kana garin da baka da kowa baka da uwa ba uba babu dangin iya bare na Baba amma har kana da ƙarfin gwiwar butulcewa umarni ko tsallake abin da muka yi niyyar yi?" Imran ya faɗa yana wani zare idanu.
"Bani da kowa amma ina da Allah, shi ke tare da bayinsa daɗi ko wuya, shi