Showing 12001 words to 15000 words out of 20315 words

Chapter 5 - BEELAL BUK BOOK 2 COMPLETE BY MAMAN AFRAH.txt

tambayarmu sai kai, to babu damuwa Allah mana maganin matsalarmu" Cewar Fatima cikin kuka duk wanda ya ganta a halin da take ciki yanzu sai ya tausaya mata.

Mutane har sun fara taruwa, juyawa Fatima ta yi ta kalli Babangida idanunta cike da hawaye ta ce.

"Tada machine ɗin mu tafi Babangida" Ta faɗa tana sanya bayan hannunta ta goge hawayenta, shi ma Babangidan bashi da ta cewa dan gabaɗaya tausayin Fatima da ma Beelal ɗin baki ɗaya ya cika masa zuciya, haka ya tada mashine ɗin ta hau ya ja suka tafi, shi kuma abokin Idrisu ya bisu da ido jikinsa sanyi ƙalaw dan kalamin Fatima sun gama kashe masa jiki.



Tun da suka ɗau hanya babu wanda ya yi magana daga Fatimar har Babangidan, sai dai Fatima tun da suka fara tafiya hawaye ya kasa ƙauracewa idanunta, saboda kawai ganin abin take tamkar almara, wai yau Beelal ɗinta ne bai kwana a gida ba abin takaici ma wai Idrisu ne ya ɗauke mata shi ya tafi da shi Lagos, wannan abin idan ta tuna shi yake sa ranta yake ƙuna. Ji take da a ce tana da dama da tuni ta zama tsuntsuwa ta bi bayansu, tana ta saƙar jakin nan ta saƙa ta warware a hakan har suka shigo garinsu, har ƙofar gida Babangida ya kai ta, yana ta faman bata haƙuri ita dai kai kawai take iya ɗaga masa dan hawaye sun ƙi yankewa idanunta, ji take har ƙwara a ce da mutuwa Beelal ɗin ya yi ake bata haƙuri da sauƙi tun da dama kowa ya san mutuwa dole ce, amma yanzu kuma yana raye bata san halin da yake ciki ba wannan abu yana matuƙar sanya zuciyarta damuwa.


Fakyar ta iya yiwa Babangida godiya ta juya ta shige gida, dan mutane har sun fara taruwa masu son jin ƙwaƙwaf suna tambayar Babangida ba a samo Beelal ɗin ba, bayan da lokacin yana nan babu wanda ya damu da su.Fatima kuwa ta san tana buɗe baki kuka zai ƙwace mata dan yanzu ma burinta kawai ta gan ta a cikin gida.

Tun da ta shigo cikin gidan idanunta suka sauka a kan kayan Beelal na wanki wanda ta wanke masa jiya da yamma, tana kallonsu wata shuɗiyar riga da shi da kansa ya shanya rigar yana ta cewa take bashi shi ma yana wankin, ta ce sai dai suke shanya tare saboda hannunsa marar lafiyar har yana cewa idan ya ƙara girma zai ke yin wankin take ce masa.

"Haba Beelal ai duk girmanka ni zan ke maka wanki saboda larurar da ke tare da kai, idan kuma Allah ya hore mini sai in ke biya ana wanke maka idan ka yi aure dan kar a ɗorawa matarka wahala dan ba kowace mace ce za ta ɗau ɗawainiyar wanki ba bare matan yanzu da basa son wahala su ma so suke a hidimta musu"

"Ni ba wani aure da zan yi Mama a gida zan zauna muke zaman mu tare da ke, ni fa a duniya kwata-kwata ba na son rabuwa da ke sai sai in mutuwa ce kaɗai za ta raba mu ita ma dan dole ce" Wannan kalaman nasa na jiya suna faɗo mata sai kuwa wani kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata ganin gashi ma ashe kwana ɗaya ya rage musu jiyan raba tsakaninsu duk da kasancewarsu masoya na haƙiƙa amma rashin imani da tsoron Allah ya sanya Idrisu ya raba su, idanunta ta sauke a kan katifar da Idrisu ya kwanta a kanta jiya wacce ke a waje ɗaure da net ɗin da ta sanya masa wani haushi da takaici ta ji a lokaci da ta kalli katifar kuka ne ya ƙwace mata. Hannu ta sanya ta toshe bakinta da kukan ke fitowa ɗaki ta nufa da ɗan gudu-gudu, tana shiga ɗakin ta faɗa kan katifar ta a ribda cike ta kwanta tare da kifa fuskarta a kan tafukan hannayenta ta saki wani kuka mai ƙarfi wanda yake fitowa da ɓacin rai haɗe da zunzurutun kewar ɗanta tilo Beelal, tana jin zafin da zuciyarta take mata, tausayin yaronta yana daɗa ninkuwa a ranta tana tunanin irin rayuwar da zai yi a wani waje da babu ita babu wani wanda ya sani sai Idrisu mutumin da ba ya ƙaunarsa kuma yanzun ma ta tabbata ba ƙaunar ce ta sanya ya ɗauke yaron ba, illa wani ƙudiri nasa marar kyau da Allah ne kaɗai ya sani, tausayin Beelal na ƙara shigewa zuciyarta tana tunani ya zai ke aiwatar da abubuwan da ba ya iya wa sai dai ita ta masa saboda NAKASAR da ke tare da shi.


Sai da ta yi kuka mai isarta, aikuwa idanun suka sake suntumewa, amma bata damu da hakan ba, cikin sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi ta ɗauki abu ta goge fuskarta tas, da hanzari ta tashi domin duba wayarta wacce Hajiya Laɗifa ta turowa wani mai pos da ya tura mata acc no sa ta turo kuɗi aka sake mata wayar ko sati biyu bata yi ba, fatan ta dai Allah sa Idrisu bai ɗauke wayar ba, wurin da ta ajiye wayar ta je ta duba cikin ikon ALLAH sai ta ga wayar tana nan, dan dama ta siyar da tsohuwar, hannunta har karkarwa yake da ta ɗakko wayar dan ta tabbata idan har da ya ɗauke wayar shikenan ya datse mata abin da ta saƙa a ranta yanzun nan. Wayar ta kunna ta kamo sunan Yayarta har ya kira kafin kiran ya shiga sai ta katse saboda tana ganin Hajiya Laɗifa idan ta ji abin da take shirin yi za ta iya dakatar da ita dan haka sai ta fsa kiranta, buɗe wayar ta yi ta fitar da sim ɗin ta karya shi, cikin hanzari ta tashi kamar an tsikareta ta fito da sauri, takalmanta ta saka ta nufi hanyar ƙofar gida.


Shagon siyar da wayoyi ta nufa, kawai jefa ƙafarta take kamar wanda ake hankaɗata, tana zuwa kuwa ta yi sa'a a buɗe, ta sanar da mai shagon wayar take son siyarwa ganin wayar kamar ma yanzu aka buɗeta a kwalinta ya shiga son jin dalilin siyar da wayar dan dai ya fara tunanin ko dai wayar ce take da matsala dan a zahiri dai babu wasu alamu da suka nuna haka. Faɗa masa ta yi amfani take son yi da kuɗin, nan ya sayi wayar dubu 25 wayar da dubu 35 aka siya haja ta siyar masa dan ita bata da lokaci ko nutsuwar da za fa yi ciniki ko jayayya da shi. Kuɗinta ya bata ta kamo hanyar gida, tana shigowa ta ɗauki ƙaramar pos ɗinta ta sanya kuɗin wani hoton kati na Beelal ta ɗakko ta tsaya kallon hoton cike da alhinin nisa da ya yi da ita, hoton lokacin Beelal yana tsayuwa aka ɗaukeshi, ƙafar nan marar lafiya ta karkace ya ɗaga hannunsa mai lafiyar sama yana dariya, tunowa da shekaran jiya tana gyaran ɗaki ta ɗakko hoton Beelal da ke game a wayarta ya dakata ya karɓi hoton yana dariya ya ce cikin in'innarsa.

"Mama kamar ba ni ba a nan kin ga na girma" Ya faɗa yana dariya.

"Eh mana ai kowa ma da haka ya girma, wata rana ma magidanci za ka zama" Ta faɗa tana dariya.

"Mama ki bani hoton in ajiye shi a wurina"

"Ai wannan hoton babu wanda zan baiwa nawa ne sai dia idan ka girma zan sa a wanka maka shi, sai kaima ka ajiye, amma dai wannan nawa ne, duk inda ka gan shi to ni ce na kaishi wurin dan babu wanda zan iya bawa sai dai in mutuwa na yi" Maganar da suka yi da Beelal shekaran jiya a kan hoton ta faɗo mata, kafin ta ankare sai ganin ɗigon hawayenta ta yi a jikin hoton cikin sauri ta goge hawayen daga jikin hoton ta sanya a cikin jakar.


Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakin kallo yana rayawa a ranta cewar sai kuma in rai ya kai, dan ita dai ta san a ƙudurin da ta yi babu gudu ba ja da baya.Ƙwaɗo ta ɗakko da mukullan ta kulle ɗakin, tana fitowa waje ma ta rufe ƙofar gidan. Shagon mai caji ta nufa wanda suke waya wani lokacin da Hajiya Laɗifa a wayarsa idan Hajiyar ta kira wayar Fatima ta ji a kashe, saƙo ta bashi a kan cewa idan Hajiyar ta kira ya ce mata ta tafi Lagos. Mai machine ta samu ta ce ya kaita Kazaure, a tasha ya sauketa ta biyashi haƙƙinsa motar Kano ta hau suka ɗau hanya. Wajen sha ɗaya da rabi suka ido cikin Kano.

"Allah sarki Yayata ki yi haƙuri da abin da zan aikata na san ba za ki ji daɗi ba, sai dai hakan shi ne mafita kuma shi ne kwanciyad hankalina dan matsawar na zauna a nan ban tafi neman Beelal ba to tabbas rayuwata za ta ƙare ne a ƙunci! Ki yafe mini yau gani a cikin garin Kano amma ba wai dan in je gidanki in kai miki ziyara ba sai dan kawai hanya ce ta kawo ni, ki min afuwa Yaya!" Cewar Fatima a zuciyarta tana share hawaye, dan shigowar motarsu garin Kano ya ƙara tada mata mikin abin da ke damunta a cikin ranta. A ƴan kaba aka saukesu, ɗan sahu ta samu ta ce dan Allah ya kai ta inda za ta samu motar da za ta kaita Lagos, har wurin ya kaita ta bashi haƙƙinsa ta samu wuri ta zauna dan ba ma lokacin motar za ta tashi ba.

Sai wajen ƙarfe uku motarsu ta tashi, amma duk zaman Fatima a wurin ko ruwa bata sanya a bakinta ba sallah kawai ta gabatar, ko yanzu ma da suke tafiya kanta kawai ta jingina idanunta a rufe tana jin yadda mutane ke ta hira a motar amma ita ko abin da suke cewa bata sani ba damuwar da ke tattare ita ta wargaza mata komai, dan rashin Beelal a kusa da ita ba ƙaramin abu bane.


MMN AFARAH 09030283375



❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*BEELAL*

💦💦💦💦💦💦


NA



MAMAN AFARAH


*FCW*💛

Book 2

Page 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣

*HAMEEDA*


Tana ƙoƙarin buɗe baki ta yi magana Musty ya aika mata da wata uwar hararar da ta sanya ta kama bakinta ta yi shiru. Hajiya Zulaiha kallon Mustyn ta yi ganin sai wani kumbura baki yake yana ƙunƙune sai ta ce

"Hameeda maza jeki uzurinki"

"To" Haeeda ta faɗa cike da ladabi ta tashi ta bar falon.

"Haba Mom wai ya kike min haka ne, a gaban wannan ƙaramar yarinyar kina son ta rainani ne?"

"Oh wato ka san ma ƙarama ce yarinyar da bata fi 7yrs ba kai kana kusan 19yrs amma kamsr wata sa'arka kawai daga shigowarta sai kake neman dukanta kuma na san halinka babu wani laifi da ta maka"

"Ko ma ta mini laifi ko bata mini ba ai dai bakya fifita ƴar aiki a kan ɗan gida ba ko"


"Sannu masu gida" Cewar Hajiya tana kallonsa.

Alhaji Tahir ne ya shigo da sallama. Amsa masa Hajiyar ta yi shi kuma Musty ya ce

"Oyoyo Dad"

"Wato baka san ma na dawo gidan ba, daga masallaci fa nake yanzu kana can yawonka na dawo ba yanzu na dawo ba"

"Haba Dad yawo kuma ai ina can wajen friends ɗina"

"Ohk hakan ma ya yi kyau"

Kallonsu kawai Hajiya ta yi ta ɗauke kai abinta ta yi wajen dinning ɗin, su ma bin bayanta suka yi Dad ne ya jawa Musty kujera ya zauna sai shi ma ya zauna Mom ta shiga zuzzuba musu abinci. Sai da suka kammala cin abincin nasu sannan suka dawo falon suka cigaba da hira abinsu.


*BAYAN SATI BIYU*


Da la'asar sakaliya ne Musty ya shigo gidan da moyarsa bayan mai gadi ya wangale masa get, yana yin parking ya buɗe mptar ya fito hannunsa riƙe da leda, hango Hameeda ya yi tana shanya wasu dosters da ta yi goge -goge shi ne ta wanke su take shanyawa.

Tun daga nesa yake kallonta da yake ta bashi baya ne, bata ma san yana yi ba. Wajen ya ƙarewa kallo sai da ya tabbatar ba kowa ya a kusa ya ƙarasa wajenta.

"Ke!" Ya faɗa ƙasa-ƙasa. Da sauri Hameeda ta waiwayo dan kwata-kwata bata san da zuwansa wajen ba dan haka maganar da ya mata sai ta ɗan razana.

"Ungo nan wuce ki kai min part ɗina ki ajiye mini a falo a kan kujera" Ya faɗa yana miƙa mata baƙar ledar da ke hannunsa. Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ɗan ja da baya ganin ya zo dab da ita ita dama kuma tsoronsa take.

"Wuce ki tafi kuma ki yi sauri kin wani miƙo hannu kina ja baya kamar wanda kika ga dodo" Ya faɗa yana miƙa mata ledar. Karɓa ta yi tare da cewa

"To" Ta faɗa muryarta har rawa take, haka ta wuce ta nufi ɓangaren nasa duk da bata taɓa ko da bin hanyar ba ma, dan ita bata son duk wani abu da zai haɗa ta da Musty dan ta lura da take-takensa ba ya ƙaunar ko da ganinta ne.


Tun da ta karɓi ledar ta kama hanyar part ɗin nasa sai sauri take zubawa da yake da ɗan tazara tsakanin part ɗin da sauran ɓangarorin. Tun da ta juya ta tafi ya shiga waige-waige irin na marar gaskiya wanda ko cikin ruwa gumi yake. Sai da ya tabbatar babu kowa a wajen kuma babu wanda ya ganshi ya kama hanya bi bayanta.


Sauri take yi dan so take kawai ta je ta ajiye ta fito masa daga ɓangarensa dan ma kar ya je ya ga wani abu ba dai dai ba ya ce ita ce ta ɓata masa. Da yake wani corridor ne a farko idan ka shiga dan haka kafin ta kai falon sai da ta wuce shi, tana shiga falon ta ajiye ledar a kan kujera kamar yadda ya buƙata, cikin sauri ta juyo za ta fita sai kawai ta ji ta yi karo da mutum, da sauri ta ɗago kanta aikuwa ta sauke su a kan fuskar Musty yana wani washe haƙora tare da shafa haɓarsa da hannun damarsa na hagun ɗin kuma ya kama ƙugu da shi.

"Ka yi haƙuri dan ALLAH ban lura da kai ba" Cewar Hameeda cikin sanyin murya. Jin bai ce mata komai ba sai wani kallonta yake hakan ya sanya ta ɗan raɓa shi za ta wuce, aikuwa ya miƙa hannu ya kamo hijabin da ke jikinta, Hameeda da ke tafiya sai ji ta yi an janyo da ita baya ƙiii an dawo da ita ta hanyar janyo hijabinta.

Sai da ya dawo da ita gabansa sannan ya kafe ta da ido kamar yau ya fara ganinta, Hameeda kuwa duk da bata san manufarsa ba sai ta ji tsoro ya mamaye ta, a take sai jikinta ya ɗauki karkarwa dan ita duk tunaninta ma dukanta zai yi ko wani laifi ta yi a shigowarta falon yanzu.


"Dan, dan Allah ka yi haƙuri Ya Musty" Ta faɗa cike da tsoro.

"Haba baby mai kyau laifin me kika yi da kike bani haƙuri in ma laifin ne ni ne nan zan miki shi yanzu, dan na san laifin da zan miki yanzu wataƙila ba za ki taɓa yafe mini ba domin laifi ne da zai ruguza rayuwarki gabaɗaya, laifi ne da zai shafi kowane fanni da kowane ɓangare na rayuwarki wataƙila ma ki kasa yin farinciki har abada!" Ya faɗa yana wani lashe baki kamar tsohon maye. Hameeda kuwa bata san ina kalamansa suka dosa ba sai dai kawai ta tsorata sosai burinta kawai ya sakar mata hijabinta ta fice daga ɓangarensa.

"Duk abin da zan miki idan kika sake kika mini kuka ko ihu sai na yanka ki, kuma ij saka ki a buhu in fita da ke in jifa a kwata ba tare da kowa ya sani ba amma idan kika yi shiru baki yi kuka ko ihu ba ana ɗan jimawa zan ce ki tafiyarki har da alawa zan baki" Ya faɗa yana kallon Hameeda da gabaɗaya kan kallonta ka san a mugun tsorace take kamar ka ce kulle ta ce cass.

"Kin ji abin da na ce ai ko?" Ya faɗa yana zare mata ido. Kanta ta shiga ɗagawa alamar ta ji. Sakin hijabin nata ya yi, wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Hameeda har sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, dan duk tunaninta ya barta ta tafi ne, tun da bata yi iju ko kuka ba, tana shirin ɗaga ƙafafunta sai kawai ta ji an yi sama da ita, an ɗaga ta kafin ta tantance sai ganinta ta yi a kafaɗar Musty ya nufi hanyar bedroom ɗinsa da ita, baki ta buɗe za ta yi ihu tunowa da ta yi ya ce idan ta yi ihu ko kuka sai ya yanka ta hajan ya sanya ta sanya hannayenta biyu da toshe bakinta.

Yana shiga bedroom ɗin ya nufi kan lafiyayyen gadonsa ya ajiyeta ya koma ya maida ƙofar ya rufe har da sanya mukulli. Hameeda kuwa gabaɗaya jikinta rawa yake dan duk tunaninta ma yankatan zai yi, yana gama rufe ƙofar ya juyo ya fara tahowa wajenta yana washe haƙora hannunsa a kan wandonsa yana cire belt ɗinsa, sai da ya cire belt ɗin ya yi wurgi da ita a tsakar ɗakin, ya cire wandonsa daga shi zai gajeran wando, rigarma ya cire ya wurgar hatta singlet ɗinsa bai bari ba. Gadon ya nufo gadan-gadan Hameeda kuwa ganinshi tuɓe daga shi sai gajeran wando ta sanya hannu ta rufe idanunta bakinta kuwa haɗeshi ta yi ta damƙe dan kar kuka ya fito a yankata.Yana zuwa ya sanya hannu ya fisge hijabin jikinta ya yi wurgi da shi da yake doguwar riga ce a jikinta sai ya shiga kiciniyar rabata da ita, hannu biyu ta sanya ta daddage ƙarfinta ta riƙe rigar dan duk da ƙaracin shekarunta dan a lokacin shekararta shida da wani abu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login