Showing 3001 words to 6000 words out of 20315 words
Chapter 2 - BEELAL BUK BOOK 2 COMPLETE BY MAMAN AFRAH.txt
ne wanda baya gajiya da buƙatun bayinsa, shi ne yake bayarwa ya ƙara kuma yana tare da duk wanda bai manta da shi ba" Beelal ya faɗa hawaye na kwaranyo masa saboda gabaɗaya abin da yake faɗa daga ƙwalƙwalwarsa yake tahowa domin gabaɗaya kalaman Mamarsa ne wanda take faɗa mas suke zama daram a ƙwalƙwakwarsa.
"Lallai gurgun mage ka ga makwancinmu wato har kai ma kana iya musayar yawu damu, a haka bakinka babu daɗi kana magana da in'inna har kana rufe idanu saboda in'innar amma a hakan kake faɗar ra'ayinka"
Cewar Idrisu da mamaki fal a fuskarsa. Shi dai Beelal bai ƙara cewa komai ba.
"Rabu da shi abokina da mu yake zancen, keke ne dai ko ba ya so sai ya hau dan shi da gurgun ni ban ga maraba ba" Imran ya faɗa yana fitowa daga shagon domin ɗakko keken a ɗaya rufaffen shagon.
"Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri ka ce kar ya ɗakko keken nan, ya kamata ɗan adam ya zama mai godiya ga ubangajinsa a duk yadda Allah ya haliccesa, Allah ya bani ƙafafu bai kamata nake yawo a keken da duk wanda ya ganni zai yi zaton bani da ƙafa ni gurgu ne, kuma in har a ƙafartawa ma nake iya rabona kawai zan samu a barar babu wanda zai haɗa min da rabon wani...
"Kai dalla ka rufewa mutane baki waye sa'anka a cikinmu? Ko dan ka ga ana ɗaga maka ƙafa, to bari ka ji na faɗa maka kai baka isa ka sa mu yi abin da bamu yi niyya ba, sai shegen surutun tsiya, ga wa'azi kamar wani limami, kai ga wanda mahaifiyarka ke koya maka sanin Allah da sanin ya kamata" Idrisu ya katse shi cikin ɗaga murya.
Shiru Beelal ya yi dan yadda Idrisu ya masa magana ya tsorata saboda da ƙarfi ya zafice shi dan haka sai ya ja bakinsa ya yi shiru.
"Baaba na ɗakko keken nan fito ka gani, ko a san a bin yi ka san maganin abu a yi shi" Imran da ke can waje ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Haka Idrisu ya fito daga cikin shagon yana washe baki, ya baro Beelal a can ciki.
"Kai gaskiya abokina ka iya bada shawara to ka ga wannan da babu shi ma sai mun nemo amma tun da gurgu ya bar wa ɗan uwansa gurgun mage gado ka ga mun huta da nema" Idrisu ya faɗa yana kallon tsohoh keken guragun da ya ya tsufa jikinsa duk tsatsa.
"Eh mana, ai mu gaba ta kaimu gobarar titi, kai kana ina fito dalla ka zauna a ciki kamar wanda kake ganin dodanni" Imran ya faɗa yana kiran Beelal da bai fito daga shagon ba.
"Ka fito da rarrafe saboda tsaro ba dan tsoro ba, dan yanzu idan ka fito da ƙafarka wani ɗan sa ido ya gani sai a gama gane lagonmu" Idrisu ya faɗa yana kallon shagon nasu yana jiran fitowar Beelal.
A hankali Beelal ya sanya hannu ya share hawayensa, ya yi dibara ya miƙe ya tahowarsa a ƙafarsa ba tare da ya rarrafo ba kamar yadda aka buƙata.
Ganinsa ya fito a tsaye sai Imran ya tafi da sauri ya je bayan Beelal ya sanya hannu ya hankaɗo Beelal, aikuwa Beelal ya tafi tagal -tagal sai kuwa ya faɗa a kan gwiwoyinsa aikuwa ya ji faɗuwar sosai wani zafi ya ziyarci gwiwoyinsa.
"Ka min dai dai ai maganin marar kunya da rashin jin magama kenan" Idrisu ya faɗa yana kallon Imran.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya haka" Cewar Aminullah da ya ƙaraso wajen cikin sauri dan tun lokacin da ya shawo kwana ya hango Imran ya hankaɗa wani yaro da ya fito daga cikin shagonsu hakan ya sanya ya ƙaraso da sauri.
"Kai ba fa da kai ake yi ba mu ba ma son shishigi da shiga shiri ba shanu" Idrisu ya faɗa yana hararar Aminullah. Aminulla kuwa ganin abin da suka yi da gangan ne sai kawai ya nufi wurin Beelal cikin tausayawa musamman ma da ya lura da larurar da ke tattare da yaron sai ya ji wani mugun tausayinsa ya mamaye masa zuciya. Cikin sauri da azama ya sanya hannu ya ɗaga yaron tsaye yana masa sannu tare da dudduba jikin Beelal ɗin dan ganin ko ya ji ciwo. Dan shi Aminullah duk tunaninsa ma yaron bara yake suka masa wannan wulaƙancin.
"Kai fa wannan zaƙiyar da kake yiwa mutane, da shiga shirgin da ba naka ba, ba ka ji ba an ce mutum ya bar abin da babu ruwansa ba, amma kai kullum cikin kutsa kai cikin abin da bai shafe ka ba kake" Imran ya faɗa yana hararar Aminullah da ke riƙe da Beelal.
"Ko ma dai me zaku faɗa ku faɗa amma dai abin da kuka yi baku kyauta ba in sadakar ce ba za ku bashi ba sai ku ce ya tafi amma ba wai ku masa wannan kora da halin ba" Aminullah ya faɗa shi ma yana kafe su da ido.
"To kai an faɗa maka kowa ma irinka ne, ko kuma an ce maka bara yake, to wannan da kake gani tun daga arewa na taho da shi kudu saboda yake bara yana samo mini kuɗi, dan haka babu ruwanka ka sake shi ya zo ya hau kekensa" Idrisu ya faɗa yana kallon Aminullah.
Baki sake Aminulla yake kallonsu yana rayawa a ransa wace uwa ce wanann marar dogon tunani za ta baiwa mutum kamar Idrisu yaro kamar wannan da sunan a zo da shi ya yi bara, Idrisu da ko ciwon kansa bai sani ba ta yaya har haka za ta faru.
"Sake shi to tunda ka ji kanun labaran sai ka kiyaye shiga abin da baka ciki wanda babu ruwanka" Imran ya ce yana wani ɗaga kai sama.
"Amma duk da kun ce ba ruwana ya za a yi ku ɗakko wannan tsohon keken ku ce ya hau bayan kuma keken ya riga da tsufa duk ya yi tsatsa, bayan ma yana da ƙafarsa ya za a yi ya hau keken guragu" Aminullah ya faɗa yana kallon fuskar Beelal cike da tausayawa dan ya san ba da son ran yaron ba.
Da sauri Imran ya sanya hannu ya fisgi Beelal daga hannun Aminullah yana aikawa Aminullah ɗin wata harara tare da Beelal ɗin.
"Ka rainawa mutane hankali har ka tsaya ja in ja damu, shin ma ina ruwanka da mu ne? Menene alaƙarmu da kai, ko muna da wani haɗi ne da kai bayan na addinin muslunci, da kuma haɗin kama hayar shago ɗaya? Dan haka ka fita idanunmu mu rufe in har kana son zama lafiya"
MMN AFRAH 09030283375
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦
NA
MAMAN AFRAH
Book 2
*FCW*💛
Page 5️⃣➡️6️⃣
Aminullah yana ji yana gani Imran ya kama Beelal ɗin ƙiii ko tsayawa babu, har sai da ya dangana shi da kan ƙarfen keken, dan wurin zaman ko katifa babu ta cire sai ƙarfen kawai, yana zaunar shi tare da yiwa Beelal ɗin mugun kallo.
"Tuƙa mu tafi" Idrisu ya faɗa cikin zafin rai, su duka daga Imran ɗin har Idrisun sai muzurai suke kamar waɗanda suka yiwa sarki ƙarya.
"Ban iya ba wallahi ko taɓa hawa ban yi ba" Beelal ya faɗa kamar zai fashe da kuka.
"Banda rainin wayo ya ma za a yi ka ce wai baka iya tuƙa kekenku na nakasassu ba, ai sabo da ku aka ƙeroshi dan haka yanzu ya zama dole ka tuƙa ko baka so" Cewar Imran yana kallon Beelal.
"Bari dai ka ga ƙarshen rainin wayo dan ya ɓata mana lokaci ne yasa yake ja mana rai" Cewar Idrisu yana fisgar keken da uban ƙarfi suka fara tafiya, Imran na bin bayansu, Aminullah da ke shirin yin magana ganin sun ja keken sai ya saki baki yake bin su da kallo, yana ɗaga hannu kamar mai neman taimako.
"Ku bishi a hankali dan Allah" Cewar Aminullah cikin ɗaga murya amma ko sauraronsa ba su yi ba.
Beelal kuwa hannu biyu ya sanya ya riƙe wajen tuƙin ganin irin gudun gangancin da Idrisu yake yi da keken ƙura sai tashi take. Sai da suka ɗan yi tafiya mai ɗan tazara Idrisu ya saki keken ba tare da ya tsayar da keken ba, da sauri Beelal ya sauke ƙafarsa mai lafiyar ya taka ƙasa hakan sai ya zamana kamar ya taka birki ne, dan yadda Idrisu ya saki keken da ƙarfi kaɗan ya rage Beelal ya hantsila daga shi har keken.
"Kai ka fara tuƙawa da kan ka ka ga mun baro waccan lungun da shagonmu yake mun fito cikin jama'a tun daga nan har zuwa ko ina ma na unguwar nan kasuwa ce dan haka yanzu za ka fara tuƙawa ka yi gaba mu kuma mu biyo ka a baya kuma kar ka nuna ma ka san mu, duk da ba lallai wani ya hango jirginmu ba, kuma ba lallai wani ya lura cewa mun sanka ba saboda babu yadda za a yi wani ya kalleka ya haɗamu da kai" Cewar Idrisu yana hararar Beelal.
"Ka ga duk wannan faɗin wajen duk wurin ma kasuwa ce amma kar ka shiga can ciki ka je ka ɓata kake bararka a iya nan, ungo nan, duk wani abu na ci kake sakawa a nan kafin a samo maka robar da za kake sakawa, kuɗi kuma kake sakawa a acikin aljihunka idan sun taru muna gefe za mu karɓa sai ka cigaba da barato wani" Imran ya faɗa yana miƙa masa wata ledar yaluwa mai sarsar da ya fito da ita a aljihunsa.
"To" Cewar Beelal yana haɗa hannayensa wuri ɗaya ya sanya hannun biyu ya karɓi ledar, dan Mamarsa ta koya masa cewa ba a karɓar abu da hannun hagu ko kuma a karɓa da hannu ɗaya sai dai duk abin da mutum zai karɓa ya sanya hannu biyu tare da ɗan rusunawa saboda hakan shi ne cikar tarbiya.
"Ka taimaki kan ka" Idrisu ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa dan har ya hango sun fara samun kuɗi.
"Me zan ke cewa barar, mai zan ke faɗa idan ina barar" Cewar Beelal cikin sanyin murya.
"Ka ji wani rainin wayo kuma yanzu kai abin da kuke faɗa ne baka sani ba, ai a gani na nakasashshe babu wanda zai koya masa yadda zai yi bara tun da dan ita aka halicceshi a nakashe"
Cewar Imran yana wani yatsina fuska.
"Allah ya haliccemu ne dan mu bauta masa kuma Allah ya hore min rai da lafiya da sassan jiki dai dai gwargwadon yadda zan nemi ilimi in nemi halal ɗin ba wai in yi bara ba, Allah ba ya son roƙo ma"
"Inyeee to wallahi wannan darasin sai dai ko ka bari sai ranar da ka koma gun wacce ta koya maka wato mahaifiyarka ka faɗa mata hakan idan da rabon zaku sake haɗuwa ma kenan, idan kuna da rabon sake sanya juna a idanu dan mu wannan karatun mun daɗe da saninsa" Idrisu ya faɗa yana hankaɗa keken da Beelal ɗin ke ka.
Daddagewa Beelal ya yi ya riƙe kan keken, ya cije leɓensa na ƙasa da haƙorinsa, ya shiga ƙoƙarin tuƙa keken cikin iko da hikimar ubangiji sai gashi ya tuƙa keken.
"Ɗan rainin wayo ashe ma ya iya ya sa kake wahalar turashi" Cewar Imran.
"Rabu da shi mana in ma bai iya ba da ya ji uwar bari ai ya tuƙa dole ne ai ya nemo mana abin da aka kawo shi takanas domin ya yi wato bara" Idrisu ya faɗa yana dariya idanunsa na hango Beelal na jan keken dakyar.
"Hahahaha ai dole ne a sha man amarya ko da taƙi" Imran ya faɗa.
*ƘAUYEN MAZARI*
~FATIMA~
Cikin bacci ta fara jiyo ana kiran sallar asuba, dan haka a hankali ta buɗe idanunta tana yamutsa fuska alamar mai bacci. Hannu ta kai gefenta domin taɓo Beelal sai ta ji baya nan, hakan ya sanya ta ɗauka ko ya gangara gefe guda ne da yake har lokacin akwai sauran duhu haske bai riga da ya fara fitowa ba.
Hannu ta kai inda take ajiye fitilar ta touchlight ta ɗauko, kunnawa ta yi ta haska amma abin mamaki haske na gauraye ɗakib sai ta ga wayam babu Beelal a inda yake kwance, bata kawo komai a ranta ba hakan ya sanya ta yi zaton ko fitsari ya fita duk da ta yi mamakin fitarsa fitsarin ba tare da ya tasheta ta raka shi ba ko kuma ya karɓi fitila ba.
Sai kawai ta danganta hakan da kawaici da sanin ya kamata irin na Beelal ta tabbata wataƙila dan ya ga tana bacci ya ƙi tashin ta ya gwammace ya fita fitsarin a duhu. Sai lokacin ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci (Alhamdulillahil lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaihin nushur) Sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin ganin shimfiɗar Idrisu ba ya kwance sai ta yi mamaki kar dai tashi ya yi dan zuwa ya yi jam'i a masallaci mutumin da ko kaɗan ibada bata dame shi ba shi dama jam'i ma ba zuwa yake ba a gida yake sallarsa shi ma ba a kan lokacin ba. Hamdala ta shiga yi tana ganin dama kwana biyun nan da ya yi da dawo wa ya canja mata gabaɗaya ba kamar yadda ta saba ganinshi ba, ashe dai canjin har na ibada. Addu'a ta shiga yi a kan Allah ya ƙara shiryar da shi ya gane gaskiya ya daina zaluntarsu ita da Beelal. Tun tana tsaye tana jiran fitowar Beelal daga bayi har dai ta fara haska fitilar daga inda take tana haska bayin tana karkaɗa fitilar tare da kiran sunan Beelal ɗin dan yanzu ta fara danganta shiga bayin nasa da kashi, dan tana ganin jimawar tashi ta zarce fitsari.
"Beelal ka kula ka fito mana mu yi sallar kar lokaci ya ƙure, kuma ma ka je ka shiga bayi babu fitila ai da ka tashe ni na baka fitilar" Ta faɗa da ɗan ƙarfi yadda zai ji. Jin shiru sai kawai ta ɗan ji gabanta ya faɗi amma bata kawo komai a ranta ba. Takalmi ta sanya ta nufi bayin cikin ɗaurewar kai dan ta san dai Beelal ko gyaran murya da ya mata, amma kuma shirun da ta ji sai ta fara tunani ko dai zamewa ya yi a bayin ya faɗi, wannan tunanin sai ya sanya gabanta mummunan bugawa a nan take sai ta ƙara sauri dan zuwa ta ga mai ke wakana. Addu'ar shiga bayi ta ( Allahumma inni a'uzu bika minal kubisi wal kaba'isi) Da mugun sauri ta afka bayin abin da ya ƙara sanya gabanta faɗuwa ganin bayin wayam babu alamar wani bil adama a ciki. Idanu ta zaro tana ƙwala kiran sunan Beelal ɗin tare da ƙara haske bayin wai ko idanunta ne basu gani dai dai ba amma sai ta ƙara gani babu ma wata alamar an shiga bayin, dan ko ɗigon ruwa ma babu.
"To ko dai Beelal da Babansa suka tafi masallacin?" Wani ɓangare na zuciyarta ya jefa mata tambayar.
"To kuma indai tare suka tafi masallaci to a ina suka yi alwala, tun da dai babu alamar ruwa ma ya taɓa bayin sannan ga butoci nan a cike kamar yadda na ajiye" Ta sake baiwa kanta amsa.
"Amma kuma Baban Beelal ba ya son ko kaɗan Beelal ya raɓe shi to ta yaya zai tafi da shi masallaci?"
"Kika sani ko ya canja ra'ayi, tun da dao kin ga tun da ya dawo ya sakar da fuska ba kamar da ba, kuma kika sani ko a masallacin za su yi alwalar" Wata zuciyar ta raya mata hakan. Wata ajiyar zuciya ta sauke jin wannan tunanin sai ta ɗan ji hankalinta ya kwanta.
A haka ta daure ta yi tsarki ta gabatar da alwala duk da ba wai hankalinta ya kwanta bane dan ta san Idrisu ko kaɗan ba ya ƙaunar Beelal in dai ba ra'a yi ya canja ba duk da cewa wanda ya ce ba ya yi da kai to kuwa ba ya yi da kai ɗin ne har abada, duk wanda ya ce ba ya ƙaunarka to ba ya ƙaunarka ɗin ko da ya dawo daga baya ya ce yana sonka to tabbas ba lallai ya kasance so na gaskiya ba so na haƙiƙa ba. Shi yasa ma manzo S.A.W ya ce idan za ka so mutum to kada ka zurfafa son sa domin wata rana zai iya zama maƙiyinka idan za ka ƙi mutum kar ka zurfafa ƙinsa domin shi ma zai iya zama masoyinka. Allah haɗamu da ma su son mu da gaskiya amin.
A haka ta gabatar da salla tare da yin addu'o in ta kamar yadda ta saba, bayan ta gama sai ta shiga gabatar da azkar ɗin safiya, tana yi amma kuma tana jiran jin shigowar su Beelal, a haka har gari ya yi haske tangararai amma babu wanda ya shigo, so take ta tashi ta fita amma kuma bata so ta yi laifi a wajen Idrisu haka ya sanya ta ƙara daurewa. Zuwa can ta ji haƙurinta ya ƙare ba za ta iya cigaba da zama ba tare da ta ga Beelal ba dan haka cikin sauri ta fito daga ɗakin gabanta na dukan uku-uku dan ta san dai matsawar masallaci suka je da Idrisu kuma suka tsaya a masallacin ko kuma a wani wajen to tabbas ba za ta fita b a wajen Idrisu duk da yana mata ɗan faram-faram sai ya mata masifa amma haka ta daure dan ta san dai duk abin da zai mata nafila ne a kan halin da take jin zuciyarta tana ciki yanzu.
Tana fitowa ta ga ƙofar gidan a buɗe, haka ta shiga duba sawun amma abin mamaki sai take ta ganin sawun Idrisu babu na Beelal, sannan tun da ta fito daga gidan sai ta ga sawun Idrisu bai bi hanyar da masallaci yake ba, a hankali take bin sawun cikin faɗuwar gaba dan tabbas sai yanzu take