Showing 15001 words to 18000 words out of 21816 words
Chapter 6 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt
yi musu murmushi har suka ƙoshi, sun ci sosai, saboda canjin test ɗin abinci da suka samu, ba irin wanda Yusra ta saba dafawa ba, ta ba su ruwa suka sha, sannan ta ɗakko jakarsu ta taya su home work, suna gamawa ta saka musu unifom ɗin islamiyya ta ɗakko alawowi ta ba su, ta zauna tana musu tatsuniya, har lokacin makaranta ya yi, da yake babu nida da yaran maƙota suke tafiya, ta ce daga yau ita za ta dinga raka su, sai da ta sake gyara fuskarta sannan ta ɗauki abincin babansu suka tafi, ta kai su makarantar ta ƙarasa shagon, wannan karon a buɗe yake, ta tsaya a gefe har mutum biyu da suke ciki suka gama, sannan ta ƙarasa da murmushi ta gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa, ta miƙa masa abincin ta ce"Ga shi, ka yi haƙuri na kawo a makare, tun kafin sha biyu na kawo maka, sai na tarar shagon a rufe, na jira wajan minti goma sha biyar sannan na koma saboda su Afna kar su dawo babu kowa".
"Ok, na je kasuwa ne" Ya faɗa bayan ya gama jinta.
Har ta juya ta tafi ta dawo ta ce"Kenan kullum daidai wancen lokacin kana kasuwa?"
Ya ce"Ba kullum ba".
Ta ce"Me zai hana ka ba ni lambarka, idan zan zo sai na dinga tambayarka ko kana nan, ko kuma ranar da ba ka nan ka kira ni ka faɗa min ko?"
Ya ɗan yi jimm, sai kuma ya ga tana da gaskiya, hakan zai fi mata sauƙi, ya miƙa mata wayarsa ta saka lambar, tana ce masa"Kursum, na san ka manta sunan" Ta ƙarasa da shegen murmushi.
Tana fita ya yi saving lambar, sannan ya ɗakko abincin ya fara ci, cokali ɗaya ya yi, ya ji girkinta ya bambanta da na Yusra, ɗanɗanon ba ɗaya ba ne, sai ya bar shi a kowa da irin hannunsa, amma abincin ya yi masa daɗi, ya cinye tass ya sha ruwa.
Kursum ba ta jima da komawa ba Yusra ta dawo, dama ta wanke fuskarta kafin ta dawo, kuma ta ƙara wanke-wanke ta gyara gidan tsaf har da turaren wuta, Yusra ta ji daɗin yadda ta tarar da gidanta, a ranar farko har ta fara jin daɗin ɗaukar ƴar aiki, yanzu da tuni yadda ta dawo a gajiyen nan aikin gida za ta hau da girki, yanzu kuwa Kursum na tafiya abinci ta zubo ta ci, ta yi wanka ta kwanta ta huta, sai la'asar ta tashi don tafiya kemis.
A shagon shi ta tsaya ta shiga da sallama murmushi ɗauke a fuskarta, ya yi mata murmushin shi ma yana amsawa "Kin dawo?" Ya tambaye ta.
Ta ce"Ga ni kuwa, ta kawo maka abinci ko?"
Ya gyaɗa mata kai.
Ta ce"Na ga alamar za mu shirya da yarinyar, ba ta da son jiki, har da kayan yara ta wanke, gida fess".
'Kuma ta iya girki' Ya faɗa a zuciyarsa. A fili kuma ya ce"Madallah! Kemis za ki je?"
Ta ce"E, zan ɗan leƙa, Nura yana can, da wuri ma zan dawo na yi maka tuwo".
"To na gode, sai na dawo" Ya faɗa yana ta kallonta, har ta tafi.
Ana kiran sallar magriba ta koma gida sai da ta ɗakko yaran a maƙota suka shiga tare, ta ɗora tuwo ta yi alwala suna idar da sallah suka fara bata labarin Anti Kursum, kamar yadda ta ce musu sunanta hakan, ta ji daɗi sosai da yaran suka saki jiki da Kursum ɗin, har ta kira Sumayya ta ba ta labari ta sake yi mata godiya sosai, Sumayya ta ce "Babu komai, ai yi wa kai ne"
GIDAN HARUNA
Sosai Haruna ya yi mamakin yadda Zainab ta ƙware, ashe karuwar gida ce zaune, duk da babu wani gyara a jikinta amma salonta ya gigita shi, da ƙyar ya bari ta koma ɗakinsu, don roƙonta ya dinga yi ta kwana a nan ɗin, ta ce ba zai yiwu ba, Baaba tana farkawa fitsarin dare, haka ya kwana ransa fess shi bai ƙi Halima ta yi wata ɗaya a gida ba ma.
Washegari da safe Halima ta kira shi suka gaisa sai ya ji bai kyauta ba, don tun da ya kai ta gidan bai kira ta ba, ya ce"Ki yi haƙuri Halima wayata ce babu kati, shi yasa ban kira ki ba, ya jikin naki?".
Ta ce"Babu komai, jiki Alhamdulillah, yanzu za mu je asibiti da Umma".
Ya ce"To Allah Ya ƙara afuwa, da daddare zan zo, Allah Ya sa dai na samu abin da zan siya miki wani abun".
Ta ce"Amin, idan ba ka samu ba ma ka zo, zuwan naka ya fi muhimmanci fiye da abin da za ka kawo, ka ga idan ba ka zo ba Umma ba za ta ji daɗi ba".
Ya ce"Zan zo in sha Allah! Na gode Halima Allah Ya ƙara miki lafiya, gaskiya zan yi kewarki kafin ki dawo".
Ta yi murmushi ta ce"In sha Allah ba zan fi kwana uku ba ai".
Gabansa ya faɗi, shi da yake fatan ta yi wata ɗaya sai ga shi tana zancen kwana uku? Ya ce"Haba Halima lafiyarki tana da muhimmanci a gare ni, saboda haka ki zauna ki warware sosai, babu komai zan jure kewarki".
Ta ce"To, sai dai yadda ta yiwu".
Da daddare da ya dawo daga kasuwa, ya sayi lemo, kankana, madara, milo ƴan saches, suga biredi da maltina ya haɗa da dubu biyu ya kai mata, bayan sun gaisa ta ce"Ga shi ba ni da lambar Zainab ballantana na ji ko tana fita a abincin nata?"
Cikin suɓutar baki ya ce"Ai ina da lambarta".
Da mamaki ta ce"Lambar Zainab ɗin? Yaushe ka karɓa?"
Sai yanzu ya san kwaɓar da ya yi, nan take ya fara in'inar da bai san yana da ita ba.
LITTAFIN WANI AUREN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 300 KACAL!
2526907490
Aisha Abdulrazaƙ
Zenith bank
KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015
KO KATIN MTN NA 300 ƳAN NIGER ZA KU TURO 300F AIRTEL
[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
FIRST CLASS WRITERS
PAGE 7
Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅
Ya ce"Na yi zaton Salma kika ce ƙanwarki, ban ji sosai ba". Ba ta kawo komai ba a ranta, suka yi sallama ya tafi.
A ranar ma haka Zainab ta je ɗakinsa suka ƙara haɗuwa. Sanda ta kwana uku a gida Baaba ta ce masa ya yi musu kwatance za su je gidan, sai ya kwatanta musu ya kuma ba su lambarta, suka je suka duba ta, Baaba ce take cewa Umman Halima"Tun da jikin nata da sauƙi ai dama komawa ta yi, kin ga Zainab babu abin da ba za ta yi mata ba, ni kuma zan dinga saka ido akanta".
Umma ta ce"Gaskiya ne, mun gode Baaba, to in sha Allah ko gobe sai ta koma, ai jikin nata da sauƙi kam, aman ma ya tsaya".
Sun ɗan jima suna fira sannan suka tafi, takaici kamar ya kashe Zainab ganin Baaba ta dage sai Halima ta dawo sai kace ita take aurenta, suna hanya ta ce"Wai ni Baaba me yasa kika damu sai ta koma? Ko mijinta bai damu ba sai ke?"
Baaba ta ce"Kar ki ishe ni da shirmen banza da na wofi, shi mijin nata ne ya faɗa miki bai damu ba?" Daga haka aka yi shiru da zancen, har suka ƙarasa gida Zainab ranta a ɓace.
Ranar ce masa ta yi ba za ta je ɗakinsa ba ma, tun da har ya yarda Halima ta dawo bai damu da ita ba, gara ta yi zamanta, ya dinga rarrashinta ta ƙi sauraronsa.
GIDAN ALI
Sai da ya yi kwana uku bai je gidan Hajiya ba, duk yadda take kiransa kuwa, saboda ba ya so su sake samun matsala da Maryam kwana kusa, yanzu ana yin sallar magriba yake dawowa gida, kwana uku bai yi zaman majalisarsu ba, sai dai a ganin Maryam an gudu ne ba a tsira ba, tun da kullum sai Hamza ya biyo shi gidan, su zauna a ƙofar gida sai su kai ƙarfe tara, ganin an jera kwana uku a haka ya sa ta fara yi masa ƙorafi, ta ce gaskiya Hamza ya daina zuwa yana hanata fira da mijinta, Ali ya ce shi dai mutum ba zai zo wurinsa ba ya kore shi, watarana Hamza ya zo, Maryam ta tashi ta tare hanya tana haɗe gira, da mamaki Ali ya ce"Maryam mene ne hakan? Ba ni hanya don Allah"
Ta ce"Babu inda za ka fita, ka faɗa masa kana buƙatar ganawa da matarka shi ma ya tafi wurin tasa matar".
Ali ya ce"To ai shi yanzi ya saki matarsa, shiyasa idan ya koma gida da wuri sai daren ya yi masa tsayi, kuma kin ga nine dai abokin, dole wurina zai zo, na ga nan a ƙofar gida ne kina leƙowa ma za ki ganmu".
Ta ce"Idan na ganku zan jiyo irin huɗubar da yake yi maka ne? Wato ya saki matarsa kai ma yana yi maka huɗubar ka saki taka ku zama ɗaya ko?"
Ali ya ce"Subhanallah! Haba Maryam wannan wace irin magana ce?"
Ta ce"To ni dai ban amince da wannan sabuwar majalisar ba, saboda haka ka faɗa masa ya daina zuwa ba ka so!".
Ali ya ce"Wallahi ba zan iya korar shi ba".
Ta ce"To wannan abokin naka ya zama kishiyata, saboda haka daga yau ka fara raba mana kwana, ranar kwanana ana magriba ka dawo gida, ranar kwanan shi ana magriba za ka dawo ka tarar da tabarma a ƙofar gida, don ba zan iya ba!".
Cikin takaici Ali ya ce"Wai me yasa kike haka ne? Gabaɗaya kin kanainaye ni, sai ka ce ke ce mijin, na faɗa miki shi kaɗai ne a gidan shi ya saki..."
"Ya je ya hau sallaya ya fuskanci alƙibla!" Ta katse shi har da ɗaga murya.
Ya juya zai fita, ta ruƙo rigarsa ta dawo da shi, ya ce"Maryam wai mene haka?"
Ta ce"Da gaske fa nake wallahi, ka bari ni na je na same shi na faɗa masa ina buƙatar mijina a kusa da ni".
Ganin ta shiga ta ɗaki ta ɗakko hijjabi Ali ya ce"Bari na je na faɗa masa". Ya fita, bai jima ba ya dawo yana ɓata rai, har lokacin tana tsaye da hijjabin a hannu, ya ce"To ga ni sai ki kwaɗa ki cinye.
Ta yi dariya ta ce"Ni da ana kwaɗon ma ai da tuni na cinyeka na huta da matsalolin da kake tara mini".
Daga haka suka shiga ɗaki, har ta kunna kallo ya kashe yana cewa"Wucewa za ki yi mu je mu kwanta, ai tun da kin hana ni fita dole ki rage mini daren".
Nan take fara'arta ta ɗauke, ta ce"Ni fa tun rana nake jin kasala da ciwon kai, kitso ma yau mutum ɗaya na yi wa".
Ya taɓe baki ya ce"Ai wallahi ko karkarwar zazzaɓi kike sai kin wuce mun tafi ɗaki, ai tun da kika kafa mini doka na yi miki sam'u wa ɗa'a ni ma dole ki bi tawa doka, ni wannan dokar ma ai gana ta kai ni gobarar Titi a Jos, babu zancen cewa kin fara bacci, idan da rabo ma sai ki ga cikin satin nan Allah Ya kawo mana babban rabo, kya samu ɗan tayin fira nan da wata tara ko?"
Ko kallonsa ba ta yi ba, ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, fargaba duk ta addabe ta, sai ta ji da ta sani ma ta bar shi da Hamzan, haka dai ta miƙa kai kamar ta yi kuka don takaici.
Kwana uku suna yin haka, Maryam gabaɗaya dauriyarta ta ƙare, saboda haka ta fara ƙaryar rashin lafiya, kafin ya dawo sai ta shige bargo ta ce zazzaɓi take yi. Ana haka ne kuma Hajiya ta dame shi da kira kan ya kamata ya zo ko awa ɗaya ne, to shi ma ya yi kewarta, kawai yana dannewa ne ganin yanzu yana yi wa Maryam fin ƙarfi, to da ya ga ta narke da zazzaɓin da ya san na ƙarya ne sai ya ƙyale ta, ya yanke shawarar zai je gidan Hajiyar yau.
Yana idar da sallar magriba ya kira Hajiya ya faɗa mata ga shi nan zuwa, ya kama hanya ya tafi, yau ma da kanta ta shigar da shi, kafin su ƙarasa ɗaki yake ƙara kallon gidan, ya ce"Hajiya wai duk girman gidan nan babu mai gadi ne?"
Ta ce"Akwai mai gadi, aikensa nake yi idan zan yi baƙo".
Ya ce"Kenan dai Hajiya akwai wasu baƙin bayan ni".
Ta ruƙo hannunsa a lokacin da suke ƙarasawa ta ce"Wallahi tun ranar da ka fara zuwa har yau na kasa sake kula wani, kai na musamman ne Aliyyu, ni fa da za ka dawo gidan nan da zama gabaɗaya wallahi zan so haka, kana ɗaki kawai a cikin AC, ka zaɓi abin da za a dafa maka ka ci ka kwanta, sannan kullum dubu goma".
Ya yi ƴar dariya ya ce"Kin ga kuwa da har ƙiba fa sai na yi".
Hajiya ta ce"A to! Ka dai duba wannan damar".
Ya sosa kai ya ce"Ai Hajiya matata nake tunani, kin san fa amarya ce ko haihuwar fari ba ta yi ba, kuma wallahi tsaye take a kaina, tana lura da duk wani motsina, shi yasa amma da ni ma zan so hakan wallahi".
Hajiya ta ce"To kai kuwa Aliyyu ya aka yi ka yi sake matarka take juya ka har haka? To me zai hana ka ce mata ka samu aiki a wani garin, sai ka zo mu yi zamanmu, duk kwana biyu ka dinga tura mata kuɗi ka kashe bakinta, ko ba zai yiwu ba?"
Aliyyu ya ce"Kuma fa kin kawo shawara Hajiya, zan yi tunani, ke zai yiwu ma in sha Allah!".
Ta ce"Ko kai fa, na gode, sosai nake sonka Aliyyu, ji nake kamar na kashe auren nan na aureka wallahi".
Ya yi murmushi ya ce"Habawa Hajiya wane kare da ɗaukar gara? Wani kayan ai sai amale".
Daga haka ta kawo masa abinci ya ci, ya yi wanka, ya fara abin da ya kawo shi, ƙarfe tara ya baro gidan, yana ta sauri saboda Maryam, a hanya ya tsaya ya kira ta, tana ɗagawa ya ce"Maryam ki yi haƙuri ga ni nan zuwa".
Ba ta ce komai ba ta kashe, sai da ya tsaya a hanya ya siya mata kwakwa da dabino sannan ya ƙarasa gidan. Yana zuwa ya ganta fuskar nan kicin-kicin.
Ya yi murmushi ya ce"Hajiya Maryam kenan, uwargidana amaryata, sarautar mata daga ke babu ƙari..."
Ta ɗaga masa hannu ta ce"Don Allah dakata, ya isa haka, na san dai duk siyan baki ne kake yi, babu komai Ali duk yadda ka tsara rayuwarka ka je ka yi ta yi, ni dai Allah Ya sani na yi iya ƙoƙarina don na ga na kula da kai, tun da kana ganin kamar takura ne shi kenan, ka je ka yi".
Ya zauna, ya janyo ta jikinsa, yana cewa"Haba Love, wallahi ba takura ba ne ba, na sani ƙauna ce, kuma ina jin daɗin yadda kike kulawa da ni ɗin wallahi, yanayin aiki ne kawai, ga kwakwa na kawo miki, na san za ta wanke laifina ai ko?"
A zahiri shi take kallo, amma sam ba ta gane inda maganganunsa suka dosa, ta yi nisa a duniyar tunanin da zuciyarta ta ɗarsa mata, dalilin kusancin da suka samu, sakamakon zamanta a cinyarsa, wani kalar ƙamshi ta ji na wata shegiyar humra mai daɗin ƙamshi, kuma ta san Ali idan zai fita da safen nan ba ya wani fesa turare ma, ko ma yau ya fesa ai ba su da irin wannan turaren, kuma ma fa wannan humra ce, kamar ta yi masa magana, sai ta bar shi a kan za ta yi bincike kafin ta tuhume shi.
GIDAN SADIQ
Rayuwar gidan Sadiq ta samu ci gaba a nasu ganin shi da Yusra, yanzu hankalinta ya kwanta sosai, tsakaninta da Kursum sai godiya da fatan alkhairi, idan tana aikin kwana ko fargabar ta bar mijinta da wata a gida ba ta yi, domin ta yarda da su, su biyun, yayinda Kursum matakan da ta tanada don shayar da Yusra maɗaci suke ta tafiya hawa-hawa.
A yanzu dai ta riga da ta gama da Sadiq da yaransa wajen girki, ya yarda a kan Kursum ta fi Yusra iya girki, don sosai Sumayya ta kashe kuɗin wurin siya mata kayan ɗanɗanon girki, wanda Yusra duk ba ta san wainar da ake toyawa ba, duk da ƴaƴanta sun sha faɗa mata girkin Anti Kursum yana da daɗi sosai, ita ba ta kawo komai ba, tun da ba ta ji wani bambanci da nata ba. Abu ɗaya ta sani Kursum tana taimakonta.
A ɓangaren Sadiq tsakaninsa da Kursum babu yabo, babu fallasa, kullum za su gaisa tana murmushin da ya gane ɗabi'arta ne, sai dai yadda ba ta gajiya da kwalliya abun yana burge shi, saboda shi mutum ne mai son kwalliya sosai, duk da bai taɓa faɗawa Yusra ba tun da ya lura ita ba ta da ra'ayin wannan zane-zanen, sai kuma tsafta da take da ita sosai abun yake burge shi, uwa-uba kuma yadda take kula masa da ƴaƴa, abun sha'awa, sun shaƙu da yaran sosai ba su da zance sai na Anti Kursum ɗinsu, saboda haka shi ma yanzu aikin Yusra ba sosai yake damun shi ba.
Sai dai wani baƙon lamari da yake faruwa da shi, wanda tun yana damunsa yanzu ya zame masa jiki, ta wani ɓangaren ma abun ɗebe kewa ne a gare shi.
Wata yarinya ce take turo masa massages kala-kala, na kulawa, tun yana sharewa har ta kai ya fara mayar da hankalinsa a kan saƙonninta, duk ranar da ba ta turo ba sai ya yi ta tunanin dalili,